CANJIN RAYUWA 4 COMPELET HAUSA NOVELS BY K MASHI.txt

Author :  halima Abdullahi K Mashi Category :  Romance

Chapter   1 / 15

1 to 3K   out of 43.9K words


Chanjin rayuwa book 4
1⃣Saboda ta samu canjin rayuwa, daga jahilci zuwa ilimi, daga rashin tarbiyya zuwa tarbiyya, daga mara mutunci zuwa mai mutunci. Sauda, da farko nayi wa Mimi wannan auren ne don in quntata mata, in qona mata rai, kamar yadda ta qona min. Amma daga baya tunani ya shige ni, nayi nazarin dalilin wannan auren zata iya samun canjin rayuwa. Ismail zai iya bata ilimi na addini wanda ta rasa daga gareni. Sannan, ilimi zaisa ta zama mai tarbiyya ko dan yaya, tunda anbar shiri tun rani. Dalilin da yasa nace kar kuje gurinta, nima nace kar su sake nemana, sbd idn bata tare damu, zata fi samun tarbiyya. Shi ba zaiji shakkar mu ba, ko tsoron mu in tayi abin hukunci. Kuma yanda na lura dashi, bashi da shakka, kinga kenan ba zaiji tsoron duk wata barazanar ta ba. Haka kuma ba zamu taimaka musu da kudi ba, sbd shi kansa banason mu kashe masa zuciya, ya kasa neman na kansa, ko yaushe yana jiranmu. Haka kuma ita kanta rashin taimaka musun zaisa ta saba da Rayuwar babu, wadda bata sani ba ada. Yanke alaqa dasu shine zaisa ita da shi suyi abinda ya kamata.
Hajiya sauda ta sauke ajiyar zuciya, "Na fahimceka sosai Alhaji, saidai nayi wani kuskure daya. "ya kalleta, na tura musu dubu dari. "karki damu, saidai karki sake tura musu kudi. Da zaki iya ma ko wayarsu karki sake kira. Ta danyi shiru tana nazari. Ya katseta, kar kisa ma kanki damuwa, nayi miki alqawarin bibiyar miki labarin duk halin da suke ciki. Ta tsura masa ido, a cikin qwayar idanunsa ta tabbatar da abin da yake fada. Tace, shikenan Alhaji. Allah yasa mu dace. Yace, "Ameen matar qwarai". Ya kama hannunta, "nasan ranki ya nutsu da yaron, kuma nima na fahimci cewa, yaron mai hankali ne. "Sukayi dariya. Yace, kinsan menene sauda? Tace a'a. yace, "Ni kaina ina cikin matsanancin kewar Mimi. Na sani sarai tunaninta ne ya hana ciwwonnan sauka. Tace, nasan za'ayi haka, amma tunda kanada wannan qudurin, wajibinka ne ka daure, ka jure, ka kuma kauda kai, sannan mu hada da Addu'a, Allah ya taya mu. Yace, Ameen ya rabbi. Ynxun kuma na samu natsuwa tunda Allah yasa kin fahimceni. Ranar nan suka yini suna qoqarin kyautata ma juna.
2⃣Haka itama Mimi tayi ta jinya, yaya Amina da Ismail suna matuqar kula da ita. 'yan uwan mamansu na Daura sunzo, sun duna jikin Mimi, sannan sun kawo musu kudin gonarsu da aka saida. Don haka shirye-shiryen tafiyar Ismail ya kankama. Haka nan 6angaren Mimi, zuwa ynxun Ismail yayi nasarar saka Mimi ta fara sallah dole, ba don ta so ba. Yawan nasiha da nacinsa ya sata sauraronsa. Ya nuna mata yadda zatayi sallah, kuma ya dauki nauyin yi mata akwalla. Ranar daya fara tsananta mata tayi sallah da kuka tayi sallar. Da farko ma bata yi ba, sai da yace shikam ba za yayi jinyarta ba, matsawar ba zata yi sallah ba. Ya nuna mata shifa tafiyarsa zaiyi. Yaya Amina ita ma cikin son ta tsorata ta tace, in ko ka tafi, nima zaman me zanyi? Kinga kenan saiki zauna babu mai jinya, ba mai kula dake. Tana kukan nata tace, yayi mata alwalla. Tun daga ranar, duk lokacin sallah in yayi, sai ta yita. Wani abin da yaba Mimi al'ajabi shine tunda ta soma sallah, sai ta samu kanta cikin wata natsuwa, ta kuma qara imanin cewa sallah tana kusanta bawa ga ubangijinsa. Haka kuma lokacin da yace zai dinga koya mata gajerun surori, bata qi ba sbd sallah.
