YARO DA KUDI Book Complete by Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romance

Chapter   23 / 30

66K to 69K   out of 87.2K words

Kawunka yazo har cikin falon nan ya karemin zagi sosai wai lallai sai ka auri diyarshi ,sabida haka mutukar nice Na haifeka dole ne ka aureta domin mu samu kwanciyar hankali"




Ranshi ya baci mutuka jin abinda Momy take fada masa




Yace"Momy kikace "uncle Salisu yazo gida ya zage ki to akan me"?




"Ga dalili nan na fada maka"
Momy tafada




"Ouk sabida a auri "yarshi yazo har gida ya zageki"
Yafada a zafafe sai huci yakeyi"


"Cam down My son, ban fada maka wannan magana ba fa domin ta daga maka hankali, kuma bance in kaje kayi mishi rashin kirki ba, ni dai kawai ga umarnin da na baka"






Shiru yayi kawai ya koma ya kwanta hade da rimtse idonsa lallai dole yayiwa tufkar hanci domin kuwa babu shegan da ya'isa yazo ya runka tadaga mahaifiyarshi hankali wallahi ,sabida a halin yanzu ita kadai ce ta rage masa
[31/05/2019 9:28 AM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"kayi shiru ba kace komai ba My son don Allah ka fitar dani kunya, wallahi nagaji da wannan cin mutumci"




Da kyar ya dago kanshi ya zuba mata idonshi wadanda suka sauya kala yace"Momy kinaso in auri Mubina ko"?




"Inaso mai My son"


"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu zan aureta tunda kinaso"




Momy ta saki fuska sosai tace"Allah yayi maka Albarka My son Ubangiji ya shiga al'amarinka, yadda kake bina kaima In sha Allahu naka yaran zasu bika"




Mikewa tsaye yayi yace"Momy nagode da addu'a, zan shiga ciki"




"Ba zakaci abinci ba ne"?
Momy ta tambayeshi




Shiru yayi yana Dan murmushi


Itama Murmushin tayi tace"OK zakayi halin naka ko"


Sai ya saki dariya kawai yace" Momy ni tun a motana na cika cikina,in kinason saura in dauko miki"




"A'a rabani da kayan zaqi nan"
Momy tafada tana tabe baki
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [31/05/2019 4:58 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*100*


Murmushi yayi kawai ya wuce dakinsa, zuciyarsa sai zafi take yi, shi yarasa mai yasa mutane sukeyin haka, amma dole zai tari Uncle dinsa, ya kiyaye zuwa gurin Momynshi yana bata mata rai duk abinda ya dameshi yafi mutumci ya tunkareshi da maganar
Amma Sam! Bazai yadda da bacin ran Momynshi ba.






Karfe goma shaura Abdul latif ya shigo gidan yayi parking din motarshi Nasir din ya kira a waya "hello Abdul din yafada bayan yaji andauki wayar


"Kashigo ne"?
Nasir din ya fada


"Eh kana part dinka ko kana gurin Momy"?


"Kashigo gurin Momy kawai"


"Ok"
Abdul yafada ya kashe wayar




Momy Na zaune cikin kwalliya kamar ko da yaushe, suka gaisa da Abdul cikin sakin fuska tana tambayarshi mutan gida


"Lafiya kalau Momy"


"To masha Allahu"


Nasir yana zaune kan kujera cin abinci ,hannunshi rike da waya yana latsawa Abdul ya karasa inda yake ya zauna kujara guda, gami da mika masa hannu
"Ya a kayi ne Alhaji"
Nasir yafada hannushi rike da hannun Abdul din




"Normal Alhaji"
Abdul yafada yana dariya




Yace"ya shirye-shirye"?


"Na kammala sai tafiya kawai"


"OK kasan abinda ya kawoni gurin ka"?


