Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TIF DA TAYA Horror STORY Complete Hausa Novel by MRS Sadauki

Author :  MRS SADAUKI Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 13

6K to 9K   out of 39K words

cewa babu wani sarki da zai gagare ni,ki sa a ranki ummarka tuni ta kuɓuta”

Muryarta na fitar da wani irin amo take cewa “ya ke shugabata in ba ki manta ba irin haka ne mahaifina ya tarar da wa'adinsa,silar zaƙulo bincike domin rubuta tarihi ya haɗu da wasu mabiya addini mabanbanta suka kashe shi a ƙarshe sai mahaifiyata ce ta maye gurbinsa domin ci gaba da rubuta littafin kudin binciken duniyar ruhaniya” tana kawowa nan da zancenta sai ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba da cewa “ina jin tsoron kar a ce ita ma Umma nata ajalin ne ya zo”


Kai na girgiza mata ina mai cewa “muddin ina raye hakan ba zai faru ba”

Rungume ni ta yi tana sauke wata irin ajiyar zuciya,yayin da ni kuma na shiga tunanin hanyar da zan bi na ƙwato Umma ɗin saboda a duniyar nan a halin yanzu banda wani masoyi da na fi so da ƙauna sama da Debora.Cikin hikima na mayar da ita cikin gida gabanin ni kuma na fita zuwa can cikin baƙin jejin garinmu mai cike da aljanai da fatalwa.


Cikin tafiyar rauni ta masu larurar ƙusumbi nake tafiya ana take mini baya,ko kaɗan ban san su wane ne ke take sawuna ba kuma ban jin tsoro ko fargaba wani abu.A haka na isa bakin wata iraciyar kuka mai zubin halittar mutum don da baki da hanci gare ta.Ina gama daidaita tsayuwata sai kuwa bisashin ganye suka fara zubowa a kaina kamar ana ruwa kafin ɗanye ƙwaya ɗaya ya faɗo a gabana.Ɗaukarsa na yi tare da tofa yawuna a kai,sai na soma juya ido babu jimawa yawun suka rikiɗa zuwa rubutu.Sai a lokacin na miƙawa itaciyar ganyen mai ɗauke da bayanin abin da ya kawo ni nan ɗin.Tafin hannuna na ji ya cika da wasu duwatsu,ina dubawa sai na ga suna sheƙi akan kowanne dutse an rubuta karlis .Ban yi jinkiri ba na nufi ɗaya daga cikin magudanar ruwa na je na yi tsaye ina kallon yadda ruwan ke a kwance sun nutsu ko motsi ba su yi.Dutse ɗaya na cilla ina sauraren yadda ƙararsa ya ratsa ruwan tare da soma yin gudu har zuwa inda nake son ya isa.


Ba a ɗauki wani lokaci ba wata iska mai sanyi ta soma kaɗawa tana fitar da wani ƙanshi irin na gawa.Can sai ga Maa ta ratso ruwa ta fito,fuskarta ta yi wani fari fat kana ganinta ka ga matatta ga kuma fararen kaya a jikinta.


Cike da soyayya na je da gudu na rungume ta,sai dai kamar na jimƙi iskan gas haka na ji babu wata alamar gangar jiki.Da sauri na ja da baya ina kallonta tana wani fitar da murmushi,wani irin tausayin kaina na ji wanda ko ranar mutuwarta ban ji shi ba.


“Me kike buƙata Nao?” don haka take kirana a duk lokacin da take shauƙi ko kuma take son isar mini ƙaunar da zuciyarta ke ƙumshe da ita.


“Maa shi kenan ba zan ƙara jin taushin gangar jikinki ba?” ita ce tambayar da na yi mata madadin na sanar da ita matsalar da ta kawo ni.


Ta ce “Naomi a zangon da nake na fita daga sawun duniyar bil'adama na koma cikin duniyar matattu,ki kira ni da ruhi kai tsaye”

Kallonta na yi,tabbas ita ɗin ruhi ce kamar yadda ta faɗa ɗin.Na kai hannu na shafi kumatuna da nake jin wani damshi,wanda na yi imanin cewa ruwan hawaye ne .Murya na ɗan rawa na ce “mahaifiyar Deborah ta faɗa hannun mugaye shi ne nake son sanin ta ya zan ceto ta?”