Kwanci tashi har taci wata daya da sati daya a asibiti. Lokacin ne kuma da Doctor din dabyayi mata dori ya dibar mata zaizo ya duba in dori yayi kyau, sai ya kwance. Ranar litinin da misalin qarfe goma na safe, likitan suka shigo shida doctor salis. Kallon qafafun nata kawai yayi, yace inasa ran cewa dorin yayi kyau. Zan kwance shi ynxun sai ku kaita ayi mata hoto, sai ku kawo mu gani. Ismail cikin murna yace, Alhamdulillahi, dama na gaji da zaman asisibitin nan, har ita ma khadijan ta gaji ko?. Ya fada tare da kallonta. Mimi ta kalli likitan, kenan in hoton ya nuna cewa, dorin yayi za'a sallameni ne? Likita yace, eh, to ku daiyi hoton mu gani. Bayan an kwance tana ta shagwa6a, ta qanqame yaya Amina. Likitan yace, a kaita hoto ynxu. Ismail ke tura ta a kujerar tura marasa lfy suka nufi gefen hoto. Yaya tana jere da shi suna magana. Yace, "Yaya Allah yasa hoton babu tsada sbd Kinsan fa babu sauran kudi, gashi kudin dakinmu dana sake biya ya qare. "Wai saura nawa ne ma kudinnan da aka ajiye sbd tafiya? Yace "ta6" ai baifi saura dubu goma ba acikin dubu hamsin din dana ba Mahmud don kar in kashe, amma duk sun qare. Tace, ai dama zara bata barin dami.
Barkanmu da sallah sis 🙌
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

5⃣A qofar gidansu yakeyin wankin, amma yanajin nauyin shanya kayan Mimi a igiyar waje, sbd duk qananan kaya ne matsattsu. Sannan har pant din ta yake wankewa, don haka sai ya daura igiya acikin zauren kusa da qofar dakinsa yana shanya kayanta a gurin. Wani lokacin ma sai ya jira sun dan sha kadan ya kwashe, sbd yaran Gidan marasa ji, wani sa'in suna zubo da kayan qasa. Yau ma daya gama wanka, yayi shirinsa zai fita, sai ya kwashe panties din da vests yaje ya shanya su kan akwatunanta, ya kunna musu fanka, sannan ya kulle qofar ya nufi gidansu Mahmud. Hirarsu kullum bata wuce ta tafiya. Mahmud yace, Ismail kasan Rabi'a ta daga hankalinta akan batun tafiyarnan? "saboda me to?" Inji Ismail. Mahmud yayi 'yar dariya, wai tana tsoron kar in hadu da wata acan in manta da ita. Nace ta daina wannan tunani, tana damun kanta bayan anyi mana baiko. Sai tace, to yaushe zan dawo? Nace mata ban san lokacin ba. Shine take fushi dani. Ismail yace, mata kenan 'yan rigima. Ni baga wannan shagwa6a66iyar Yarinyar ba. Lokacin da zan fito fa kuka takeyi, wai bazan fito ba. Mahmud yasa dariya, to ba yaya Amina tananan ba? Yace bata nan, tana gidansu. Tazo dai da safe, amma ta koma sbd batajin dadin jikinta. Kasan Allah, Mahmud na gaji da zaman asibitin nan, ita kuma gata da shegen son jikin tsiya. An ce, ta dan dinga dan takawa, amma taqi. Shiyasa na barta ita kadai don tayi zuciya ta motsa.
Mahmud yace, Ismail saidai fa kayi ta haquri, domin yarinyarnan cikin shagwa6a ta taso, hakan ya zama jinin jikinta. Ai ma kaci nasara tunda tana cin duk abin da aka dafa aka bata, sannan ta amince zata zauna daku. Ismail yace, ni damuwa ta ynxun, inda zan barta in zamu tafi. Mahmud yace, inda lafiyar ta lau ne, da sai mu tafi tare da ita. Ismail yace, kasan Allah, ko lafiyarta lau bazan iya tafiya da ita ba, haka kawai taje ta dameni. Tunanina in barta gurin yaya Amina da mijinta, tunda suna da dakin yara, da kuma dakin da mahaifiyarsa da take ciki kafin ta rasu.
