Author : mammy kabeer Category : African Stories & Novels
juyar dashi zuwa abin tsoro.
Hannunta ya kama zuwa bakin kwamin wankan ,cikin ɗaure fuska ya kama rigarta yana ƙoƙarin cire mata ,da sauri ta riƙe hannunsa dan harya kawo rigar wajen cinyarta." Hamma zanyi da kaina kayi haƙuri" fattu ta faɗa tana mai zaro ido ,ganin da gaske yake ƙoƙarin cire mata rigar.
Sakin rigar yayi tare da juya mata baya yace " kiyi wankan yanzun nan zan dawo " ya faɗa yana ja mata ƙofar.
Koda Adeeb ya fito daga toilet ɗin Safa da marwa yake tayi cikin dakin,ba abinda yake masa yawo acikin zuciyarsa ,sai abinda rashad yayi ƙoƙarin yiwa fattu,wato taɓa jikinta.
Hannunsa ya sanya tare da dukan bangon dakin da ƙarfin gaske ,yana huci cikin wata irin zazzafar murya yake faɗin" Rashad kayi kuskure na farko ,idan har ka sake yunƙurin taba min matata ,yayi shiru yana huci kamar wani zaki,kafin ya mike tsaye tare da barin ɗakin, shida kansa ya gyara gurin da fattu ta ɓata ,dan bazai sa wani ya gyara gurin da fattu ta ɓata ba.yana gamawa kuwa
Kai tsaye bangaren ammi ya nufa yana shiga ya tarar da ita zaune ana taje mata gashi.
Zama yayi akusa da ita ba tare da yace komai ba.
Cikin girmamawa gaba É—aya haÉ—iman suka gaida Adeeb tare da ficewa daga É—akin.
Cike da kulawa ammi ta kamo hannun Adeeb tare da shafa kansa " mu Prince kayi haƙuri da abinda ya faru tsakanin ka da Rashad , ba yadda banyi dashi akan ya gyale yarinyar nan, domin kuwa kai kazo da ita ,kuma a ƙarƙashin kulawar ka take bana son tashib hankali,amma sai cewa yayi ai ba matar ka bace dan kazo da ita ,wai shi sonta yake kuma ba wanda ya isa yashi tsakaninsu da ita.
Amma my prince kai menene alakarka da yarinyar nan ?dan musan yadda zamu bullowa lamarin ,tun kafin asami matsala"ammi ta faɗa tana mai kallon Adeeb da son jin abinda zaice akan alaƙarsa da yarinyar.
Adeeb kuwa wanda ransa ya ƙara ɓaci sosai da abinda ammi ta faɗa masa cewa rashad ɗin ya faɗa ,cikin furzar da wata zazzafar iska Adeeb ya kalli ammi kafin yace " amma dole na ɗauki mataki akan rashad ,bazan taba bari ya cutar da yarinyar nan ba ,dan ita ɗin amanata ce " yana faɗin haka ya mike tare da barin dakin.
Murmushi ammi tayi tare da lumshe ido ,lallai burinta yana gab da cika akan waÉ—an nan yan uwan.
Bangaren nanny ya nufa yace ta bashi kayan fattu ,cike da kulawa nanny tace " ayya É—an nan ,daka dawo da ita nan ta shirya ,dan kuwa zamanta acan gurinka akwai matsala ,kasan akwai yan sa ido " nanny ta faÉ—a cike da kulawa.
Kallonta kawai Adeeb yayi, tare da karbar kayan data ciro masa harda pant É—in data sakawa always ," zata dawo " kawai ya faÉ—a tare da barin dakin.
Fattu kuwa lokacin data kammala wankan ta sosai taji jikinta yayi mata daɗi ,saidai kumasam ƙin shiga cikin kwamin tayi ta kunna shaya tayi wankanta,saidai damuwarta ɗaya yadda taga jinin nan yaƙi daina zuba. Hawaye ta share daga idanunta kafin ta janyo wani ƙaton bargo ta daura ƙirji dashi.