"Sai kafada"
Nasir ya fada yana danna waya




"Zan kawo maka takkadun Maryam ka duba don Allah ka dauke ta aiki a hospital dinka ,kasan a nan zan barta cikin Estet din mu Na family kafin in kammala ginina ,in kuma nasamu gurin zama zan dauketa mu tafi tare"




Ba tare da ya kalleshi ba yace"wacece Maryam"?




Abdul ya sha kunu yace"bana son iskanci fa"




Fuskarshi ya hade yace"ban fahimci wace Maryam kake nufi ba,ai shiyasa na tambayeka"


"Ok My wife dina yarinyar gidan nan"
Abdul yafada babu wasa a fuskarshi




Nasir ya dago kanshi yana kallonsa tsawon minti uku bai ce komai ba, ya saki Murmushi gami da cewa "a yanzu dai bama bukatar ma'aikata, in ma muna bukata to batayi ilimin da zata yi aiki a wannan asibitin ba"




"Mai kake nufi"?
Abdul yafada rai a bace




"Bana nufin komai"
Yafada hankalinshi Na kan wayarshi




"Look Nasir ka tsaya kayi min maganar da zan fahimta bafa na son wulakancin ka Wanda ka saba"
Abdul yafada ranshi a mugun bace




Momy ta waiwayo da sauri ganin yadda Abdul din yake daga murya tace"lafiya wai naji kuna magana Sama-sama"?
[31/05/2019 5:21 PM] ®Binta Umar Abbale: "Momy wai sabida yaron nan bai da kirki nace masa, ya dauki yarinyar nan aiki a asibitinsa, shine yake fada min magana"




Momy ta kalleshi tana murmushi tace"duk abin ai ba Na zafi bane Abdul wace yarinya kake magana a kai"




"Momy Maryam nake miki magana fa"




"Ok Dota wai"?


"Eh Momy"?
Abdul ya fada yana mikewa tsaye ranshi a bace




Momy ta kalli Nasir yana zaune har'ila yau hankalinshi na kan wayarshi




Tace"Myson Dan Allah ina Neman alfarma nima ka dauketa aiki,wai maiye duniyar ne ,tunda dai Abdul din ya amince tayi ai shikkenan , Wanda ya taimaki wani shima Allah zai tai makeshi"




"Momy ki rabu dashi don Allah kar Allah yasa ya dauketa zan cigaba da nema mata"




"A'a duk baza ayi haka ba , ka koma ka zauna mu kashe magana"
Momy tafada tana kallon Abdul din


A gogo ya kalla yace"Momy wucewa zanyi wallahi banason abin bacin rai , zamu iya rigima dashi yanzu"




Cikin mamaki Momy tace"akan mace zakuyi rigima da Dan uwanka Abdul"?




Kunya ta kamashi sai ya sunkuyar da kanshi kawai




Momy tace"koma ka zauna"


Ya koma ya zauna kawai gami da dauke kanshi yaki yadda ya kalli Nasir din


Shi kuwa babu abinda ya dameshi




Momy tace"Myson "mai kace a kan maganar"?




Tafi minti biyu kafin yayi magana, daga bisani yace"Momy ni a yanzu bani da lokaci amma zata iya zuwa gurin Dr Sofia tayi mata intervio shikkenan sai ta ajeta a matsayin da ya dace"






"To ai babu matsala sai taje din"
Momy tafada,ta cigaba da cewa kai Abdul kaji abinda yace"




"Momy babu komai ai sai taje tunda naima takeyi,Allah ya rufa asiri"




"Ameen ameen"
Momy tafada ta cigaba da cewa dan Allah kar Ku yadda wata mace ta farraqa tsakaninku kunji ko"




"Momy kar kidamu insha'Allah"
Abdul din yafada yana mikewa da niyyar tafiya yayiwa Momy sallama








Bayan fitarshi Momy tace"don Allah my son ka rage girman kan nan gami da izza domin babu inda zata kai ka"






Dariya yayi sosai har sai da habarshi ta lo6a yana kallon Momy din yace" Momy yaya ake girman kai don Allah mutane da dama suna fadin haka a gareni , basu San cewar ni haka nuture dina ne ba"






