Author : halima Abdullahi K Mashi Category : Romance
Hakanan ko qaramin yaro ya nuna masa kurensa a harkar karatu yana kar6a. Sannan ko yau yayi tafsir, bayan ya tashi wani yace masa, jiya fa kaza ba daidai bane, in ya dawo gobe zaiyi bayani cewa jiya nace kaza, ba daidai bane, wani dan uwa yayi min gyara. Haka nan shi yayi imani cewa, daukaka ta Allah ce, ba wai iliminsa ne ya kaishi ba. Daukaka daban, ilimi da hikimar wa'azi daban. Ismail ya zama cikin uzurin da sai yayi kwanaki baije gidansu Mimi ba. Ita kuwa Mimi sai take zargin ko don yaga ya soma zama wani abu shine zaija baya dasu. Yau kwana uku tanason ganinsa don taji wacece matarsa din daya bada sadaka harda ita. Amma baizo ba, saidai su ganshi a TV in yana tafsir ko lacca, wadda aketa faman gayyatarsa. Yana yiwa maza ko mata, wata lacca da aka nuna yayi wa mata mai taken Ramadan lacca. Tasha mamakin yadda yake fadawa mata su riqe mazajensu, da hanyoyin kula da miji. Ya kuma kwadaita musu irin romon ladan da zasu samu a gurin mahaliccinsu. Sai taga duk ta zama wata sokuwa, domin ita kanta da take macen bata san abubuwan dashi ya sani ba, na game da yadda ita kanta mace zata kula da kanta. Ta jima tana Mamaki, kuma ta sake yarda Ismail ya dara kallon da takeyi masa.6⃣3⃣Shikam Ismail yakan kira yaya Amina su gaisa, yaji lafiyar Mimi a gurinta, kuma tana sanar da Mimin, domin bashida lokacin kansa. Ba su suka ga Ismail ba, sai azumi yana ashirin, misalin qarfe uku, lokacin Ummi tana daga citta zata kai niqan geron kunun tsamiya, ta gai dashi. Ya amsa tare da cewa, ina mamanki? Mimi qin dago kai tayi. Ummi tace, tana ciki. Yaya ce ta fito tana fadin dan gyangyadi ne ya soma dauka ta, sai kuma naji muryarka sama-sama. Yace, nine kun ganni sai yau. Ya saci kallon Mimi, cikin zolaya yace, 'yar amanata ma na lura fushi takeyi dani. Ko kallo ban isheta ba. Mimi ta dago ta dubeshi, ya dan rame, hakan sai ya qara masa kyau. Shaddar jikinsa mai tsada ce sosai, mai ruwan siminti, hular kansa ta dace sosai. Ta maida kanta taci gaba da firar dankalin da dama shi takeyi tun kafin ya shigo. Ta kammala ta kwashe 6awon sannan ta kai kicin ta wanke hannunta, duk yana kallonta, suna 'yar hira da yaya. Ta zo ta shige dakinta. Ya bita tare da cema yaya, bari inyi lallashi. Can saman Gadonta ta harde qafafun ta. Ya shigo da sallama,a ciki ta amsa. Ya tsaya a gaban gadon, "yau fushi kkyi dani? To, kiyi haquri. Ya ranqwafo tare da sa hannuwansa duka biyu ya dafa gadon. Kinji. Sam ta kasa fada masa cewa, rashin ganinsa ne ya bata haushi. Sai ta kauda kai. Yace, kullum ina fada ma yaya ta gaisheki, sannan ina fada mata uzururruka na, ko bata fada miki? Ta turo baki, ni fa rashin zuwanka bai dameni ba. Cewa din dakai ni matarka ce. Ya zauna, na fada a ina? Cikin salon shagwa6arta ta nuna TV, "anan mana, daka bada sadaka, harma kace, da na yaya. Yayi murmushi, yana son salon shagwa6arta. Yace amma nace matata khadija? Ni fa nufina wadda zan aura. Ta ware idanunta ta kalleshi, zakayi aure ne? Yace eh mana insha Allah. Ta ta6a baki tare da cewa, Hu'um! Zuciyarta fal da takaici. Ta dubeshi, "to ni yaushe zamu rabu? Tayi tambayar cikin daurewar fuska yace, kinsan dai ko ba lokacin azumi ba, laifi ne mace ta nemi a sake ta, babban laifi ne ko!? Ta sake turo baki, ai shi ma alqawari cikashi abu ne mai kyau ko? Yayi