ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 88

93K to 96K   out of 262.2K words

sai kukan kawai take yawan yi,

matar kawun ne dataji irin wayar tashin hankli da dabanci da sukeyi da zinariya shine ta zaunar da ita ta mata nasihohi masu ratsa zuciya tareda bata shawara akan maza ta koma taje ta nemi mijinta gafara tun lokci bai kure bamata ba.


kuka ta dingai ranar kamar wacce taji wa'azin amma inaaa har cikin ranta so take taga ta bar nan, kuma koda zata bawa bappa zaidu badai tabayar dan nadama ba, saidan ta samu ta lallabashi ya bata koda half ne na kudin zinariya dan tasan yana nan yana kashe ma fatima fiye da haka..itama tana da wnn kudin amma ji kawai data bayar tay asara gara ay duk abunda za'ayi. gashi bata iya managin capital ba, miji zai dora mata business kafin kace wani abu ta cinye kudin tass itakanta bazata san metayi dasu. maganan da akey yncu ko yarta sultana tafita yawankudi a banki amma dake babansu na aka musu ido yasaka bata isa ta kwashe kudin yaran ba.

babban gudurinta shine inhar ta koma gidan sa wallah wallaj saita dau fansa akan fatima dan ynxu babu wani lungu da sakon da gulmanta baije ba akan cewa wai wata kyakkwan bazaura data fi karfinta a duniyanci ta kwace mata miji da yaranta harfa kiran layin matar kawuntan akeyi na msmn ana mata gori akan haka....

yau sassaafe da abun ya isheta taji kirjnta na zafi kamr zai fita, sai kawai taji gara taje ta roki kawunta ya barta taje ta bawa bappa zaidu hakuri tunda iyayenta sun sha kiranshi suna bashi hakuri amma haryau baizo ba.....


see you guys monday dan Allah ayi share

surayyahms 08060712446
[17/11, 18:26] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: PAGE⏯️2️⃣3️⃣💫
Abunda Ke Boye(buk1).....
wajajen bayan sallan fajr ammi babba tafito sanye da hijabin datay sallah dashi ahnkli takr tafiya tana kifi kifi da idanunta yanayinta kamar na wacce kejin tsoro nan ta taho har kofar falon kawunta malam hamza

tsayawa tay cak abakin kofar tana tunanin irin kalmomin daya dace tabashi haquri dasu ko dama zai dan kyaleta yau taje tabawa bappa zaidu haquri dan ya maidata dakinta, dan gabaki daya zamanta anan gani take kamar cutarta akeyi awaje gashi izuwa yanxu jitake komi ya fara fita mata akai gara kawai taje ta dauki mataki tun kafin fatima ta gama kawo karshen zamanta a gidan mijinta da kuma rayuwar yaranta..

cikin sauke ajiyan zuciya tayi sallama afalon lkcin matarsa ne kawai a zaune akan sallaya tana lazimi..

tun daga kofar ta leƙa ganin baya ciki wani karamin tsaki ya kufce mata tabita tahaɗe rai batace uffan ba ta juya abunta ta koma dakinta tana kan sake sake aranta har saida karfe bakwai da rabi na safiya yayi kawunta bai shigo gidan ba and the more she waits the more lkci yana tafiya, tarasa abunda yakemata dadi, tasan inhar bata buga sammako ta same bappa zaidu a gida ba bazata iya samunsa akoina ba sai in har yamma yay inya dawo gida ita kuma sam bataso taje gidan bare makwafta suce ta dawo bikon miji ajinta yabi ya zuba..

ta shiga wani yanayin na ujula da tunani, can sai da karfe takwas ya kusa cikawa kafin taji sautin shigowar kawu wanda babu shiri ta taho ta samesa ko zama baiyi ba yaji sallamarta abayansa

"kawu ina kwana??

tafadi kanta na kallon kasa kamar mutuniyar arziki tanamai rusunawa

bai amsa ba ya mata wani irin kallo yace "ke kuma raihanatu me ya kawoki???

dan shiru tay kafin can tafara masa magana da sanyin jiki da taushin murya..

