Author : NONE Category : African Stories & Novels
[20/10, 16:16] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _*ABUNDA KE ƁOYE....*_
_Love And scandal💕_
Bismillahirahmarahim...
1️⃣
Tun da ta ji kalaman Bappansu na karshe cikin lumshe ido da qarfi tasakar musu wani irin tsumammen kuka me daga hankali tareda kara cukuikuyo shararar doguwar red colour bridal veil dinta daya rufeta rass har izuwa kasa kaidaga ganin yanayin shigarta kasan ta sabuwar amaryace wanda baifi mintina kadan ne ya rage adaura mata aure ba..
A hankli jikinta yake rawa rawa koinanta yadau kyarma tsaban takaici da wata iriyar matsanancin ruɗani dake famar cinta acikin ranta wanda bazata iya fasalta yawarsa ba, wasu maqudan hawaye ne kawai suka shiga gangaro mata akan fuskarta yuuu wanda daga ganinsu kasan bata shirya musu ba.
yanayinta mai cike da jin tsoro da kuma tsananin tashin hankali tadada sunkuyar dakai ayayinda take agurfane a tsakiyar babban falon nasu zagaye da dattaijai mutane hudu, inda tsiraran hannayenta da kafafunwanta masu sulbi da haske da sukaji wani irin hadadden xane na jan kumshi suke dafe akasa daf da inda ruwan hawayen nata ke diddiga kamar an kunnashi.
kuka kawai take rabzawa ahankali wanda zafinsa saida yy kama da kamarna wanda zata cire ranta ta fetar wajje, cike da dauriya tadago kai jin tsananin zafin maganganun bappan nasu nadawo mata kai, babu shiri kuma dakyar tadago kai takalli dattijuwar mata dake sanye da hijabi kusa da ita tana goge hawayen dake sauka acikin kwayar idonta tadan sunkuyar dakai da wani irin sanyin jiki babu wata alamar dai yau zata budi baki ta kareta, zuciyarta a raunace ta kalli bappan nasu da yay maganan shima fuskarsa still na hade ne tamau tamkar bakin hadari jitay bata samu kwarin gwiwar cemasa komai ba shima dan gabaki daya batasan ya zata fara fidda kanta acikin wann cakwakiyar ba
babban surkuwan gidan nasu anty rainahanatu da ake cewa Ammi babba dake falon itama duk tabi ta tsime sai tsaki take sakewa jifa jifa dan dama ta tsani auren, babu dai wanda yace uffan acikinsu, kara runtse ido ayaanah tay sosai tadinga rabza kuka me sanyi me kuma hade da zazzafar shesheka duk ta rasa ya zatayi, can dai hannunta dake rawa rawa ya fara motsi ba acikin hayyacinta ba ta capke bakin zanin wata tsohuwa data rabza uban tagumi agefen bappan nasu ta mugun tsimewa da tsananin fushi har idanunta sunyi jaaa zirr tanakan girgiza kafafunta a masife
cikin rawan murya da gunjin kuka takamo hannun tsohuwar ahnkli cikin raunateccen magiya muryanta bai fita sosai tace "Don girman Allah hajiya kice su bappa suy yi hakuri wallh wallah bansan komi ba banyi masa komi ba don Allah kice su dan saurareni ni ban san wanda yayi min haka ba..."
