Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TIF DA TAYA Horror STORY Complete Hausa Novel by MRS Sadauki

Author :  MRS SADAUKI Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 39K words

je ya ɗauko ta ya miƙawa yarima.Ya karɓa tare da soma shafar kanta,“zan je na duba na gani in sun gama shirya wurin taron” Ali ya faɗa tare da ficewa.


Yarima ya miƙe tsaye tare da zuwa bakin window yana kallon yadda ake ta kai komo cikin masarautar.Ko ina yayi kyau,hatta dawakai an yi musu ado na sarauta .Dokinsa wanda yake hawa a duk lokacin da zai fita yayi wani irin kuka,tantabarar hannunsa ta fizge tare da fita a guje tana kaɗawa yarima iskan fukafukinta da sauri ya lumshe ido kafin kuma ya ware su yana kallon yadda ta je ta hau kan dokin,duk wannan ɗin ma bai sa ya zargi wani abu ba kawai murmushi ya yi tare da fita.

Masjid ya fara zuwa,bayan an gama sallah ne duk aka dugunzuma zuwa wurin da aka ware domin gudanar da shagalin bikin baikon.

Zinare sarki ya ware masu yawa ya bayar matsayin kyautar mun gani muna so.Ayyub wanda ya kasance mahaifin gimbiya A'ishah da matuƙar farin ciki ya shaida wa dukkan taron jama'ar ya bai wa yarima damar auren ƴarsa,duk sai aka yi kabbara tare kuma da yin addu'o'i kafin a fita zuwa can inda za a yi wasar dawakai.




Ta madubin tsafi Dadda ke kallon komai,tun lokacin da aka yi shelar yin baikon ta shirya baƙin tsafi mai ƙarfi ta tura domin hallaka yarima.Ita dai gimbiya A'ishah cike take da farin ciki duk gajiyar nan ta jiya sai ta neme ta duk ta rasa,duk da cewa kuwa ta sha bacci sosai sai wuraren goma na safe ta farka.A bakin mahaifiyarta kuma ta ji abin da ke faruwa,sosai ta so a ce ta fita ta ga yadda komai ya wakana sai dai hakan haramun ne a masarautarsu zuwan mata a irin wannan taron.



Cikin rangaji ta ƙaraso ta zo ta yi tsaye ita ma tana kallon yadda ake wasar tseren .Wani irin murmushi ya suɓuce mata lokacin da ta ga yarima Naslam ya je kusa da dokinsa za su yi wasar tseren shi da wanda ya yi nasara akan dukkan dakarun da aka tsara wasar da su.Ita ma Dadda nata murmushin ta saki tana jin cewa saura ƙiris burinta ya fara cika don ta jefa kibiyar tsafi akan dokin yarima saboda in ya hau shi sai ya masakance.

Yarima ya hau kan doki yana mai ambaton sunan Allah tare da yin kabbara,Dadda ta ɓata fuska tana mai ɗan satar kallon gimbiya A'ishah wacce har yanzu murmushi ya ƙi barin fuskarta.


“Dadda dube shi ki ga yadda yake da ƙwarjini da cikar zati, wannan shi ne mijin A'ishah ”


“Haka ne ki yi fatan Allah yasa ya ci gasar kar ya kwabsa abin ya zama abin goranta miki” Dadda ta faɗa tana mai shafar madubin haɗi da yin wani surkulle daidai nan su yarima suka fara gudun.Ƙafar dokin ta ƙure da ido ta na shirin aika masa wata gubar tsafin kawai sai ganin bakin tsuntsuwa ta yi ya caki madubin ya tarwatse.

A tare suka ja ba,kafin su kalli juna.Da wani irin gudu kuma gimbiya A'ishah ta fita don jikinta ya bata babu lafiya,mayafinta ta ja ta rufe fuskarta lokacin da ta isa filin sukuwar.

Yarima NASLAM wanda ya lashe wasar tseren dokin ya juyo yana kallon inda take a tsaye,suka haɗa ido da sauri ta sunne kai tana wani murmushi kafin ta juya da sauri ta koma.Ya ja numfashi yana jin a ransa ya yi dacen mata.




An ɗauki tsawon lokaci kafin Ummilo ta farfaɗo wannan karon ma tana yin wasu kalamai a cikin Yaren da ban fahimci me take nufi.


