Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

GIMBIYA BALARABA Kauna, Iko, da Yaudara by Bintubatula

Author :  Bintubatula Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 19.4K words

uban kwalliya ta k'ananun kaya wanda suka d'ame ta,, b'ata fuska yayi lokacin da yayi arba da ita, kusa dashi ta zauna tana gaishe shi cikin wani irin salo,, a dakile ya amsa, yace"Wannan wane irin iskanci ne zaki futo da wannan kayan na jikin ki"? Azima ta sunkuyar da kai tana fad'in 'Yallab'ai me ye laifin su" A fusace! Yace"Ba duguwar magana na nema ba,, magana ta farko ta k'arshe kar ki sake futowa da irin wannan kayan in zaki saka kayan ki ki saka Ke ka dai a daki ba sai kin nunawa jama'a ba, gida cike da mutane ki futo min da wannan shashancin" Ganin ransa ya b'aci yasa ta fara bashi hakuri , ko sauraron ta baiyi ba ya mike ya nufi gurin cin abunci ransa in yayi dubu ya baci"! Balaraba kuwa taji dadin abunda yayi wa Azima ta lura tayi shigar ne Dan Taja hankalin sa, a randa ba girkin ta ba, dariya kawai take mata Cikin zuciyarta tace"Wallahi wani lokacin mutumin nan na burge ni da halinsa baudadden mutum ne!


Gyaran murya yayi Balaraba ta mike da sauri kar ta samu rabon ta,, Azima ma ta mike jiki a sanyaye,zama tayi, daya daga cikin kujera ita kuma ta fara zubawa kowa nashi cikin nutsuwa, Halisa tayi sallama ta shigo,,, itama ansha kwalliya kamar masu zuwa gasar fidda kyau!! Gwara ita material ne, a jikinta dinkin riga da sket kusan irin na Balaraba kala ce kawai ta banbanta,, gaishe shi tayi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba,, sama-sama suka gaisa da junansu ko wacce na danne Kishi a zuciyarta. Balaraba ta zubawa kowa nashi ta zauna ta fara cin nata cikin nutsuwa.