amugun fusace tsohuwar ta warce hannunta da wani irin fushi me tattare da buhun barkwanon masifa caraf ta mike tsaye tana cewa "Ni da Allah sakeni ki wallh haushi kike bani, wato ke har kinsan ki aje mu anan kiyita rabza mana uban rantsuwa akan karya alhalin ke din ashe babban munafukace ko Ayaanah?toh tirrr da halinki. makanki kikayi bawa mu ba dan ganan abu mun gani ido da ido me kq zakice mana kin cuce kanki, kin tozarni.. kin kuma kashe aurenki tun ba adaura shi ba. Allah ya isanmu ma irin tarbiyan da muka taru duka muka baki agidan nan nide Allah ya isa tsakanina dake muguwa kawai!wallah ko su zaidu zasu yafe miki nikam bazan taba yafe miki ba, baqar almuramura, Allah sai ya mana sharia, dan koda aka kawoki daga kauye ubanki saidai yaje har dakina yayimin zagin kaca kaca ya hadamin da mugun baki cewa zakizo gabana ki lalace a binni, wato shine kikeso ki dada tabbar masa ke asalin watsaiyace, kin zo gaban ƴayana kin zamo cikkyar marar mutunci marar kamun kai kika maida kanki yar kwaltaa abayan idanunmu yo shikenan ranar aurenki ne kika zabi ki toxartani kiji dadi ko? meye burge ki da wann rayuwan ynx uban wayema xai amince yakara aurenki a fadin duniyan nan wayyo na shiga uku ni me tuwo Wallah baki isa ki kasheni ba wani dan uban Dukan bazata takai mata ajiki abazata tana kuka cikin raki tana cewa...
..toh wallh ki sani uwata Azumi bata tsinemin ba, kafin ki dauko mana abun kunya gwara tun wuri mu mu kunyata ki yo meya burgeki da irin wannan rayuwar ta yan iska inba samun waje ba?
daga ita har ayanahn kuka sukeyii ganin ta kara tantameta duk dama dukanta take kanyi tanata kukan sosai kuma acikin ruɗani, bakinta har na rawa cikin kukq da magiya takecewa "Hajiya dan Allah ki saurare ni, nasan kinsan ban aikata komi ba, wallh zaki iya dubani kigani, wallah wallh wallh ban aikata abunda kuke tunanin na aikata ba.. sharri.. aka...bansan yaushe...
bata karasa me zatace ba taji saukar wani dan uban saukar ginannen mari da tsohuwar ta kai mata me mugun zafi a bqki sanda ta saketa tariqe bakin ma batasani ba.
"banace miki kiyi min shiru ba, makira kawai annamimiya duk za'a taru amiki karya ne bayan ga shaidu nan zaidu ya kawomin su kaca kaca?kece acikin bidion nan fa ayaana bayan kinsaka natara dangina da mutanen anguwa kafff, nayi shelar aurenki kina gani hakanan akayita zagina akanki, akace min naci amana, nayi son kai, har mayya sai da aka kira ni, kai meye ma ba acemin a anguwan nan ba? haka naruntse idona kyam sabida aurenki da yaron nan rufin asirine agaremu baki daya amma dan tsabr rashin sanin darajar kai saida kika kekeshe idonki kika tozarmu "Ayaanah.. ni menayi miki?...toh wallah wallah baki isa ki dora min hawan jini ba, muna da yadda zamuy dake inke ban isa dake ba ai akwai wanda na isa dasu agidan nan, ki tashi ki bace min ana kar na tattaki nakaiki har lahira.
Ayaanah ta mike jiki babu kwari duhu duhu take gani agabanta har ta fita a falon tana kuka sosai kamar ranta zai fita..
direct dakinta ta nufa don tasan komei xata ce anan babu wanda zai saurareta ders too much evidence dat are pointing againts her which she knew nothing about, bayan tashiga daki kan gadonta tanufa tana rabza kuka sosai ayayinda kanta da kirjinta ke bugawa dan harga Allah batasan wani irin hukunci kuma za'a yanke mata ba.
bayan wucewar ayaanah daki tsohuwar tana kan kuka ta kalle bappan nasu tace "yau naga ikon Allah Zaidu. dan Allah ayaga hotonan nan bideon ma duk agoge kaji? sann ayi maza arabata da wayann mutanen banzan datake bibiya, banason wani a dangi ma yasake jin labari bare ganin shaidun nan.
tun be amsa ba ta dada rushewa da wani kukan kmr an bugeta,
"Allah mun gode maka, wai sai ka haifi ɗa amma baka haifi halinsa ba wallah mahaifyar ayaanah mutuniyar kirki ce yanxu meye wannan take so maqiya na suce akaina kenan..