“Alhamdulillahi lazhi ahayana ba'ada ma'amattana wa'ileyhi nushur” ta furta tare da ware idonta a kaina,na sakar mata murmushi na ce “sannu Ummilo” ba ta amsa ba sai martanin murmushin da ta maido mini tana mai shafar gefen fuskata kafin kuma ta miƙe ta fita.Haka na take mata baya sai na ga ta shiga banɗaki,can kuma ta fito ta soma wanke hannuwa da baki da fuska da hannuwanta hatta kai da kunne sai da ta shafa haɗi kuma da wanke ƙafafu.

Mayafinta ta gyara kafin ta zo ta fara yin wata irin bauta da ban san ta mece ce ba,ni dai ido kawai na tsura mata da na ga ba ta da niyyar idawa kawai na je gun baby Mila na ɗauke ta dama tun ɗazu ta tashi.Madara na soma bata tana sha tana kallona cikin ido, murmushi na saki ina jin sonta na ratsa ni.


Banah wanda tun bayan abin da ya faru ya koma can ƙofar gida yayi tsaye,sai yanzu ya shigo yana mai tambayata “mene ne can Ummilo ke yi?”

“Ina kifin har yanzu ba a gama dafawa ba?” na tambaye shi ,don sau tari in yayi mini tambayar da raina bai so ba nuna masa nake yi kamar ban ji ba sai na ɗauko masa wani zancen.

Fita ya yi ba tare da ya ce mini komai ba,can kuma sai ya dawo riƙe da kwano yana tiriri.Kamshin kifin ya daki hancina,nan take yawuna ya tsinke sai na shimfiɗe Mila na karɓa na soma ci shi kuma Banah yana aukin kallona.Ina gama ci na ji wata kasala ta rufe ni,sai na kwanta ni ma sai a lokacin kuma Ummilo ta shigo.

Banah ya ce “ga kifi nan da Naomi ta rage ki ci”

Da fara'a kuwa ta karɓa tare da gyara zama ta sa hannunta,sai dai fa ta gagara ci sai yamutsa fuska take haɗi da yunƙurin kai shi bakinta.Can dai ta haƙura tare da ajiye kwanon tana mai girgiza kai ta ce “in na ci wannan ai tamkar na cinye kaina ne,a'a sam maita ai ba hauka ba ce da zan ci jinsina ”


Banah ya ƙanƙance ido yana kallonta kafin kuma ya fice ya bar mu.Maƙoshina ne na ji yana wani irin zafi kamar ana hura wuta,murya kamar ta mai koyon magana na ce “Ummilo sanyi nake ji ki rufe ni” sai kuwa ta miƙe ta ɗauko bargo ta luluɓa mini.Daga wannan kwanciyar ban ƙara farkawa ba sai washegari da zakara ya fara cara,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na yunƙura zan tashi sai dai na kasa sakamakon bayana da na ji ya riƙe kafaɗata ta ƙara nauyi.


“Banah?” na kira sunansa kasancewar ni da shi ke kwana a ɗaki ɗaya,Ummilo kuwa cikin jerin ɗakunan da aka yi daga baya take kwana ita da Mila.

Shiru ban ji motsinsa ba,sai na ƙara yunƙurin tashi a wannan karon gangar jikina ta baro shimfiɗar sai dai na gagara tsayuwa kan ƙafafuna na faɗi kwacaaa.Jeren kwanukan da ke ɗakin duk ya baje,ƙarar ta jawo hankalin Ummilo ta shigo tana tambayar lafiya sai dai muna haɗa ido da ita ta ɗau haske.Da sauri ta zo ta taimaka mini na miƙe tsaye tare da riƙe ta gam,murya na ɗan rawa na ce “ki kai ni banɗaki na yi wanka” ita ce ta kai ni,sannan kuma ba ta fito ba sai da ta yi mini wanka.Bayan ta saka mini kaya sai ta miƙo mini wani icce ta ce na riƙe,na karɓa ina jin ƙusumbina da ya ƙara girma ya rinjaye ni na yi mini wani motsi.....