6⃣Mahmud yace, hakane, kai ai yaya Amina tanada zumunci. Nasan ma ba zata qi ba. Ismail yace, ba zata qi ba insha Allah. Yaya Amina, aita zamar min uwa saidai ince Allah ya bani ikon yi mata biyayya. Mahmud yace, Ameen, ai tafiyar tamu ma tazo. Naji yana cewa nan da qarshen wata, sati uku dai a taqaice. Ismail yace, tabbas tafiya tazo, Allah dai yasa a sallamemu kafin ranar. Kai ni gobe ma zan samu likitan ince masa sallama kurum nakeso. Mahmud yace, kafin su sallameku, ya kamata itama ta dan taka su gani. Matsa mata ai zakayi. Sai daf da magriba sannan suka rabu. Gida ya koma ya kwashe kayan shanyarsa, sannan ya daukar mata wasu kayan ya nufi asibitin. Yana sauka ana tada sallah. Don haka sai ya bada ajiyar ledarsa cikin wani shago, ya shiga sallah. Har zai bari sai yayi isha'i, sai kuma ya tuna itama tana buqatar yin sallar. Zaune ya same ta akan gadonta, taci kuka ta gode ma Allah. Tausayinta ya kamashi, amma sai ya dake tamkar baiga fuskarta ba. "Muje kiyi alwalla! " Tayi banza dashi. Yazo zai dauke ta zuwa bandaki, tace, ka barni, ka tafi abinka. Dama nasan dole ka gaji dani, iyayen da suka haifeni ma sun gaji dani, sun gujeni bare kai da suka jona maka ni? Banga laifin ka ba. Amma meyasa kasa nayi maka alqawarin zama tare da ku bisa sharadin cewa zaka kula dani, sai gashi tun kafin mubar asibitin ka gaji? Nasan kaida 'yar uwarka kuna dawainiya dani, amma yadda ka nuna nima 'yar uwarka ce, na zata za'a dan jima kafin in gundureku.
Ismail yadan tausasa murya, cikin sigar lallashi yace, wai waya fada miki cewa, mun gundira dake ne? Ni kin bani haushi ne yadda kk qi kidan taka ko sau daya ne. Kuma khadija wanki naje nayi miki, ya sake matsowa kusa da ita daf, yasa hannu ya dago fuskarta, cikin wani salo ya kira sunanta, khadija! Ta dago jajayen idanunta ta kalleshi. Yace, "Wlh baki gundiremu ba, kuma bamu gaji dake ba, kuma ke 'yar uwarmu ce. Tace, nidai nafiso ka bani saki na, ka tafi abinka. "Ya dora yatsansa akan la66anta, "shhhh, ki daina cewa haka mana qanwatah. Kiyi haquri! In kaiki kiyi alwalla ko? Taqi magana. Da qyar ya lallasheta, sannan ya kaita alwalla. Bayan isha'i ne tana cin cake da fanta, yace, kinji tafiyarmu zuwa qarshen wata ko? Tayi takwa-takwa da fuska "to ni kuma ina zaka barni? Ya kwaikwayi muryarta, shine nakeson muyi shawara dake.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwan

3⃣Mimi, wadda ake turawa tana jinsu, duk qarma-qarmar da yakeyi tana jinsu, kuma ta sani. A zaton ta ma da kudinta akeyi mata komai, har suka qare ya shiiga nasa. Tace, to yaya Amina su sallamemu mana tunda dai babu kudi. Yaya ta kalli Ismail, "Nima nawa tunanin kenan, ko ya ka gani? Ismail yace, bari dai ayi hoton mu gani. Allah yasa dai kudin babu yawa. Ynxun ma tunanina ko zan barku anan inje in amso ragowar na hannun Mahmud. Yaya tace, muje dai, in kaji kudin, sai ka tafi. Dubu shida da dari shida ne kudin hoton, don haka dole ne ya tafi ya amso ragowar kudin, kafin ya isa, saida ya kira layin Mahmud din, don haka mai acha6ar da ya kaishi, shine ya dawo dashi. Don haka suka biya akayi musu, sannan suka amshi sakamako suka koma. Sai sha biyu sannan likitan ya dawo ya duba, yace Alhmdlh, kuma tana da jiki mai kyau. Don haka zata iya soma koyon tafiya. Ismail ya kalli doctor. Ismail ya kalli Doctor salis yace, za'a iya Sallamar mu? Sbd gsky duk abinda muke dashi ya qare. Doctor salis yace, karka damu malam Ismail, kayi qoqari sosai. Ba duka namiji za'a samu ya tsaya kan matarsa haka ba. Mimi ta dago, ta kalli Ismail, idanun ta da alamun tambaya. Sai yayi murmushi, ya kalli likitan, ai yaya baya kasa dawainiya da qanwarsa. "Take likitan ya kalli Mimi, sai ya tuna 6aran6aramar da yayi, don haka yace, "oh na manta hakane, yaya ne ashe. "
