Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

TIF DA TAYA Horror STORY Complete Hausa Novel by MRS Sadauki

Author :  MRS SADAUKI Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 39K words

“wane sarki?”

Kai ta girgiza sai kuma ta soma yi wa jaririn wanka,ta saki murmushi ta ce “mace ce ashe” sai ta fito da ita daga cikin ruwan,ta cire uban kallabin da ta yane kanta da shi ta saka jaririyar a ciki.

“Wace ce ke?” na tambaye ta.

“Ni kaina ban sani ba,amma sai nake jin tamkar an aiko ni nan ne saboda isar da wani saƙo” ta bani amsa tana mai ɗago kai ta dube ni.Idona ya sauka kan goshinta nan na ga irin tabon nan da ke a goshin NASLAM ita ma yana fitar da haske sai dai bai cutar da ni ba,hakan kuma sai ya yi mini daɗi na ji a raina cewa ko da a ce ita ma wannan Ubangijin Ka'aba take bauta ma zan iya zama da ita.





Wuraren ƙarfe tara na safe daular abu NASLAM ta samu wani rikitacen labari.Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya yarima ya miƙe kan ƙafafunsa bayan ya yi wanka da magani ya kuma sha a cikin shayi.
Cikin tafiyar jarumta ya soma ratsa dakarun har ya isa inda Sarki ke tsaye yana jawabin yadda komai zai kasance,kamar kuma yadda Sarkin ya tsara jakariya Ali ne zai jagoranci tafiyar.


“Zan tafi ni ma don haka a shirya dokina” ya faɗa yana mai kallon mahaifinsa cikin ido.Sarki ya kawar da kai,don ya san ko da a ce ya yi yunƙurin hana shi ba zai ji ba.
Haka duk suka fito kowanne ya hau doki,da yarima zai hawa kan nasa sai da jakariya Ali ya taimaka masa amma a haka suka tafi.

Tun a bakin ƙofar shigar garin suka fara cin karo da kayan tashin hankali,babu shiri yarima ya diro yayin da kuma jakariya Ali ya soma take masa sawu.
Gawarwakin mutanen da aka kashe,Ali ya kalla sai ya ga duk kusan kalar mutuwar iri ɗaya ce.Ya kai hannu ya damtsi ƙasa sannan ya kai kusan hancinsa ya sunsuna,yarima ya dube shi tare da cewa “me ka fahimta?”

“Farmakin Mayu ne” ya basa amsa,ran yarima ya ƙara ɓacewa amma a haka suka ci gaba da duba ko ina har suka shiga gidan da matar nan ta haihu.

Cak jakariya Ali ya tsaya yana kallon ustaza Jamila,wacce ta bayar da dukkan lokacinta domin yin hidima ga addininta.Yarima ya ƙarasa yana mai cire rigarsa ta sarauta ya luluɓe ta,tare kuma da baiwa dakaru umarnin a ɗauke ta a kai ta can masarauta tun yanzu ba sai an jima ba......
[10/04 08:51] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

07


Ustaza Jamila ƙanwa ce ta jini ga jakariya Ali,mijinta ma ya mutu ne a wajen yaƙin haɓaka musulunci sai ga shi ita ma ta mutu wurin da'awar jawo hankulan waɗanda ba musulmi ba.Kamar yadda tsarin masarautar yake,suna aika maza da mata garuruwa don koyar da mutane karatu.


Yarima NASLAM ya dafa kafaɗar jakariya Ali yana mai cewa “ dukkan rai zai ɗanɗani mutuwa,ka sa a ranka lokacinta ne ya yi.Mu ma muddin namu yayi babu makawa a duk inda muke mutuwa za ta riske mu”


Idon Ali sun kaɗa sun yi ja sosai,muryarsa ma cikin wata irin sarƙaƙiya take fita.“Na yi imani ga Ubangijin Ka'aba,dukkan wata ƙaddara mai kyau da akasinta daga gare shi take.Sai dai babbar damuwata ɗaya ce ,cikin jikinta sam babu shi a yanzu hakan yana nufin kenan ta haihu in kuma ya tabbata haka ina jinjirin yake?”


Shiru yarima Naslam yayi na wani ɗan lokaci kafin ya ce “a duk inda yake Ubangijin Ka'aba ne zai tsare shi,ka dai kawai ka sa kyakkyawan yaƙini ga ubangijinka ” kalamansa suka yi tasiri a zuciuar jakariya Ali, wannan ya basu damar ci gaba da binciken ko ina.