Sarki! Yaji dad'in girkin Balaraba sosai ya bude ciki ya ci ya k'oshi ya yagi tissue ya goge bakin sa,, da kuzari a jikinsa ya mike daga gurin, falo ya koma ya zauna,, to suma dai su Halisa sunji dadin girkin shiyasa babu wacce tayi k'orafi suka cinye plate din tass ko wacce ta tashi tana goge bakinta,, Balaraba ta gyara gurin tsaff!! Ta isa in da suke,, k'asa-k'asa yake kallon ta ganin tana k'okarin futa,, yace"Ina zakiji kuma? Duk gashi muna zaune da juna" A takure take jin jikinta kasan cewar tana cikin halin rashin tsarki,, wannan motsa jikinta da tayi Duk pad din ta ta jik'e haka take a rana sai ta sanya sau biyar,, tace"Yanzu zan dawo zan Dan watsa ruwa ne"" Nan ma akwai toilet kin shigo kenan ki dawo ki zauna" wannan halin nasa yana bata haushi wallahi, to in ta dawo ta zauna yana da pad din da zai bata oho masa,,, zama tayi kujerar dake daf da bakin kofa ranta a bace, duk ya lura da yanayin da take ciki,, Azima sai watsa mata d'an iskan kallo take,, Ita ko Halisa sai hira take masa yana biye mata,, goma shaura, sukayi masa sallama ko wacce ta wuce part d'inta, falon yayi shiru da shi sai ita mik'ewa yayi ya nufo inda take zaune,, Balaraba ta sunkuyar da kanta tana jiran taga me zaiyi,, kulle k'ofar yayi ya cire key din,,, ta kalle shi bakin ta na rawa tace"imm... Ina da Uziri a gurina fa,, yanzu zan futane in je in dawo naga kuma ka kulle kofar" Tsayuwa yayi a kanta yayi mata rumfa! Cikin wani irin voice yace"Me zaki je kiyi? Uhumm kin ce wanka nan babu toilet ne"? Girgiza kai tayi yace"To kin gani, tashi muje ki gyara min shimfid'a ta"" ta d'ago dararan daran idonta tana kallonsa,, lallai akwai rigima kenan mutuk'ar ya san halin da take ciki, yaya za'ayi ta fada masa,,, hannunta ya kama ya mikar da ita tsaye,, zura hannusa yayi ya rungumo k'ugunta suka fara tafiya, a haka suka dunga hawa mattatakala duk rabin jikinsa na jikinta,, lokaci guda ya soma neman nutsuwar sa,,, zama tayi gefen gado ya shiga toilet ya futo daure da alwala yace"Ki shiga kiyi wankan sai ki dauro alwala kizo muyi nafila" babu musu ta mike ta shiga toilet din,, Wanka tayi sosai,, ta sanya towol ta goge jikinta ta maida kayan jikin ta,, tana futowa taga ya shimfid'a dadduma yana tsaye yana jiran ta,, hijab ya mik'a mata, ta karb'a amma bata sanya ba,, ik'ama yake so ya tayar ya kalle ta yana fad'in"Ki sanya mana" A nutse tace"Bani da tsark" Yaji wani irin fad'uwar gaba, amma dake Namijin duniya ne,, sai ya maze Dan kar ta gane,, yayi minti biyu yana nazarin ta daga bisani ya tada sallahar shi,, zama tayi gefan gado jikinta a sanyaye , Ya dade kan dadduma yana addu'a har ta fara gyangyad'i,, ya mike a nutse ya kashe wutan dakin,, bed din ya nufa Balaraba tayi tsuro tana kallon inuwar sa,, sai da yw zauna sannan ya cire jallabiyar da take jikinsa,, babu zato taji ya jawo ta jikinsa, gabanta ya dunga fad'uwa duf!!duf!! Zif din yake k'okarin zugewa tayi saurin dafe hannusa,, kansa ya zura tsakanin wuyanta yana sakin ajiyar zuciya daki-daki,, k'okarin hanashi take, amma sai da yayi nasarar zuge mata zuf din ya cire rigar ya jefar kwantar da ita yayi k'asan shi yayi mata rumfa, Balaraba sai motsi take da bakinta taka cewa komai duk inda ya kai hannunsa sai ta kai nata duk a k'okarin ta na hana shi abunda yakeyi ya ta kasa,, sai ma jikinta da yayi la'asar sakamakon uban soyayyan da yake zuba mata,, Balaraba taji kamar ba a duniya take ba,, ta shagala Wanda ba san ma yayi nasarar cire mata brziyya ba,, aikuwa ta gigice amma yanai mata wani salo tuni ta bada kai bori ya hau suka hau soyayyar su irin ta ma'aurata,, Sarki! Ya sha mutukar wahala lafin ya samu nutsuwa,, Balaraba kam jin ta take a sama, ta manta