murmushi, "haka ne, amma banda haramtaccen alqawari. Ina nufin kayi alqawarin laifi. Misali mutum ne yayi alqawarin aikata wani laifi da Allah baya so, to ba'ason ya cika. Tace, jiya fa naji kana cewa saki halasne, a cikin tafsirinka. Yace, sai kuma nace me? Allah baya sonshi, dukda halas ne. Na lura in kinyi ilimi nan gaba za'ayi fama dake kema.6⃣4⃣Yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi 'yan dari biyar-biyar. Yace zan sallameku sbd batun sallah dake gabatowa. Tace, ai yaya zaka bawa kudi. Ni ina zuwa kasuwa? Yace, nima bance kije kasuwa ba ai. Tace, to naga zaka bani kudi ne. Yace na fasa baki ki shirya gobe muje tare. Tace, kana son sole sai wanda ya sanni ya ganni kai kam. To shikenan, ki rubuta min abinda kk so. Ya miqe ya shiga dakin yaya ya qirga dubu goma ya bata, yace ta saima yara kayan sallah. Tayi godiya tare da cewa, kaima da kk fama da kanka. Kaima fa dalibi ne har ynxu. Yace wani bawan Allah ne ya sameni nayi masa bayanin yadda zai fidda zakkarsa, shine da ya cire ya bani. Yaya tace, Allah ya taimaka. Ai ranar da kayi wa'azin zakkarnan, dole zukatan mutane su raunana, indai da sauran imani, su fito da zakkar su ba da. Yace kinsan kudi shiga zuci ne dasu. Sai su dinga ganin kamar in sun bada zakka kudin zai qare. Ba su san in sun cire haqqin Allah daga cikin dukiyarsu ba, Allah zaisa musu albarka, qila ma tafi ta da. Tace, rannan ma munji ka bada sadaka harda mu. Allah ya saka da alheri. Yace, Amin. Tare da miqewa. Ya koma dakin Mimi, "bani in kin rubuta. Ta miqa masa 'yar guntuwar takarda. Ya amsa, ya bude. Sai yaga ta rubuta cewa, duk abinda ya sauwaqa. Ya kalleta, zuciyarsa dajin dadin hakan da tayi. Yace nasan ba zan iya sai miki abinda kk so ba, amma zanyi iyakacin qoqarina. Ya juya ya fita. Kwana uku bayan nan, Ismail yazo Gidan da safe, misalin qarfe takwas, Mimi tana varcin safe. Ya gaisa da yaya sannan ya shiga dakinta. Bai mata dogon kallo ba, ya aje ledar hannunsa ya duba durowar gefen gadonta ya dauko takarda da biro ya rubuta cewa, ga kayan nan, in kin farka ya ke mai yin kyau a varci. Ya dora takardar a tafin hannunta. Sannan ya fice, yayi sallama da yaya ya wuce.
[25/09 9:28 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa
6⃣5⃣Mimi kuwa tana farkawa taji da abu a hannunta, sai ta duba, taga abinda ya rubuta. Sai tayi murmushi tace, waton in idanuna biyu banida kyau, amma a varci inada kyau. Ta dauki ledar ta bude, wani tsadadden leshi ne mai kalar 6awon dorawa, sai Atamfa 'yar England sai takalma masu kyau da tsada. Ba anan tasha mamaki ba, saida taga irin man shafawarta da hodarta, sai kuma jan bakin da take shafawa. A fili tace, "ina Ismail yasan wadannan? Lallai zan tambaye shi inji. Ta ciro hijabai dogaye guda uku, sai niqabi guda daya. Tace, wai harda wannan yakeson in sa, ta6! Na dai saka hijabin in zanyi sallah. Ta kaima yaya ta gani. Suka tayata murna. Tace, in yazo anjima sai ince yakai dinki ko? Yaya tace, eh kam ya kai don inda na kai nasu Ummi macece, kuma ba wani qwarewa tayi ba. Dama su Ismail sun kafa kwamiti qarqashin jagorancin Mahmud inda za'a dauki sunayen marayun Unguwar, da na kusa dasu. Don haka sai suka sai kayan abinci dana sallah na yara, maza da mata. Sannan sukaje suka kai ziyara gidan yari, inda yayi musu wa'azi tare da basu taimako. Ana saura kwana biyu sallah, ya