"E ai duk da haka my son kana karawa da wani ni dai nace ka daina"




"Insha Allahu Momy kiyi min addu'a"




Momy ta zauna suka cigaba da hira cikin so da kaunar juna.
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [01/06/2019 5:11 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*101*
Nasir bai tafi America ba sai da yaje gurin kawunshi Salisu, sabida yadda yaga Hankalin Momy shi ya tashi a kan al'amari, nan uncle Salisu ya rika kwantar da kanshi yana rarrashinsa, da yayi hakuri ya auri Mubina, Nasir yayi mamaki ganin yadda yake kwantar masa da kai sai kawai ya basar , yace" magana ta wuce amma don Allah kar ka kara tayarmin da hankalin Momy domin abinda kayi mata ya daga mata hankali, zan wuce america, sati biyu zanyi zan dawo in yaso sai muyi maganar, Abin mamaki Dadyn Mubina ya dinga washe baki yana shi wa Nasir albarka nan Nasir ya tafi ya barshi sai mamakinshi yake,lallai mutane basu da kirki, wato in kana da kudi komai kafada dai-dai ne ,shi kanshi yasan ba don Allah uncle din nashi yakeso ya hadashi aure da diyarshi ba.




****
Yau satin daya da tafiyar Nasir ,Abdul ma ya tafi bayan ya kammala komai na maganar aure rana kawai ake jira,cikin so da kaunar juna sukayi sallama da Maryam.




Momy kadaici duk ya dameta sai ta fito harbar gidan ta zauna kan kujera kawai nan su Nafi'u suke zama da'ita suna hira Maryam ma sai ta samu gurin zuwa , siyi ta hira cikin fahimta






Ranar Momy ta tashi ta shiga ciki sai ta bar wayarta kan kujera Maryam na zaune suna chating da Abdul sai Murmushi takeyi kawai da'alama hirar tana mata dadi




Wayar Momy tafara kara da sauri ta kalli fuskar wayar, Myson ta gani yana yawo a fuskar wayar.




Gabanta ya fadi tayi kamar ta dauka wata zuciyar tace kar ki dauka, wayar ta katse kafin ta farga wani kiran ya kara shigowa,




Sai da takusa katsewa sannan ta daga batare da tace uffan ba




Ajiyar zuciya taji yana saukewa kafin taji wani irin voice da ya kusa sumar da ita a zaune Momynahhh"
Taji ya fada yana ajiye numfashi






Shiru babu magana


"Please Momy kiyi min magana mana yinin yau banji muryarki ba ayyuka sun dame ni"




Maryam tana ta kokawa da zuciyarta, jikinta yayi bala'in daukar dumi domin Nasir ya gama kashe mata gangar jiki, gaskiya tana bala'in kaunar Nasir






"Momy"
Maryam taji yafada da ainihin muryarsa ,sai taji kamar ma acikin damuwa yake


Sai tayi saurin kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya daki-dai
[01/06/2019 5:38 PM] ®Binta Umar Abbale: Momy ta dawo gurin, ta kalli Maryam dake zaune tace"Dota na barki ke kadai ko"




Maryam tayi murmushi tace"A'a Momy chating nakeyi ma"






Wani kiran ne ya kara shigowa wayar Momy a karo na uku




Momy tayi saurin daukar wayar tana dariya




Tace"Myson yau nayi fushi ,nayi ta tsammanin kiranka tun da safe naji shiru nace Allah yasa lafiya"




Ajiyar zuciya ya sauke yace"Momy ina ta magana shine kika shareni ko"




Cikin mamaki tace"yaushe akayi haka, My son"?