“Babu buƙatar yin haka,saboda ita ɗin ba kanwar lasa ba ce.Za ta iya fitar da kanta kar ki wani damu kanki” Maa ta faɗa .


Na ce “amma kuma ita ce da kanta ta aiko da takarda domin sanar da mu”


“Ta yi haka ne domin ku ci gaba da rubuta littafin bayanai ba wai don kawo mata agaji ba.Ki sanar da Deborah cewa lokaci ya yi da ita ma za ta ɗauki muƙaminta na rubuta tarihi kamar yadda mahaifinta ya karɓa gun mahaifinsa,ita kuma mahaifiyarta ta karɓa daga mahaifinta,yanzu kuma ƙaddarar littafin tarihi ta dawo hannunta” Maa na gama furta haka sai ta soma nitsewa cikin ruwa haskenta na tarwatse wa haɗi da disashewa.A gaban idona ta ɓata,na lumshe idona ina mai furta kalaman tsafi tare da buɗe su kuma a nan na tsinci kaina a ɗakina.


Deborah na kwance amma ba bacci take yi na.Kallonta na yi kafin a takaice na sanar da ita abin da Maa ta shaida mini,da wani irin sauri ta miƙe ta zauna tana kallona can kuma ta soma furzo da wani irin furuci sai na ji tsafin da take yi ba irin nawa ba ne yana da banbanci kamar yadda Hausar wani gari ba ɗaya take da ta wani garin ba.
Babu jimawa sai muka soma jiyo kukan jemage yana wani tsala shi kamar zai fasa gidan,a tare muka fita nan muka yi gamdakatar da wani baƙin jemage baƙi ƙirin da shi ga kuma wani irin girma na ban mamaki.

Kan ƙafafunsa ya sauka bayan ya cillo wani tsohon littafi ya dira a tafukan hannun Deborah.
Kallo ɗaya na yi masa na fahimci cewa shi ne wanda aka wakilta domin tsare littafin ya basa kariya.A hankali ya soma yin tsalle har ya isa gun Deborah,babban farcenta na ƙafar hagu ya kama ya fasa shi tare da soma shan jininta irin sosai ɗin nan don har sai da ta soma yin wani irin haske irin na rashin jini amma ko kaɗan ban yi yunƙurin tsayar da shi ba har sai da ya gama sha sannan ya tashi sama,sai dai bai yi wani nisa ba ya ɓace ɓat.
Sai a lokacin na je na kama ta na ja ta zuwa ciki na zaunar da ita,magani na ɗauko na soma rufe mata yatsan da shi wanda har yanzu yake ɗigar da jini.


“Ki kwanta ki huta na san kin gaji” na furta.

“Ki soma karanta littafin kafin ni na karanta miki ” ta furta tare da miƙo mini,kamar ba zan karɓa ba sai kuma na kai hannu na karɓi littafin na ajiye a gefe.Ido ta lumshe ta soma yin bacci mai kama da mutuwa,wanda na yi imani cewa a cikinsa ne za a miƙa mata wasu asirai da kuma power kariyar kai da kuma ta abin da aka damƙa mata amanarsa.


A cikin wannan daren ne na soma karanta littafin tarihi wanda ya ƙunshi rayuwar jarumai da kuma irin gwagwarmayar da suka yi fama a kai.Na samu sirrika dayawa,na yaƙi da kuma yadda ake sarrafa maita ta sigogi daban-daban.
Wannan littafin ya ƙara saka mawa zuciyata cewa duk inda babu magic to lalle babu rayuwa mai inganci, Magic shi ne komai na duniya a cikinsa ne za ka samu ƴanci da kuma gata.Rufe shi na yi tare da raɓawa gefen Debora na kwanta,ina lumshe idona na soma jin wani irin motsi a cikin kunnena tamkar ƙwaro na tafiya.Ƙara nutsuwa na yi sai na soma jin tamkar ana yi mini magana ne,amma ta ina? Ban sani ba.Ji na yi ana danne ni ana saukar mini nauyi,na furzar da huci mai zafi jin wasu kalmomi daga wata murya da ban san mamallakinta ba.