cikin sauke ajiyan zuciya bappan nasu yace Ahtoh nide nagaya muku hajiya Auren ayaanah dai ya fasu, shida bakinsa yakirani yace min ya fasa bazai aureta ba, snn shine ma ya tura min wann shaidojin ga kuma jama'a sun taro dama sai an daura auren ayaanahn ne kafin agabatar da na su zainab Arifah, ni duk rasa mafita yanxu kam ai jin kunyan mutane ne kawai ya rage mana saidai in....
wani caraf babban surkuwan gidan Ammi babba ta capke maganan abakinsa tanamai cewa 'a'a, yaa Zaidu tsaya, ai magana kam ya riga ya kare tunda auren ayanah ya fasu me kuma zamuyi ai kawai afito fili kawai aje a bayyana masu kawu babba komi kar abata musu lokaci kasan yadda yaci buri akan auren yarsa zainab Arifah yatara manyn mutane kar abata musu lokci akan aikin banza. hhmm ayyuriri dama anbar yarinya tana abunda tagama dama kam ai babu wani abun da za'a samu a karshen rayuwrta face jin kunya, kuma ai wanda suka taru sua bude mata hanya ta lalata kantan sunsan kansu..
da gefen ido ta jefa baqar maganan ga dayan dattijuwa dake sanye da hijabi agefe, ganin bata ko dago kai ba taji wani irin dadi aranta dan dama wnn irin ranar kawai take jira na jin kunya danta gumsa musu bakin ciki.
fade fade take inda take shiga bata nan take fita ba, ganin dai babu wanda yace mata uffan haryanxu yasa tafara daga musu hankli burinta kawai aje filin taro a fallasa komi..
hidima biyu ne ga lokaci nata tafiya inma tsoron zubda ma kawu babba kimansa akeyi, toh mezai hana kawai a tura ayanahn takoma inda tafito ace kawai guduwa tayi takoma kauyensu if not wallah kaf zuria sai munji kunya bana kadan ba dan abundai akwai zubar da kima da mutuncin manya aciki.
tunda ta fara maganar kauda kai kawai bappa zaidu yay kamar wanda baijin surutan nata ahnkli yanamai lallatsa wayarsa da alama yana rubuta wani sakone, yana gama rubuta sakon ya tura ya tabbata ya isa snn yakashe wayarsan, sai a sann ya juyo ya kalleta adan taikace amma baice mata uffan ba kawai ya girgiza kansa..nan take falon ya kuma dauka da wani irin shiru bakaramin hade rai ammi babban tay ba sabida ta tsani tay magana duk taga an shareta..
within 5 scnds karar waya yakatse shirun nasu,dayan dattijuwar matar dake zaune shiru tana hawaye ita ta dauki wayar after uttering few words ta katse wayr snn ta kalli bappa zaidu da sanyin jiki ayayinda muryanta ke fita a cikin nitsuwa kuma ahnkli tace
"yaa zaidu, Mujaheed ne yakira yace in sanar dakai cewa yaga sakonka kuma yana daf da isowa gidan nan shima yanzu".
babu yabo babu fallasa cikin sassauto da bacin ran dake fuskansa ya kalleta cikin sauke karamin ajiyan zuciya snn ya amsata da "toh fatima Allah ya kawoshi lafiya, komi yar hakuri ce dan haka ki kwantar da hankalinki everything will be fine.
kanta akasa tana share kwallanta Tace mishi toh Ameen. dan kadan ya mayar mata da sanyin murmushi ita kuma tay maza ta sauke kanta kasa adan kunyace.