Yammacin ranar, Ismail babu yadda baiyi ba da Mimi ta dan soma takawa, amma taqi, sai kuka takeyi wai ba zata iya ba. A qarshe haushi ne ya cika Ismail ya fita waje ya zauna akan benci. Tunanunnuka ne kashi-kashi suka addabeshi, yana mamakin yadda yaketa neman layin Hajiya sauda, amma baya samu itama kuma ta daina kiranshi. Sannan yau sati uku kenan da ita hajiyar ta sallami Mahmud daga koyar dasu hasana. Ko yaushe in Ismael yayi ma Mahmud wannan qorafin, sai yace, karka damu ni dama ko basu sallameni ba, dole in barsu tunda kaga karatu zamu tafi. Game da rashin waiwayar 'yarsu kuwa ka qara haquri.
4⃣Gashi yana tunanin ina zai samu kudi, ko ba don ciwonta ba, ko don sbd tafiyarsa. Sannan in an sallamesu, ina zai ajeta? Domin gsky bai kyautu ba yasa ta dakin zaure.Duk bama wannan ba, gurin wa zai barta? Yana jiyo ta daga ciki tana magana cikin shagwa6a, "to kazo mana, ka kamani zan kwanta ne fa kaji! Shiru yayi mata, sai dai zuciyar sa tana tambayarsa meyasa ynxun Mimi bata kiran sunansa? Bata cewa, Ismail, bata cewa, malam. Nauyinsa take ji, ko menene? Oho! Tayi, har ta gaji tayi shiru. Saida yaji kiran sallar la'asar, sannan ya shiga dakin. Har lokacin idanunta da hawaye. Ya kalleta, sai kuma ta bashi tausayi, yace, khadija! Taqi kallonsa. Ya gane alamun tayi fushi kenan. Yace, zan yi miki alwalla ne, nima zan tafi masallaci. Ta kumburo baki, to ka kiramin nurse Ramatu. Inaso inyi fitsari ne. Yace, ba zan kira wata ba. Muje in taimaka miki. Nurse dinnan fa da kkga tana kulaki, ina bata wani abu. Kwanakin nan da bani dashi, ban bata ba, kinga tana shigowa? Mimi tace, to fa, kai namiji ne, shine zaka taimaka min? Banida lokacin 6atawa khadija, sallah zanje. Menene zaki 6oyemin wanda ban gani ba? Kuma tunda ni matsayin wanki nake, ai ba wani damuwa. Ta zaro idanu, me ka gani? Bayan yaya Amina ce takemin komai. Da zaka ce... "kafin ta kai qarshen maganar, har ya dauketa cak ya sakata a toilet din. Ya zaunar da ita a kan kujerar da yaya Amina kan zaunar da ita in zatayi mata wanka. "sai kuma me zan taimaka miki dashi? " ka fita nidai kawai! Zaki iya yin komai harda fitowa? Tace, nidai ka fita! Murmushi yayi sannan ya fice, "to karki dade, kusan mintina hudu tace, "to kazo ka fito dani! Tayi maganar, ranta a 6ace. Ya shiga, inyi miki alwalla? Ta turo baki, "ni nayi abina. "A qasa yayi mata shinfidar sallah, yace, kiyi a qasa, tunda an kwance maki. Yasa mata hijabin sannan ya fita. Bayan ya dawo ya soma hada kayan da yaya Amina ta cire mata da safe. Yace, zanje gida inyi wankinmu, ya dan taru, sai kuma inyi wanka. Ta 6ata rai, cikin shagwa6ar ta tace, ni kuma ka barni da wa? Yace, da Allah mana! Dama shine mai tsarewa. Kinga kuma kinji sauqi babu laifi ko? Ya qarasa cikin sigar lallashi. Ta matse kafada cike da shagwa6a, idanunta suka soma zubo da hawaye, nidai bazan zauna ba. Ya ce, (cikin takaici ) karki zauna, inkin gaji da zaman Asibitin kidan taka mana, ki yarda kidan taka ko a sallamemu, amma kinqi. Ya dauketa cak ya dora ta akan Gado. Sai na dawo. Bata dai ce komai ba, shi kuma yayi tafiyarsa.