a wace duniyar take, ita dashi sai sauke nuffashi suke,,,,, wani irin kullewa mararsa take,, shi kansa yasan ba duka ya zubar da abun ba, yanzu shine damuwar sa, zai iya shiga mugun hali, mutukar bai samu yayi sex ba, domin shine katt! Shine za samu sukuni,, a galabaice ya kira sunanta, ta amsa murya na rawa yace"Ki yarje min na je gurin "yar Uwar ki na biya buk'ata ta, ina Cikin wani hali" Sosai ta tausaya masa,, cikin raunin murya tace"Babu damuwa, ai dama amfaninmu kenan, na yarje maka kaje kawai" mik'ewa yayi yana zura jallabiyar sa,, Albarka kawai yake sa mata,,, sauka yayi daga bed din ya d'auki key zai futa, ta kira sunansa juyo wa yayi yace"Menene uhumm? Kiyi hakuri Yanzu zan dawo"' shiru tayi haka kawai taji kwallah na k'okarin zubo mata,, ya fuce da sauri,, Azima tafi Halisa dauriya, saboda haka shashen ta ya nufa Cikin duhun dare, dam ma akwai hasken futulu a wasu guraran,, Azima na zaune a gefen gado ta zabga uban tagumi sai tunani take kana kallonta kasan akwai abunda yake damunta,, taji ana bugu tana k'okarin tashi taji karar wayarta,, tana dubawa taga Sarki! Ne hannu na rawa ta d'auka, yace"Bude min kofa" jiki na rawa ta je ta bud'e masa ya shigo ta mayar da kofar ta rufe,, kai tsaye bed din ta ya nufa,, ta bishi a baya,, tana shiga ta ganshi yana k'okarin cire Riga, tace"Lafiya Yallab'ai "? Kwanciya yayi bed din ta yace" Zo" Azima ta gane me ke da akwai,, zuciyar tace mata Allah ya kawo miki shi har dakin ki,, da sauri ta nufi friji ta d'auko Lemo mai sanyi ta k'araso kusa dashi,, tace"Yallab'ai tashi ka fara shan Lemo nasan ranka a b'ace yake"" sama-sama yake jinta ya mike ya karb'i lemon dake hannuta ta bud'e masa ya shanye Tass! Ta karb'i robar ta aje,, kashe futular tayi ta rungume shi,,, cikin mawuyacin hali ya biya ma kanshi buk'ata,, yana gamawa yaji wata irin muguwar kasala ta rufe shi,, da k'yar ya koma part d'insa, Balaraba na zaune ta rafka tagumi jiran dawowar sa kawai take, ya shigo ta bishi da kallo ya shigowa ya kwanta babu abunda yace mata,, kusa dashi taje ta kwanta gabanta na fad'uwa,,, da k'yar bacci ya dauketa mai cike da mafarkai! Asubah ya farka tare!dashi, ya d'aga kafa zai sauka k'afar tak'i d'aguwa yayi-yayi taki motsi sai wani yammmmmmmmm!!! Take masa.
[9/26, 8:47 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*




```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*



_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________


_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_




*🅿109*






Kalmar Innalillahi wa'ina ilahi raji'un itace ta futo daga bakin sa, yunk'urin d'aga k'afar ya kuma yi a karo na uku, tak'i motsawa,, hannu yasa ya d'agota yaji wani Yammmmmmmm! Mara dad'i Dole tasa yayi saurin aje ta saboda ji yayi abun har tsakiyar kansa,,, zufa duk ta jik'a masa jiki kamar babu sanyi asubah,, salatin da yake ne,, ya farkar da Balaraba ta mike a zabure itama bakin ta na fad'ar kalmar Innalillahi wa'ina ilahi raji'un, saboda wani irin mumman mafarki da tayi,, hannuta ya Kamo ya rik'e tamm!! Suka tsurawa juna ido,,, gumi taga goshin sa nayi,, yana ta cije baki!! Bakinta na rawa tace"Yallab'ai baka da lafiya ne"? Da k'yar ya gyda mata kansa, yace"K'afata ta rike min" gabanta ya fad'in,, cikin zuciyarta tace"Kar dai mafarkina ya zama gaskiya,, hannu takai kafar tana shafawa idanunta har sun soma zubar da ruwan hawaye,, a hankali yace" cire hannun ki babu dad'i" da sauri ta cire hannun nata tana kallonsa,, cikin dauriya yace"Yaya za'ayi nayi sallah" tace" Ko in kama ka mik'e"? Gyad'a kai yayi yana murmushi me ciwo yace"Baza ki iya ba,, mik'omin waya ta""" sauka tayi da sauri ta d'auko wayar ta mik'a masa,,, numbar