Author : Bintubatula Category : African Stories & Novels
[9/23, 12:35 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
```MARUBUCIYAR```
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*
_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________
_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_
*NA GAISHE KU*
💝💝💝💝💝💝💝
```AISHA SHAKA```
```AISHA IBARAHIM```
```ASIYA KEBBI```
```AUNTY BABY```
```FARIDA SK```
```DOTANA MAHILLAH KDN```
```MAMAN HANIF```
```MAMAN KHAUSAR```
```MAMAN SUHAIMAT```
```MAMA QUIN```
```MUM BASMA```
```NAFISA IBRAHIM```
```NANA AYSHA KDN```
```NAFISA AHAMAD```
```PREETY```
```IBNAT BARHAM```
```SEEMA ATIKU```
```ZAHRA```
```MAMAN UMMYTA```
```CIMA KADI```
```SHAFCYN SAFNY```
```HAFSAT USUMAN```
*KUNA DA YAWA YASIN, WANDA BAI JI SUNAN SA, YAYI HAKURI GURIN COMMENT YASA NAKE GANE WANDA YAKE BIBIYAR LITTAFIN, NAGODE K'WARAI DA GASKE*
*🅿106*
Part hud'u ne a shashen nasa guda biyu a jere, biyu na kallon juna, gurin zaman mutum hudu. kenan, dama tuntuni Mama tasa an gyarawa Balaraba wanda yake kusa da nasa sauran biyun kuma Halisa da Azima,, ko wacce danginta sun kashe mata kudi sosai duk da da akwai wani abubuwan da suka tarar a ciki,, ko wacce tana tare da bayin ta kasancewar su "yayan mulki, Mama ta had'a Balaraba da bayi mata gudu biyu ko sa dunga d'ebe mata kewa Balaraba babu yadda zatayi ne , amma da don ita ne, bata bukatar wasu bayi,, dakanta ta rako ta har d'akinta,, tana k'ara yi mata nasiha.
To su Shahid suka gama barkwancin su suka d'ebi matansu suka tafi,, suka barshi shi kadai a falo yana sak'e-sak'e daga bisani ya mike ya haura sama domin ya watsa ruwa.
Gimbiya Halisa bayan " yan rakiyar ta sun tafi sai ta mike ta shiga toilet ta sake sabon wanka da turaririka masu kamshi ta futo ta goge jikinta sosai ta mulka turaran fata ta d'auko wasu kayan bacci masu dogon wando ta sanya a jikinta ta d'auki hula ta sanya, hijab din da take sallah ta zura ta kulle shashen ta, kai tsaye nasa ta nufa.
Yana sama lokacin da ta shiga falon tsitt bakajin komai sai sautin Ac, sama ta hau gabanta na fad'uwa wai ango na kai kansa ga amarya yau ita ya kawo kanta.
Yana zaune kan kujerar miroow yana gyara sumar shi tayi sallama ta shiga,, amsa mata yayi yana daure igiyar rigar baccin sa,, zama tayi gefan gado Kamar munafuka, ya kalle ta tw cikin madubi yana b'oye dariya yace "Kin gama fushin kin zo"
Sakin fuska tayi tana wani fari da ido, ya d'auke kansa yana girgiza kai ya cigaba da taje sumar sa, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta kalle shi,, wani irin shauki yana tsirga mata, mik'ewa tayi yace"Je ki dauro Alwala muyi nafila ta godiya ga Allah". Gyara zama tayi tace"Da Alwala ta" "Babu laifi sai ki tashi muyi" mik'ewa tayi ta gyara shimfidar dadduma suka tada sallama, ya jima sosai yana addu'a kamar yarda addini ya tana ya shafa itama ta shafa, mik'ewa yayi ya kashe futular dakin domin wani sa'in baya son haske mussaman in zai kwanta ya zauna gefan gado yana Dan kallonta babu yabo babu fallasa yace"Kinci abunci" daga kai tayi yace"To zo ki kwanta,, Halisa ta mike tare da cire hijab din ta ta haye kusa dashi tana nanak'ar shi,, shiru yayi yana shakar kamshi ta, mutsu-mutsu ta dunga yi , ya jawo ta jikinsa ya rungume yana sauke ajiyar zuciya, to takaice dai anan labari ya sauya suka shiga soyayya.