[17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa

7⃣Ta aje cake din hannunta akan gado, "Nidai ka tafi dani mana." yace kwantar da hankalinki, wannan ba abin damuwa bane, ga yaya Amina, sai ku tare, inkin sauqi sosai, in nazo sai mu tafi. Tace, to ka fadawa yaya Amina dinne? Yace, ban fada mata ba, amma nasan cewa ita babu matsala. Tace, shikenan yaya jikinta fa? Yace, da sauqi, dukda banbi ta gidanta ba. "Ya ciro wayarsa, bari in kira Abban su saddam ya bata mu gaida ta. "sun gaisa da abban su saddam, sai ya tambayi mai jiki. Abbansu saddam yace, gatanan tanata rawar sanyi, ta qudundune, ta dai sha magani. Ismail yace, to ka gaisheta. Khadija ma tanayi mata sannu. Abbansu saddam yace, zataji. Ya kalli Mimi, kinji har ynxun jikin ko? Tace, Allah warki yaya! Allah ya bata lfy. Washe gari yaya bata samu zuwa ba, sbd jikin nata. Ismail yace, to yau yaya zamuyi da wanka? Ko in miki? Ta zaro idanu, tana kallonsa, a ranta tace, shi wannan nufinsa dole sai yaga tsiraici na ne? A fili tace, na haqura sai taji sauqi. In tazo zatamin, harda gashina zata wankemin, yayi datti, duk ya dameni. Yace, wai meyasa baki yarda dani ba, sai kace zanyi miki wani abu. Ki tsaya ko gashin ba sai in wanke miki ba? Naga yadda tayi miki ranar nan mana. Tace a'a karka samin ruwa a kunne. Ni saloon nakeson zuwa. Yace to yau kidan taka ne mana khadija. Kinga basu so mu tafi da wata matsala ne. Da sunga kindan taka zasu sallamemu, sai in kaiki duk inda kk so. Ranar dai da qyar ya samu ta dan taka, daya biyu yana sagale da ita, sai ko ta fada jikinsa. Wani iri yaji, tsigar jikinsa ta motsa. Yayi mamaki, bai ta6a jin haka ba aduk irin daukanta da yakeyi mata a cikin wannan jinyar. Cikin sauri ya dagota daga jikinsa, muryarsa a sarqe ya dago ta, "kin cika ragwanta, to zauna kidan huta.
8⃣Cikin sati daya, mimi tana dan fita tare da taimakon yaya Amina don taji dan sauqi ta dawo, da kuma taimakon uban gayya, Ismail. Burinsu lokacin a sallamesu, domin basuda kudi a hannunsu. Ranar litinin kuwa Doctor salis da lukman, likitan da yayi mata dori suka tabbatar ma da mimi sallama. Ismail yayi murna tamkar dan kurkuku a ranar daya fito. Duk sunyi murna sosai. Yace, ma yaya Amina ta shirya kayansu, shi kuma zaije ya dan karkade dakinsa. Yaya tace, ina zata? Gidanmu zamu wuce tunda mun riga mun sanar da Abbansu saddam. Yace da inason indan gyara mata dakin na Gidanku, tare da dan sa mata abin kwanciya kafin dai mu wuce. Tace, hakane. Tare da Mahmud suka share ko ina na dakin sannan suka dauki shatar tasi zuwa asibiti. Likitoci da Nurses sunyi masu murna da barin asibitin, nan ne ma Doctor salis ya basu tabbacin cewa, duk lokacin da wata bukatar taimako ta taso, to qofa a bude take su tunkareshi. Yaba Ismail katinsa mai dauke da lambobinsa a jiki. Ismail ma bai qwauron baki ba ya fada masa cewa, shi zai tafi karatu ne a madina, amma duk

1 / 15