kawo masu Mimi cefane jibgi guda, da kuma kaji, sannan Washegari ranar jajibiri masu hali sukayi ta aiko masa da nama cikin manyan ledoji. Yaba Malam Aminu, harda Mahmud, sannan ya miqa cikin gidansu. Irin wadannan abubuwan suna burge Mimi.6⃣6⃣Hasana da usaina suna zaune suna kallon rufe tafsir din Ismail, Hasana tace, kai Malam yayi wlh! Na qosa daddy yayi mana izinin zuwa muga sis Mimi. Itama nasan ynxun ta hadu. Usaina tace, ai na dauki number din da ya bada wadda yace mutane suyi message kawai banda kira in sunada tambaya, so muyi masa text cewa, mune. Sainya fada mana gidansu, sai muje muga sis Mimi. Muryar Hajiya sauda ta katsesu da cewa, Allah yasa in samu labari. Wai ba ku nace ma tana lfy bane. Kuma fa na fada muku cewa, akwai matsala in munyi yunqurin zuwa gurinta zata sake guduwa. Karku damu tunda muna samun labarinta. Muyi ta Addu'a komai zai wuce. Hasana tace, Hajiya shi Malam a matsayinsa na Malami ba sai ya nemi lambarki ba kiji komai daga bakinsa? Usaina tace, ya fa san nan gidan meyasa ma ba zaizo ba? Hajiya sauda tace, Nice da laifi, don na tura masa saqo cewa, naji dalilan mahaifin Mimi, kuma na gamsu dashi. Don haka nima zaka jini shiru. Kaima kayi haquri karka sake nemana ko a waya. Ina mai sake baka amanarta. Lokaci yana zuwa da zamu nemeka da kanmu. Kunji tun daga lokacin ban sake nemanshi ba, shima bai sake ji daga gareni ba. Hasana tace, to sai zuwa yaushe ne sannan za'aje gurinta? Usaina tace, ke kam kamar bada hausa Hajiya tayi magana ba? Hajiya sauda tace, zaku soma musunku ko? To ni nayi nan! Ta nufi kicin. Ranar sallah, Ismail ya matsawa Mimi wai ta shirya suje masallaci. Da ma tun ranar jajibiri yake fada mata lokacin da yazo ya kawo mata dinkinta. Tace, ba zataje ba, qila 'yan gidansu zasuje. Yace, ba ga niqabinki ba, sai ki 6oye fuskarki, dama amfaninsa kenan. Zama haka ba ya yiwuwa Mimi, dole sai da dan fita ana dan motsa jiki. Balle sallar idi wadda daga shekara sai shekara. Ba tada za6i dole ta shirya cikin leshinta, yayi mata kyau matuqa, tayi alwalla, sannan ta shafa hodarta da jan baki, ta saka hijabin da niqabi. Suka fito tace, yiwa yaya sallama. Ummi ma da take ta rabon abinci gidajen maqota tayi kyau cikin kayan sallarta. Su kuwa su saddam dama sun tafi da abbansu a mashin.6⃣7⃣Ismail yayi kyau cikin wani tsadadden yadi, mai ruwan madara, malum-malum ce ta dauki aiki. Hularsa da takalminsa sun dace da kayansa. Yayi kyau matuqa. Ita kanta Mimi lokacin da ya shigo Gidan, sai da Zuciyarta ta buga. Daga lokacin da Ismail ya soma tafsir zuwa ranar sallah, yayi abokai kala-kala, kowa yanason ace suna hulda, masu da kuma talakawa. Daga cikinsu ne wani yazo har gida ya daukeshi, shine yace, su biyo ya dauki matarsa. Mutane sukanyi mamakin ganin Ismail a wani guri daban. Duk wanda ya tambayeshi yakan ce masa, shi ba lazauni bane. Matarsa kuma ba tada isasshiyar lfy, shiyasa ya barta gidan yayarsa. Bayan sun dawo sallah ne Ismail yaci abinci anan gidan, sannan ya miqe zai fita. Sai Mimi taji sam batason ya fita. Amma ba tada ikon hanashi, wani sonshi ne taji a cikin Zuciyarta. Tana kallonshi ya fice. Bayan sallah da kwana tara Ismail suka shirya nasu-yanasu sai makaranta. A ranar ne Mimi taji inama itace, Rabi'a. Ranar ce, tayi kuka sosai, wanda batasan ko na menene ba. Ismail yayi zaton ko tana yi ne don