"Yanzu Momy na kira sau biyu ina ta magana naji shiru"




Momy tayi murmushi tana kallon Maryam tace"ba nice na daga wayar ba Myson Dota ce wallahi ni Na shiga cikin gida"




Shiru yayi na minti biyu sannan yace"Momy mun gama magana da uncle ,in nadawo za mu tsayar da magana ina fatan haka yayi miki"




"Yayi dai-dai Allah yayi maka albarka"




"Ameen ameen Momyna"


Sukayi shira sama-sama sannan yayi mata sallama dama a cikin busy yake yanzu ma free ya samu shiyasa ya kirata sabida duk abinda yakeyi hankalinshi na kanta.






Bayan Momy ta aje waya ta kalli Maryam cikin murmushi tace"Dota Son'ya kira waya kinki magana mai yasa"?






Maryam tayi murmushi tana tunanin abinda zata ce ,da kyar dai tace "Momy kafin inyi magana ya kashe wayar shiyasa"




Dariya tayi tace"ina fatan dai kinje anyi miki intarvio kamar yadda ya fada"




"Momy ban je ba"




"Mai yasa Dota"


Shiru tayi kanta a kasa domin tun lokacin da Abdul ya fada mata ga yadda sukayi da Nasir wai lallai taje asibitinsa gurin wannan matar da ta tsana taji kwata-kwata aikin ya fice mata a rai sabida in har Sofia ce zata mata intervio sai dai ta hakura da aikin






Momy tace"ban sanki da haka ba Dota kije kinji ko tunda dai yace ki je babu matsala"






"Shikkenan Momy zanje insha Allahu gobe"




"Yawwa Dota Allah yayi miki albarka, kema na kusa yin missing dinki ko"?






Maryam ta rufe fuskarta da gyale tana murmushi




Momy ta rinka dariya tace"ke kam kin fiye kunya wallahi"




Da sauri Maryam ta mike ta bar gurin fuskarta a rufe






Momy ta bita da kallo tana dariya kawai tana girgiza kai Yarinyar tana burgeta sosai
[06/06, 01:50] +234 808 996 5176: [01/06/2019 6:28 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*102*


Lokaci yana ta matsowa Malam Ya'u yayi shirye-shiryensa aunty ma ba'a barta a baya ba tana ta gyara "yar ta Maryam kuwa ganin lokaci ya matso jikinta duk yayi sanyi komai take kokari takeyi soyyayar Nasir tanata sasakar zuciyarta tarasa yadda zatayi da komai bata jin dadinshi, saura kwana uku daurin aure Nasir ya dawo gada america, Momy ta rinka murna tare suka shirya masa abinci mai rai da lafiya ita da Maryam, shiyasa suna kammalawa Maryam ta gudu sabida Sam! Bata so yazo ya tadda ta ya ci mata mutumci


Momy ta rinka shi mata albarka


Wanka tayi ta kimtsa jikinta domin sunyi waya da Abdul yace gashi nan zuwa






Shi kuwa Nasir yana zaune Momy ta tisa shi a gaba tana lallabashi lallai sai yaci abinci shi kuma yana botsarewa




Momy ta kalleshi tana shan kunu tace" yanzu zamuyi fada dakai wallahi dube ka fa duk ka yi Dan wuya nasan baka cin abincin kirki ko a can sai ciye-ciyen da kasa ba"




Shagwaba yake mata sosai kamar wani yaro kankani


Ita ko kamar ta bashi abincin a baki haka takeji sabida yadda taga duk yayi rama sati biyu kacal shiyasa kwata-kwata bata kaunar taga yayi wata dugowar tafiya




Sai da yagama sangartarshi sannan ya fara cin abincin




Momy tace"ni har fargabar kayi aure nake sabida ban San matar taka ko zata tsaya ta kula da kai ba"




Murmushi kawai yake mata yana kara jin so da kaunarta cikin zuciyarsa




Bayan ya kammala ya goge bakinshi , ya maida hankalinshi kanta yace"Momy a wannan satin zan fitar da zakka, zanje can birnin kudu zanyi musu a can"




"Masha Allah my Son Allah ya kara albarka"




"Ameen Momy"
Nasir yafada yana mikewa yace"zanje inyi Wanka in kwanta in huta Momy"