My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[13/04 09:45] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

Daga yau discount ya ida.
Last free page

10


Wata rusunawar dole ce ta zo mini saboda girman ƙusumbina ya wuce a yi kwatance sam tsayuwa ko tafiya babu sanda ba zai yiyu a gare ni ba.A haka na fito daga banɗakin ina jin wasu canje-canje na daɗa ƙaruwa a jikina,ban zame ko ina ba sai a ƙofar gida inda mutane birjit ke a wurin dukkansu kuma a ƙarƙashin ikona suke.Tamkar sun ga ubangijinsu haka duk suka tsaya da abin da suke yi suka zube ƙasa tare da yin kwanciya suna yi mini wani irin kirari da ba a taɓa yi mini shi ba.Idona na ƙanƙance ina kallon Banah da ke can ɗan nesa da ni yana wani irin murmushi da ban san mene ne ma'anarsa ba,don ko kaɗan ban zargi cewa a cikin kifin da ya bani na ci ba ne wannan girman ƙusumbin ya ƙaru.



“Sabbin dokoki sun sauka,don haka al'ummar gari ku kasance cikin shiri ga dukkan abin da shugaba za ta zartar” Banah ya faɗa yana mai takowa yana doso inda nake hannunsa riƙe da kwari da baka.
Sai da ya zo dab da ni sannan ya saita kibiyarsa a sama yana mai furta ɗalasiman tsafi,ji kake shuuu kafin wata wuta ta baje a sama.Babu kuma jimawa sauran jama'ar gari suka fara ɓullowa ta kowace kusurwa,tuni wurin ya ɗauki harama ya cika tanƙam.Sai kuma a lokacin ne na soma yin magana,“daga yau an zartar da yin hadaya duk ƙarshen mako,ruhikan ruwa su ne ke da alhakin zaɓar wanda suke so ko dai mu ɗauke shi mu bayar ko kuma su da kansu su kira mutum zuwa can domin ɗaukar ransa.Abu na gaba shi ne duk wani jinjiri da za a haifa sai an kai shi bakin kogo uwa gijiya ta saka masa albarka tare da ƙa'ide masa adadin shekaru ko watannin da zai yi a duniya”


Yanayin fuskokinsu duk sun nuna ba su ji daɗin wannan sabon tsarin ba,sai dai babu wani mai zarrar yi mini magana duba da irin ƙarfin ikon da ya ƙara hawa kaina ba tare da ni kaina na shirya masa ba.


A haka aka watse na koma ciki na tarar da Ummilo a zaune ta yi uban tagumi.Tana ganina ta miƙe tsaye tare da nufo ni,“na tuna wace ce ni ” shi ne abin da ta furta mini.Cike da jin daɗi na ce “kin tuna? Kai wannan babban abin farin ciki ne amma ya na ga ba ki murna?”


Idonta ya kawo ruwa tana mai cewa “na fito a yankin da aka haramta maita da kuma tsafi,ba tare da shuwagabannin sun yi la'akari cewa ba babu wani babban tarihi da magabatanmu suka shuɗe suka bari kamar Magic,ita Maitar ma ba ta fiya ƙarfi ba. Surukina kafin mutuwarsa ya yi matuƙar ƙoƙarin wurin ganin ya daƙile duk wata baƙar shirka,sai dai abin takaici Mayun ne suka haɗin gwiwa wurin kai shi barzahu.Wannan ya fusata mijina har ta kai shi da yin wani tsari shi ne kafa masarauta,yasa an gina babban wuri tare da yin shelar duk wanda ya shirya karɓar addinin gaskiya to ya shigo a cikin sabon ginin da aka yi.Ta wannan hanyar ce aka yi walƙiya aka gano mayu da matsafan cikinmu,sai ya soma yaƙarsu har ya yi nasara a kansu.Sai dai abin da bai sani ba ita maita bibiyar jini take yi,ga shi dai ya kashe tushenta amma bai cire inda ta yabanya ba.Sannu a hankali lokaci na tafiya mace-mace ya fara yawaita a daular,a bisa binciken wani mai bayar da magani ya gano cewa cutar maita ce sai kuma aka ƙara ƙarfafa tsaro.Tun ana yi wa mutum afuwa in an kama shi da cutar maita har aka zo zamanin yarona inda ya yanke ɗanyen hukuncin cewa duk wanda aka kama da laifin maita ko tsafi kisa ne kawai” tana kawowa nan ta yi shiru tare da kamo ni tana cewa “zo ki zauna hakan za ki gaji sosai,ya kamata ma Banah ya nemo miki sanda mai kyau”


Kan kujerar da aka sassaka da icce ta zaunar da ni kafin ta ci gaba da bani labarin.