Halisa ta gurzu gurin Yallab'ai wanda tazo tana da ta sani jikinta duk ya shika Sai nishi,take to itama dai Kamar Azima ne bata fuskanci Komai sai bak'ar azaba.
Babu laifi ya samu nutsuwa da ita,, amma dai duk da haka yana jin zai iya k'arawa tausaya mata kawai yayi ya rabu da ita,, abunka da mara jiki kafun Safiya ta kara zabgewa, da kanta taje gasa jikinta da ruwan zafi ta futo daure da alwala lokacin ya shirya tsaf yana k'okarin sauka kasa, ba tare da,ya kalle ta ba yace"In kin gama ki sakko k'asa"
Kallo ta bishi dashi wato ita bazai tsaya ya riketa ba kamar yadda ya rike Azima aikwa bazata sauka ba,,
Ma'aikatan sa ne suke aikin gyara gurin an gyara komai yadda ya dace, abun kari ma na kan daining gwanin sha'awa, yana saukowa suka dunga kwasar gaisuwa yana amsa musu Cikin nutsuwa suka futa,, minti goma tsakani Azima ta shigo cikin Uwar kwalliya sai baza k'amshin take ga gwal ko ta Ina, kusa dashi tazo ta zaune tana masa k'yataccan murmushi,, tace"Yallab'ai barka da Safiya fatan ka tashi lafiya"? Kwalliyar tata tayi masa kyau ya juyo yana kallonta fuska a sake yace"Lafiya Lou na tashi, kefa"? Tayi wani fari da ido tace"Ni ma haka" hannunsa ta rike tana wasa da zoban dake hannunsa, Cikin dubara tana cirowa tana mayar wa cikin wani irin salo"" sosai abun yake tab'ashi ,tsigar jikinsa ta hau tashi,, Sarki! Mutum ne mai Lafiya da kuzari ko Yaya yaji mace a kusa dashi sai yanayin jikinsa ya sauya, ya rik'e hannunta yana murzawa kad'an-kad'an, Azima ta samu abunda take so,, sai tw hau zuba masa hirara cikin sigar Jan hankali.
Cikin nutsuwa tayi sallama ta shigo,, duk su biyun suka daga kai suna kallonta, k'asan mak'oshi ya amsa,, yana d'auka kansa kamar Wanda bai ji dadin ganinta ba,, itama d'auke kanta tayi har ta k'arasa in da suke, ta zauna kujerar dake kallonsu, fuskarta a sake, tamkar bata ga abunda suke ba, tace"Barkanku da Safiya Yallab'ai fatan ka tashi lafiya"?
Ido da ido suke kallon juna ita dashi, itace ta fara kauda kanta,, ya amsa da "Lafiya nake kefa"?
" Nima Lafiya lau na tashi"
"To masha Allah"
Cikin kissa Azima tace"Yar uwa ya kike"?
Balaraba ta saki fuska tace"Ina lafiya lau" daga haka taja bakin ta tayi shiru, Azima ta cigaba da yi masa surutu shiko hankalinsa na kan Balaraba, gyaran murya yayi yace"Jimana" Balaraba har tasaba da wannan sunan, idonta ta d'ago tana kallonsa, baza ka tab'a tantance abunda yake zuciyarta ba.
Cikin bada Umarni yace"Ki hau sama ki kira Halisa" Kallonsa tayi cikin mamaki, shima ita yake kallo,, zuciyarta tace "Kibi umarninsa ki dakewa zuciyar ki" mik'ewa tayi a nutse ta fara tafiya, ya bita da wani mayan kallo, dama abunda yake so kenan yaga kwalliyar ta,, tana sanye da atamfa "yar ingila dinkin Riga da zani ne simple sai dai rigar " yar k'arama ce,sosai iya kacinta cikinta bata rufe mata mazaunai ba,, tayi amfani da siririn mayafi tayi rolling din kanta dashi,, sannu-sannu take taka k'afar bene jikinta na motsawa as'usuel,, tanayi bada wata manufa sai dai hakan da ya zama nutural d'inta ta shige dakin" daga tashin ta har shiga dakin a kan idonsa ya dunga mik'a wuya yana lek'en ta sam ya manta da wata Azima dake zaune a kusa dashi,, ajiyar zuciya ya sauke ya dawo hayyacin sa,, Azima ta muzanta sosai ganin yadda kamaninsa suka sauya sosai jikinta yayi sanyi tarasa wace irin masifa ce wannan, ta lura fa mutumin nan ya kwallafa rai akan Balaraba ko dame ta fisu oho,
Suna had'a ido dashi ya b'ata fuska gami da waskewa yana kallon agogon hannunsa kamar Wanda zashi wani guri, ya mike ya nufi daining cikin k'asaita, bayansa tabi jiki a sanyaye.