bai saketa ba. Sai yace, karki damu khadija, shekara kamar kwana ce, in na dawo komai zaizo qarshe, kinji? Bayan tafiyarsu tayi ta dana sanin qin yarda da tayi ya sai mata waya. Amma tace, bataso. A fili tace, kashh! Menene ma zai sa ince ban son waya? Tsaki taja, tare dayin tagumi. Ynxun kam ta gama fahimtar cewa, Zuciyarta tana matuqar son Ismail, sai dai tsoronta daya shine, shi baya sonta. In ba zata manta ba ya sha fadin cewa, shi mace mai kyau yakeso ya aura. Tuna hakan sai taji jikinta ya mutu. Ta kalli kudin daya bata kafin ya tafi. A fili tace, dole ne in nemi wanda zai siyomin waya ko don in hada hulda dashi. Tsaki taja, a ranta tace, ta yarda jama'a rahama ne, inda tana hulda dasu da ynxun ta samu mai siyo mata. Dakin yaya Amina taje, tace yaya inason a siyomin waya ne. Yaya Amina tasha mamaki, "ke kuwa meya hanaki yarda Ismail ya siya miki? Don nasan babba zai sai miki. Tace, lokacin banason wayarne, amma inasonta ko don inji Rediyo. Amma fa karki fadama kawun su Ummi. Tace, shikenan ki kawo sai qanin abban su saddam ya siyo miki. Ta dauko dubu bakwai, cikin dubu ashirin din da Ismail ya bata kafin ya tafi.
[25/09 9:30 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa
6⃣8⃣Zainabu kuwa tunda taga Ismail a TV, hankalinta yayi matuqar tashi. A fili tace, Ismail yafi qarfi na ynxun. Ta saka kukan takaici, tayi har ta gode ma Allah. Innarta cikin tsantan nadama tace, zainabu kiyi haquri, qila zaku hadu ne ko anan gaba. Tunda yana sonki, na san ma zai dawo gareki. Zainabu dai bata tanka ba. Innar ce da kanta ta fita neman labarin Ismail, har gidan mahaifinsa gurin su fatu. Anan ne fatu take fada mata cewa, Ismail yana madina garin manzo, dama zuwa yayi don can yake karatu. Ta qara da cewa, Ismail fa ya wuce da tunaninki, mu kanmu mun dangana bare ke. Dole mu dangana ko don alherin da yakeyi mana. Azumin nan shine geron kununmu, shine waken qosanmu. Da sallah tazo kuwa, zo kiyi kallon hidimar, dinkunanmu da yara, ke har cefanen sallah. Innar zainabu tace nima ai nadamar ta kawoni, ban san yaya zanyi da zainabu ba, taqi sauraron kowa. Fatu tace, dama ta saurari kowa, sbd Ismail da ya yafe tunaninta. jiki babu qarfi ta koma Gida.6⃣9⃣Ya zuwa wannan lokacin, rikicin su Na'ima ya kai su ga zuwa kotu, inda shi Abbas ke qarar Na'ima, akan ta bashi dansa. Ita kuma Na'ima tace, ba zata bada shi ba. Duka 6angaren guda biyu sun dauki lauyoyi. Inda ake fafatawa tare da dage zaman sauraron shari'ar. Nadama kuwa, Momy Nafisa tayi akan auren nan yafi cikin buhu. Ita kuwa Na'ima nata ganin alhakin Mimi ne. Duk lokacin da tace haka, sai momy Nafisa tace, ki daina wannan maganar, ai komai muqaddari ne. Na'ima tace, qaddarar da mutum yake qadddara ma kansa ba. Da mun bar Mimi ta aure shi, na tabbata hakan ba zai faru ba. Haka Allah yake ikonsa, sau da yawa sai mutum yayi ha'inci, sai kuma kaga ya dawo yana nadama. Kukan Na'ima da yawa, ita ba a karatunba, ita ba ga auren ba. Ynxun ne take burin in ya saketa, ta koma makaranta. Shi kuma yace, tana bashi dansa zai sake ta. Lauyoyinta suna ta zuba hujjojinsu kan cewa, dole ne ya saketa tare kuma da bar mata danta don itace tafi dacewa ta kula dashi. Su ma nasa lauyoyin hujjojinsu suke bajewa akan cewa shine yafi dacewa ya riqe dansa a matsayin sa na uba. Nidai nace, ku kuka sani, mu dai 'yan kallo ne.