Bayan sun gama haka suka haƙa rame aka rufe sauran kafin su juyo su dawo masarauta inda Sarki Haroon da sauran al'umma ke dakon jiransu.

Suna shigowa sarki ya je ya tarbi yarima tare da soma tambayarsa abin da ke faruwa.

“Farmakin Mayu ne,duk sun kashe mutanen gari da alamu kuma sun tafi da wasu.Babban baƙin cikin shi ne ba su bar wani sawu ba da zai sa mu gane ta ina suka fito ”

Barham da duk ya ji abin da yarima ya faɗa sai ƙara matsawo yayi yana mai cewa “a yadda ka yi bayanin ya tabbata cewa wannan rundunar Mayun ta samu jagoranci Banah maharbi”

Sarki da yarima Naslam sai duk suka maido dubansu ga Barham ɗin,shi kuwa kai ya jinjina kafin ya ci gaba da cewa “tarihin da ya fara zuwa na wannan ƙarnin ya bada labarinsa,Banah maharbi ne kuma babban matsafi wanda ya fito daga tsatson aljanar ruwa.Mahaifinsa ya kasance masinci ne,ya iya ruwa sosai a irin alƙawarin da mutane ke ƙullawa da ruhikan ruwa mahaifin Banah ya yi gamo da wata aljanar ruwa har yayi tarayya da ita suka same shi.Tun da aka haife shi a cikin jeji ya tashi tare da fatale da aljanu,kafin mahaifinsa ya mutu ya koya masa farauta da kuma baƙin tsafi na ƙarnin baya sannan kuma ya ɗora shi kan turbar yi wa aljana ZAƘUMA bauta” Barham na kawo nan da zancensa masarautar ta ɗauki wani salo,guɗa ce kamar an kawo amarya ta karaɗe ko ina kafin kuma iska ya soma tashi babu jimawa kuma aka soma yin wasu yayyafin jini.

Hankali a matuƙar tashe Barham ya ce “Attakbirrrr!”

Dukkan mutanen da ke wurin suka amsa da “Allahu Akbar!” nan take yayyafin jinin ya tsaya cak wanda duk ya ɓata fuskokin mutane.Sai kuma sararin samaniya ya soma ɗaukar launin ja yana nuno inuwar wata halitta marar kyawun gani can ita ma ta ɓace komai ya dawo normal.



Ran sarki da na yarima ya ɓace,saboda ba tun yau suka saba ganin ire-iren waɗannan surkullen ba.
Barham ya ce “ Aljana ZAƘUMA ce,wato uwar gijiyar Banah da ita yake tsafi.A kullum yana shayar da ita jinin mutane,ita kuma tana basa ƙarfin iko ”


“Ina zan samu shi Banah ɗin?” yarima ya tambaya.

Barham ya ce “Ubangijin Ka'aba ne kawai ya san daidai ina yake a yanzu,saboda tamkar guguwa haka Banah yake bai zama wuri ɗaya yawo yake yi gari-gari yana shanye jinin al'ummar yankin”

Yarima zai buɗa baki ya sake yin magana amma sarki Haroon ya dakatar da shi ta hanyar cewa “yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne yi wa ustaza Jamila sutura,don haka a kira gimbiya A'ishah ta yi mata wanka”

Sai a lokacin ne kawai Ayyub ƙanen sarki Haroon kawai ya saka bakinsa,“ gimbiya A'ishah tana kwance babu lafiya tun jiya,na so na sanar da kai sai kuma wannan al'amari ya danne niyyata ”

Hankali a tashe yarima ya ce “meke damunta?”

“Ciwon ido ne mai tsanani ,idanunta sun zama kamar gauta ” Ayyub mahaifi ga gimbiya A'ishah ya faɗa .

Yarima bai ƙara cewa komai ba ya shiga can ciki,direct kuma sashensu gimbiyar ya wuce.


A kwance ya tarar da ita don tun lokacin da Dadda ta fice ta bar ta take nishin azaba idonta sai ƙara ciwo suke yi saboda ta ga abin da bai kamata a ce ta gani ba.

Tana jin muryar yarima ta yi ƙarfin halin buɗe idon nata sai dai tamkar mai ɗauke da sabuwar makanta haka take ji dole ta ja su ta rufe.


