Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Canjin Rayuwa 4 Compelet Complete Hausa Novel by Halima Abdullahi K Mashi

Author :  halima Abdullahi K Mashi Category :  Romance

Chapter   14 / 15

39K to 42K   out of 43.9K words

katseta, baquwa kikayi. Ta kalli Mimi fuska rufe, tace to ta shigo daga ina? Mimi taje ta rungume mahaiyarta. Sannan ta daga niqabi. Da sauri tace, Mimi ce! Nan dai akayi ta murnar ganin Mimi. Amare suna gidan mai musu gyaran jiki. Da yake sai washegari Asabar ne za'a daura auren. Hajiya da kanta ta kirasu ta fada musu, sai gasu. Murna tamkar zu cinye ta. An kawo mata wannan da wancan duk an jibge mata, sai dai hankalinta yana can gurin mijinta. Hajiya sauda tasa ta gaba, tana cewa, in bakison wannan me zakici? Saboda kowa yaga tsohon cikinta. Ta kalli Hasana, "wai ina Malam ne, ko suna gare da daddy? Hajiya sauda tayi murmushi, yana tare dasu daddynku, harda sy yayanku. Sannan Mimi ta soma tsakurar abincin don batajin yunwa, kuma ta saba ci da Mijinta.
1⃣0⃣1⃣Su Hajiya Binta suka iso da yaranta. Ita ma rungume Mimi tayi don murna. Kowa sai mamakin ganinta yakeyi. 'yan uwan hajiya sauda da dama basu san Mimi ba , sunanta sukeji, yau sai gata gasu. Hatta kakarta saida aka nuna mata. Yau dai ta gane 'yan uwa dadi garesu. Ashe ita 'yar dangi ce, gaba da baya haka? Daddy ma sai kiranta yakeyi yana tambayarta ana bata duk abinda takeso ko? Dariya takeyi, sannan tace, ana bani daddy. Suna dakin daddy ita da Amaren, sbd ko ina mutane sun cika. Ta ce ku tashi muje gurin gyaran jikin, nima za ayi min. Ta ciro waya, "bari in fadama Malam zamu fita.Ta kira wayarsa, dai dai lokacin da ya daga Hajiya sauda ta shigo, tace, musu su koma gurin gyaran jikin. Sai taji mimi tace, Malamina, na zata zanga Miss call dinka? Ka shareni ko? Cikin sigar shagwa6a ta fada. Yace kinsan dai ko a mafarki My Dija ba zan shareki ba. Na barki ne ku walwala da 'gan uwanki. Tace kana inane ynxun? Yace inason zan tafi masallaci, amma sai na koma gida na dauki takardar budubar dana rubuta. In zan dawo zan biya in dauko yaya Amina. Tace da ka kyauta min. Ta zo dasu Ummi, kaji My Malam? Yace zan fada mata. Kina son wani abu ne daga gida? Tace, illa mai da hoda na, sai turare. Yace shikenan. Tace zamu fita da Amare. Yace zuwa ina? Tace inda za'a yi musu kwalliya. Take yaji bari ya gwada ta. Sai yace, a'a ki zauna ki huta abinki. Bata zata ba. Don haka ta danyi dim, sannan tace, shikenan Malam, sai kunzo din. Sosai ta burgeshi, ya san ko ina zatayi masa biyayya. Sai yace, Dijana kuje kawai, sai kun dawo. Tace Allah Malam in baka so, ba zanje ba. Yace, na tsokane ki ne kawai. Basu Hasana ba, hatta mahaifiyarta saida Mimi ta burgeta. Lallai Malam ismail ya ciri tuta. Hajiya sauda ta dauko zanin anko, da wasu sufofi guda uku, da lesuka masu tsada, ta kira telan su, ta bashi tare da cewa gobe takeson su, amma anko yau za'a dinka. Tela yace, an gama! Don yasan Hajiya akwai sauke kudin dinki. Haka bayan sun dawo gyaran jikin ne Hajiya sauda ta zube Hijabai kan gado sabbi sun kai kala goma, tace, Mimi ta za6a in ma tana sonsu duka ta kwashe, ga takalma da jakarsu. Mimi tace, Hajiya kin siyane dama kin ajiye? Tace a'a saida sj mukeyi. Su Hasana suke kaiwa makaranta. Daga baya kuma sai muka kama shago. Odarsu ma mukeyi yanxun daga dubai da china. Mimi ta za6a, ta kuma za6arma yaya Amina, itama harda jaka da takalmi.