Momy tace "Allah ya huce gajiya sai ka fito"




Dakinshi ya nufa komai tsaf-tsaf dashi sai qamshin turaran wuta yakeyi sai ya zube tarkacan dake hannunshi ya nufi toilet domin ya Dan watsa ruwa ko jikinshi ya warware dama wayoyinshi duk ya kashesu sabida yasan yanzu, za'aita damunshi a hanashi hutawa da Abbas kawai sukayi waya








Bayan ya fito ya sanye wando 3Q sai kawai ya kwanta kan bed dinshi yayi rigin gine gami da dafe kanshi da duk hannunwanshi, shi kadai yasan abinda yake damun zuciyarsa
[01/06/2019 7:30 PM] ®Binta Umar Abbale: Kullum abin kara kaimi yakeyi mutukar zai kwanta bacci babu dare babu rana sai yayi wannan masifaffaen mafarki wai gashi yana yin sex da yarinyar da yai wa muguwar tsana a rayuwarshi.




In ya farka kuka ne kawai baya yi sabida tsabar bakin ciki da bacin rai jikinshi kaca-kaca yake tashi dole komai dare yaje yayi Wanka ko da yaje america ma bata canza zani ba, sabida abin ma ya kara qaimi sabida yadda"yan matanshi na can suka matsa masa kullum sai sunzo sun dameshi, sai tayi da gaske yake tsallake kai dinsu domin yayi alkawari bazai kara kusantar zina ba ,shima romance din da yakeyi so yake Allah ya yaye masa






Da kyar bacci ya dauke shi mai dauke mafarkai kamar ko da yaushe yau ma haka ya tashi jikinshi kaca-kaca yayi ta jan tsaki dole ya sake wani wankan ya fito yanajin nauyin jikinshi sabida baccin magariba dama haka yake sawa jikin mutum duk ya mace




Momy ya samu zaune a farlo bayan yadawo daga sallah magariba sai kawai ya zube gabanta yana rike cikinshi






Momy tace "Lafiya My son"




"Momy marana ta dameni da ciwa wallahi"
Yafada yana rimtse idonsa




Kallonsa Momy tayi tana nazarinshi kadan ta dauke fuskarta tace" mai ya jawo maka ciwon Mara"?




"Momy ban sani ba nima"
Yafada yana kokarin bagarar da maganar




Momy tace"shiyasa banaso kake shaye-shayen kayan zaqin nan mybe sune suke haddasa maka ciwon"
Momy tafada tana kauda kanta sabida ta Riga ta gama fahimtar abinda yake damunshi.
[06/06, 01:50] +234 808 996 5176: [02/06/2019 6:54 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*103*


Shima bai sake cewa komai ba, kawai sai ya lumshe idonshi gami gyara kwanciya kan kujera
Momy ta rika satar kallonshi tana nazarinshi, dole ne ta matsa masa yayi aure ,sabida duk ta gama fahimtar abinda yake damunshi, ta sauke ajiyar zuciya kana tace"Myson " bude idonshi yayi ya zuba mata su, tace"Yaushe kuka tsayar da maganar daurin auran"?
Zakudawa yayi yana ciccije bakinshi yace"zamuyi waya in anjima" Momy tace"mai zai hana a hada dana Abdul, nan da sati biyu masu zuwa" gabanshi ne ya fadi jin abinda Momy tace, amma sai ya gwada mata halin nashi




Yace"Momy waye Abdul kuma"


Girgiza kai kawai tayi sabida ta San halin kayanta




"Abdul latif na kawunka Muktar"


Yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi


"Kayi shiru baka ce komai ba"


"Wane date ne"?


