YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romance

Chapter   7 / 30

18K to 21K   out of 87.2K words

idan ya dake ki kamar yadda ya saba kinji doughater"




Shiru Maryam tayi tana wasa da hannunta.




Sai da Mom din takara Maimaita tambayar,sannan tace"Allah Momy babu Abinda yayi tafada A fili a zuciyarta tana Jan Istigifari.


Taci gaba da cewa ,Dama Dama Wannan Abokin nashi ne,sai tayi shiru takasa karasawa,




Ina jinki ya kikayi Shiru Momyn tafada"




Shine Yake kulani Momy nikuma bana so tafada kanta a kasa,




Momyn tace"To ae kina da gaskiya Mutuncin "ya mace tsare kanta babu ruwanki dashi ko ya kulaki ,gaisuwa kawai na lamunce kiyi dashi kinji ko kuma zanyiwa Nasir magana tunda ba kyaso tayi masa magana duk inda ya ganki Kar yakara shiga lamarinki"




Gabanta yafadi jin Abinda Momyn take fada,




Da sauri ta dago kai tace"A,a Momy ba sai kin yiwa Ancle maganar ba Dan Allah"




Harararta Momyn tayi kadan tace"ae dole in yi mishi magana yajawa Abokinshi kunne domin a kanki zan iya batawa dashi"




Sunkuyar da kai tayi tana Murmushi kadan tace"Dan Allah Momy mubar maganar bana so ki batawa Uncle rai"




Dariya Momyn tayi gami da Mikewa daga kan daddumar da sukayi sallah A kanta tace" in dai a kanki ne ran Nasir zai baci kuwa ,




Mikewa tayi ita ma tabi bayan Momyn suka sauka kasa ,a tare Maryam din na kokarin fita da niyar tafiya bangaransu Momyn ta dakatar da ita,tace Lallai sai ta tsaya sunci Abinci tare ,ba yadda ta iya haka ta bi bayan Momyn can dainnig in da kayan Abinci ke jere iri iri na haduwa na Alfarma,




Momyn ta hada Mata komai tsaf ,Cikin nutsuwa Maryam tafara cin Abincin suna hira da Momyn kadan kadan ,sai da Momy ta tabbatar da Maryam ta koshi sannan ta kyaleta ta tafi bangaransu.






Lokacin da tashiga shashin nasu Ana sallahr isha'i Aunty da su Nafi'u duk sallah suke ,sabida haka Alwala ta daura ita ma tabi sawun su.






Aunty na idarwa tafara hidimar Zubawa yara Abinci ,ta kalli Maryam dake zaune kan dadduma bayan ta idar da sallah tana Addu'a ,"kefa a zuba miki ? Nasan dai kinci gurin Momynki ko?




Daga kai Maryam tayi A nutse tace wallahi kuwa Aunty a koshe nake Amma da safe naci dumame dama yafi dadi"




Tabe baki Aunty tace Allah ya kaimu . mai kika tsaya yi a ne a can?








*✍🏻,,,,,,,*
[23/03, 00:15] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?




πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*YARO DA KUDI*
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—






*✍🏻writing By*
~*Binta Umar*~
~*Maman Abdul Wahabu*~


*MRS AHAMAD GWADABE*






_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176






_INA MIKA SAKON TA'AZIYATA GA "YAN UWA DA IYALAN ALHJI RUFA'I GWADABE ,MUNA ADDU'AR ALLAH YAJI KANSHI YA GAFARTA MASA ALLAH YA YAFE MASA ALLAH YA KYAUTA TAMU BAYAN TASUπŸ‘πŸ»_






*πŸ…Ώ32*




Aunty Momy ce ta Sani gyaran dakin Ancle Maryam tafada cikin Nutsuwa.






Ayya to ae kin kyauta Aunty tafada.


Ancle din ma ya kwana biyu bai shigo min ba Aunty tafada tundai ranar da yadawo"






Ita dai Maryam bata ce komai ba domin Aunty bata son Laifin sa ko kadan.








