Author : mammy kabeer Category : African Stories & Novels
na gani,dan kuwa sosai lamarinta ya tsayamin araina ji nake kamar inada wata alaƙa da yarinyar" suhaimat ta fada tana mai lumshe idonta.
Azabure ammi ta kalli sarauniya suhaimat tana mai dafe ƙirji"na shiga ukuna ,suhaimat gurin yarinyar kikaje?me kika gani?da wa kikaga tana miki kama?ammi ta faɗa cikin rudewa da tashin hankali,dan bata taba tsammanin suhaimat zataje gurin fattu ba.
Kallon mamaki suhaimat ɗin ke bin ammi dashi ,kafin tace "uktee ,yanaga kin rude haka?daga jin cewar naje gurinta?kuma dawa kike tsammanin zanga tana kamar?ta fada cikin mamaki tana kallon ammi,da sai lokacin ta fahimci tayi baran -barama kuma tana son bada kanta.
Cikin sauri ta saita kanta,kafin tace "ai nayi mamakin yadda kika damu da
baiwane,har kikaje dan ganinta"ammi ta faɗa cikin basarwa.
Murmushin suhaimat tayi kafin tace "wllh yadda nake jin yarinyar nan cikin raina ,ko su zayyad bana jinsu haka"ta faɗa cike da shauki akan fuskarta.
Wani shegen kallon ammi ta jefa mata ,tana mai faɗin ,aikuwa saidai kiyi ta jin wannan shaukin cikin ranki,amma keda ƴarki har abada,bazan ƙara bari ki ganta ba,dan kuwa kashe shegiya zanyi kowa ya huta.ammi ta fada cikin ranta.
Amma afili saitayi murmushi tana faɗin,"ke dai suhaimat kina nan da son jama'a har yanzu,sukuwa mutane ba abin yarda bane ,Gara ki kula"
Jinjina kai suhaimat tayi kafin tace "ai idan har kana abu tsakaninka da Allah ,to tabbas Allah zai zama gatanka, kuma bazai taba ba maƙiya Sa'a akanka ba,kuma kinsan shi sharri dan aikene,idan ka cutar da wani to kana zaune zakaga sakayyar Allah"cewar sarauniya suhaimat kenan cikin murmushi take bayaninta.
Kallonta ammi keyi,cike da sanyin jiki,sai take ganin kamar magana suhaimat ke faɗa mata afakaice,amma ai tasan suhaimat bata san komai game da halayyar ta ba ,bare tayi mata shagube.dan haka ta Badar da maganar sukaci gaba da hira.
"Ranka ya dade ,hakika al'amarin Adeeb babban abune,wanda Allah shine kadai zai iya kareshi,domin kuwa sihirin da akaiwa yaron nan,badan ƙarfin addu'ar dake tare dashiba, to tabbas mutuwa zaiyi,domin kuwa sihirin anyi shine badan ya rayu ba,saidai akasheshi. Dan haka ba abinda zamuyi face addu'a domin Allah ya kareshi da duk wani mai nemansa da sharri" Shaikh lateef ya faɗa ,yana mai kallon mai martaba ,
Shiru abie yayi cike da tsantsar mamakin waye yayiwa ɗansa wannan aika aikar,kallon ƙaninsa waziri yayi cikin damuwa yace "ɗan uwana kanaji? Kana jin abinda Shaikh ke faɗi, me Adeeb ya tsarewa jama'a ?yaro mai hakuri,hankali da hangen nesa,ba ruwansa da kowa bai tsarewa kowa komai ba,amma ana neman ganin bayansa,Allah ka karemin ɗana ,ka raba shi da sharrin makiya,yanzu Shaikh menene abinyi.
?"abie ya faɗa cikin damuwa yana jin kamar ya zubda hawaye.
Jinjina kai Shaikh lateef yayi yana Jan carbinsa dake maƙale adan yatsansa.
