Author : Maman mubeena Category : African Stories & Novels
ba..last word din da doc barak ya ji kenan Allah ya karbe ranshi
Imidietly khal yasa aka saka gawar sa a motan da xaibi da shi airpot kafin kace kobo gaba daya gawar ta sauya hallitar zuwa wani irin mummunan abu babu kyan gani..
Akwana biyun da suka wuce Subaya bata samun shi awaya,gashi damuwar ya nuna boro boro a fuskan ta,boye kanta ma take dan tasan jahan tana ganin ta shikenan dole asiri ya tonu
A wani fannin zuciyar ta har tsoro take dan tasan jahan Aarah kam bazata dauki maganan da sauki ba
Ta nemi yasmine awaya bata same ta ba...amma da dija ta dawo da shike tana da nunber ta sai ta kasa hakuri ta kira ta sukayi dogon video call
Anan itama ta ji duk sauran bala'in da suka fuskan ta wanda bata sani ba
Dija fadar maganan takeyi kamar wanda dama ta dade tana jiran ta sauke nauyi,anan subaya taji cewa khal da bahiyya suna son juna, sannan khal yakanje london domin yaga bahiyar sa..
Abun ya dame ta sosai, Kenan ta raba yardan dake cikin soyayyar wayannan masoya?
Daga nan wani silent zazzabi ya shige ta. ,tafiya take acikin gida kamar mace amma ita kadai tasan ba a dai dai take ba.
To kafin nan a gidan su bahi tun ranar da tagaya mashi tana da aure,kaamil ya ki ya fito daga room dinshi har na kwana biyun sai abun ya fara daga masu jahan khatun hankali
Anyi anyi ya bude kofar dakin yaki,rabun su da su kagan shi awani hali irin haka tun lokacin da khal yaje prison a ta dalilin shi..
Jahan khatun tuni ta daga hankalin ta sosai dn tasan babu lpya acikin lamarin
Nan aka shiga bincikawa har dai junnut ta ce ko akan bahiyya ne?
She tot ko dan basu samu daidaituwa bane, but taga bahiyya lpyar ta lau bata masan wai kaamil ya kulle kanshi a daki yaki fitowa ba
Junnut tayi iya kokarin ta dan taji daga bakin shi amma yaki,she has no choice than ta gaya musu cewa ita tana ganin cewa akan bahiyya ne ya kulle kanshi
..tunda ita last maganan datayi da shi kenan
Toh Aranar da safe bahiyya ta farka da mugun bakin cikin rashin sanin ina mijin ta yaje kwana biyu,tana fitowa daga room din shin suka yi ido biyu da jahan khatun
Tace good mrning maam tana dan rusunawa aladabce..jahan khatun ko amsawa batayi ba
cikin wani irin wulakantaccen yanayi ta jawo ta ...tace mata biyoni. .Nan suka iso har sashen kaamil,suna kaiwa tasa ta agaba tace sai kice mashi ya fito tunda ke ce munafukar
Bahi cikin mamaki ta dube jahan anma batayi musu ba,ta shiga knocking kofar tana rokon shi ....hilda da jahan khatun din kamar zasu mutu....dan su kam basu ga abin so ajikin bahiyyar ba
Jahan din ma jira take kaamil ya fitoo tayi masa kaca kace ta tura shi us ayau din nan..
Da bahiyya ta dage na magiya sai gashi kaamil ya fito...gaba daya ya galabaita idanun shi yayi ja.
Ita kanta bahi sanda taji kanta ya sara data dube yanayin shi
...ran mahaifiyar shi ne ya dada harzuka data ganshi Ahakan...ta daure fuskan ta sosai batace masa uffan ba
Bahi ne take masa tambayoyi cikin nuna kulawar ta tace ko baka da lpya ne?..to lokacin yanaji da radadin zafin rasata...baiji kunyar su ba ya fara tambayar ta meyasa tace bata son shi again?