****************


Karfe takwas saura na safiyar Litinin Maryam tsaf cikin Unporm dinta na Makaranta, Tana zaune gefen Babanta suna karyawa a gurguje ,ta kalli su Naf'iu tace "kuyi sauri Wallahi idan ba hakaba in tafiyata"






Ya Maryam ni dai naga Mutafi kawai Mubarshi tunda kullum sai yasa munmakara,




Duka Nafi'u ya kaiwa Miftahu jin Abinda yake cewa yace "bana hana yimin Rashin kunya ba"






Maryam tayi sauri ta riqe hannunsa tace "ai ba karya yayi maka ba ka dakeshi sai na rama masa"






Dariya Babansu yake musu yace"kai Miftahu kafiye tsokana kai kuma Nafiu sangirma kamar gyambo"




Aunty tace "Haka sukeyi si tayin koka ye kokayen shashanci"








Mikewa Maryam tayi tana gyara books din hannuta gamida da gyara jakarta tace"ai sai Ku tashi Mutafi ko"




Duk suka miqe a tare suna yiwa iyayen nasu Sallama.




Mi kewa Malam Ya'u yayi shima ya biyo bayansu Dan haka yake musu haka yake rakasu har kusa da makarantar sannan ya dawo gida dake makarantar babu nisa da gidan Alhji Huseen din.




Suna fitowa harabar gidan sosai Nasir ya fito daga part dinshi jikinshi sanye da kayan motsa jiki jikinshi a Murmurde ,sakin Fuska yayi lokacin da Idonshi yayi tozali dasu Nafi'u Yace "Morning My boys gami da dumqule hannusa kamar yadda yake musu ,Da sauri Nafi'u ya karaso yana dariya ya daki hannun Sosai yace"Morning Ancle katashi Lafiya"




Kalau Aboki na Nasir din yafada yana Jawo hannun Miftahu suna gaisawa,




Farin ciki ne ya Lullube Malam Ya'u yana tsaye Fuskarshi tamkar gonar auduga Dan dadi.






Nasir ya Mika masa hannu kamar ko da yaushe yace "Arrama Barka da Asubah"




"Barka kadai Nasiru katashi Lafiya"




"Lafiya Alhmdilahi"




Yace "kuzo in aje Ku a Skull din ko"


Yayi can inda motarshi take a je.




Ayya ai da ka barsu ma Nan makarantar tasu take bakin hanya"Malam Ya'u yafada






Ai fita zanyi Arrama Kawai su shigo na sauke su Nasir din yafada,
Ko gama rufe baki bai yi ba Miftahu yayi gaba dama yana kwadayin shiga Motar Ancle din.




Cikin sanyi Murya Maryam tace"Ancle ina kwana"?






Yanajin ta ya share ta,bata daddara ba ta kara maimaitawa,






Shiru yayi a karo na biyu yana kokarin bude mota Malam Ya'u yace' Maryam na gaishe da kai Nasir"






"Ok ya joyo Ya Dan kalli inda take yace" Lafiya Maryam yaya kike?




Dadi taji ganin yadda Ancle din ya Amsa gaisuwarta.






Tace"lafiya lau Ancle ,banza yayi da ita ya tada motar bayansu Nafiu sun shiga ko sauraron ta bai yi ba yafara kokarin tafiya.






Tace "Ancle ban shiga ba fa"




Wata harara yayi mata yaja tsaki kadan Dan ganin Malam Ya'u na gurin ya daka ta tashiga tukkuna sannan yaja motar






Malam Ya'u ya karasa bakin get din yana kokarin bude masa kofa,




Ya fice daga gidan.




Yana fita ya tsayar da Motar ya waigo yana kallonta A wulakance ,yace ke saukar min A mota"








*BINTA UMAR ABBALE*




_MARUBUCIYAR_


_*NANA KHADIJA*_


_*YARO DA KUDI*_


_*GIMBIYA BALARABA*_


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ»
[26/03, 01:44] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—




*✍🏻writteng by*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~




~*MRS AHAMAD GWADABE*~






_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU_
08089965176






*πŸ…Ώ33*






Diri diri cewa Maryam tayi jin Abinda yake cewa sai tasa masa ido tana kallo cikin tsoro!