"Ranka ya dade ba abinda zamuyi masa daya wuce addu'oi,sannan zan hada masa maganin karya sihiri wanda zai sha yayi wanka dashi,amma fa kasancewar samutum akoda yaushe abune mai matukar wahala,dan kuwa Aduk lokacin da ya shiga yanayi na ɓacin rai mai tsanani to tabbas akwai yuwuwar komawarsa macijin " Shaikh ya faɗa yana mai kallon abie.
Wazirine ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Shaikh cikin damuwa kafin yace "yanzu ba wata hanya da Ya kamata abi,Dan arabashi da wannan iftila'in?ta yaya za'ace mutum yana komawa wata halittar? Shaikh aduba dai "waziri ya faɗa yana kallon Shaikh.
Murmushi Shaikh yayi yana mai girgiza kai,kafin yace ,tabbas da 'ace akwai hanyar da zanbi dan ganin na raba yaron nan da wannan al'amarin ,to danabi ,kamar yadda na faɗa muku, anyi amfani da mugayen aljanu waɗanda suka samo macizan da ba irinsu afadin duniyar nan,kafin aka hada lakanin da akayi masa sihirin dashi, dan haka addu'a itace kadai mafitarmu"
Ajiyar zuciya abie ya sauke ,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa da ɓacin rai,sosai yake jin tausayin Adeeb,waye wanda ke son ganin bayan Adeeb? Me ya tsarewa mutane haka?
Dole ya tsaya sosai ya kula da rayuwar dansa ,ta hanyar bashi kariya ta kowace sigar.
"Shikenan Shaikh Allah ya shige mana gaba ,ya bamu Sa'a akan abinda muke nema"cewar abie yana mai lumshe idonsa lokaci guda damuwarsa ta baya ta dawo masa ,yana tuna abinda ya faru shekarun baya,sam baya son abu makamancin abinda ya faru a baya ya sake faruwa.
"Yanzu ranka shi dade,ina son aturomin yarima zuwa anjima dan akwai abubuwan da zamu tattauna dashi"Shaikh lateef ya faɗa yana mai mikewa dan barin dakin.
Bayan fitarsa waziri ya kalli abie wanda yayi shiru fuskarsa gaba ɗaya ta sauya ,ta koma kalar damuwa sosai,
"Ranka ya dade ka kwantar da hankalinka,In Sha Allahu komai yazo ƙarshe,ba abinda zai sake samun yarima"waziri ya faɗa cikin kwantar da murya aƙokarinsa na kwantarwa da abie hankali.
"Allah yasa waziri,amma abin yana damuna ,kasan yadda nake son Adeeb ,bana son abinda zai tabashi komai ƙanƙantarsa,domin shine magajina"
"Ba komai ranka ya dade mubar komai hannun allah."cewar waziri.
Jinjina kai abie yayi kafin yace ,sai kuma wannan matsalar ta Rashad,Dole in ɗauki mataki mai ƙarfi akansa,jira nake kawai ya sami lafiya"
"Haka ne yaya dole ahukunta Rashad ,Dan yana don bata mana suna" cewar waziri cikin damuwa.nan dai sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar.
Rashad yana nan har yanzu kwance kamar gawa ,ko motsi bayayi, gaba ɗaya kamanninsa sun sauya ,abin tausayi,kullum amma cikin kuka take tana tausayawa halin da ɗan nata ke ciki,
Gimbiya Zulaihat ma tun daga wannan ranar bata kuma ganin Adeeb ba,dan tsoronsa take ji sosai,amma har lokacin tana nan akan bakanta na son aurensa.
Adeeb kuwa yana dakin da fattu ke kwance tana barci,kallonta yake cike da tausayi,gefe guda kuma wayar da ammi tayi gaba ɗaya ta tsaye masa arai,ga maganar da nanny ta fada masa,shi gaba ɗaya ma ya shiga ruɗu baisan me Yakamata yayi ba,yanzu gurin wa zai je neman shawara?waye zai sanarwa da damuwarsa?yanzu tsoron mutanen fadar nan yake ,dan kuwa cike take da mutane marasa amana da gaskiya.
Ahankali ya shafa gefen fuskar fattu tare da sumbatar goshin ta kafin ya mike tare da ficewa daga ɗakin.