kallonsu ammi abban takeyi kamar zata tashi tsaye ta haɗiyesu su da mugun bugu, dan ɗan wnn calm gestures da yake yawan wakana tsakaninsu bakaramin kona mata rai yakey ba, wato itace datake matarsa na sunna ma bazai amsata ya bata hakuri ba caraf yahau amsa wannan makirar matan. satar kallonsu kawai take tana raya abubuwa masu tsauri aranta ayayinda babu abunda idonta yakey face hararar fatimar tareda jan musu kananan tsaki
share hawaye tsohuwar tay adede lokacin da wani gulluton baqin ciki ya kara rufe mata kirji inta tuna hotonan nan
ganin datayi kmar babban surkuwan gidan anty rainahatu wato Ammi babba zata kara yin wani magana, nan tay marmaza cikin katseta a masife tace "haba, haba..ya isa haka mana ke kuwa Raihanatu, kinyi ta maganan nan duk anji ra'ayinki akan ayanah amma kisani nide ban aminta da gurguwar shawarar kin nan ba, yoo sai kuma aje har babban masallacin jumua ayi shela ace ma jama'ar Annabi S.A.W. cewa yarinyar nan tagudu ranar daurin aurenta sai kace muna kwapcen wasan kwaikwayo?,..
adan masifa ammi babban tace amma hajya kema kinsan halin kawu babba wallh bazai lamunci azo da batu daga gidanan a tozarta shi a bainar muhimman mutane ba aranar daurin aurensa yarsa zainab arifah ba.
fuskar tsohuwar ba asake ba takalle bappa tace "zaidu maganan nan fa ya kare bama sai anje ga tozarta zayyanu agaban mutanensa ba tunda abunda kuke gudu kenan, dolene kawai ayi auren Ayanaah ayau din nan, babu wata zancen guduwa ko fasa shi, tunda shi wanda ya sakar mata fuska ya mata alherin shi ta cutar ta tozarta, yau koma uban waye mukaga dama dashi za'a a daureta yau, inyaso taje can can gidansa ta karashe rayuwarta dashi inma kashe kanta zatayi a dakin miji gara tay da akanda tazauna min agabana ta cigaba da tonamin asiri tay karuwanci a birni ubanta juma nacan kauye yayimin dariya, aure kam kamar an daurashi ayau ko tanaso ko bataso
wani irin shiru wajen yakara daukawa a falon ayayinda fuskar sauran matayen looks soo soo confuse da furucin tsohuwar duk da alama basu wani gama fahimtar inda maganan tsohuwar ya dosa ba, to da waye kenan za'ayi ma ayana auren dolen? da mujaheed ne ko wani ne nadaban daga waje? saidai tun kafin dayansu ta budi baki tay tambaya bappa zaidu yakalle su duka biyun fuskarsa ba a sake ba still cikin gyaran murya yace ya kamata kubami wuri zanyi wata magana da hajiya"..
babu tantama kowaccensu cikin dattijan matan suka mike tsaye cikin hadiye tambayar dake ransu snn suka fice waje.
babban surkuwan gidan anty raihanatu da ake kira da Ammi babba nan tay wani sashe na gidan da sauri sauri tana bambami, dayan nitsatsiyar matan kuma dake sanye da hijabi anty fatima da ake cewa ammi karama nan tanufi dakin Ayaanah kai tsaye jikinta duk a sanyaye, ta iso kofar dakin Ayaanah bata sani ba, kife kai tay akan gadonta tana ta kuka me karsashi gashi ita kanta tarasa amsar da zata bawa kanta, kanta duk ya kulle, she was like is this actually happening to her aranar aurenta, abu ne da batay tsammani ba sai gaba daya sai taji ta fice hayyacinta, she wish zata bude idonta taga mummunan mafarki kawai take,
kwankwasa kofar dakin da akay da dan karfi yasa tadaga idonta da sukayi jaaa suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi tabude har akagaji da Knocking aka bar wajen.
Sai can wajen after good 40 mins data dan dawo hayyacinta tana xaune saman gadon kafin ta jawo wayarta da kyar da kamar zata bude sai taji xuciyarta ya kara rauni, MTN sim card dinta take son cirewa ta karyashi sai taga tarin missed calls din kawar aikinta Ruthy yafi guda talatin da wasu irin zafafan text messages da ya ninka calls din daga wajen ango to be din nata, ko wani message data bude zance daya yake yi, " i trusted you, nina miki kaza nina miki kaza lokcin baki da kaza..kinci amanata ayanah, bazan yafe miki ba.." kowani kalma da ya rubuto mata suna daukene rashin mutunci da gori, tsana da zafin cin amana da butulci dayake famr tunanin tay masa.