Ya buga mata wata muguwar tsawa "get out nace kin tsaya kin sanya min ido shegiya Mayya mai kama da Aljanu kici kanki kurwa kurr!
Yafada A harzuqe!




Da sauri Maryam tabude murfin motar tafice tana jin wani mugun bakinci idan anyi duniya Dan Manzon Allah baza ta qara kula Uncle ba ko me za'ayi kuwa sai dai Aunty ta daketa a kan taqi kulashi.




Tana sauka ko sakon daya bai qara ba yafigi motarsa hade da bula mata kura! Jikin Unporm,






Wani hawayen bakin ciki ne yafara fita daga idonta tanayi tana karkade jikinta kana takama hanyar tafiya kamar yadda suka saba tunda dama skull din bawani nisa da gida.






Kan ta karasa skull tayi kokarin daina fitar hawayen Amma kana ganinta kasan tayi kuka sabida yadda idonta yayi ja!








Sukuku su nafi'u sukayi ganin Abinda Ancle yayiwa Yayarsu ,Miftahu yace "Uncle Yaya Maryam tayi maka Laifi ne?






Yana kokarin kunna kida kamar yadda yasaba yace"No" Babu Laifin da tayi min Abokina Kawai bana Ra'ayinta ne Na tsaneta!






Miftahi"yace Uncle mai tayi maka katsane ta mu kuma ba ka tsane mu ba?






Dariya yasa kadan yana mamakin tambayar kwakwa irin ta yaron yabashi hannu suka tafa yana dariya yace" Ai ba lallai sai mutum yayi ma laifi ba zakiji baka sonshi boy Yayarku tsoro take bani idan nakale ta tamkar Aljana"




Dariya Nafi'u ya qyalqyale dashi gami da dukan kafadar Nasir din sai kace wani sa'ansa yace"Lallai Aboki Yaya Maryam din ce Aljana duk kyawunta kaji kuwa yadda a skull a ke maganar kyanta A kwai Ancle Bash dinmu kullum sai yayi mata Magana bata kulashi bakaji yadda Abokai na suke cewa wai duk tafi mu kyau. Wai suna kama da wannan "yar india Ashwariya" idansu iri daya Dan Na Yaya Maryam din har yaso yafi na Aswariyyan blue,




Tabe baki Nasir yayi yana girgida kai Alamar yana jin dadin Music din dake fita kasa kasa cikin motar tasa yace"gaskiya waddan nan Friends din naka sun cuci Aswariyya da suka hadata da wan can tab!!
Da nasansu sai na Zane su da bulala domin sun batawa star ta kyawunta"


Yafada yayin da yakeyi parking. Daidai get din Makarantar.




Dariya Nafi'u yayi yana bude mota yace"to Uncle ko in kira makasu ne"


"Aa No" barsu kawai Zamu hadu ne wataran Amma kafada musu duk sanda muka gadu sai Na Zane su da kyau yafada Cikin sakin Fuska da barkwanci


Dariya yaran sukeyi suna kokarin daukar Lounch book din su Ancle din ya fito da wasu tarin Sweet masu bala'in tsada da dadi Dama ba ya rabo dasu cikin motar kasancewarsa ma'abocin son kayan zaqi ya basu yace"gashi nan kuje kura ba ko"




Cikin nutsuwa suka karba kana suka daga masa hannu suka nufi cikin makarantar,






Yana kokarin juya mota Maryam ta karaso jikinta a sanyaye ko kallon in da Motar take ba tai ba kai tsaye cikin Makarantar ta nufa,






Shi ma ya ganta yayi saurin dauke kai daga kanta gabansa na faduwa kadan bala'in jin haushin yarinyar yakeyi bai San meye dalili ba ,ko kadan bai tausaya mata ba tafiyar dasu kai suka barta.