Kai tsaye amma ta fito daga part ɗin Rashad bayan ta gama kukanta ta koshi,tunani tayi kan cewar ya kamata akawo karshen wannan al'amarin dake dukunkune cikin fadar nan,dan haka tana da bukatar magana da nanny Dole taje tayi magana da ita yanzu .
Dan haka can ta nufa ,cikin sa'a ta tarar da nanny zaune afalo, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin damuwa da alhini.tana ganin amma ta mike tana mata maraba cikin girmamawa.
Zama amma tayi tare da kallon nanny tace"zauna nanny inason muyi magana dake . "ta fada tana mai kallon nanny ,wacce itama kallonta take.zama nanny tayi jikinta asanyaye kafin tace "wace magana kike son yi dani ranki ya dade?inaga da kin aiko ankirani nazo gurinki dan gudun zargi ,idan aka ganki anan"nanny ta fada cikin damuwa.
"Ajiyar zuciya amma tayi kafin tace ,ya kamata mu daina boye-boye nanny akan abinda muka san menene gaskiyarsa,ki duba halin da ɗana yake ciki ?kuma duk akan wannan makirar matar ,nasan cewa kome ya faru shirinta ne,meyasa zamu zauna mu zuba mata ido tana aikata abinda taga dama?dan haka dole mu kawo ƙarshen zalunci ta"amma ta faɗa cikin ɓacin rai da damuwa.
Ajiyar zuciya nanny ta sauke mai ƙarfi kafin tace "ranki ya dade wannan abun fa abune mai matukar hadari ,dakuma tarin ƙalubale,domin nayiwa magajin fada maganar hadarin sarauniya Nazli, na sanar dashi wanda ke da hannu akan hadarin, amma sam bai yarda dani ba yayi fushi mai tsanani.tunda ya fita bai sake dawowa ba.dan haka ina ganin mudan jinkirta zuwa wani lokaci,har wannan abinda ya faru yayi sanyi"
Jinjina kai amma tayi cike da gamsu,tace "wannan gaskiya ne ,dan kuwa nasan mai martaba ma jira yake Rashad ya farfaɗo ,kafin ya yanke hukunci akan abinda ya aikata .Allah shine kawai zai fitar damu " ta fada kwalla na cika idonta.
"Kiyi haƙuri ranki ya dade ,komai yayi farko, yana da karshe ina sha Allah muke da nasara"cewar nanny cike da damuwa akan fuskarta.
"Shikenan nanny Bari na koma can gurin Rashad din"Amma ta faɗa tana mikewa.
Biyota nanny tayi tana mata sallama ,har farfajiyar gidan suka fito nanny na kara kwantarwa da amma hankali.
Daidai lokacin kuma Adeeb ya fito daga part ɗinsa ,idonsa ne ya sauka akan nanny tsaye tare da amma.
Kallonsu yayi cike da tsantsar mamaki,da kara tabbatar da zarginsa akansu.
Suma kallonsa suke cikin yanayi na damuwa da rashin jin dadin ganinsu da yayi .
Tafiya amma tayi daga gurin ,ganin irin kallon da Adeeb ke mata.
Nanny kuwa jikinta ne yayi sanyi sosai.da hanzari ta nufi gurin da Adeeb ke tsaye........
Hmmmmm masu karatu muhaɗe next page .
Takuce anty mammy
Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
29/08/2022, 11:07 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 63/64
_______________Jikin nanny ne yayi sanyi sosai,ganin Adeeb atsaye,kuma ya gansu tare da amma,tasan yanzu kam kome zata faɗa masa ,bazai taba yarda da ita ba.ahankali take takawa zuwa gareshi,gaba ɗaya jikinta ba kwari,
Shikuwa Adeeb yana tsaye ya kafeta da Mayun idanunsa ,masu sanya mutum yaji shi cikin tsoro da fargaba.
Nanny Tana karasowa tace "magajin fada ,fushi kake dani ko"?
Ta fada cikin sanyi murya da mutuwar jiki.