"Ai lokaci yayi nan da sati biyu masu zuwa"


Gabanshi ya rika wani irin bugawa fat!fat!fat , ta tabbata kenan Abdul zai auri ta batare da ya kawar da wannan muguwar sha'awar tata dake damunsa ba


Jikinshi yayi bala'in sanyi sosai da sosai


Yace"shikkenan Momy Allah ya nuna mana sai ayi yanda kikace"




"Allah yayi maka albarka,My son"
Momy tafada


"Ameen ameen Momy"


"Yanzu wane shirye-shirye kakeyi, yau tilas kaje gurin Mubina ku gaisa"




"To Momy za'ayi"
Yafada idansa a lumshe




Momy taga duk yayi sanyi tace" naga jikinka yayi sanyi My son ko Na takura maka ne"?




"A'a Momy ina da damuwa ne"




Ita ma jikinta tayi sanyi Yaron ta yana cikin damuwa lallai itama tana cikinta






"Kafadi min abinda duk yake damunka"?
Momy tafada babu alamun wasa a tartare da ita,gaba daya ta maida hankalinta kanshi




Shiru yayi yana da wurwurar abin cikin zuciyarsa yana jin ya fada mata ko kar ya fada mata.






Momy ta kara maimai tamasa tambayarta.




A jiyar zuciya ya sauke gami da bude idonshi sannan ya gyara zamanshi yana kallonta yace"Momy wani mafarki nakeyi Wanda yake damun zuciyata kuma ba da kowa nakeyi ba sai da wannan yarinyar ta cikin gidan nan, shiyasa nace miki mayu ne, kinki yadda Momy yarinyar ta rike wuta a kaina kullum sai tazo cikin bacci Na ta takura min babu dare babu rana Momy ina cikin musiba"
Ya karashe maganar gwanin tausayi, domin shi abin ma tsoro yake bashi
[02/06/2019 9:11 AM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"wane irin mafarki ne wannan My son"?




Shiru yayi


"Tambayarka nake fa"


"Momy mubar maganar"


"Naqi bari"
Momy tafada kai tsaye idanta tsaye a kanshi




Murmushi yake shima ya zuba ma ido


Momy tsaf ta fahimci abinda yake damunsa


Tace"My son fitinar ka yawa gareta,Allah ya rufa asiri"


Dariya ce ta subuce masa ya dinga yi




Momy itama dariya take tana girgiza kai


Yace"yau hutawa zanyi Momy babu inda zani"




"Gwara ka huta ai,amma dai dole da yamma kaje gurin Mubina ko"




"Eh Momy yanzu ma sabida ita na kashe wayana sabida tun ina jirgi take takuramin"




Dariya Momy tayi tace"soyayarku a ta mussaman ce"




"Wane irin ta mussaman Momy nifa Sam bata yi min ba wallahi Dan dai kawai Na faranta miki rai ne"




"Nima nasani Myson yarinyar tarbiya bata isheta ba ,amma in dai tana sonka zaka iya juyata kayi mata tarbiya"






Tabe baki yayi yace"wani babban abin haushi ma ,Hanifa kanwarta tana tan tana tada hankalinta sai faman shirme take min a waya wai yaya zanyi mata haka"




"Wace Hanifa kake magana"
Momy tafada cikin mamaki




"Kanwarta, itama wai sona take Mtsss




Momy tayi dariya tace"to Allah ya sawaqe,Allah ya kawomu wani zamani ni "yasu"






"Momy shashanci ne da iskanci kawai babu maganar zamani anan"


"Allah ya kyauta"
Momy tafada


Nan dai suka zauna hira sama -sama har wajejan sha biyu Na dare ,sannan Momy tace yaje ya kwanta




Yana shiga dakinshi ya kunna wayoyinshi nan da nan sakkoni suka rika shigowa, ko sauraron wayar baiyi ba sai da yayi Wanka yayi shirin bacci sannan ya fara duba sakkonin




Message din Mubina sun fi goma tsaki ya ja yafara duba sakkonin mutanenshi, wayarshi tafara kara sunan Mubina yana yawo kan fuskar wayar


Kin dagawa yayi har ta katse , ta kara kira a karo na biyu nan

23 / 30