“Mahaifin matar ƙanen mijina shi ne mutum na farko da ɗana ya fara cirewa da hannunsa saboda laifi mafi muni da ya aikata ya kashe mahaifan hadiminsa wanda ya ɗauka tamkar amininsa.Ƙarfin wannan raɗaɗin ya saka ita kuma matar ƙanen mijin nawa ta ɗauki tsanar duniya ni da ɗana ta ɗora mamu” nan ɗin ma shiru ta yi tana kallona tsakiyar ido da dukkan alamu akwai wani sirri mai nauyi da take son sanar da ni wanda baki ba zai iya furtawa ba.


Ta idonta kuwa ta shaida mini cewa “ni mayya ce! Ina ɗauke da kambun Maitar prophecy” sai kuma ta yi saurin janye idonta daga cikin nawa kafin ta je da sauri ta shige ɗakinta.Na lumshe idona tare da buɗe su kafin na yunƙura dakyar ina dogara sanda na take mata baya.


A zaune na tarar da kan shimfiɗarta,na ajiye sandar hannuna ni ma na zaune tare da kamo hannunta.Sai ta ɗago ta dube ni tana wani irin murmushi da ya fi kuka ciwo kafin ta ce “ban taɓa yin maita ba,ban taɓa cin ɗan wani ba kawai dai abin da na sani wani lokacin ina rikiɗa na zama kifi a irin haka ne har ita Dadda ta ganni cikin wannan siffa shi kenan ta je ta sanarwa sarki ai ni ma mayya ce.Ba tare da maganar ta fita waje ba aka titse ni sai na faɗi gaskiyar magana,in kuma na yi shiru na ƙi faɗa gobe gaban al'ummar gari za a yanke mini hukuncin kisa bayan an tabbatar shi ne kawai na yanke shawarar bin dare na gudu.Amma duk da haka bai ishi Dadda ba sai da ta jefe ni da baƙin tsafi ta haukata ni”


Na ce “don me yasa kika gudo kika bar ahalinki? Me yasa ba ki zauna ba ki sanar da su babu wata baiwa a duniyar nan da ta wuce maita? In ma ba ki son a sani ai sai ki ɓoye kayarki ”


Kai ta girgiza mini tana mai cewa “akwai wani garin magani da ake shaƙawa mutum a hanci muddin yana da ɗigon maita a jininsa to zai bayyana cikin ɓoyayyar siffarsa ne ya dinga tonawa kansa asiri”

Na ja dogon numfashi kafin na ce “shi kuma yaronki fa,kin yi tunanin halin da zai shiga bayan tafiyarki? Me yasa ba ki taho da shi ba?”

Wani murmushi ne wannan karon ya suɓuce mata bai bayyanar da tsantsar farin ciki da dukkan alamu tana mugun son ɗan nata.Ta ce “Ba fa yaro ne ƙarami ba,ko a lokacin da na bar masarauta ya haura talatin da ɗaya kawai dai a idona ne nake ganinsa ƙanƙane”

“Me sunansa?”

Kai ta girgiza cike da kunya tana mai cewa “a al'adarmu ba mu faɗar sunan ɗan fari, wannan yasa na yi masa laƙabi da Noor”

Samun kaina na yi ni ma da yin murmushin kafin na ce “me Noor ɗin ke nufi?”

“Haske!” ta bani amsa.

Na ce “zan so na gansa kuwa,da na ji daɗi sosai ni ma zan yi babban yaya” ina faɗar haka sai ta ɗan ƙara matsawa ta jawo kaina ta ɗora kan cinyarta,sai ta cire luluɓin kaina ta soma warware manyan kitson kaina tana mai cewa “wata rana za ki gansa ai ”

“Yaushe kenan?”