Lumshe ido Adeeb yayi ,zuciyarsa na masa zafi yana mamakin abinda nanny tayi masa,ace wai nanny ta hada kai da maƙiyarsa tana tayata ƙoƙarin cutar dashi,matar daya ɗauka matsayin uwa ?mutum kenan.
"Ko kaɗan nanny bana fushi dake,kawai ina godiya ga Allah ne ,daya nunamin gaskiya ,na gane irin mutanen da nake tare dasu,na daukeki tamkar mahaifiyata nanny,Amma bansan nayi babban kuskuren yin hakan ba,dan Allah kiyi haƙuri"ya faɗa yana mai haɗe hannayensa guri ɗaya alamun neman afuwa.
Sosai nanny kejin ciwo cikin ranta ,damuwa da taraddadi sun cika mata zuciya,dama tayi wannan tunanin,tasan idan har Adeeb ya gansu tare da amma ,to shikenan,kuma kome zata faɗa masa bazai yarda da ita ba,amma Allah shine shaida bata da nufin cutar da Adeeb ko kaɗan.
"Magajin fada wllh abinda kake zargi ba haka bane ,kada ganina tare da amma yasa maka kokwanto akaina, wllh nima Ina jinka tamkar tareeƙ bazan taɓa cutar dakaiba magajin fada.
Nanny ta faɗa cike da damuwa aranta.
Girgiza kai kawai Adeeb yayi tare da barin gurin,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa .
Kallonsa kawai nanny keyi,tana fatan Allah yasa ya gane gaskiya cikin sauri kafin komai ya daɗa lalacewa.
Ba kowa cikin falon ammi,sai ƙamshi dake tashi ta ko'ina ,dan ammi akwai son kamshi,kai tsaye ya nufi dakin kwananta, nocking yayi amma shiru,hakan yasa shi shiga cikin dakin kai tsaye.saidai nan ma ba kowa cikin dakin.
Harya juya zai fice ,sai kuma zuciyarsa ta raya masa ya duba wanann akwatin da yaji ammi na magana akanta.
Dan haka juyowa yayi yana karewa dakin kallo.
Ahankali yake duba dakin dan neman wannan akwatin,amma yayi iyakar dubansa bai ganta ba.
Harya hakura sai kuma ya hango wata akwati mai kyau da ɗaukar ido,yasan akwatin Dan acikinta ammi ke ajiye kwalakwalanta ,dan haka sai yayi tunanin ba komai cikinta, har ya juya da nufin barin dakin,sai kuma zuciyarsa ta kwadaitu da son duba akwatin .
Dan haka ahankali ya zauna tare da ɗauko akwatin, danna lanbobin bude akwatin yayi,dan kuwa tuni yasansu, aikuwa saiga akwati ta bude,gwalagwalai ne acikinta iya ganin ka ,masu kyau da ɗaukar hankali,kallo ɗaya zaka musu kasan an zubar da maƙudan kudade wajen mallakar sarkokin.
Dubawa yayi tayi amma baiga komai aciki ba,sai wani dan karamin akwati mai kyau da ya gani,kallon akwatin yake da mamakin meye acikinsa aka wareshi ?lallai yana son ganin abinda ke ciki.dan haka hannu Ya mika tare da ɗauko akwatin ya bude.
Mamaki ,al'ajabi ruɗu da kuma faduwar gaba sune suka ziyarci zuciyar Adeeb,sakamakon ganin sarƙar nan ta Hulwa data bace ,cikin wannan akwatin,
Me yakawo sarkar Hulwa cikin kayan ammi?har akayi mata adana ta musamman?me hakan ke nufi,shidai yasan ammi tana da sarkokin da suka ninka kudin wannan bare yayi tunanin ta daukene dan bata da mai tsada kamar wannan ,to me hakan ke nufi kenan?innalillahi meke faruwa ne acikin gidan nan?kodai akwai Abinda ammin nashi ke kullawa da gaske ? Wayyo ina zaisa kansa ?dawa ya kamata ya yarda ne cikin fadar nan? Dauko sarƙar yayi cikin sauri ya maida komai inda yake sannan yayi saurin barin dakin na ammi ya koma part dinsa. Zuciyarsa na zafi kamar zata kama da wuta .