"kawu dama haquri nazo nakara baka,kai kanka fa shaidane wallh wallah nay nadamar abunda na aikata ma miji na duk sharrin shaidan ne.

ganin bai tanka ba adede nan ta fashe masa da wani irin makirtaccen kuka tana cewa "kawu dan Allah na rokeka kaji tausayi na kabarni naje dakaina yau nabashi hakuri kodan darajar yarana dana barsu acan sukadai batare da kowa ba nasan zai yafemin...babu ranar da basu zuwamin a mafarki suna bidana, dan Allah kawu kaji tausayi na..wallah sharrin shaidan ne, kuma nayi nadama
..tana fadin hakan tana kuka kamar ba ita ba.

bakinsa a bude yake ta kallonta ayayinda ta cigaba da kukan kamr dagaske nadaman tay

shide baice mata uffan ba face ganin yadda matarsa tafito da sanyin jiki tanata rarrashinta yasashi ya sauko snn sukayi magana yayi mata fada sosai
..snn yace yaune kawai zai iya bata izini tafita don neman gyaran aurenta amma muddin ya kasance bappa zaidu bai saurareta ba toh saidai fa duk su hakura su jira hukuncin da zai yanke nan gaba tunda sudin sunyi iyakan bakin kkrinsu na sasantawa shikuma bai basu fuska ba. itade duk abunda aka fada cikin ladabi take amsawa da na'am.. suna kammala maganan ta fara shiri, aron kayan matar kawun nata ta amsa ta saka ajikinta tay kwalliya ta fito tawani shaa doguwar blue hijabi wajajen karfe goma saura tafita daga ita sai kudin motar ta nufi cikin gari

tun acikin abun hawa ta dinga lissafin yadda zata bi komi har ta iso wani sabuwar estate na masu hannu da shuni..

agaban wani katafaren gida aka sauketa ta ciro kudi ta bawa me adedeta snn ta nufi cikin gidan kai tsaye da karfi tahau buga gate din kamar tazo filin yaki,

mai gadi ya leko da zimman zai yi masifa saidai yana ganin itace yay maza yazo gabude kofar ta shigo ciki cikin rusuna kai yace ina kwana hajya?

wani dan uban walakntaccen kallo tamasa sama da kasa snn taja tsaki muryanta a dakile tace"Ramatu tana ciki? yace eh tana ciki..yana furta hakan bata jira ba kai tsaye ta wuce cikin gidan agaggauce.

wata babban falo ta alfarma ta ratsa ta samu lkcin masu aiko suna kan jera breakfast akan dinning table, cikin dauke kai ta wuce sama har bedroom din aminiyarta tana isa tafara bubbuga kofar tanacewa "ramatu.. ramatu..ramatu ni dan Allah kibude min kofa bani da lokaci sosai sauri nakeyi...,

hjy ramatu dake gaban madubi taci wani uban kwalliya na manyan mata ta saka cool orange shadda dayasha aiki daga sama har kasa tana kan karasa saka dan kunnen gwal dinta a kunnenta cikin mamko da kyabe baki tace "Ina xuwa..

wani expensive turare ta dauka ta shafe jikinta dashi kafin nan ta fito tana bude kofar kuwa sukaci karo ammi babba atsaye wacce batace mata uffan ba ta wuceta ta shigo ciki ta tsaya cak a tsakiyar dakin tana huci ahankli..

juyowa hajy ramatu tay daga bakin kofar tace "ikon Allah, yau ga wani sabon salo. ke kuma raihanatu meye haka zako shigomin kamar an koroki ?

ammo babba tace kamar ya ramatu?

wani tuwon harara ta watsa tace "naganki gatsau agidana mana, badai bashi kikaxo nema ba dan inkudine wallah bazan iya bayarwa ba...ai kinsan da haka kikayi ganganci kika fasa magani me tsada sai kace ke kadaice me yara a duniya..

a hatsale ammi babba tace "aah dakata min ramatu karki sake ki gayamin maganan banza mana
..ke kinsan nafi karfin million goma. matsalar dana samu da mijina ne kawai ya tsareni da tuni anwuce wajen..

karasowa hajy ramatun tay tace ohhh dama can kina da hanyar fitowa kibada kudin shine kika bari zinariyar mace take cimana mutunci tana lalata mana suna agari sai yau kenan kikaga dama zaki wani bugamin sammako kamr nina miki asara???