Lokacin da aka kawo wa Mimi wayarta, ta hada ta tasa aka sai mata layi ta saka aciki. Number Ismail kawai ta dauka a cikin wayar yaya Amina. Wtsapp Mimi ta bude, cikin sa'a kuwa da lambar yakeyi, hotonsa ne ma yasa a D.P dinsa,yana sanye da farar jallabiya. A saudiyya ya dauki hoton daga gani. Wannan lokacin ma yana online. Mimi tayi murmushi sannan tayi masa sallama. Sam bai kula sallamarta ba, duk da tayi ta kusan sau goma. Tace, nasan yaya zanyi. Ta sauka daga kan wtsapp din ta tura masa message, da cewa. Dama haka malaman suke basa son sauraron al'ummarsu, balle su basu fatawa akan matsalolinsu? To, ka sani bin Abdurrahaman, in har na mutu ban samu mafita a matsalar da nake ciki ba, to ka sani har da kai zunubin, domin na kira baka daga ba. Kuma nayi maka magana ta wtsapp baka kula ni ba. To ynxun ga message dina nan. Tana turawa tayi murmushi, sai ta kashe wayar ta aje.7⃣0⃣Bata sake kunnawa ba sai bayan kwana uku. Tana kunnawa saqonni guda uku suka shigo, data duba daya na MTN, biyu na Ismail dama da Malam tayi saving. Murmushi tayi, sannan ta bude saqon. Gajerrn saqo ne, kawai cewa yayi, ki fadi matsalarki. 'yar dariya tayi don ganin cewa zatayi wasa da hankalinsa. Ta hau wtsapp nan ma saqon iri daya ne. Ta soma tunanin me zata rubuta masa, wanda zaija hankalinsa, ya saurareta? Sai ta soma rubuta cewa, Malam Allah ya sani tunda nake ban ta6a ji ko ganin matsala irin tawa ba, ko da a film ko kuma labarin qirqira. Sai ta tura masa. Daga nan sai ta kashe wayar. Washegari data hau wtsapp sai taga yace, ki fadi matsalarki kai tsaye ba tare da kin gutsutsura batun ba. Ke nake sauraro. Dariya tayi, sosai sannan ta tura masa cewa, roqo na da kai, shine in kaji wannan matsalar tawa ka taimakamin, kuma ko da kisan kai ne ya kasance hukunci na to zan dauka. Ta tura masa. Haka tayi ta tura masa wadannan saqonni na wasa da hankali, tun yana nuna mata yanason jin ko wace matsala ce, ta daina jin tsoronsa ta fada masa, har ya gaji yayi banza da ita. Tare da haka, in ya kira yaya Amina yakance, a bashi Mimi su gaisa. Cikin ja masa ajin data saba yi take amsa su gaisa. Inya tambayi matsala, sai tace babu. Kwancitashi su Ismail sun kammala karatu na digiri, tare da sakamako mai kyau. Hukumar qasar ta tuntu6i daliban da aka yaye a wannan shekarar, ko akwai wanda yakeson yin aiki tare da su bisa ga albashi mai tsoka? Su Ismail kam cewa sukayi sunfi son suzo su amfanar da ilimin da suka samo ga al'ummar qasarsu. Sannan Ismail yanason samun nasa iyalin, ya gaji haka.
Mimi bata ta6a yin murnar dawowar Ismail ba kamar wannan karon. Domin gsky tayi kewarsa, tanason ganinsa, sosai matuqa. Wani abu da ya sake burge ta shine tasha gwada Ismail da sim kala-kala, don taga ko yana hulda da mata, amma sai ta sameshi a natsattse wanda bashi da lokacin shashanci. Sun iso gida cike da murna da doki. saidai Ismail ya baro madina cike da burin komawa don samun digirinsa na biyu, in komai ya tafi masa daidai. Dakinsa ya sauka, wannan karon zai kama masauki amma sai ya saita lamuransa.7⃣1⃣Shi mahmud bashi da wannan matsalar