Tare suka sauko Halisa sai ya mutse fuska take,, kai tsaye daining din suka nufa,,,, kallonta yayi yace"Ke da nace ki sauko k'asa shine kika zauna". Karyar da kai tayi tana fad'in"Jiri nake ji shine na koma na kwanta shiru tayi kawai yana kallon Balaraba da ido yayi mata magana wai ta had'a musu abunci, ta gane Abunda yake nufi sai ta share shi zuciyarta na zugata kar tayi wato Dan yaga ita ba "yar sarauta bace shine yake sanya ta Aiki.. " Nace ki had'amin abunci gimbiya" Abunda ya furta kenan ya waske tamkar bashi ba,, Dan kar ta bashi kunya yasa ta fara had'a musu abuncin cikin nutsuwa tana addu'ar Allah yasa kar ya k'ara tsuro mata da wata futinar.
*INA LABARIN WAZIRI DA TSITO KULU ME D'AKIN KUDU*
MUJE ZUWA.
[9/24, 5:59 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
```MARUBUCIYAR```
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*
_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________
_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_
*🅿106*
Hannuwan ta ya zubawa ido kurr!! Sun sha uban Jan lalle wanda yayi jajazur har ya fara yin b'aki, sosai abun ya burge shi kuma ya bashi sha'awa,, nata duk ya fi tafiya da imaninsa, nasu Halisa bak'i ne, irin wanda ake zanawa shima yayi kyau babu laifi, kowa da kalar nashi,Cikin nutsuwa ta had'a plate uku kowa da nashi,, ta mik'a masa nashi tana fad'in "Bisimillah" Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido yace"Ke ina naki plate d'in, kin had'awa kowa nashi" babu yabo babu fallasa tace"Na ci abunci kafin na futo,, kai tsaye yace"Ko kinci dole kici na nan, ka'ida tace, wannan" Cikin mamaki ta kalle shi, ganin yanda ya b'ata fuska yasa ta fara zuba abuncin domin bata son ayi ta Jan magana,,Shiru gurin yayi, sai motsin cokola, satar kallonsa take yanda yake cin abunci kamar baya so,, ita kanta taunar sa ma abun kallo ne, Halisa kanta ya k'ara girma ganin yanda yake kula da ita domin shine ma ya tsiyaya mata ruwa,, ya mik'a mata lokacin da ta k'ware ganin, yana sanya Balaraba aiki yasa suka kara mike kafa suna ganin sun fita daraja a gurin shi kuma yasan su dama basu saba da aikin wahala ba,, shine ya fara mik'ewa daga gurin,, ganin ya tashi yasa ta mike da sauri ta gudu part d'inta... To Azima ma da ta kammala mik'ewa tayi ta wuce part din ta, aka bar Halisa tunda itace take da miji a hannu jiya da yau.
********************
********************
Tsito da Waziri ne zaune cikin duhu,, Aljani Mak'asudu ya hauro kan Tsito nan suka fara magana da Waziri,, yana fad'a masa buk'atun sa, Mak'asudu yace"Akwai alkwarina a kanka na k'afa biyu kar kace na manta da wannan alk'awarin ina sane dashi, kuma sai na bi jinina,, wannan buk'ata kuma da kawo mana, zata biya amma da sharad'i idan ka kuskura ka kauce sharad'in da muka gindaya maka to sharrin zai koma kanka kaji!!!!!!! Ko"!!!!!!!? Waziri yace"Arne ya dafa maka ai duk sharad'in da kuka gindaya min ina me tabbatar maka da cewar zan bishi bazan kauce ba" Mak'asudu yasa dariya yana fad'in"Shikkenan ni zan jirge!! Yanzu amma zan Sanar da Tsito duk sharad'inmu sai ya fad'a maka" Waziri yace"A sauka lafiya Mak'asudu me mukulin mulki mak'asudu d'an gidan K'azaza gaba salamun baya salamun Ubana"" Tsito ya dunga wata irin katantanwa a tsakiyar d'akin yana wani irin ihu!!!!!! D'if dakin yayi shiru kamar anyi ruwa an d'auke.