Æudewa tayi tare da fitowa falon ta tsaya jikin bango ,bata son ta zauna jinin ya Æ™ara batata.abin mamaki tsaf taga an gyara gurin data bata É—in nan.
Ko waye ya gyara oho!fattu ta faÉ—a cikin ranta .
Adeeb ne ya shigo ɗakin riƙe da kayan fattu dake ta zuba ƙamari,kallonta yayi tare da kawar da kansa ,ajiye kayan yayi akan gado yace " kisa kayan ki sameni afalo" sannan ya bar ɗakin.
Bayan fattu ta sanya kayan harda pant din Dan ta gane yadda ake sakawa tunda nanny ta faɗa mata .kanta ta yane da mayafin kayan,sannan ta nufi gaban madubi,turare ta gani dan haka ta ɗauka tare da bude murfin kwalbar gaba ɗaya tana masa shafawa irin ta mai. Sannan tana yaba ƙamshin wannan man shafawa azuciyarta.
Saida ta gama sannan ta fito falon.
Tun kafin ta gama buɗe ƙofar ƙamshin turaren ya bugi hancin Adeeb ,da sauri ya dago kansa,lokacin data ƙaraso kusa dashi gaba ɗaya falon ya kiɗime da ƙamshin wannan mayen turaren na Adeeb, turarene irin mai shegen kyau da tsada r nan, kwalbar yar karama ce ,wacce kuɗi ta yakai kusan dubu dari biyar ,ɗan kaɗan ake shafawa amma sai yayi sati bai bar jikin mutum ba.shine malam fattu ta shafa matsayin mai.
Kallonta yake hatta ƙara so kusa dashi ta tsaya .
Wasa take da yan yatsunta,yayin da kanta ke ƙasa.
Lumshe ido Adeeb yayi sakamakon yadda ƙamshin turaren nan ke ratsa dukkan wani sannan na jikinsa.
Buɗe ido yayi yana kallonta kafin ya kamo hannunta ya zaunar da ita ,hancinsa ya kai daidai wuyansa yana ɗan shaƙar ƙamshin jikinta.
Lumshe ido fattu tayi lokacin da hucin numfashin Adeeb ya sauka akan dokin wuyanta.
Kallonta Adeeb yayi idanunta alumshe ta damƙe gefen kujerar da take kai,
Kalli yarinyar nan mafa A ce kalli daga É—an matsawa kusa da ita yadda take cakumo kujera ,hmmm. Adeeb ya faÉ—a cikin zuciyarsa yana mai ci gaba da kallon fattu.
" Ki buɗe ido ki,saiki saki kujerar karki Yahaya ko" Adeeb ya faɗa yana mai matso da fuskarsa saitin ta fattu,duk da yadda ƙamshin turaren nan ke ƙoƙarin hawa masa kai.
Da sauri fattu ta buÉ—e idonta tana mai kallon Adeeb ,tare da sakin kujerar ,kunya kamar ta kasheta .
Turo baki tayi tana mai ƙif-ƙif ta ido.
" Me yasa kika samin turare?" Adeeb ya faÉ—a yana mai kawar da kansa .
Kallonsa fattu tayi kafin tace " Hamma bansa turare ba ,kawai na shafa mai ne" fattu ta faɗa kanta a ƙasa.
Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin yace" haka ake turare agarinku?
" Dan murmushi fattu tayi kafin tace "Hamma to mu ina zamuga wani turarema ,mufa ko mai ma bamu cika shafawa ba" fattu ta faÉ—a tana É—an watsa hannu,kamar ba ita ta gama kukan tsoro ba É—azu.
" Shiyasa kikayi min ɓarnar turare ko? Bakisan yana da tsada ba ?Adeeb ya faɗa yana ɗan kallon gefenta.
" Ayya Hamma bansan turare bane ,kawai ƙamshin ne yayi min daɗi,shine na shafa amma kayi haƙuri Hamma zan siya maka wani" fattu ta faɗa tana ɗan dafa kafaɗar Adeeb.
Kallonta yayi kafin ya kalli hannunta data É—ora akan kafadunsa.
Zare hannun tayi da sauri tana mai sunkuyar da kanta.