Yaja Motarsa ya bar gurin Cikin Nishadi da'Alama yanajin dadin duniyar"










Tana Shiga cikin Makarantar Uncle bash ya tare kamar ko da yaushe,sai ta saki Fuska tace"Uncle ina kwana?
"Lafiya kalau habibty Yau kin Makara da yawa fa Yafada idonshi tsaye kanta ji yake tamkar ya lashe ta ya huta!






Dariya tayi kadan har dimful din ta ya motsa ,Abinda yake mutukar so kenan a gareta tace Uncle kenan kullum sai kace na makara dubi time fa takwas yanzu tayi tafada tana kallon Agogon hannunta,




Hannun yabi da kallo gami da kurawa fatar ta ido ganin wata lafiyaryiyar fata tamkar ka matsa jini ya bulo harda wani gashi gashi a kwance,


Yace"ae nufi na kin Makara baki zo naganki da wuri ba,


Murmushi tayi tana gyara zaman hijab dinta ganin yadda yake satar kallon hannunta ,tayi gaba kawai ta rabu dashi anan domin in Dan ta daka ta tashi sai su lalace anan gurin ,gashi dokar Makarantar babu soyayya tsakanin dalibi da daliba ballantana Malami da daliba dayawa Malamai da daliban makarantar basu fahimci Son ta yakeyi ba sai suke ganin kamar haduwar jini kawai kasancewar Maryam din tana da kokari cikin skull din gami da tsabbata da ladabi da biyyaya shiyasa kowane Malami yake son ta,










*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_


*NANA KHADIJA*


*YARO DA KUDI*


*GIMBIYA BALARABA*




πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[28/03, 00:52] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?






πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—






*✍🏻WRITTEN BY*
_*Binta Umar*_
*MAMAN ABADUL WAHABU*


~*MRS AHAMAD GWADABE*~






_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_
08089965176






*πŸ…Ώ34*








Har a katashi daga skull Maryam najin bakin cikin Abinda Uncle yayi mata.






Sabida haka ranta a bace ta shiga gida tun da get Baban gida yake Jan ta da wasa kamar yadda ya saba ,Amma bata tanka mashi ba tayi wucewarta ciki ko jiransu Nafi'u batayi ba idan sun gama shirmensu sa shi go domin su ma haushinsu takeji ganin A gabansu Uncle din yaci mata mutumchi basu nuna damuwarsu ba Sai kace shashashai suka zauna cikin motar duk dai yadda suke dashi ba kamar ita ba ne.








Aunty tana kallon yanayinta tasan yau halin nata ne ya motsa idan ba'ayi sa'a ba haka zata kwana ta yini bata kula kowa ba.




Tace"Aunty sannu da gida"


"Yawwa Maryam kundawo Lafiya"? Ina su Nafi'u?




"Suna can gurin Baban gida" tafada yayin da take kokarin shiga farlour nasu,






Tabe baki Aunty tayi tace"Miskili kafi mahaukaci ban haushi"


Ta cigaba da Aikinta cikin kwanciyar hankali.






*******


To Nasir yau kwata kwata bai fita yawo ba tun safe yana part dinshi a kulle bayan ya dawo daga motsa jiki bacci yake bai tashi ba sai bayan la'asar ,yana duba wayarshi miscall din Dady Har biyar ,gabanshi ne yafadi a fili yace Lallai yau a kwai rigima a gidan nan.






Mi kewa yayi da jiki a mace ya shige toilet domin wanka Alwala ya daura bayan yaga ma wanka n yafito ya kimtsa cikin qananun kaya As'usel sannan ya tada Sallah nan cikin dakin nashi Wanda in da da ne fita zaiyi suyi tare da su Malam Ya'u






Bayan ya idar yayi Addu'oinsa iya yadda ya sawwaqa ya mike daga kan daddumar ,yaje ya dauki wayarshi yana laluben numbar Dady nashi yasan yau sai ya sha fada






Bugu daya tayi Alh Huseen ya daga gami da gyaran Murya.