cikin yatsina fuska ammi babba tace "abeg abeg is enuf..ni duk ba tashin hankali bane ya kawoni wajenki, eh naji na amince zan dauki asara kudi kuma zan bayar dashi amma bayau ba sai gobe, kinga dakyar na yaudare kawu cewa haquri canje bayarwa wa miji na na fito nan so dolene kawai kizo ki rakani mukoma wajen bokanki
inhar shida aljanunsa sun karya asirin nan ne da sukamin akan fatima gara insani dan wallh labarai marasa dadi suna zuwa min daga asibiti, na yadda fatima da mijina suke buga soyayyrsu kamar zasu hadiye juna, kuma ynxu haka duk iyayena an aika masa sunsha zuwa har gida suna basa hakuri akan ya maidano daki na amma kinga yay banza dasu baice komi ba...inde har dagaske aure fatiman zaiyi toh wallah gara shi in kashesa kowa ma yayi asarar miji..arzikinsa kuma ai gadon yaya na ne...bani da case!!dan wallah danayi zama da fatima a matsayin kishiya gara na mutu, ko shi ya mutu dan wallah wallah bazaiyu ba.

jikin hajiya ramatu har na ɓari ɓari tazo da sauri ta rungume ammi babba cikin buga shewa tace yawwa raihanatu sai ynxu kika farka a bacci, naji dadin wann maganan naki..ai dama can kece kika tsaya kina musu sanya da tuni an wuce wajen..

ammi babba na share hawayenta tace kawai ki dauki waya ki kira mana bokan kice masa muna zuwa ynxu, daga nan sai mu wuce banki nay drafting cheque na karbi kudin zuwa wajen bokan for now tunda kinga duka katunan banki na da wayana duk suna gidan mijina.

hajy ramatu tace Haba haba raihanatu kudin zuwa wajen boka ai bazai gagareni ba basai munje kinsha wahala a banki ba..ina da wasu kudi anan. jikinta na rawa taje ta bude mata drawer kudine sabbi aciki famm wanda ba'a ma taɓasu.

da wani irin ido ammi babba ta kalleta tana karkada kai tace "hmmm ramatu kenan wato kina da kudin kaini wajen boka amma kiban aro na biya bashi dayatsaya min a wuya kince sam baki dashi..hmm ai dama walakanci basai ka mutu ba.

cikin yatsina fuska haj ramatun tace wancan fa matsakrku ce banawa ba..badai zan baki bashi ba..wnn din ma inbaki so ai sai afasa dama inada inda zanje wallah

ammi babba tace a'a thisbis my only chance kawai muje inci abinci mutafi dan makahon yunwa nakeji daga nan sai mu wuce wajen bokan sharply kinsan dai ban isa injima awaje ba kawu zai fara min masifa

fitowa sukayi har dinning suka cin abincin suna labari akan lamarin dake afkuwa wanda rabi duk hirar bappa zaidu da fatima ne..

suna kammala ci suka shirya suka fita,tafiya ne me dan nisa cikin wani kauye 3-4hrs ne zai kaisu ya kuma dawo dasu.


fannin su ammi karama kuwa kusan kominsu acikin kwaciyar hankali da girmawa akeyinshi.
yau suke cika kwana shida a asibitin amma kowani rana jikin ayaana na improving sosai dan within this few days da aka mammata test har speciliast doctorn yazo dakansa ya dakatar da magananan kaita kasar wajen ganin jikinta yana samun sauki sosai..

presence din ammi karama da mutuncin da sultana take mata yasa tazama soo relaxed kwana biyun nan, babu wani abunda ta rasa, ko yake damunta.. maheer kullum zai siya mata su ice cream su sha tare da sultana, matsalar ta daya shine daga zarar taga ibaad sai taji kawai zuciyarta yana yawan bugawa da karfi taciki, duk dama baiya mata fada ko tsawa kwana biyun nan...amma itade haka kawai takejin mugun shakkarsa msmn dataga kamar har sultana ma haka takeji. ibaad baicika zama acikinsu ba, daga yazo few minutes yaci abincin sa, inya sata taci nata abincin ta koshi shknn zai fita masallaci ya kyalesu. life was calm and peaceful, badon ma suna jiran sakamakon karshe na kwajin da akayi ma ayaana ba da tuni an sallamesu sun koma gida.