Shatima ya kira,,,, ya fada masa halin da yake ciki,, cikin tashin hankali Shatima ya futo daga gida,, kai tsaye gidan sarautar ya nufa lokacin har an idar da sallahr asubah,, Balabara na durkushe a gabansa jikinta sanye da hijab,, ba ta cire ba,, Shatima yayi sallama ya shigo,, zama yayi yana duba k'afar,, cike da alhini yace"Kurum wayar gari kayi kaji k'afar taki ta kuwa"? Sarki! Ta girgiza kai shi kadai yasan ciwon da yake ji yace"Da sauk'i ai idan kin takuwa tayi,, taki motsi fa" Shatima ya Dora hannunsa k'afar yana salati,, wayarsa ya Ciro yana kiran dector dake duba Sarki!! Yace"yazo yanzu yanzu,,, "Kamani in mik'e in kama ruwa sai in d'aura alwala inyi sallah". Shatima ya mike yana kici-kici ya samu ya mik'e inda Allah ya rufa asiri ma k'afa d'aya ta taku itama da k'yar da dafa bango suka je toilet yayi uzirin sa, kana ya dauro alwala suka futo,, dadduma ta shimfuda masa,,, cikin zuciyarta sai tasbihi take Allah ya gajar ta musu wahala
[9/26, 8:42 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: Da Jan k'afa suka k'araso gurin yayi nufin ya tsaya abun ya gagara,, sai ya zauna a nutse yayi sallahr sa,, duk suna tsaye suna kallonsa Balaraba sai goge hawaye take,, Shatima ko ya kira numbar Shahid yafi Sau a kirga bai d'auka mybe baya kusa,, dector ya shigo da kayan aiki,, cikin girmamawa ya gaida shi ya amsa a nutse ya fara yi masa tambayoyi,, Sarki! Ya fada masa duk abunda ya faru,,, A hankali ya kama k'afar yana dubawa,, lafiya Lou da ita a ido,, matsata yayi sarki! Ya cije baki!! Yace"Kar ka k'ara matsawa,, dector ya cire hannunsa da sauri yana neman afuwa,, yace"Yallab'ai ina ganin dole zamuje hospital dakai domin mu auna k'afar dole kuma a d'auke hoton ta, domin sanin maganin da ya dace da ita" Gyad'a kai kurum yayi,, Shatima yace" Bari insanar da Mama Halin da ake ciki,, babu Wanda yace masa komai,, yana sauka k'asa suka ci karo da Halisa ta shigo,, da fara'a ta tsaya suna gaisawa da alama batasan abunda yake faruwa ba,, Shatima ya wuce bai fada mata ba,, kai tsaye sama ta nufa cikin k'asaita! Tana shiga taga Balaraba durk'ushe gaban shi tana kuka, ga dector a tsaye a gefe yayi shiru fuskar sa ta kalla taga alamun alhini ta k'arasa da sauri kusa dashi,, cikin kid'ima tace"Hubby menene wai naga duk kuna cikin damuwa!" Kallon ta yayi zuciyarsa a dake!! Yace"Babu komai ke me kika gani" ? Baki na rawa tace"Tashin hankali na gani"" d'auke kansa yayi baice mata komai,, Balaraba ta kalla tace"Menene "? Kafar sa ta nuna mata, tana kuka! Halisa ta kalli k'afar da sauri,, taga ta Dan kumbura" jiki a sanyaye tace"Ciwo take masa"? Balaraba ta girgiza kai tana fad'in "Idan ciwo ne da sauk'i yau tunda ya tashi ya kasa tafiya da ita tak'i motsi d'azu da k'yar aka kai shi toilet yayi alwala " Halisa tace"Innalillahi wa ina ilahi raji'un kuka ta fashe dashi tana k'unshe baki tace"Wannan wace irin masifa CE"???? Tsawa!! Ya daka mata yana fad'in"Bana son shashanci da koke -koke addu'a zakuyi min""""" a gigice ! Ta mike tana fad'in"Au! Da gaske ne Ashe? Sai ta kalli Balaraba Cikin daga murya tace"Ke nake zargi! Munafuka meye ribar ki anan, me yasa ranar da ya kwanta damu haka bata faru ba,, me kike nufi, bak'ar algumguma wato kina so ki kashe ki samu tumunin takaba"? Taji kamar ta watsa mata ruwan zafi,, a jiki ta dago jajayen idonta da suka rine!! Bakin ta na rawa tace"Mey...... Ka tsaye ta yayi ta hanyar daga mata hannu sai tayi shiru gami da toshe bakinta da gefen hijab dinta tana k'okarin b'oye kukan da yake k'okarin kufce mata a karo Mara adadi,,,, Halisa yake kallo cikin tsantsar b'acin rai da takaici.
[9/27, 4:53 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*