“ A duk inda kike a faɗin duniyar nan sai na nemo ki,ni ne nan zan kashe ki da hannuna ƙaramar matsafiya muguwa mai idanun maciji” muryar namiji ce amma ban san wane ne ba, sannan ban fahimci abin da yake nufi ba har ya ƙara yin wani furucin “ina ma ace annabi sulaiman bai yi wafati ba,da na roƙi alfarmarsa ya tura rundunar aljanu su gana miki azabar da ta fi ƙarfin tsafinki ”

Saurin buɗe idona na yi,ina mai tambayar kaina “wane ne kuma Annabi Sulaiman?” sai dai banda amsar wannan tambayar,in akwai wanda zai faɗa mini ita to bai wuce Deborah ba wannan yasa na kasa haƙuri na kai hannu na shafi fuskarta.Ta buɗe idonta tarau a kaina,sai dai babu ɗigon baƙi a cikinsu da alamu har yanzu ba ta dawo daga balaguron ruhi ba.

“Wane ne Annabi Sulaiman?” na tambaye ta,idanunta ne suka dawo normal nan take ta tashi zaune sannan ta bani amsa da cewa “ ya kasance ɗa ga Annabi Dawuda shi ma kuma annabin Ubangijin Ka'aba ne.Yana da matuƙar power don a tarihin annabawa shi ne kaɗai ya mulki mutane da kuma aljanai,sannan kuma yana iya yin magana da dabbobi da kuma jarirai waɗanda bakinsu bai buɗe ba.Ya yi mulki cikin hikima da adalci ga al'ummarsa”


Zuciyata ce na ji tana wani irin bugawa na jin bayanin da Deborah ta yi mini.Kamar mai tsoron sake jin wata buwayar na ce “amma me Annabin ke nufi?”


“Mutum mai isar da wahayi daga Ubangijin Ka'aba zuwa ga al'umma ” ta bani amsa kai tsaye.Ban ce mata komai ba sai tashi da na yi na fito waje ina kallon taurari ina kuma juya kalamanta.
Ƙofar gidan na ji ana bugawa,na je na buɗe sai na ga gungun matsafan garin ne da alamu sun fito maitar dare ne suka biyo.


“Ranki shi daɗe mun samu baƙuwar fuska a yankin nan,wani mutum ne maharbi mun tsince shi a wata gona yana bacci.Mun ɗaure shi da duk wata igiyar tsafi amma ta ƙi yin tasiri a kansa saboda girman tsafinsa wannan dalilin ne yasa muka zo zuwa gare ki” ɗaya daga cikinsu ya faɗa .

Raina a mugun ɓace na ce “me yasa ba ku kashe shi ba?”

Kallon juna suka yi kafin wani kuma daga cikinsu ya ce “ kamar dai yadda ya faɗa miki ɗin ne,tsafinsa nada matuƙar ƙarfi da dukkan alamu mutum ne na daban ko a duniyar ruhaniya”

Ban ce komai ba na yi gaba a fusace yayin da su kuma suka take mini baya.Tun kafin na isa gonar nake jiyo numfashin baƙin tsafinsa,ina isa ya yi saurin tashi tsaye muna fuskantar juna.Ɗan saurayi ne da ba zai haura shekara ashirin da takwas ba,sanye yake cikin kayan maharba ya rine gefen fuskarsa da baƙin abu yayin da kuma ƙirjinsa aka zana wata baƙar kunama.

Ban tsaya tambayar wane ne shi ba na kai masa farmaki,ya tare kafin kuma mu shiga masayar kalaman tsafi muna haɗawa kuma da yaƙin gangar jiki.Kamar yadda suka faɗa ɗin tabbas shi ɗin na daban ne,ban ida fahimtar haka ba sai da ya kai ni ƙasa ya saita kibiyar tsafinsa daidai idona.

Yana jan wani numfashi ya furta “kafin a farmaki baƙo a fara tambayarsa da wace aniya ya zo,duk waɗannan matakan tsaron na ruhikan ruwa da kika saka ba su iya tare ni na shigo yankin nan ba sai ke ce kike tunanin za ki hana ni yin abin da na zo yi?” shi abin da ya furta,amma duk da haka ban saurare shi ba na fito da wuƙar mahaifina na daɓa masa ita a ƙirji daidai kunamarsa yayi wata irin kururuwa da ta saka dajin amsa wa kafin ƙyafta ido sai ganin kunamu muka yi suna zubowa kamar ana ruwa.....
[08/04 12:12] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