Wajan minti goma Tsito ya dawo dai-dai cikin duhu ya kalli Waziri yace"Da alama d'azu muna magana da kai Mak'asudu ya hauro ko"?
Waziri ya gyad'a kai yace"Akwai sak'on da yace zai fada maka ka fada min" Shiru Tsito yayi yana sauraron Mak'usudu sai gyad'a kai yake alamun yana sauroro,, bayan ya gama sauraron Mak'asud'u ya kalli Waziri yana fad'in"Yace"Mu nemo bak'ar kulb'a da bak'ar kunama sai bak'in b'era dunka sai tsohon kadan gare Wanda ya soma sab'a saboda tsufa, duk a yanka su a cire musu fatar jikinsu,, a shanya ta bushe, sai ka kafa kusa a d'akin ka, duk ka kafe fatocin bango d'aya ka samu Jan yanki kasa a tsakiya, bayan nan kuma hanjin su,, a had'a shi guri guda a sanya su su bushe a dake lukwi sai a zuba masa a abunci, da iziinsa sai ya mutu idan bai mutu ba to zai rasa wani b'angare na jikinsa, sannan in ka kuskura mutum ko guda ne, ya shiga dakin Da ka kafe fatocin nan to abun zai dawo kanka,,sai magana ta k'arshe yace"Ka tafi bakin kogi da k'aton rago me tozali ka yanka masa zai shanye jinin" Waziri yace"Duk za'ayi da izininsa mutukar bukatar zata biya, yanzu yanda za'ayi na samu wad'annan dabbobin shine abun dubawa" Tsito yace"Wannan babu matsala gobe sai ka futa dani a mota ni zan samo maka,, sai dai ka ware min lada na" Waziri yace"Duk kar ka damu zan maka kyauta ta ban mamaki in zaka tafi" Nan sukayi sallama Waziri ya futa yana godiya ga Mak'asudu.
*************************
*************************
Kwanan Sallau Uku a asibiti yace ga garin ku nan, Lantana ta dunga kuka kamar ranta zai futa,, Uwa! Ma duk da ya sake ta ta koko da mutuwar Sallau,, Shamsiyya kuwa tun sanda ta dawo daga gidan Arrama ta kwanta ciwo kariris,, Amai da zazzab'i duk ta rame ta jeme sai uban zubar da miyau da takeyi,, jama'a 'yan zaman makoki dayawa duk San fahimci ciki ne da ita Uwa! Ta gane da sauran mutan gidan rudanin mutuwa ya hanasu nuna b'acin ransu domin hausawa nacewa wani tashin hankalin yafi wani,,, Lokacin da Balaraba taji mutuwar Sallau kuka ta dungayi sosai, Mama tai ta rarrashin ta, tare suka tafi
Da ita da du Halisa Madabo ma taje,, Sarki kuwa dashi akayi jana'izar Sallau, unguwar ta d'auka wanda ma bai yi niyyar zama gurin mutuwar ba dalilin zaman Sarki! A gurin ya zauna,, ya sa aka kafa rumfuna sosai mutane suka zo suna kwasar girgi harda wadanda suka futa kasuwa, sai su dawo domin su kwashi abuncin gidan mutuwa, kullum sai sun zo har a kayi sadakar uku,, Balaraba suka dawo gida cikin jamami,, tayi mamaki da har aka share zaman makoki bata ga Iro da Mabaruka ba, har dai ta gaza hakuri ta tambayi Iya ina suke, sai tace"Mabaruka dai tafi sati hudu rabon ta da gida, shi ko Iro tun kafin ki bar gidanan aka neme shi aka rasa, tace"Shamsiyya fa"? Iya ta girgiza kai tana goge kwalla tace"Tana cikin daki ta d'auko abun kunya shiyasa take buyarwa jama'a" Balaraba ta dunga share hawaye tana tausayawa rayuwar su,, Shamsiyya kuwa tana jin ance ga Balaraba tazo zata dunga lekowa tana taga tana kallonta tana fad'in ina ma itace.