1⃣0⃣2⃣Qarfe uku akayi kamun Amare, lokacin ne kuma za'a saka anko. Mimi tayi kyau matuqa, duk da cikinta yasa tayi qiba. Kwalliyarta tasa ta saje da amare, duk da itama har ynxun da 6ur6ushin amarci, tunda bata dade da fara amarcin ba. Jeren kumbo ne akayi. Wannan karon ne na farko da Mimi taga irin bikin nan, kuma yayi matuqar burgeta. Yaya Amina sun iso da yaranta sunga tarba gurin Hajiya da ita kanta Hajiyar. Sunci, sunsha, sannan aka kwashe su a mota zuwa gidansu yaya Abba inda acan ake kamu din. Sai dare sannan Ismail ya kira Mimi yace, su yaya Amina su fito ya maida su gida. Tace abar Ummi, tunda zasu dawo gobe, sbd gobe ne daurin aure. Hajiya ta had musu kayan biki. Mimi ce ta raka su har gurin mijinta. Sun shiga mota, shi kuma ya fito, suka ke6e da Mimi. Yace, ke kam nasan sai an gama biki ko? Tace, sai yadda kace. In kuma kafison na koma, sai mu tafi, ka kawoni da safe. Ya kai hannu ya kama nata, ki zauna kuyi bikinku. Daddy ma dazu yace min, wai inyi haquri sai an gama biki, in barki. Tace ai yadda kasan yana tsoron kar in gudu, ba ayin awa daga bai kira layina ba. Ismail yayi dariya, gurina ya amshi lambar. Ya murza hannunta, yau zanyi kewarku, da dana. Tace mu ma haka. Har ya kai mota zai shiga, ta ce Malam! Ya dawo, tayi qasa da murya saitin kunnensa, "don Allah kar kayi tunanin kowa sai nawa. Ya shafi kumatunta. Yace ai kinyi kane-kane a zuciyar nan. Baki bar gurin da zata tuna wata ba. Zan kiraki an jima, in bakiyi barci ba. Ta shafi kumatunsa, zan jira ka. Saida motarsa ta fice, sannan Mimi ta juya zata koma cikin gida. Ashe duk daddy yana kallonsu daga inda yake zaune. Sai ya fito ya kira Mimi, Uwata! Da sauri ta nufeshi tace, ina ka 6oye daddynh, tun dazu banganka ba, sai dai waya. Yace muna ta fama da jama'a Uwata. Naga mijinki ya tafi. Tace yayarsa ce da yaranta. Yace naji dadin ganin yadda kuke da mijinki, kina sonshi, kuma naji dadin ganin yadda kk samu canjin rayuwa. Tace daddy kullum ina saka cikin addu'a Allahvya saka maka da Aljannarsa, sbd kalar mijin daka za6amin. Yana sona sosai daddy. Kuma shine ya nuna min hanyar wuta data aljanna. Daddy ka yafemin laifukan dan yi mak.
[29/09 2:42 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣0⃣3⃣Yace, Mimi ba kiyi laifi ba, daidai kk yi da kk gudu. Kinga momynki a bikin nan? Mimi tace, Inason in tambaya, amma sai abin ya shigemin. Ya bata labarin komai. Yace, ynxun haka Na'ima tananan gida. Momyn ku suna bikin qaninta shiyasa bata zo ba, amma Na'ima kunyar fita takeyi. Ko makaranta sai dai tasa hijabi. Mimi tayi ta mamakin Abbas, tace ban zaci zaiyi haka ba daddy. Shima yace, nima ban zaci basuda tarbiyya ba, har na takura rayuwarki. Ai nine silan komai. Kije ki kwanta. Zamuyi magana, sai an watse biki. Gado daya suka kwanta da Hajiya sauda. Mimi tasha labarinsu Na'ima. Hajiya sauda tace, ai gara wahalar da kk sha, da ace ke kk auri Abbas. Daddynku fa har cewa yai gara da Allah yada kk bijire masa. Mimi tace, ni ko inacan ina dana sanin bijire masa. Kuma lokacin don dai Nomy Nafisa tace min duk abinda Za'ayi kar in yarda, wai daddy yace in naqi yarda zaya haqura. Sai daga baya na gane kamar da makirci. Nan dai Mimi taba Hajiya sauda labarin komai. Hajiya tace, saida Hajiya Binta tayi zancen nan, amma nace kar a zargeta, dama 'yarta take son takai gidan. To ai in baka da haqqin mutum, gashinan yadda suka kwashe. Sun raba dare, suna hira kafin sukayi varci. Washe gari daurin aure, ansha sha'ani. Tela ya kawo dinkunan Mimi, sai shiga takeyi tana fita. Yaya Amina sunzo harda Rabi'a. Mahmud ya kawota don shima yayi mota. Sun ga kula, kuma sun kwashi kayan walima. Shi dai Ismail sai kallon Mimi yake, sbd kyawun data qara. Ta jashi ciki, wai ya gaida su kakarta, da kuma dangin mamanta. Inna sa'ade tace wannan Malamin nan bane shaikh Ismail bin Abdurrahman? Mimi tace, shine. "Dama shine mai gidanki? Mimi cike da alfahari tace shine. Sukayi ta sa masa albarka. Suna fadin shirye-shiryensa da suke kallo, da kuma irin qaruwar da sukeyi.