05


Yadda baƙaƙen kunamun suka dabaibaye jikina shi ya fi komai ɗaga mini hankali,ga shi kuma masarafin tsafina ya ƙi aiki.Idona ƙurrr kan mutumin da na cakawa wuƙa yana tsaye ƙyam kan ƙafafunsa,yayin da kuma kunamun suka buɗe hannuwansu da alamu umarninsa suke jira su shiga harbata.
Tafin hannunsa ya buɗe ya soma yin furuci cikin Yaren tsafi wanda ya sha banban da nawa,a hankali duk kunamun suka yi ɓata dabo sai a lokacin na yunƙura na tashi zaune ina kallonsa cike da mamakin me yasa bai kashe ni ba kamar yadda na yi yunƙuri.


“Wane ne kai?” na tambaye shi.Bai bani amsa ba sai nuni da yayi mini da wuƙata wacce har zuwa yanzu tana nitse a cikin ƙirjinsa.A hankali na miƙe tare da zuwa na ciro wuƙar,abin mamaki sam babu ko da ɗigon jini da ya zuba illa kawai alamun an huda ƙirjin.


“Banah!” ya bani amsa,na maimaita sunan a bayyane kafin na ce “me ya kawo ka YANKIN MUTUWA?”

“Ke!” ya bani amsa kai tsaye,kallon ban gane ba na yi masa kafin na ce “ni kuma?”

Kai ya jinjina mini kafin ya ciro wata sarƙa da ke a wuyansa mai tambarin gumki ya miƙo mini,na karɓa tare da juya ta sannan na ɗago na dube shi.


“Ba ki ga komai ba?” ya tambaye ni.

“Me kake son nuna mini?”

“Duba da kyau dai” ya sake faɗa ,sai na nutsu da kyau nan ne na ga gumkin jikin sarƙar zanen mace ne da ƙusumbi a bayanta.


Na shafi ƙusumbin da ɗan yatsana,nan take ya kawo wani haske kamar an kunna ƙwan lantarki.Banah ya matso kusa da ni shi ma ya ɗora nasa yatsan kan nawa sai hasken ya ƙaru a hankali kuma muka fara yin sama ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka lula can cikin iska.


Mutanen gari ne suka fara fitowa,sai kuma suka shiga yin kiɗa da bushe-bushe yayin da wasu kuma suke rawa.Ban taɓa tunanin cewa wai hakan aure ne muka ƙulla ni da Banah ba sai da wasu ruhika suka bayyana a gare mu suka yi mana bushara da hakan tare kuma da ƙara mana power.

Sarƙar nan mai hoton gumkin mace da ƙusumbi ita ce kabancin sadakina,ita Banah ya saka mini a wuya kafin mu sauko ƙasa.


Gefe na koma ina kallonsa,ba mummuna ne ba amma kuma ba za a kira shi da mai kyau ba.A kallon farko za ka tabbatar da cewa shi jarumi ne a fagen tsafi,kumatuna da ya shafa shi ya katse mini ɗan guntun nazarin da nake yi a kansa.

“Tunanin me kike yi?” ya tambaye ni,da sauri na juya masa baya ina mai basa amsa da cewa “ ban san wane ne kai ba,daga ina kake kuma amma kai tsaye ka zo ka aure ni ba tare da neman shawarata ba”


“Naomi ba fa ni ne na tsara haka ba,allolin prophecy suka ga dacewar mu haɗu ni da ke domin mu cika alƙawarin da magabatanmu suka ɗauko”


Da sauri na juyo ina kallonsa na ce “to ka riƙe ni matsayin abokiyar aiki kawai” ina gama faɗar haka na soma tafiya cikin rangaji saboda yanayin larurata.Ina jin yana take mini sawu har muka isa gida,Deborah na tarar a tsaye kamar mai jiran zuwana.

Da ido ta tambaye ni shi kuma wancan na bayana? Na juya na dube shi da sauri ya ƙaraso ya gabatar da kansa ga Deborah sai na ga yanayin fuskarta sam babu annuri.


“Zo ina son yin magana da ke” ta faɗa tare da kama hannuna muka shiga cikin ɗaki.

“Ta ya aka yi ya zama mijinki alhalin tarihi bai nuna za ki yi aure ba a doron duniya?” Deborah ta tambaye ni tana wani tsure ni da ido.