Kwantar da kansa yayi kamar wani mummuni yace"Dady barka da Yam a"?




"Barka kadai" mai kakeyi tun dazu nakira wayarka ya kai sau biyar baka daga ba"? Ko kana can gurin shadgancin naka"




Shafa kai ya soma tamkar yana gabanshi yace"Aa Dady wallahi ina gida ma"




Da sauri Dady yace "kana gida kanaji ina kiran wayarka kaqi dagawa ko sabida kar in dame ka? Yafada cikin bacin rai!




"Aa No" Dady ba haka bane Bacci nake yi ne wallahi kasan A kwai gajiya a tare dani ban gama watstsakewa ba" yafada kamar gaske.




"A kwai gajiya a tare da kai Amma duk dare kana waje Dady yafada cikin tuhuma




Dariya yafara qasa qasa yace dady kenan kasan ina da Abokai sosai So Dole in Dan fita mu gaggaisa da juna"






Tsaki Dady n yaja yace" Mubar wannan Maganar duk Abinda kake ciki nasani Nasir babu Abunda zaka boye min"




"Ok dady Mubar ta tunda ba kaso" Nasir din yafada hankalinshi kwance




Dady ya cigaba da Cewa" kana sane dai dacewar Monday ta Sama zaka fara Aiki ko A sabon Asibitinka ko?




"Eh dady Ina sane "






Ok A kwa likitoci da Muka tanada Manya zamu riqa biyansu Albashi mai tsoka domin su ruqa taimakon Al'umar Musulmi" dady yafada yana sauke nuffashi






"Ok Dady ae babu damuwa nima can Ina da wasu da Nayi wa Alkwarin daukarsu Aiki Abokan karatu nane duk Mata ne Amma ba"yan Najeria ba ne
Daya a gana take daya kuma can kudu ne ban dai riq sunan garin nasu ba"




Dady yace"in dai ka Aminta dasu ae shikkenan mu dai muna bukatar wa"yanda zasu kawo mana ci gaba A gurin"






"Eh in sha Allahu Dady Teema da Mery sun San Akinsu zasu kawo cigaba"






Ok sai ka zauna dasu sosai ka yanke musu Albashi ko ?dady din yafada






"Eh in sha Allahu zan kira ko wacce a waya tazo mukara yin intervieo da su"




"Hakan yayi duk Wani shirye shirye ka gama shi kafin ranar bana son shashanci"




"Ok Dady kar kadamu duk yadda kace za'ayi haka"




Kashe Wayar Dady yayi ,




Sai yabi wayar da kallo yana sakin Murmushi ,A fili yace Dady na Momy kenan.




Ficewa yayi daga sheshen nasa kai tsaye part din Momy ya nufa kanshi a sunkuye yana faman daddana wayarshi,














*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_


*NANA KHADIJA*


*YARO DA KUDI*


*GIMBIYA BALARABA*




πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[30/03, 01:54] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?






πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—








*✍🏻WRITTEN BY*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~




_*WANNAN BOOK DIN NASIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_
08089965176






*πŸ…Ώ35*






Daga can bakin get ya hango Mutananshi su Nafi'u sun dawo daga makarantar isilamiyya Baban gida ya tsayar dasu yana tsokanar Maryam.


Bata tanka masa tayi gaba kawai tabarsu Nafi'u gurin domin tun safe takejin dacin Rai ita a rayuwarta ta tsani wulakanci da to zarci shiyasa bata shiga sabgar "yayan masu kudin unguwar ko a makaranta suka hadu kowa harkar gabanshi yake sai kaji suna ta yadda mata da habaici su nace sai girman kai ita ba" yar kowan kowa "yar mai gadi,






Tana hango Ancle ta dakata da tayi niyyar shiga gurin Momyn ,sai tafasa sabida ganin can ya nufa shima.