"Ina zaki sami kuÉ—in da zaki siyamin wani? Kinsan kuÉ—in da ne" Cewar adeeb yana É—an murmushi.dan yasan yanzu fattu zatayiwa turaren kuÉ—i.
" Karka damu Hamma zan tara kudi mai yawan da kai kusan dubu uku ,saina siya maka turaren da yawa.
Dariya ce ta kama Adeeb ,wai dubu uku !sai kace kudin sadaka .
" Shikenan ki tara dubu ukun saina kaiki kisiyamin" cewar Adeeb kenan yana mai kallon wuyanta.
Hannu yakai kan wuyan nata ya É—an shafa cike da mamaki kafin yace " Hulwa" dagowa tayi tana kallonsa,yace "ina sarkar nan?"
Hannu fattu ta kai tare da shafa wuyanta ,taji wayam, shiru tayi tana É—an tunani ,ina ta ajiye sarkar nan kuwa?amma ta kasa tunowa," Hamma bansan inda sarkar take ba" ta faÉ—a cikin damuwa tana shafa wuyanta.
Shiru Adeeb yayi yana nazari,lallai sace sarkar akayi,kuma akwai wanda yake zargi ,dan haka kallonta yayi yace " waye yazo dakinki " shiru tayi na É—an lokaci kafin tace Hamma Ni bansani ba dan nayi barci "
"Shikenan tashi muje" Adeeb ya faÉ—a yana mai haÉ—e fuska sosai,yasan ba kowa bane ya É—auke wannan sarkar face Rashad ,kuma amma ita zata sashi ya É—auke,shi yasan dama saita bashi matsala sosai,amma zai É—au mataki .
Amma kuwa hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba da ganin halin da Rashad ke ciki,yanzu akan wannan yarinyar Adeeb yayiwa Rashad wannan dukan.
Lallai ya taɓowa kansa.
Kuma dole mai martaba yasan da wannan batun ,
Rashad kuwa ba abinda yake sai tunanin zuwan gobe ,lallai ya shiryawa goben nan Allah ya nuna mata dan kuwa zai bar wa Adeeb babban darasi akan fattu.
Sorry kwana biyu ina biki shiyasa kuka jini shiru.
Muje zuwa masu karatu
Mrs babi ce 💘💘💘
29/08/2022, 10:59 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 47/48
_________________Kai tsaye part ɗin nanny Adeeb ya nufa da fattu,suna zuwa kuwa nanny ta gyara ko ina sai ƙamshi ke tashi,dakin fattu suka shiga ,ya zaunar da ita abakin gado.kallonta yayi na ɗan wani lokaci yana tunanin wannan ƙamshin na jikinta yayi yawa ,kuma zai iya sanyata mura ma,dan shi kansa ƙamshin ya buwaye shi.
Ahankali ya buɗe bakinsa yana mai faɗin " nanny ahaɗa mata ruwa tayi wanka saita sake wannan kayan" ya faɗa yana kallon nanny dake kusa da fattu tana faɗin" ke ƴar nan !wannan ƙamshin fa?tunda kuka dosa part ɗin nan nake jin ƙamshin,turaren magajin faɗa,ashe ajikinki yake"cewar nanny Tana mai kallon fattu,kafin ta dawo da kallonta kan Adeeb tana mai cewa" ai dole ma tayi wanka dan wannan turaren yayi yawa ajikinta,kasan shi kuma turare shu'umin abune,yanzu zai saka cikin wani hali,barin ma wannan turare naka mai sanyi ƙamshi, ga yara irin su Rashad birjik afada" nanny ta faɗa tana mai kama hannun fattu suka nufi toilet.
Shiru Adeeb yayi yana kallon ƙofar da suka shiga,lallai dole ma ya hana fattu sanya turare dan maganar nanny gaskiya ce,shi kansa cikin wani irin shauƙi yake jinsa,hakanan tunda ya shaƙi ƙamshin ajikin fattu.
Tashi yayi cikin nutsuwa ya fice daga É—akin.