1⃣0⃣4⃣Haka da suka ratso ta falon mata, sai gaida shi akeyi irin gaisjwar ban girma, wadda mazoya suke yiwa wanda suke so. Haka biki ya tashi, sbd Amare sunada nisa. Mimi taso zuwa kai Amare. Daddy yace, ki bari ki sauka lfy, sai kije ma kowa. Tace to shikenan, ba don ranta yaso ba. Ta haqura don dan zaman nan ta san dadin 'yan uwa. Washegari duk mutane 'yan biki suna ta tafiya, don haka Mimi sake kwana tayi. Hajiya Binta da zasu wuce tace ma Mimi, sai kin haihu kuma zamu zo. Har mota mimi ta rakasu.
Yau dai Alhaji da Hajiya da kuma Mimi sun zauna sun sha labari, inda Mimi ta basu labarin bayan rabuwa, suma suka bata. Kuma taji mamakin yadda Alhaji yabi diddigin inda suke. Ashe shine ma ya ba ismail gidannan. Kuma sai yau Alhaji ya gano Nafisa ta hada komai, don mimi ta fada masa har yadda tasa ta ta turo masa text. Ransa ya 6aci, kuma yace, sai yaci mata mutunci. Hajiya sauda tace, a'a karka yi mata komai. Banqi ka fada mata ba, don tasan ka sani. Amma ai Allah ya gama nuna mata sakamakon maci amana. Mimi tace, hakane daddy. Take ta kira ismail, ta fada masa yazo, shima yasha labari. Kuma sai ranar yaji dalilin daddy na sharesu, kuma ya gamsu. Domin in har Mimi tana cikin gatanta ba zata juyu agareshi ba. Sun bar gidan goman dare. Bayan motar su shaqe da abubuwan biki. Suna kwance sunyi kewar juna tace, Malamina yaushe zamu koma Abuja? Yace sauran kwana uku, kin manta ko? Tace na manta sosai kuwa. Ai naji dadin zuwa gida lokacin bakinnan . Naga 'yan uwa, sun ganni. Ta rungumo shi, Allah barni da kai har abada. Yace, Amin tace, kayimin alqawarin cewa ba zakayi min kishiya ba. Yace, Dija banida ra'ayi, amma bansan qaddarata ba. Ina son kema kimin alqawari, in qara aure yana cikin qaddarata ba zaki juyamin baya ba. Ta qanqameshi, "nayi maka, amma zan shiga wani mawuyacin hali, sbd ina tsananin sonka.