Kan ta a qasa cikin Niqab kamar ko da yaushe tazo ta wuce shi tayi bangaransu,




Yayi mata wata tsawa cike da Neman fitina yace"ke Aljana a kwaba tsaya nan gurin"






Tsayawa tayi jikinta a sanyaye sabida ta tsani wannan sunan da yake kiranta dashi wai Aljana wannan tsabar qiyayya dame tayi kama.




Ya karaso gurin Cikin Yanayin tafiyarshi ya tsaya daf da ita ya sanya hannu ya fuzge Niqab din ,yana mata wani wulakantaccen kallo yace" Ke Nan gidan ba gidan "yan Shi'a bane sannan bana "yan izala bane da zaki riqa sanya Abu kina rufe fuska sabida tsabar Munafurci da Annamimanci wallahi duk randa Na kara ganinki da wannan Abin sai nasa an lalata miki fuska.


Tunda yafara maganar kanta a kasa yake ,sai da yama tadago kai ta dallare shi da idonta da suke sakashi faduwar gaba,ta zuba masa shi!






Saurin dauke kansa yayi daga kanta gabanshi yana faduwa kamar ko da yaushe in ya kalli kwayar idon ta.




Sai ta sunkuya ta dauki niqab din kawai bata tan ka masa ba ,tana da gowa ya tattaro yawo ya tofa mata a fuska yana ya mutse fuska yabar gurin yana duba wayarsa jin kira ya shigo ,Anwar ne ya kirashi,




Maryam ko Niqab din ta sanya ta goge yawon da ya tofa Mata ta nufi bangaran nasu tana kukan bakin ciki wai ita yaya zatayi da Uncle ne a rayuwarta mai tayi masa ne mai zafi a rayuwa.


Allah yasa duk wannan Abun dake faruwa su malam Ya'u basa gani sabida tazarar dake tsakaninsu da get din




"Yace yaya kai ne mutumi na"




Daga daya bangaran Anwar yace"kai Nifa wannan "yar iskar ta takura min wai yau bata ganka ba gashi takira wayarka taji a kashe shine tun safe ta addabe ni lallai sai Na kawo ta gidan Ku"




"Wa cece wai"?




"Wacece kuwa in ba Baby ba"




"Mtsss wallahi kar ka sake ka kawo ta nan Allah ranka sai ya baci Ka sake ka nunawa Baby gidan nan zata zo ne kawai ta takura min"






"To kayi mata waya kawai yanzunan tace dani gata nan zuwa wai in kawo ta" yarinya sai kace mayya ta makale maka sai kace mu ba maza bane"






"Ae kuwa zan kira ta ni kai Na fara gajiya da nacin ta wallahi"






Dariya Anwar yayi yace "wato gishiri ya salance kenan?"






"Ko daya Wallahi jarabar ta ce ta ishe ni"




"Mtssss ae sai kayi A boy kasamu dama kake wasa da ita billahillazi dani nasamu damar ka da Sai na ragargaji "yan mata iya son rai Na"


Yaci gaba da cewa yanzu "yaya zanyi gurin yaudarar my Maryam dina ne Wallahi kwana nake tunanin ta gaskiya yarinyar ta hadu da yawa,






Dariya Nasir yayi yace" kazo kawai da zuman zaka Auri shegiya daga nan sai ka Aiwatar da qudirinka a kanta yan zunan ma ta dawo daga makaranta Wai ita lallai kintsatsstiya har da rufe fuska.








_DUK WACCE TA ZAGE MU KAN TA TA ZAGA LITTAFI DAI MUN SIYAR BA MUCE LALLAI KI SIYA BA DA BAMU YADDA DA KANMU BA BAZA MUCE MUN SIYAR BA SABIDA MUN SAN A KWAI MASU SIYA IN KE BAZAKI SIYA BA DAMA BAMA BUKATAR KI SIYA DIN DOMIN BAKI DA KUDIN SIYA SHIYASA KIKE RARAGEFE KIKE NEMAN NA BATI SIDDAN KI KARANTA ,BABU YADDA ZA'AYI MU BATA LOKACINMU MU YI RUBUTU BATARE DA MUNSAN A NASIYA BA

7 / 30