```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*



_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________


_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_




_ALHERIN ALLAH YA ZO INDA KIKE_

*NANA AISHATU KADUNA*

_Hak'ika inajin dadin comment dinki ubangiji Allah ya kara kauna da aminci nagode sosai ina miki fatan alkairi a rayuwar ki🥰_



_*Kuyi hakuri yau pege din babu yawa zazzab'i ne ke damuna wallahi Ku sanya ni cikin addu'ar Ku*_






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_




*🅿110*




Suna had'a ido dashi ta kara rikicewa tana fad'in"Wallahi Hubby kar ka yarda da ita,, itace Silar faruwan wannan al'amari ko mara kunne ne yaji wannan abun yasan da akwai lauje cikin nadi,, shiyasa hausawa suke cewa idan takalan mutum mugun ice ne, idan ya samu guri yafi mai kudi iko,wallahi yanzu na daina ganin laifin masu kud'in da suke gudun talaka domin halin su ne ya ja mus............."Halisaaaa!!! Rufe min bakin ki anan gurin"" ya katse ta cikin wata muguwar tsawa"" gum! Tayi da bakin ta tana shashshekar kuka,, Balaraba na durkushe a gurin kai a kasa tana zurarar da hawayen bakin ciki,, murya a cunkushe! Yace"Duk futa bana son ganin Ku" da sauri dector ya futa Halisa ta futa simi-simi,, mik'ewa tayi kwata-kwata jikinta babu lak'a, suka had'a ido saurin d'auke kansa yayi ransa a bace kalaman Halisa ba k'aramin kona masa rai sukayi ba,, wuce tayi tana waigen sa, duk yana kallonta,,, tana futa ya sauke ajiyar zuciya me zafi.


Tana sauka taga Halisa da Azima suna maganganu k'asa-k'asa suna ganinta suka hau rafka mata harara, d'auke kanta kawai tayi,, Mama ce ta shigo bayanta Jakadiya da Shatima Shahid da Madabo cikin tashin hankali ta nufi sama suka rufa mata baya,, kansa a kasa yaji shigowar su,murya Maman shi yaji a kansa, ya d'ago idonsa,, da sauri ta tsuguna kusa dashi tana masa magana,, cikin nutsuwa ya warware mata duk abunda ya faru,, cikin tawakkali tace"Allah yana ji yana kallo ko wane hali da kake ciki abunda za za'ayi yanzu muje hospital din ayi hoton kamar yadda dector ya fada insha Allahu komai mai sauk'i ne" A nutse ta ce da dector "Je ka d'auko while chair,, a d'auke shi,, da sauri ya futa, shiru dakin babu Wanda yayi magana har dector ya dawo su Shahid ne suka kama shi suka Dora shi kai, a hankali suka dunga sauka dashi, daga kafar bene, Mama na bayansu tans goge hawaye a fakaice.

Balaraba ta mike da sauri ta tsaya har suka k'araso gurin,, kallonta yayi yaga duk ta tayar da hankalin ta, ta bashi tausayi wannan alama ce da ta nuna tana cikin damuwa kuma ta damu dashi sosai,, babu yabo babu fallasa yace da ita"Wannan kukan da kike ya isa haka, cuta fa ba mutuwa bace, shikkenan ni Allah bazai jarrabe ni, ba Wannan ba yana nufin shikkenan bazan kara taka k'afafu na ba, insha Allahu inaji ajikina wannan abun na lokaci kankani ne saboda haka Wannan koke-koken da kukeyi ya Isa haka" Balaraba tayi shiru tana gyad'a kai, Azima kuwa ai batayi shiru ba sai cewa tayi "Duk ba anan take ba Yallab'ai dole muyi kuka Hak'ika an zalince ka kuma bazamu bari ba,, wallahi ka gurgunce sai mun d'auki mummanan mataki akanta " duk jama'ar gurin suka bita da kallo cikin mamaki,,,!! Mama tace "Ku muje mu wannan tsayuwar bata da amfani,, Azima da Halisa suka rufa musu baya, Balaraba aka bari a baya tana tafiya salau-salau babu kuzari ko na kwabo a jikinta.


Buba direba ya bud'e bayan mota suka d'auke shi suka saka ciki da gyara masa zama sosai sannan kowa ya shiga ya zauna,, ganin Matan nasa na k'okarin shiga ne ya dakatar da Buba,, kallonsu yayi cikin bada umarni yace " Ko wacce ta koma gurin ta""" umarni ya bawa Buba ya tada mota suka futa,, dake safiya CE, babu jama'a sosai a harabar gurin sai dai-dai Ku, motar na fucewa suka yo kan Balaraba da bala'i kowa na fad'in albarkacin bakinta,, Balaraba lalurar mijinta itace a gabanta

2 / 7