Ni ma ɗin kallonta na tsaya yi saboda gaskiyar da ta fito daga bakinta wacce na san ita kanta ba san ta faɗe ta ba.

“ Ba zan yi aure ba?” na tambaye ta,sai a lokacin kuma na ga ta sha jinin jikinta tare da soma yin kame-kame .


“ Tun yaushe kika gano haka?” na sake jefo mata wata tambayar.

Ta yi ɗan ƙasa da murya tare da sauke idonta daga cikin nawa ta ce “tun ranar da Umma za ta bar garin nan zuwa neman tarihi a wasu guraren , ta shaida mini cewa ba za ki taɓa yin aure ba muddin alamomin prophecy sun bayyana a gare ki.Ita ce da kanta ta nuna mini tsanin nan da ke cikin ruwa,ni kuma na ja ki muka je”


Sosai na ji ɗaci har ƙasan raina jin wai ba zan yi aure ba alhalin a duniyar nan babu abin da na fi so kamar na yi aure na haifi yara.A daidai wannan lokaci ne kuma na ji wani abu game da Banah,ko da a ce auren bogi ne to zan karɓe shi ko ba komai dai za a kira ni sawun ma'aurata kuma zan haifi ƴaƴa.


“Ƙusumbin da ke gare ki ba zai taɓa barin maza su yi sha'awarki ba,in akwai waɗanda da za su so ki to ki sani mata ne ƴan uwanki ” Deborah ta faɗa tare da kamo hannuna alamun rarrashi.


“Wannan furucin naki duk ƙarya ne,kin faɗi haka ne saboda kin jima kina sha'awarta wannan dalili ne ma yasa kika tunzura ta har kika kai ta karɓa muƙamin iko alhalin wa'adin karɓarsa bai yi ba.Kin san cewa muddin Maa nada rai ba za ki taɓa samun Naomi ba” Banah ya faɗa yana mai shigowa ɗakin.


Kallon tsana Deborah ta soma binsa da shi kafin ta ce “muddin ina raye ba zan taɓa bari ka cutar da Nao ba”

Ya yi wani murmushi kafin ya ce “na gode da tunatarwa ” sai kuma ya maido dubansa gare ni yana jefo mini kallon so da ƙauna ya ce “ ki sa a ranki Banah yana sonki kuma zai zauna da ke ko da kuwa dukkan jikinki ciwo ne”

Wata ajiyar zuciya na sauke jin furicinsa ,kafin na dubi Deborah na ce “ba zan so ki tsani Banah ba saboda shi ɗin murfin rufin asirina ne.Deborah ki sani zuciyata ba za ta taɓa lamunta rashin miji ba”

Kai ta girgiza mini tana mai cewa “Banah ba mijinki ba ne,in ma dai akwai shi to ba na ce a jinsinmu ba ne don kuwa tarihi bai nuna hakan ba”

Da sauri Banah ya zo ya shiga tsakiyar mu yana mai ɗan ture Deborah ya ce “dama ba tun yau matsafan tarihi ke ƙirƙirar ƙarya ba domin cimma manufarsu” kallona ta yi,sai na kawar da kai ita kuwa da sauri ta fita.





“Ba zan taɓa lamunta ki auri ɗan maƙiyiyata ba,ki sani cewa ko bayan raina kika auri Naslam ban yafe miki ba“ Dadda ta faɗa tana yi wa A'ishah wani mugun kallo.

“Ki haƙuri Dadda amma ina son yarima fiye da raina,ki sani cewa in kika hana ni aurensa to tamkar kin yi mini shamaki da duk farin cikin duniya” A'isha ta faɗa tana hawaye.

Dadda ta yi mata mugun kallo kafin ta ce “da dukkan alamu har yanzu ba ki warke daga cutar haukan naki ba,ɗan matsafiya kike sha'awar aure ki haɗa zuri'a da shi?”


Ta dubi mahaifiyar tata da jajayen idonta kafin ta ce “ Dadda babu wanda ya tabbatar cewa Ummi Naslam na yin tsafi,kawai ƙage aka yi mata wannan dalilin ne ma yasa ta bi dare ta bar masarautar nan”


“Wato ƙage na yi mata? Don ubanki da idona na gani tana tsafi.Tashi ki ɓace mini ko na sabauta ki ” ta ƙarashe cikin tsawa,da wani irin sauri kuwa

3 / 13