Lokacin daya koma part din nasa fattu ta farka,tana zaune tana kuka,tsoro takeji,har lokacin barin ma dataga ita kadaice cikin dakin,ina Hamma ya tafi ya barta?karfa wannan Rashad din ya dawo mata? Gashi wannan innar ma bata dawo ba,wannan tunanin yasata ƙanƙame jikinta tana kuka.
Adeeb kuwa cikin wani irin yanayi na sarewar zuciya ya shigo cikin dakin,abubuwa sunyi masa yawa cikin zuciyarsa,jinsa yake kamar bashiba, kansa banda ciwo ba abinda yake ,wai meke shirin faruwa da rayuwarsa ne ?me hakan ke nufi ?me amminsa ke nufi da ɗauke sarƙar Hulwa?
Kukan hulwar da yaji Yone yasani saurin ƙarasawa cikin dakin.
Tana jin motsi sa ta zabura atsorace tana mai kallon ƙofar dakin.ganin Adeeb ne ya shigo yasata saurin yunkurawa ta mike da gyar tana kuka tare da kallonsa.
Da saurinsa ya ƙaraso inda take ,yana zuwa ya kamo hannunta tare da shafa gefen fuskarta yace "menene kike kuka?inane yake miki ciwo ?ya faɗa cikin mugun sanyin murya ,wanda har saida fattu ta ɗago kanta ta kalleshi,
Idanunsa sunyi jajur sosai jijiyoyin kansa sun fito rudurudu,fuskarsa tayi jajur ,kana gani kasan yana cikin damuwa da tashin hankali.
Cikin kuka fattu ta faɗa ƙirjinsa ta rungumeshi, tana faɗin "tsoro nakeji Hamma ,ko ina ganin ƙaninka nake yana min gizo Hamma" ta fada cikin kuka tana ƙanƙame Adeeb.
Cike da tarin damuwar da baisan menene mafitarta ba shima ya ƙanƙame fattun ajikinsa yana mai lumshe ido da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi,
Ahankali yake faɗin"kiyi haƙuri Hulwa , dagani harke muna cikin damuwa, Hulwa komai bayamin dadi na kasa gane dawa ya kamata in amince cikin fadar nan,Hulwa kowa na fadar nan so yake yaga bayana bansan me na tsare musu ba" Adeeb ya faɗa cikin murya mai tattare da karaya da sarewa.
Shiru fattu tayi tana sauraron abinda yake fadi,ita fa sam bata fahimci inda zancen sa ya nufa ba,ahankali tace "Hamma ,su waye ke son kamin bayanka"?
"Shiru yayi yana mai kara rungume fattu ajikinsa,dan sosai yake jin nutsuwa na samunsa sakamakon rungumeta da yayi,zuciyarsa tana yi masa sanyi .shafa gashin kanta kawai yake bai ce komai ba.
Kusan minti biyar suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin zareta daga jikinsa ya zaunar da ita abakin gado,kallonta yake ,har zuwa lokacin idanunta basu koma yadda suke ba,akwai kumburi da kuma dan jaa kadan acikinsu.
Hannunta ya kamo cikin nashi ya rike gam-gam yana kallonta.ji yake kamar ita kadai ta rage masa wacce zai fadawa damuwarsa,saidai fattu yarinyace,idan ma ya faɗa mata damuwarsa bazata fahimci me yake nufiba.
Kallonsa fattu tayi itama,tabbas akwai Abinda ke damun hamman nata,ko menene oho."Hamma meke danunka?baka da lafiya ne ?ta fada cikin muryar marasa lafiya ,wadanda suka sha kuka.
Ahankali ya koma kusa da ita ya zauna ,kallonta yayi yace "Hulwa abinda ke damuna yana da yawa,ina cikin wata sarkakiya wacce Allah ne kawai zai fitar dani,bani da wanda zan fadawa damuwata ahalin yanzu,bana son sanar da abie na komai,dan gudun ɓacin ransa,saboda tsoron kar ciwonsa ya tashi,kiyi ta min addu'a kinji hulwatee" Adeeb ya faɗa yana mai riƙe habar fattu tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa.