Dakin ammi ya nufa lokacin tana zaune gaban wani ƙaton akwati mai ruwan gwal ,sai sheƙi yake da ɗaukar ido,ba komai bane cikin akwatin sai sarƙoƙinta na gwal kala -kala.
Wata yar ƙaramar akwatin ce ahannunta tana mai kallon sarkar fattu data adana aciki.
Murmushi tayi tare da faɗin"nayi alƙawarin keda haɗuwa da ahalinki saidai alahira,zanyi ƙoƙarin toshe duk wata hanya da zata sadaki dasu,domin cike burina" ammi ta faɗa cikin zuciyarta tana mai murmushi da ƙarewa kyakyakywar sarƙar kallo.
Kamar daga sama ta tsinkayo sallar Adeeb .dan haka cikin azama ta maida sarƙar cikin dan akwatin tare da rufe babban ta maida shi ajiyarsa.
Zama Adeeb yayi kusa da ita ,ba tare da yaga abinda tayi ba.cikin zafin zuciya yake magana da harshen larabci" ammi zan ɗauki mataki mai tsanani akan Rashad da mahaifiyarsa ,Dan kuwa sun ƙetare iyakarsu" Adeeb ya faɗa yana huci cikin ɓaci rai.
Wani daÉ—ine ya mamaye zuciyar ammi ,amma a zahiri da sauri ta kamo hannun Adeeb tana mai marairaice fuska tace " haba habeebee ,me yayi zafi ?me sukayi maka?Indai akan wannan maganar ce ,to kabar komai ahannuna zanyi wa tubkar hanci,bazai kara zuwa gurin ta ba"Ammi ta faÉ—a tana mai shafa bayan hannun Adeeb É—in.
Girgiza kai yayi cike da jin tsanar Rashad da Amma,kafin yace " ba wannan maganar bace,ammi Rashad ya ɗauke sarƙar da zata zama makamin da zai sada yarinyar da mahifanta,kuma nasan wannan tabbas shirin Amma ne, Ammi na rasa me kika tsarewa matar nan ta Tsaneki da ahalinki baki ɗaya,kullum burinta ta ganmu cikin tashin hankali ,why Ammi ?" Adeeb ya faɗa cikin mugun damuwa da tausayin Ammin nashi.
Sosai Ammi ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ,kafin ta fara magana" habeebee nima bansani ba ,duk yadda nake ƙaunarta da iyalinta,amma sam bata gani tun kana yaro take ƙoƙarin saita ga bayanka ,amma Allah bai bata Sa'a ba, kai dai karvi gaba da haƙuri, sannan kabi komai cikin lumana.kuma awannan karon na goyi bayan ka ɗauki mataki akansu har sai sun bayyana sarƙar nan" Ammi ta faɗa cikin ƙarfafa gwuiwa ga Adeeb . Jinjina kai yayi cike da gamsu da shawarar ammin nashi.sun jima suna tattaunawa akan al'amarin ,ba abinda ammi ke yi sai tunzura Adeeb cikin cikima da basira.
Amma kuwa tana zaune abakin dagon Rashad,yayin da take shafa masa maganin zafi aciwonsa bayan yayi wanka da ruwan dumi.sosai take jin zafin abinda Adeeb yayiwa Rashad,kalli yadda yaji masa ciwo kamar wani marar gata?lallai saita É—auki mataki,dan bazata yarda da wannan cin mutuncin ba.
Kallon Rashad tayi wanda yake É—an runtse ido idan ta shafa masa maganin
zafin.
"Haƙiƙa Adeeb yana wuri gona da iri masarautar nan,kaima fa ɗane ba bawa ba,dan me zaiyi maka irin wannan dukan?saikace ya sami yaronsa, haƙiƙa bazan amince ba ,dole mai martaba ya shiga maganar nan,kuma wllh nayi alƙawarin sainaga bayan Ammi ,dan kuwa ita ke daure masa....yake abinda yaga dama.haka kawai an maidamu kamar wasu matasa iko agida,bazai yiwuba ,sam bazan laminci wannan abun ba" Amma ta kai ƙarshen zancen ta cikin fushi sosai da bacin rai.