wasu irin raunattun hawaye suka shiga bin kuncinta bawai dan zafin words dinsa ba sai gani datay wai har ya aminta da komi dayagani akanta kai tsaye, dan tay tunani in akwai wani wanda zai iya bada kwararren shaida mai kyau akan iliminta da tarbiyanta da shine mutum na farko da zai bayar, fita tayi daga Inbox din hawaye me zafi na sauka a idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da gori masu zafi aciki, gashi shidin ba yaro bane bare tace ko yana furta kalaman nan ne da gigin yaranta wai yau namijin datake ikirarin zata auresa kenan ke kirarta da watsatsiya karuwa hmmm.
kirijnta taji kamar sai fashe Kashe wayar kawai tayi ta ciro sim card din ta karyashi into 2 pieces kamar yanda tayi niyya snn tajefar da wayar can can saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, sam batay tsammanin haka kwakwalar maza ke aiki akan zargi ba dan wasu tsauraran maganganun nasa ya mugun tsaya mata a zuciya har tanaji ina ma tun farko bata sake ta amince mishi zata aureshi ba.
Knocking din kofa aka sake yi, ta kalli kofar sai kuma tamike a hankali ta nufi kofar ta budeshi ahankli,dayan dattijuwar matan ta gani tsaye suna hade ido nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta tabi ta sunkuyar dakanta kasa cikin sanyin jiki
matar ta shigo dakin ta kulle kofar ayaanah ta bi ta da kallo harta nemi waje ta xauna agefen gado snn ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya me tafe da hawaye tace "Ammi karama don girman Allah kiyi hakuri, nasan kema zakice na tozarki wallah bansan komi akan wann abun ba.
matar ta sauke wani ajiyar xuciya ahnkli cikin nitsuwa tace "Ayaanah i am not here to judge you, bare ma ai an riga anyanke miki hukunci auren nan naki bazai fasu ba, su hjiya sunce za'a daurasa a yau, kuma tun da har bappanku ya amince da wann hukuncin da hajiya ta yanke miki kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasu ke dai naki addu'a, nima ina nan ina taya ki da shi..
wani irin numfashi me karfi ayaanah taja abazata wasu sabbin hawayen da bata san dasu ba suka cigaba da sauka mata yuuu amma batace komi ba
cikin lallami ammi karama tace is okay kiy hakuri ayaanah snn kisani nobody is perfect but as long as we learn from our mistake ai shikenen, dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji everything will be alright kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya isa miki da ya janyo miki wnn masifar harda kuma auren dole da wanda ba musani bama tukuna.
a mugun mugun rikice Ayaanah tadan mike tsaye is like sai yanxu kunnenta ya farajin batun auren dolen da ammi ta ambata..
atake jikinta sai ya fara rawa cikin dafe kirji tare da sakin birkitacen kuka me tafe da rudewa tace "ammi Auren dole da wani wanda baku sani ba kuma? auren dole fa kikace Ammi? dama badashi za'a daura auren ba..?
jiki a sanyaye matar ta dan gyada mata kai tace shikam ai yace ya fasa saidai wani to wanin ne bansan ko waye ba.
a mugun ragwabe ayaanah ta fado kasa tare da durkusowa kasa cikin kuka mai kara, tarike hannun matar tana cewa dan Allah kar ayi min haka Ammi wllh xan iya mutuwa, ammi talk to him plss ai bappa yana jin maganarki sosai, dan Allah kiyi ma hajiya magana i can explain myself wallah wallah bansan komi ba, basai sun min auren dole ba nasan zata saurareki kodan karamin lokaci su karamin i will find a way out of this.
cikin runtse ido tare da jin tsananin tausayinta matar tace nima basu gaya min komi akai ba, amma dai mujaheed is on his way. kinga tunda angon shi yace ya fasa i have no idea what they are planning to do now, ga dai su can a falo inaga by now kuma inaji kmr ma har ma an daura. i am very sorry dear, kisani cewa I trust you.