“A'ishahhh?” ya kira sunanta cike da tausayinta.Murya na ƴar rawa ta amsa da “na'am yarima”

“Mene ne ya shiga idonki?” ya sake jefo mata tambaya,sai dai ba ta kai ga amsawa ba jakariya Ali da Barham suka shigo.


Barham ya matsa kusa da kanta yana ajiye jakar kayan aikinsa,bai ɓata lokaci ba ya soma zuba magani yana wanke mata idanunta duk da yana haɗawa da Magic babu wanda ya sani in ba ita gimbiya A'ishar ɗin ba.

Cike da aminci ta buɗe idonta da suka dawo normal tana kallon Barham da yake yi mata ta idanu.

“In yau na wanke miki ido kin samu lafiya ki sani gobe ba zan yi ba,zan bar ki da mugun halinki ”

“Ban taɓa ganin inda maye yake gorantawa ɗan uwansa ba sai kai Barham” ita ma ta basa amsa ta ido.

Ya ce “ni ba maye ba ne,ban taɓa yin maita ba hasali ma ina adawa akan duk masu yinta.Ke ma kin san cewa iya Magic kawai nake yi shi ma ba don komai ba sai don ci gaban masarauta”


“Me yasa dole sai ni kake son na bayyana kaina? Don me shi yarima ba ka damu da tasa maitar ba?” ta tambaye shi,sai dai shi Barham ɗin bai bata amsa ba ya juye kansa ya mayar da dubansa ga yarima Naslam yana mai cewa “ba wani babban abu ba ne ya same ta,kawai wani ɗan tsautsayi ne”


Yarima NASLAM ya dube ta yana mai cewa “ki kwanta ki huta” sai kuma ya fice jakariya Ali na take masa baya.



Wasu mata aka samu suka yi wa ustaza Jamila wanka.Sai da aka ma fito da gawar ne sannan gimbiya A'ishah ta san abin da ke faruwa,sosai ta ji zafin mutuwar har da zubar da hawaye.Ana yi mata sallah aka kai ta gidan gaskiya,sai kuma a wannan lokacin ne jakariya Ali ya nuna rauninsa ya soma yin hawaye waɗanda zubar da su ba ƙaramin sanyaya masa zuciya suke yi ba.


Sai da aka yi kwana uku ana jimamin mutuwar ustaza Jamila kafin kuma lamurra su ci gaba da tafiya.

A yau ne yarima yasa aka fito da matsafiyar nan da ta raira waƙa tsafi.Gaban sarki aka gurfanar da ita,tare da umartar ta da ta faɗi laifinta.


Amma ta yi shiru ta ƙi cewa komai sai yariman ne ya shaidawa sarki yana mai ƙara wa da “a yanke mata hukunci nan take ban son ajiyar mayya a cikin masarautata ”

Sarki Haroon ya kafe ta da ido yana kallo kafin ya ce “ki amsa laifinki sannan ki tuba ki rungumi addinin Musulunci domin tsira da ranki”


“Babu wani addini da zan shiga,na fi son zama babu alƙibla.Sannan kuma ni ba mayya ba ce duk da ina da ilimin sarrafa maitar,maganar ƙarshe kuma ita ce zan koma gida”

Rai ɓace yarima Naslam ya zaro takobinsa da niyyar sauke mata kai amma jakariya Ali yayi saurin riƙe shi yana cewa “ka nutsu yarima kar ka yi saurin yanke mata hukunci jira na kira Barham”


Zuciyarsa na ƙuna ya ce “ba ka ji yadda take magana ba sam babu ɗa'a?” bai ma kai ga cewa wani abu ba Barham ɗin ya shigo.


Kallo ɗaya ya yi wa matar ya gane wace ce ita,hakan yasa ya ƙarasa gun sarki yana mai yin ƙasa da murya ya ce “kar ku kashe ta,za ta yi mana amfani a nan gaba” sosai sarki yake ɗaukar shawarar Barham saboda shi ɗin aminin mahaifinsa ne sannan kuma dattijon arziki na masarautar.


“Ku mayar da ita” sarki ya faɗa wanda hakan sam bai yi wa yarima daɗi ba sai kawai yayi zuciya ya fita daga wurin.