...shidai yanzu ji yake yi kamar yaki yarda da maganan auren nata..gashi bata so ta furta agaban kowa cewa khaldun ne ya aure ta..
Jahan is already murmumring..su junnut kuma sun sa ido suna kallon su kowa da abunda yake rayawa aranshi,hawayene akan fuskan kaaamil wanda ya sako shi ma bahi yana ta famar marairaice mata..
Kunya da fargaba duk sai ya hanata sakat
Dan Jan shi gefe tayi ta daure tayi masa maganganu masu sanyi
...cike da nuna mashi gaskiyan lamarin ta sake xayyana masa cewa wallhy da auren wani akanta so babu batun soyayyar su...
Yace wanene mijin?
Tace a gaskiya sirrin ta ne kuma in har yana son ta dagskiya to ya shirya rike mata sirrin ta
..wani hawayen ya sauke mata,zaiyi magana sai ga jahan ta iso kan su sai ya share hawayen sa yayi shiru
...tace ke wacece haka da zaki zo gidana ki shiga rayuwar dana?
Tambadaddiya..yar iska irin ki?..toh ta Allah bata ki ba..inma aiko ki akayi kiyi seducing dinsa ki cuna masa bakin ciki dana naji haushi..to wallhy nafi karfin ku..da na yafi karfin ki..
Bahi ta dagi kamar zatace wani uban..cikin hatsala tace will u get out of my sight?
..a tsorace bahi
ta zame .. jiki ba kwari ta barsu anan..
Jahan bata tsaya lura da condition din dayake ciki ba ta dinga zuba masa masifa da xagi ta inda ta shiga bata nan take fita ba.
Ta jaddada masa cewa ko bata duniyan nan badai ya auro mata wannan yarinya ba
Saidai in zai sake wata uwa ba ita ba..
Junnut ta matukar tausaya ma kaaamil
...da sauri ta bi bayan bahi dan taji kan maganan
Hilda kuwa dama abunda take so kenan tuni ta shiga sa ma jahan khatun baki suna scolding kaamil
Ita kuwa bahi ko dakin nata ma bata isa ba taga sakon sadat mai dauke da mummunan baraxana kamar yadda yasaba..
Wani siririn hawaye ya kufce akan idanun ta,ajiyan zuciya tayi tana karantawa wai
Ya bata 2hrs cewa idan bata same shi ayanzu ba zai sa ayi ma khal din ta allurar mutuwa
..gashi ta ga khal kwana biyu baya nan she just assumed that dagaske aikin yaje maybe yana hannun dan uwansa barak adeel..
"Mayafin ta kawai ta dago zuciyan ta cike sa tunani kala kala,kaamil na bata tausayi sosai,kuma bata son wani abu ya taba mata mijin ta...adai dai bakin door ta fito sai ga junnut..
Wani kallo suka maida ma juna tayi sauri ta karaso
Tace bahi we need to talk...wai Meya faru tsakanin ki da kaamail ne..bahi mesa zakice baki son shi?
Junnut look disturbed and serious
Bahi tayi shiru..cos hawayen rudani duk sun rine mata idanu kuma bata so ta bude baki har zuciyan ta yasa ta furta ma junnut abubuwan da bata da niyya.
Junnut ina sauri ne amma dana dawo zamuyi maganan
.
Kafin junnut ta bude baki bahi har ta xame ta bar ta awajen ta,quickly ta shiga mota ta bar gidan
..bata wani iya tuki ba amma haka ta daddage Straight ta isa location din daya ce mata yana jiran ta
taje Wajen babu mutane,hasali ma bayan gari ne sosai
Babu mutane dayawa sai ajiyayun motocin fa ba amfani dasu
Daga nesa Ta kare mashi kallo Ba shakka kuwa shi din ta gani zaune akan bakar motar shi ba laifi ya fada sosai...