“Ranar da lokacin komawa ta can ya yi,ai zan tafi da ke ne ki ga yayanki in ya so sai Banah ya tsare miki daularki ”

Shiru duk muka yi,bayan ta gama warware kitson sai kuma ta ɗebo ruwa ta zuba yaɗo ta wanke mini dogon gashina sannan ta ƙara yi mini wani kitson mai kyau duk da ƙwaya biyu ne kacal amma ya yi kyau.Wunin ranar ne muka ƙara yin wata shaƙuwa ta musamman ni da Ummilo ta dinga bani labarin Yaya Noor lokacin da yana ƙarami da kuma abubuwan da yake so da waɗanda ke saurin saka shi fushi.


“Wane abinci ya fi so?” na samu bakina da tambaya.

“Gurasa da zuma,yana matuƙar son cin gurasa yana dangwala ta a cikin zuma” ta bani amsa tana murmushi.

Na ce “ni ma ina son zuma,kullum in na je farauta sai na je na nemo ta na sha”

“Wato yayanki kika ɗauko wajen son zaƙi.Bani labarinki,ina iyayenki suke?” Ummilo ta faɗa .

Wani iri na ji duk babu daɗi kafin na ce “dukkansu sun mutu,shi Abbana ban san shi ba ita kuwa Maa a ranar da na karɓi prophecy ɗina ta yi gushewa.Ina sonta sosai,ina jin kewarta a kodayaushe samunki ne ya maye mini gurbinta nake jinki tamkar ke ce ita” na ƙarashe faɗa hawaye na silalo mini masu zafi.Na ƙanƙame ƙafar Ummilo ita kuwa ta shiga shafar kaina haɗi da rarrashina kafin ta ce “ina matsafiyar tarihi sai yaushe za ta zo?”

“Ta ce na yi miki sannu da jiki ma tun jiya ”

“Ina amsawa,ina ne gidansu?”

“Ita ma ba ta da iyaye mahaifinta ya rasu,mahaifiyarta kuma an damƙe ta”

“Ayya ki ce ta dawo nan wurina sai mu zauna tare” Ummilo ta faɗa ,sam ban ji zan iya yi mata muso ba hakan yasa ba tare da na shawarci Banah ba na ƙara aika saƙon wasiƙar tsafi zuwa ga Deborah ba ta kuma ɓata lokaci ba ta zo har da ƙullin kayanta.A ɗakin Ummilo na yi mata masauki ,a ɗan wunin da muka yi a tare sai kuma muka ƙara ɗinkewa ni da ita muka manta mun taɓa samun saɓani.


Da dare muna zaune bayan mun gama cin abincin,Ummilo na ririga Mila da ke yin rigima ta ƙi yin bacci sai ta soma rera waƙa wacce ta saka mu duk nutsuwa.Ba da Yaren da muke magana ba ne,haka kuma ba Yaren tsafi ba ne wani yare ne can daban da ita kaɗai ta san ma'anarsa amma sosai na ji daɗin baitin.Babu jimawa Mila ta yi bacci sai ta shimfiɗe ta tana murmushi tare da cewa “a duk lokacin da Noor ya fitine ni da kuka wannan waƙar nake rera masa ko kuma in ina son saka shi bacci”

"Amma Ummilo da wane yare ne wannan?” na tambaya,Deborah da ke rubutu cikin littafin tarihi ta yi karaf ta bani amsa da “Yaran serena ne,yare ne da halittun ruwa ke yi ita kuma waƙar suna yinta ne domin janyo wani ruhi zuwa gare su domin aiwatar da abin da suke buri”


Ido na tsura mata ina kallonta ta hasken farin wata,kafin na ce “ ta ya aka yi kika sani?”


“Ta ya ba za ta sani ba,matsafiyar tarihi ce fa” Ummilo ta faɗa .

Deborah ta yi murmushi tana mai cewa “tun jiya da na yi tozali da Ummilo na cika da mamakin me ya kawo Siren a nan”

Na ce “ai na lura da yanayin yadda kike kallonta,to sai da safenku zan je na kwanta” na faɗa tare da lalubo sandata na miƙe na shiga ciki.

Kan gadona na kwanta tare da yin shiru ina nazari,can sai ga Banah ya ratso rufin ɗaki ya shigo.Sam hakan bai kuma bani mamaki ba,illa kawai na mujiya da na zuba masa ina kallon yadda jikinsa ya ƙara rinewa kamar wanda ya fito daga cikin rijiyar kunama.
Gefen gadon ya zauna tare da miƙo mini wata ƴar kwalba ya ce “shafa mini”

7 / 13