Jakariya Ali ya bi bayansa yana mai cewa “ gaggawa aikin sheɗan ne,matar can tana ɗauke da wani ɓoyayyen sirri wanda nake jin cewa ita ce makullin da za mu yi amfani da shi wurin buɗe duk wata ƙofa da ta yi mana wuyar shiga”


Ba tare da yarima ya ce masa wani abu ba ya soma cire kayansa na sarauta yana ajiye wa.Toilet ya shiga ya soma yin wanka ko zai ji sassauci,har ya fito jakariya Ali na nan.Shi ne ma ya taimaka masa wurin tsane jikinsa ya saka kayan zaman gida,daga nan sai suka wuce can inda tantabarunsa suke.


Yana son tsuntsaye, wannan yasa ko ƙunci yake sai ya ziyarce su yake jin daɗi.Jakariya Ali ya buɗe su,da gudu kuwa duk suka shiga fitowa suna nufo shi,ɗaya ta sauka kan kafaɗarsa ya kai hannu ya damƙo ta yana shafar jikinta yana murmushi.

Sai ya ji kamar ana kallonsa,ido ya baza cikin tantabarun nan idonsa ya sauka kan baƙuwar tantabara idonta ƙurrr kansa.Kasancewar bai yarda da canfi ba sam bai kawo komai a ransa ba,haka ya ratsa ya je ya ɗauko ta wani irin shock ya ratsa shi nan ɗin ma bai sa a ransa wai lamari ne da ya shafi sprituality ba.


Jakariya Ali ne kawai ya farga da abin da ke faruwa,amma kuma sai ya ja bakinsa yayi shiru.Duk yadda yarima ya so tantabarar ta saki jikinta amma abu ya cuttura kawai sai ya wuce da ita can ɗakinsa yana mai cewa “ban san daga ina ita wannan ta zo ba,da alamu ta ƙi sabawa da sauran ne”

Jakariya Ali ya ce “ dama ai kullum cikin samun baƙi tantabaru ake yi,ita ma za ta saba”

Cikin ɗakinsa ya sake ta,ai kuwa sai ta shiga yin walwalar.


A can ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa abubuwa ne duk suka dagule mata,ga rashin ƙawarta Jamila ,ga ɓatan Dadda kusan kwana uku har yanzu ba ta dawo ba,ga kuma yanayin jikinta da take jin ya sauya.Zaune ta yi cikin halin ƙaƙanikayi tana wasiƙar jaki,sai ta ji ana magana ƙus-ƙus ba ta jin abin da ake cewa, da ta nutsu sosai sai ta gane a cikin drower kayanta.A hankali ta je ta buɗe,ɓerayen da suke gurgurar kayanta suka saki ihu a tare wannan karon sarai ta ji abin da suka ce.


“Wayyo an kama mu yanzu an yi ƙoƙarin kashe mu” shi ne abin da ɓerayen suka faɗa kafin su fara gudun tsira,har kan ƙafarta ɗaya ya faɗo amma ta kasa yin motsi saboda shock.Ita maitarta iya ta juya baƙi ya dawo fari ce,sai ga shi yau ta ƙara samun matsayi.Jikinta ne ya hau rawa,babu shiri ta nufi ƙofa don zuwa wurin Barham ta sanar da shi sai kuma ta yi kiciɓis da Dadda wacce ta dawo daga jejin Mayu.Da sauri ta ja baya,ita kuwa murmushin mugunta ta sakar mata tana mai cewa “Allah yasa dai ba ƙoƙarin tonawa kanki asiri kike yi ba? To ki sani muddin yarima ya ji labarin ke mayya ce to zai fasa aurenki, ba kuma zai yi jinkiri sauke miki kai ba kin fi kowa sanin halinsa fiye da ni yadda bai da tausayi akan mayu”

Idon gimbiya A'ishah ya kawo ruwa,yanzu ne kawai ta yarda da maganar Barham .Tabbas a matakin da take a yanzu ta riga da ta makaro babu ta yadda za a yi ya cece ta.

Dadda ta ci gaba da yi mata gargaɗi mai ban tsoro,“ in kuma kin shirya yin mutuwar kare sai ki je ki faɗa ,sanin kanki ne hatta sarauniya Sarat ta bar masarautar nan saboda laifin maita ballantana ke karan kaɗa miya ”


“Amma Dadda ni ban ce miki ina son zama mayya ba,don me za ki bani kambunta?” gimbiya A'ishah ta faɗa .


Dadda ta bata amsa da “saboda duniyar nan muddin babu maita da Magic to tamkar miya ce babu magi,ki zo na nuna miki mece ce ainihin rayuwar Mayu na tabba in kika ga irin shagalin da ake yi ke kanki za ki ji daɗi ki kuma gane gata ne na yi miki ” shiru gimbiya A'ishah ta yi kafin ta je da gudu ta rungume Dadda.