Cike da tausayawa fattu ke kallon Adeeb,kafin itama ta sanya hannunta akan fuskarsa tana shafa gefen fuskar tashi, kamar yadda yake mata .sannan tace "Hamma zanyi ta maka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, kuma kaima kayi ta addu'a Allah maji rokon bawansa ne ,Allah ya bawa abie lafiya Hamma,amma me zai hana ka sanar da innarka itama ta tayaka addu'a" fattu ta faɗa bayan ta cire hannunta daga kan fuskar Adeeb.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Adeeb ya sauke lokacin da fattu ke shafa gefen fuskarsa ,ahankali ya lumshe idanunsa yana jin wani irin sanyi yana Ratsa zuciyarsa.
Ahankali ya bude idonsa lokacin da yaji ta cire hannunta daga kan fuskarsa.kafin yace "Hulwa ammina tana daga cikin mutanen da nake son boyewa damuwata ,ahalin yanzu bazan iya sanar da ita komai daya danganci lamarinaba,ke dai kiyi ta min addu'a kinji"ya faɗa cikin murya mai cike da ban tausayi.
Sosai fattu kejin tausayin hamman nata yana Ratsa zuciyarta.ahankali ta ɗora kanta gafen kafadunsa tare da rungumoshi ta gefe.tayi shiru cike da tunanin meke damun hamman nata.
Ahankali shima ya dora kansa akan nata kan yana jinsa tamkar marayan da bai da kowa.
"Hamma wannan innar bazata dawo ba ko?" Ta fada ahankali idanunta alumshe.
Shima idonsa alumshe yake yana shafa kan fattu ,yace "kina so ganinta ne?
"Daga kai tayi alamun eh sannan tace " eh Hamma ina son ganinta ,ina kaunar ta har cikin raina ,kuma tace daga yau itace inna ta"
Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin yace " Hulwa ita kadai kike kauna ? Ni baki kaunata?ya faɗa ba tare da yasan ya fadi hakan ba .saida ya faɗa sannan ya fahimce me yace .
"A'a Hamma ina ƙaunarka sosai mana,ina sonka,kaidin kamar baffana kake ,bani da kowa saikai, Hamma bana son wani abu ya tab aka ma" ta fada tana ɗago kai tare da kallon Adeeb.
Cikin wani irin farin ciki da jin dadi Adeeb ke kallon fattu,zuciyarsa cike da jin dadi yace "da gaske kike Hulwa?" Ya faɗa cikin murmushi yana kallonta.
Jinjina kai tayi itama cikin murmushi tana kallonsa.
Ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta gamm yana mai lumshe ido , sosai yake jin wani irin. Daɗi da Nutsuwa cikin zuciyarsa.
"Kina son ɓata min shiri ko ?,kisani wllh idan kikayi wani kuskuren dana rasa damata,kema zaki karbi naki hukuncin ,kin sanni kinsan halina,kuma kinsan abinda zan iya aikatawa ,dan haka ki kula da kanki,komai yana ƙoƙarin lalacewa saboda sakacinki,to bazan laminci wannan abinda kike yiba.wllh zan aikaki gurin da duk wanda zai zamenin matsala nake aikawa.akan wannan karagar zan iya batar da kowa"
Wani mutum ne daya lulluɓe ilahirin fuskarsa ke fadin wannan maganar cikin ɓacin rai yana kallon ammi,wacce ke tsaye cikin tsantsar tsoro ,jikinta sai rawa yake cikin tashin hankali tace "dan Allah kayi hakuri ,wllh ina yin iyakar ƙoƙarina akan wannan abun ,kuma aKwai shirin da nake yi ,karka damu ka kara hakuri "ta fada cikin rawar murya,tana kallon mutumin da baka ganin komai bace kwayar idanunsa.
Cikin fushi mutumin ya damƙi wuyan ammi ya hadata da