wajajen karfe 12pm da rabi ammi babba da babban kawarta hajya ramatu suka iso wani karamin kauyen fulani acan tacikin jejin makiyaya wanda haryau da bukka suke yin gidajensu ajejin..

gaban wani katoton gida suka wuce mai babban zaure da dakuna kala kala kamr fadar sarki an zagaye gidan gabaki daya da katangar karare..

akofar gidan suka parker jeep dinsu snn suka shigo zauren gidan suka zauna akan tabarma after like 30 more minutes suna zaune wata babbar mace data toshe fuskarta da face mask ta fito ta wuce snn akamusu iso suma suka shigo ciki

shu'umin dattijo futuk ne tsiriri da farin gemu ke zaune akan kujerarsa ga kayan tsafi kala kala barbaje acikin dakin.

suna shigowa ya fara hangame baki yana kallon hajy ramatu dake mutumiyarsa ce sosai ya saba kwanciya da ita, da wani irin rangwadi hjy ramatun ta rusuna gabansa tana rausaya jiki cikin kashe masa murya tace"..malam nawa nina Allah yaza zamaninka malam ranka shi dade ina miko gaisuwata me dadi musmn ga kayan aikin ka masu dadi.

wani shuumin murmushi yay yace "hajy ramatu kenan gidan dadi, toh dani da kayan aikina masu dadi duk muna amsa gaisuwa...ku samu waje ku zauna inji meke tafe daku?

tana murmushi ta miƙe daga rusunan suna zama ammi babba ta hade rai daga baya bayan kawartan tace "malam ina wuni "wani irin kallo yamata snn yace "lafiya hajya...snn ya juyo da kallonsa kan hajy ramatu yace toh ina sauraranku meke tafe daki yau kuma?

...murmushi tay tace malam akan dai maganar mijinta ne,
kwana biyun nan gabaki daya abubuwa sun rikice mata harma ya koreta agidansa, snn munji labari soyayyarsa yake kwasa da wancan matar, harma syyn nasu ya dawo kamar sabuwa. shine mukace bari muzo muji kome ke faruwa.

cikin gamsuwa da bayanintan ya gyada kansa baice komi ba ya jawo wani katon tukunya ya kunna wuta akai hayakin na fara tasowa yafara sumbatu yana maganganu da hayaqin kamar wanda yake magana da asalin mutum da wani irin yare..

yana gama maganan wutar ya kashe kansa, nan ya tuntsire da wata mahaukaciyar dariya ya juyo ya kallesu duka yace "Asirin hana yuwar aure yana nan daram bai karye ba..saidai adduar da sukeyi da maganin kariya da suke karba shine yake saka asirin yake yin sanyi amma badon ya karye ba..kunyi daidai da kuka zo, idan da ba haka ba wata rana zakuji cewa sun sami wani lakani da zai warware musu sihirin.

cikin jin sanyin jin ance asirn bai karye ba ammi babba tace "toh malam dan Allah yanzu ya za'ayi ka kara zafafa abun nan a raba su,ya zamana baya son ganinta itama bata son ganinsa, su tsane juna..dan wallh ina cikin tashin hankli malam, matar nan ta kwace min mijinaz snn tazo ta kwace min yarana..tunda nabar gidansa yau kwana shida kenan amma ko sau daya yarana basu nemi ni awaya ba suna can atare da ita..nide ko ma miye ne kayi dan matar nan tariga tagama da rayuwar aure na.

shuumar dariya yay yace ki kwantar da hanklinki hajiyabai aure kam fa bazai taba yuwa ba..aljanun mu sunce babu aure a tsakaninsu wann shirmen da sukeyi duk zasuzo su dena kece matarsa na qaddara ,gidanki ne ke kadai zancen kshiya babushi ma a qaddararki.

wani dan uban murmushin bazata ammi babba tay tare da sakin wata katuwar ajiyan zuciya hummm masha Allah malam, ai iren iren maganan da nakeson ji kenan toh inde har hakane kuwa godiya nake Allah yakara maka basira nide yanxu ataimaka min dai na koma gidan mijina tunda kace bani da wata matsala da su anan gaba

cikin gyada kai yace 'angama' ke dai kije ki kwantar da hanklinki
aure fa babu shi aljanu sunce mana kece matar mutuwarsa..