Yana ganin ta daga nesa sai ya shiga motar ya zauna
dayaga ta iso kusa sai ya bude mata door din..bata rai tayi Tana kallon shi sai taja ta tsaya taki ta shiga...wani mugun dariya ya fashe da shi..he is happy to see her zuciyar shi sai harbawa yake dan sosai ya fahimci cewa son yarinyar ya shige jikin sa sosai..
Bahi ta hade ranta sosai batayi hawaye ba kuma batace uffan ba
Da yaga dai ba shigan zatayi ba sai ya fito yana da wani irin miskallaen murmushi taki ta hade ido dashi ta kau dakan ta.
Hannun sa ya miko kamar zai janyo ta jikin shi yana mata wani irin kallo,da wani irin muryan tsana da hantara cikin fushi tace masa What did u want?
Ya sakar mata murmushi Yace ohw woah ..haba yan mata... hush down mana,bakiyi kewa ta ba?Taja tsaki mai sauti...dariya yayi yace lallai auren nan ya bata min ke..
U no longer respect me... Cako hannun ta yayi abaxata ya matse a nashi tasa masa ihu tana finficikewa abun wuyar sa ne ya fadi ajikin ta ita tagani shi bai lura ba yanata faman kokawa da ita tayi sauri ta cusa acikin hannun rigar ta..da karfi ya hada ta da jikin car din shi ya matse bakin ta yana kokarin shakar gamshin jikin ta cikin wani yanayi,hawayen ta mai zafi su suka fetso ..,yana ta kallon inda ruwan hawayen da ke saukowa akan hannun shi..
Wani irin mugun yanayi ne a fuskan sa na bakar kishi da azaban mugun ta.
"Kinzo sabida nace zan kashe shi ko?toh kisani zuwan ki bazau hana komai ba...ke Kinsan ina son ki". Amma sabida ke wawiyace kin bari har an aura maki aure da wani wawan
..toh ki nitsu da kyau kiji abunda xan fada maki..
Sake ta yayi ya fito da briefcase daga motar shi ya mika mata hawayen ta take sharewa kafib ta karba tana karantawa
Yace...this is subayas life..50% of her wealth shine anan,kuma sauran nasan inda zan same su.
Nasan kin gaji ko? Toh Shiyasa na sama mana mafita..i have the money now, saura ke bahiyya..
" tayi masa shiru cahn ta dago kamar marar laka ta kalle shi..Magana tayi kamar Jikin ta a matukar sanyaye tace ...
Sadat Am married..
dan Allah ka rabu dani..ba kasamu kudin ba?kasan ba a aure akan aure..da sauri yace mata anayi mana...ni nasan yadda zamuyi
..kisa aranki cewa sai kin aure ni idan ba haka ba ..
Tun bai gama ba Ta toshe kunnen ta a mugun zafafe tace pls stopppp
Jifa tayi da file din akasa agabn sa tace ni bazan aure ka ba..Nace maka ina da aure,bani da wata alaka dakai yanzu..ba kudin bane a hanun ka ai sai ka kama hanyar ka..go and deal with ur wicked issures....wannan
Rayuwar ka ne, kuma wallhy ka dena kira na awaya ni bana so Muryn ta na rawa cike da masifa ta juya zata tafi..
Bai tsare ta ba
Hankali kwance yayi furxan iska Yace 1 more step yarinya.... Taku daya yarage miki ki dawo bazawara matan mamaci...wani dumm taji kirjin ta ya buga amma bata juyo ba tace...r u planning to kil him dan ka aure ni?
Cike da isa da basarwa Yayi murmushi yace
A'ah,..Not witout ur permission idan kina si ya mutu yanzu zansa akashe shi..bahiyya,..na dauko dukiyan nan na zo dashi ne dan na kasance tare da ke,saura kirisss komai ya kammala
Duka arxikin subaya zai dawo nawa.