[30/09 6:43 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣0⃣5⃣Washegari sunyi girke-girke sbd ziyarar dasu daddy zasu kawo musu, da su yaya Abba da sauran qannenta. Yaya Amina da Rabi'a sune suka taya su. Gidan tamkar biki, haka ya cika. Daddy yaba Mimi kyaututtuka sannan kuma ya fada musu yaba sauran 'ya'yansa irinsu, sakamakon wa'azin da yaji a wani kaset daya kalla na Ismail, mai taken yin adalci ga iyali. Sannan yayi wa ismail kyautar qaton fili, yace ya gina irin makarantar da yakeso. Take ya yanke shawarar zai gina jami'a ta musulunci, duk da ya san ba abune mai sauqi ba, amma zaiyi hakan. Su Malam Aminu sun samu kyaututtuka. Shi kujerar makka, mahmud gida. Sunkai har dare a gidan, sannan suka tafi. Ranar da zasu koma Abuja, sunzo sallama daddy yaba su makullin wani gidansa dake Asokoro, yace su zauna har sai ranar da suka gaji suka tashi don kansu. Ranar wata talata, Mimi ta tashi da naquda, ismail bai fadama kowa ba, saida ta haihu. Kuma abin da ya burge malaman asibitin mai zaman kansa, yadda ismail ya shiga har cikin dakin haihuwar yana shafa kan matarsa tare da lallashi da addu'o'i har ta haifi santalelen yaron su mai kama da su. Hajiya sauda ya soma fadawa, sai daddy da kuma su yaya Amina. Duk da sun yanke cewa gida zata dawo, saida su Hajiya sauda sukaje Asibitin da take a Abuja. Shi kansa Alhajin saida yazo. Momy Nafisa tazo asibitin, sai kunyar Mimi takeji, sbd Alhaji yazo ya warwareta, kuma ya fada mata cewa taci darajar sauda, sbd itace tace, in barki da ishararki. Ranar ta kira sauda tana bata haquri. To yau kam ta yarda cewa, duk wanda yace, tukunyar wani ba zata tafasa ba, tashi ko dumi tabar yi. Yadda taga Mimi, Mijinta yana ji da ita, ga daukaka, ga kuma soyayyar da take yiwa mahaifinta ta dawo sabuwa.
A katsina gidan suna ya cika. Dan yaci suna Aminullah, sunan Malam Aminu, Ismail yasa, domin ya nuna masa qauna. Hasana da Usaina sunzo. Abin sha'awa suke ta kula da 'yan suna. Gurin bada abin tsaraba in mutane zasu tafi, sun samu alheri. Malam Aminu kuwa yaji dadi sosai, wannan kara da ismail yayi masa. 'yan gidan su ma sunzo. Zo kaga idanu gurin fatu, sun ga abin duniya, abinci kuwa sunci sun diba a leda, duk da Mimi tasa anyi musu kyaututtuka na musamman matsayin dangin masoyin mijinta.
1⃣0⃣6⃣Kwanaki arba'in sukayi, duk sati Malam ke zuwa duba su. Abin da yaba Mimi mamaki ta kuma qara miqa masa wuya, yadda shine ya kawo mata abubuwan da zata yi amfani dasu don gyaran jikinta, sannan ya fada mata abubuwan da zata yawaita ci. Yaso sunayin arba'in su dawo, amma tace yayi haquri sudan zaga suga 'yan uwa. Da gusau suka soma (har naji kamar in bisu inje gurin tawa Baida'u Gada) sannan kaduna, duk kwana dai-dai sukayi, sannan suka dawo, sukaje Dangin Hajiya sauda. Sun zaga acan kwanansu biyu. Duk da ba masu kudi bane , taga soyayya irin na dangin uwa. Sannan sukaje masari suka kwana daya, daga nan sai Malumfashi gurin Hajiya Binta. Bayan sun dawo ne kuma suka soma shirin komawa gida Abuja. Har da Hajiya sauda da yaya Amina a 'yan rakiya. Qannenta kuwa su Hasina dasu husna, harda kuka don sun saba da Al'amin. Shi kansa Alhaji yayi keawar dan jikan nasa. Ranar 'yan rakiya suka dawo suka barsu da kayan arzikin da suka rakasu da shi.
Qarfe taran dare, Mimi cikin kayan varci, tana ta lila Al'amin a gadonsa ya soma varci, sai taji qamshin turaren masoyinta, kafin ta waigo sai taji hannuwansa a jafadarta. Cikin murmushi ta juyo, "Malamina ka shigo tun yaushe? Yace baki ganni cikin shirin varci ba? Tun lokacin da kk wanka, na san ni ake yiwa wankan. Don haka nace, kema bari inje in miki. Suka sa dariya. Ya tsugunna ya sumbaci goshin dan nasu, sannan yayi masa addu'a. "Muje ki amshi darasin da kk tara ma kanki." Cikin shagwa6a tace, Malam mu bar karatunnan sai gobe. Ya dora yatsansa akan le6unanta, tare da fadin "shhhhh, wannan ba halinki bane. Na shaide ki baki cikin mata masu juya baya. Ya kai bakinsa kunnenta yayi mata rada, suka tallafe juna zuwa gadon aurensu. Na juya zugum-zugum don in anyi radan nan inajin haushi banjin me suke fadi.