Kallonta Rashad yayi shima cikin ɓaci rai,yana mai faɗin "amma kibar wannan maganar atsakanin mu ,kar ki bari mai martaba yaji,dan kuwa da kaina zan ɗauki mataki,wllh saina yi masa abinda sai yayi dana sanin aikata min wannan abun akan wata bare,ke dai kawai ki zubamin ido" Rashad ya faɗa yana mai kitsa abubuwa cikin ransa.
Wannan kenan.
Baƙi sun fara zuwa ta ko ina ,manyan sarakai da yan siyasa na ƙasar Misra, ko ina acikin gidan jama'ane keta kaiwa da kawowa,dan kuwa yau ne za'a gudanar da ƙayatacciyar walimar murnar dawowar prince Adeeb gida,daga ɓangaren Amma baƙi sunzo sosai,matan sarakuna na ƙasashe da dama,da matan manyan masu kudi da yan siyasa.dan haka hadimai sai kaiwa da kawowa suke dan kula da baki.
Yayin da bangaren Ammi kuwa ,ba magana ,dan kuwa itace uwar taro ,mai gayya mai aiki kenan,sosai ta tara manyan matan sarakuna dana yan siyasa ,da matan manyan attajiran larabawa,kai harda na ƙasashen Afrika .
Ammi taci uwar kwalliya cikin kaya na alfarma ,tayi ado da gwala-gwalai sai ƙamari take bugawa tana cikin matan data gayyata suna ta hira kafin a fara gudanar da taro.
Busar sarewace ta karfe fadar ,alamun da ke nuna wasu baƙin sarakan sun sami hallara,murmushi Ammi tayi dan kuwa ta gane busar ko ta wace ƙasace, ba kowa bace bace ƴar uwarta gimbiya Zulaihat ,wacce ke auren Sarkin gana.dan haka cikin farin ciki ta mike tare da cewa matan tana zuwa.kafin ta fice zuwa farfajiyar da aka ware musamman dan tarbar baƙin ta ,gurine ƙayatacce wanda yasha ado ,aka wadatashi da komai na jin dadi.
Tana tafe haɗimanta na biye da ita ,murmushine ɗauke akan fuskarta wanda ya ƙara ƙasa ta fuskar tata.
Wata farar mace ce kyakyakywar gaske ta fito daga cikin lafiyayyar motar da aka bude,masha Allah matar ta ko ina ta hadu ,fuskarta ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa,idanunta na kan Ammi rungume juna sukayi cikin farin ciki,ammi keyiwa matar Barka da zuwa.
Wasu kyawawan yara ne su biyu suka fito daga É—aya gefen,da ala'ma yaran tagwayene duba da yadda suke tsananin kama da juna.yaran zasu kai shekara goma ,saidai yanayin jin dadi da hutu,yasa zaka yi tunanin sun wuce hakan,suna sanye da kaya iri É—aya ,cikin shiga ta ya'yan sarakai.
Gurinsu ammi suna nufo cike da murna suka rungume Ammi,ita cikin jin daÉ—i ta rungumesu tare da sunbatar gishinsu,tana mai faÉ—in," yazeed and zayyad my children" ammi ta faÉ—a tana shafa kansu.
Part É—in ammi suka nufa gaba É—ayansu,cike da murna.
Adeeb ne zaune bakin gado yayin da tareeÆ™ ke gefensa ,yana tashi shiryawa,shi dama Adeeb baida aboki ,tareeÆ™ kaÉ—ai ne abokinsa kuma yaronsa,dashi yake ko wace irin shawara ,dan haka ya zuma suna zaune suna shiryawa,dan Adeeb baya barin kowa ya shigo masa part É—insa, shi fa akan dole yake abubuwan masarauta, dan sam sarauta bata burgeshi, yafi son kasuwancinsa.
Kallon tareeƙ yayi yana mai faɗin,"tareeƙ nufa na gaji da wannan shirin Please ya isa haka" ya faɗa yana ɗan kwaɓe fuska cikin salon shagwaba.