★YANKIN MUTUWA


Zuwan baƙuwar haure daga duniyar turɓaya shi ya canza mana yanayin shigarmu.Na ajiye fatar dabba na koma saka kaya,waɗanda Banah ne da kansa ya shiga duniya shi da sauran matsafa suka kwaso su a can duniyar tuɓaya.Kai tsaye za a iya cewa suka sato,saboda dare ne suka bi suka dinga shiga kanti suna ɗebo kaya bayan an kawo haka aka zube su aka rabawa kowa ciki kuwa har da ƴar jaririya da na samo wacce har zuwa yanzu ba a saka mata suna ba.


Ummilo shi ne sunan da nake yi wa matar wacce duk ƙoƙarin Banah na son saka mini tsanarta bai yi nasara ba.
Zaune na yi ina kallon yadda take bai wa baby madarar da aka tatso daga dabbobi.Hannu na kai na shafi fuskar Babyn ina mai cewa “Ummilo wane suna kika zaɓa mata?”

Ta yi wani murmushi mai ƙayatarwa kafin ta ce “ina son sunan Jamila saboda na riƙi ƴa mai irin sunan nan” sai kuma ta yi wani irin shiru kamar mai yin nazari,a nan ne na fahimci cewa kamar ƙwaƙwalwarta na son tuna wani abu da ya danganci rayuwarta.


Ina shirin yin magana sai gani na yi gari ya ɗau wani irin duhu,yayin da kuma mutanen da na zube suna yi mini hidima suka soma yin ihu.Duk yadda na so yin tsafi abu ya cuttura,kamar minti biyar sai komai ya dawo normal.Idona na sauke ƙasa sai na ga duk ɗigon jini ne ta ko ina kamar an yi ruwansa,ina ɗago kai kuma muka haɗa ido da Banah fuskarsa kicin-kicin kafin ma na kai ga tambayarsa sai cewa yayi “ tun da kika shigo da jaririyar nan a yankin nan bala'i ya soma sauka,don haka mun yanke shawara ni da sauran matsafa za mu bayar da jininta matsayin hadaya ga ruhikan ruwa........
[11/04 17:07] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

08


“Ta ya za ka ce a ɗauki jaririya a kai wa Teku matsayin hadaya? Wannan sam ba mai yiyuwa ba ne.Wannan al'amarin da ya faru kuma ko kaɗan bai da haɗi da da jaririya Mila wani baƙin ƙulli ne daga maƙiya kuma zan binciko na gani duk masu hannu a ciki” na faɗa .

Banah ya ƙanƙance ido yana kallona,na je da sauri na ɗauki Mila daga kan cinyar Ummilo na goge mata fuskarta da yayyafin jini ya ɓata.Can ɗaki na yi tsinke,ina daidaita mata kwanciya ya shigo yana mai cewa “ita kuma Ummilo sai yaushe za ta tafi tun da kin karya doka kin ce ba za a kashe ta ba”


Ba tare da na juyo ba na basa amsa da “ nan ɗin masarautata ce,Ni ke da ikon barin wanda zai zauna da kuma wanda zan kashe,ka tsaya iya matsayinka na mijina in ina son shawarinka ni ce da kaina zan neme ka”


Cike da takaici Banah ya fito daga ɗakin ya jefi Ummilo da wani mugun kallo wacce yake jin tsanarta sai dai fa alƙaluman tsafinsa sun kasa rubuta sunanta .Direct can bayan gari ya nufa,bai yi nisa ba ya soma furzo kalaman tsafi nan take busashen ganyen da ke zube a ƙasa ya soma tashi sama kafin kuma ya haɗa wata baƙar guguwa wacce ta yi ambaliya da gangar jikinsa ya ɓata .Cikin wani kogo ya bayyana mai ɗauke da kunamu baƙaƙe ƙirin kuma ga su manya-manya.Suna ganinsa duk suka soma basa hanya,shi kuwa haka ya dinga ratsa tsakiyarsu har ya isa can ƙarshen kogon inda wata halitta ke kwance tana ƙyafta ido kamar mai jin tsoron buɗe su ɗin.


Zubewa yayi yana mai yi mata sujuda ba tare da kuma ya ɗago ba yake cewa “kin ce

5 / 13