[01/10 8:04 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa

1⃣0⃣7⃣Watan Al'amin uku, yaro mai cike da kuzari da lfy. Sukazo katsina suka sallami dangi suka wuce Madina don yin digiri dinsa na biyu. Yaso Mahmud ya taho, amma shi yace sai nan gaba. Don haka komai na game da makarantarsa ya barma Mahmud. Watansu uku da zuwa, Azumi gazo, don haka suka dawo gida sukayi Azumi, sbd tafsir din da ismail keyi. Bayan sallah suka koma. Lokacin aikin Hajji sukayi shiri da dansu don yin aikin Hajji. Mimi ta zazzo umura, amma bata ta6a aikin Hajji ba. Koda yake umura dinma, lokacin zuwa kawai take, amma batasan me zatayi ba sai siyayya. Rayuwarsu irin ta larabawa suke kwaikwayo gurin soyayya. Don haka ko yaushe suna nane da juna. A makka ne sun fito harami zasu je masaukinsu, Ismail dauke da Al'amin a kafada sanye cikin jallabiyya fara sol, Mimi cikin baqar doguwar riga ta rufe fuskarta da niqabi tana rataye da jakar tarkacen Al'amin, tana kuma maqale da hannun mijinta suna tafe kamar taurari. Sai kawai ta hango Na'ima. Tace, Malam ga Na'ima suka tsaya a gabanta. Zata kauce, Mimi ta daga niqabinta, tace Na'ima. Wata kunya ce ta rufeta, sai kuma ta rungume Mimi. Mimi tace keda wa kuka zo? Tace nida Momy. Masaukinmu zan koma wancan Hotel din. Mimi tace, muma nan muka sauka. Ta kalli Malam ta gaida shi, sannan suka wuce zuwa masaukin.
Momy Nafisa taji kunyar ganinsu, nan suka gaisa ta dauki Al'amin tana fadin yaro yayi girma. Na'ima bata tsaya 6ata lokaci ba ta shiga neman gafarar Mimi cikin kuka. Itama Momy sai tayi narai-narai tana roqon gafara. Mimi ta rungume Na'ima, tace babu komai, komai ya wuce, nima ku ya feni. Ismail yayi musu nasiha tare da nuna musu illar hakan. Sukayi godiya. Anan ne ma Na'ima tace, ai Malam ina ganinka a makarantarmu, 6oyewa nakeyi. Bayan ya dauki Al'amin ne yace bari suyi gaba kafin ta shigo. Na'ima tace, sis Mimi sai kin qara riqe wuta, sbd 'yan Makarantarmu suna bala'in son Mijinki, don dai dai ne yarinyar da bata labarinsa. Mimi tace, sunyi au gama. Momy tace ke Na'ima karki tada mata hankali, gashi kun saje da larabawa. Mimi tace hakane momy, gsky ta fada, kiran wayarshi da mata keyi ma kadai in nace zan damu, sai jini na ya hau. Sauqi na basa gabansa. Ta jima sannan ta koma dakinsu.
1⃣0⃣8⃣Duk lokacin da suka samu wani dan hutu ko na sati daya ne sai sunje Nigeria. Hakanan daddy yakan nuqo gari yazo ya gansu. Bayan sun shiga shekara ta biyu, lokacin Al'amin yana da wata takwas yana gudunsa ko ina, sunzo. Da zasu koma, Ismail yace, Dija ina ganin ya kamata mubar Al'amin gurin su Hajiya, don mu samo Rumaisarmu ko? Ta kalli dan nata dake varci tace Allah sarki Aminullah, har ya bani tausayi. Zanyi kewarsa. Yace ko yaya kk gani? Tace duk yadda kace babban Malami. Alhaji Bashir tamkar ya goya su Mimi don murna sun bar masa jikan daya shiga ransa. Saidai bai nuna ba don tsoron kar yayi masa irin na Uwarsa. Shekara kwana ce inda rayuwa, domin su Mimi sun dawo gida bayan Ismail ya samu shaidarsa mai kyau, ta samun digirinsa na biyu. Ya iso cike da burika, musamman gina jami'ar Musulunci a katsina. Sun gyara gidansu sosai. Da yake Mimi ma bata zauna ba, a Nadina taci gaba da neman ilimin addini, sai Makarantar nan tasu ta koma qarqashin kulawarta. Zumunci kuwa ita da Rabi'a, tamkar 'yan uwa. Ta sa Ismail ya gyarawa su yaya Amina gida.

14 / 15