Murmushi tareeƙ yayi yana mai ɗaurawa Adeeb wani agogon azurfa ahannunsa kafin yace " yallaɓai yaufa dole kayi haƙuri ,dan kuwa saikayi shiga irin ta yarima sosai " tareeƙ ya faɗa yana ɗan danne dariyarsa ganin yadda Adeeb ya wani marairaice kamar zaiyi kuka.harararsa Adeeb yayi yana mai faɗin" dariya ma zakayimin ko?ai kaima mugune nasani ,shiyasa kake ta lodamin kaya haka kamar wani dan dako"
Dariya sosai tareeÆ™ ya sanya yana mai faÉ—in" yallabai kasan fa yau sauka gaji da ganin yan mata ,dan zasu yi ta kawo maka hari ne,Suda iyayensu,dan haka dole kayi adon da zaka rikitasu" tare ya faÉ—a yana kallon yanayin Adeeb É—in.
HaÉ—e rai Adeeb yayi yana mai gwabe baki yace " aikuwa zasu wahalar da kansu ne kawai,dan duk ba wacce zata burgeni acikinsu" ya faÉ—a yana mai mikewa tare da gyara kwalar rigarsa.
Murmushi tareeƙ yayi kafin yace "amma yallaɓai yau idan Madam ta ganka zaiyi wahala ta gane ka ,dan kuwa kayi matuƙar kyau Masha Allah,yau lafiya ayarimanka sai" tareeƙ ya faɗa yana mikawa Adeeb wani takobi ,wanda ke matukar gyalli da ɗaukar ido.
Murmushi ne yakub cewa adeeb,jin tareeÆ™ ya ambaci Madam,kallon kansa ya karayi cikin madubi,masha Allah,ko aljanu ya kalli Adeeb to tabbas dole saiya yaba kyau da Allah yayiwa adeeb.
" Kasan bata da lafiya ma,kuma bazata je gurin taron nan ba,zata zauna tare da nanny ,acikin gida,dan haka muyi sauri muje In dubawa sai mu wuce " Adeeb ya faÉ—a yana mai rataya takobin.
Murmushi tareeƙ yayi yana mai jin dadi cikin zuciyarsa,tabbas hasashensa yana neman zama gaskiya,dan kuwa ya kula Adeeb ya faɗa kogin SOYAYYA ,wanda hakan yayi masa daɗi,fattu itace daidai da Adeeb." Yallaɓai kayi kama da mai son zuwa ganin budurwarsa fa" tareeƙ ya faɗa yana ɗan sosa kansa.
Ƙeyarsa adeeb ya ɗan buga kafin yace " ka manta dai ba budurwa ba ,mata zakace ,kuma kasan hakkin ta ne induba lafiyarta ,kafin na sawwaƙe mata,iya muje" Adeeb ya faɗa yana mai kamo hannun tareeƙ.
Murmushi tareeƙ yayi yana mai cewa " zaka dawo hanya ma yallaɓai" ya faɗa cikin zuciyarsa.
Suna fitowa kuwa hadiman da suke ƙofar part ɗin suka ɗauka kirari da bushe bushe irin na larabawa,runtse ido Adeeb yayi cike da damuwa,dan shikam wannan bushe bushe baya so ,dan dai ba yadda zaiyine.
Cikin takun izza da isa yake takawa ,tareeÆ™ yan gefensa sai hadiman dake binsa baya suna busa.
Kai tsaye ya wuce part É—in ammi,da gudu su zayyad suka taho suka rungume ,Adeeb cike da murna ,dan kuwa sun saba dashi sosai.dagsu yayi daya bayan É—aya yana dariya ,
Gimbiya suhaimat ma cike da murmushi take kallon Adeeb,yaron yana burgeni sosai,yana da nutsuwa ga don yara,har ƙasa ya durƙusa ya gaida gimbiya suhaimat,da amminsa, sosai ammi ke yaba kyan da Adeeb ɗin yayi,wani lambu ta ɗauko na na zinare ta sanya masa hannunsa ,tare da wani turare mai kanshi daɗi.
Murmushi yayi tare da mata godiya sosai,kafin ya É—an juyo yana kallon gimbiya suhaimat,haka kawai yaji gabansa ya