*************************
*************************
Duk abubuwan da Mak'asudu ya ce a nemo sun nemo kuma sun aiwatar da aikin kamar yarda yace d'in abunda ya rage wa Waziri shine zuwa bakin ruwa ya yanka rago shima ya sa d'amba gobe da Asuba zai futo domin an samo ragon irin wanda Mak'asudu ya buk'ata...
Yau ne girki Balaraba ya kama,, duk dama wancan kwanakin ya na Cikon na Halisa ne, sai Azima da yayiwa kwana uku, wannan mutuwar da akayi yasa Balaraba taga kamar kwanakin sunyi sauri, ita fa bata lissafin komai yanzu duk bata cikin hayyacin ta domin mutuwar Sallau sai ta dawo mata da ta iyayen ta sabuwa,, jiki a sanyaye take yin komai, k'arfe shida ta kammala girki mai rai da lafiya tayi Wankanta gami da fesa turare ko ina a jikinta, tana sanye da wani material sky blue yayi mata masifar kyau, inda tayi amfani da k'aramin mayafi tayi rolling dashi,, anyi mata kitso ta tattare shi a tsaki ta sanya manya-manya ribom sai ya zama kamar a cuci tayi kyau sosai d'inkin Riga da sket ne,, tayi fuskarta fayau,, ko kwalli babu sai mai leb'e da ta goga,, a nutse ta dunga d'ibar kayan abuncin tana kaiwa part d'insa,, su Amina da Hadiza bayinta sukayi-sukayi ta barsu su d'aukar mata tak'i tace"su barshi itama ladan take so, sai suka hak'ura suka k'yaleta ,, lokacin yana sama ta gama shige da fucen ta, ta koma part d'inta sai bayan tayi Sallahr magariba ne, sannan ta kimtsa, da niyar komawa part din nasa.
Da shirin zuwa masalaci ya sauko hankalin sa bai kai kan daining ba, sai Mai dafa masa abunci fa ya gani a tsaye tsakiyar falo ya sunkuyar dakai kasa, gyaran murya yayi da sauri ya dago yana masa barka da sakkowa, Yace"Kana tsaye gashi ana shirya-shiryen tayar da sallah" Yace"Allah ya taimaka ke Nazo zan jera abunci na ga an jera wani nace Allah yasa ba laifi nayi ba"
Kallon daining teble din yayi yaga wasu had'addan kuloli ba Wanda aka saba zuba masa abunci ba,, girgiza kai yayi kawai, yasan aikin Gimbiya ne, yana k'okarin tafiya yace"Yau an hutar sheka, gobe ma kar kayi gudun asara ka futar muku da Wanda ka girka" Yana gama maganar ya futa,, Shi kuma ya koma kicin, cikin zuciyarsa take cewa amma wannan matar tasa ta tarbiyantu ba kamar sauran ba, Allah ya kyauta.
[9/25, 7:58 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
```MARUBUCIYAR```
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*
_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________
_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_
_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_
*🅿108*
Sai bayan sallahr Isha'i ya shigo, zama yayi a falo da carbi a hannunsa yana ja,, a hankali ya dunga jin wani sanyayyen k'amshi na ziyartar hancin sa, d'aga kansa yayi yana kallon inda yake jin motsi, Balaraba ce take saukowa daga matattakala cikin nutsuwa, a sirance ya sauke ajiyar zuciya ya su kunyar da kansa wani Abu na tsunkullin sa,, ta k'arasa daining cikin nutsuwa ta gyara komai ta tako a hankali ta zauna kujerar dake kallon sa, kansa na k'asa bai dago ba, a hankali tace"Barka da dare" d'ago kansa yayi yana kallon ta, minti biyu yace"Barka kin wuni lafiya"? "Lafiya Lou ta fada'a tana wasa da hannunta,, yace" Ya k'arin hakuri kuma" ? "Alhamdullahi" Shiri falon yayi sak'e-sak'e take a zuciyarta, shi kuma yana k'okarin ya cika carbin sa,, sai da ya kammala sannan ya aje ya d'auki wayar sa, numbar Halisa ya kira tans d'auka yace"Ki futo muci abunci " kashewa yayi ba tare da ya saurari abunda zata CE,ba, numbar Azima yake nema, sai gata ta shigo cikin