wani irin murmushi ta karayi tanajin wani irin matsanamcin dadi na ratsata mata jikinta irin wanda ta jima bataji shi ba...

wani kullin magani ya ciro ya bata yace mata taje dashi ta jika a gora duk sanda zataje rokonsan ta kurkure bakinta da ruwan maganin babu makawa zai dawo da ita..

karban maganin tay tace masa nawa ne, yace aa kyauta ya bata

rusuna kai tayi tana masa godiya, nan hajya ramatu tace mata taje kawai ta jirata a mota bari itama tama bokan special godiya ata ciki.

bafulatin yana lumewa yar cikin dakinsa hajy ramatu ta sabi jiki ta bishi ciki suka rufe kofa

bata damu da salon karuwancin kawartan ba cikin kyabe baki ta fita can waje tana murmushi danyau bakaramin kwanciya hnklinta yay da taji batun bokan nan ba...

daga cikin dakin bokan kusan minti talatin yay yanakan durjan hajy ramatu sai can bayan har kura ya lafa snn yake gaya mata asalin maganan asirirrince...

cikin girgiza kai yace....hajiya 'ina tausayin kawarki dan gaba fa bazai mata kyau ba, da ace itama zata yi wayo irin naki tazo tana jiyar dani dadi nida aljanu na muna gamsuwa da romonta aida kuwa taga aiki da cikawa

hajy ramatu tace bangane ba malam dama akwai wata matsala ne?amma ai dazu naji kace mata komi lafiya, kuma aure bazai yu ba kode raihantu zata mutu ne???


yace a'a..bazata mutu ba, amma fa abunda zai faru agaba zata gwammaci da mutuwar ma tayi, dan kuwa wayancn mutanen nata sun rike Allah inkin lura shiyasa banfiye son mata aiki

,.magungunan dana baku na hana yuwar aurencan badan da baqaqen ifiritan aljani mukayishi ba da tuni sun kwanceshi. kuma ita waccan din datake gudun itace ma asalin matarsa ta qaddara, lokacin aurensu ne dai bazaizo musu da wuri ba, amma kuma fa manyan aljanunmu da suka shafa sama shekaru dubu daya suna harka sunce min zasuyi auren harma da rabon yan biyu atsakaninsu anan gaba.

a firgit hajy ramatu tamike tsaye cikin doka kirji tace "nashiga uku, haba malam...kace min wasa kakeyi dan Allah?...

jin yay mata shiru yana karkada kai tace...innalillah wa inna ilaihi rajiun lallai kuwa akwai matsala yanzu dan Allah ko kashe daya acikinsu bazakayi ba??...wnn abun inhar yazo ya faru wallah wallah raihanatu mutuwa zatayi

cikin kyabe baki yace.."ai kafin ta kashe wani acikinsu sai inta shirya mutuwar itama, ai suma ba azaune suke ba, mijinta yana can yana neman makansa kariya itama matar tana neman makanta kariya akwai kaikayi koma kan masheqiya ajikinsu, inhar dagaske kinason kawarki toh maza kijje kibata shawarar kartaje wajen wani boka da maganan kisa dan wallh kanta zai dawo, snn kiy duk abunda zakiyi ki rudeta ta cikagaba da yarda da cewa auren nan bazaizo yu ba. inba haka ba sakamakon da zata tarar fa mutuwa ne shima bamai dadi ba..

jikin hajiya ramatu a mugun sanyaye ta koma ta zauna tay jimmm....can kuma tace toh bakomi malam inaga mafita daya kenan.. in sha Allah bazan bari tasan asalin gaskiyar ba, sn inka amince zanyi kkri naga na shawo maka kanta inta yarda zatana jiyar da kai dadi saika taimaka arage mata wani abun ..niko haihuwar yan biyu acire shi acikin qaddararsu, fisabillah malam da wanne raihanatu zataji???

karamin dariya yay yace "babu komi kuje kawai...aiwnn magani dana bata zaisaka mijin ya maidata zuwa gobe. karku damu inyaso duk abunda kukeciki zanji daga wajen aljanu

godiya ta masa snn ta tashi ta tattare kayanta data zubar akasa ta saka ajikinta babu kunya ta fito ta same ammi babba acikin mota, wanda har suka iso cikin garin kano masifa kawai suke

32 / 88