Gaban ta ya dawo ya zuba mata kasallalun idanun shi yana mai dura hannayen shi acikin aljihu...kudi ba wani abu bane a familyn hamood subaya zata sake tara wasu
But If u love subaya to be alive saikin bani hadin kai..
Ta hadiye firgicin ta tace to me kake so nayi,na kashe aure na?.... yace no..alkwari zakiyi at the expense of familyn da suka taimake rayuwar ki suka dawo dake mutum..
Ayanzu ki dauka Rayuwar saood da subaya duk suna hannun ki..
Sai Kimin alkwari zaki dawo nan gobe da yamma ki same ni.
Yau xanje na kwato sauran files din subaya,sai mujee swizeland tare dake..zan boye ki anemi ki arasa dan na samu daman tattara komai cikin nitsuwa ba tare da hankalin kowa na kaina ba..
The moment im done,zamu je wata duniyar da babu wanda zai same mu..
Auren ki zai warware idan mijin ki yayi shekaru bai ganki ba...u wl be mine har abada,bazan taba cutar dake ba
For this statement "Wani saukar tassss yaji akan malalan kumatun shi,a bazata ya dago ya kalle ta ta zuba mashi furious eyes din ta har jikin ta na tsuma ..
Yace Bahiyya kika mare ni?..dada sauke masa wani marin tayi.... zai matso kusa ta daddage ta daka masa wani firgitaccen tsawa tanace masa enouhg...
Sannu lucifer first son of the devil....ta fada azafafe cikin idanun shi ta sako zafi sosai kamar uban ta ya zaga
Ka dauka ko zanji tsoron ka ne?its over now ..bani da lokacin jin tsoron ka...ko baka san kai mahaukaci bane..?
Mamakin yadda ta birkice masa yasa shi shiga shock Zaiyi magana ta nuna mai yatsa tace ni kayi min shiru... u better Listen to me now..
Ba kabani gobe nazo nan ba?..
Dan kadan ta shafa jikin ta ta fito da magic necklace dinsa...ta nuna mashi.
To na amince zanzo..its a chaklenge kacika alkwarin ka,leave subaya and her family alone ..i assure you nima zan cika maka Alkwarin ka .
_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_
_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._
_bismillahirrahmanirahim._
_3⃣4⃣-Villain 2♡_
Sadat Wani cize labbasan sa yayi zuciyar sa cike da fargaba yana kallon abun wuyar tsafin sa a hannun ta.. yayi tunanin,..ko ya danne ta ya kwace ne?.. .bahi yau ta bashi mamaki...wani tunani yayi yace ok..challenge acepted..zanyi komai yadda kike so bazan taba kowa ba..but u most return adaidai wannan lokacin...keep my necklace safe..
....Yaga Ko kula shi bata yi ba,Yayi kwafa cikin salon mugun ta ya juya ya kama hanyar motar shi ya barta da necklace din kamar bai damu ba, bayan yasan wannan abun wuyar shine gatan sa shine sa'ar sa arayuwa..
Amma gani yake kamar bahi baxata iya komai ba..firgicin dake taso masa yayi kokarin kaucarwa ya kama hanyar zuwa kano.
Bahiyya Dukawa kasa tayi tana Kuka
Tana tunanin rayuwar ta tin daga farko kamar wacce akace mata mutuwa zatayi agoben
Muddin komai ya faru yadda sadat ya fada,its fine by her,atake ta aje kanta ajerin mata marasa saa a duniya
Tasan idan ta tafi komai zai iya dai daita cikin sauki.
Jahan da alhj hamood baxasu rasa rayukan yayan su ba and With time Khal zai iya mantawa da ita ya auro junnut dinsa
And she dont have to compete for anything in life
Aranta take kokarin amincewa akan wannan shine babban sadaukarwan da zatayi musu dukkan su dan ta gyara rayuwar su..
..gani take kamar koda tabi sadat din ma mutuwa zatayi da bakin cikin shi soon.
Da kyar ta tattara kanta ta kama hanyar gida,tun a mota take kiran dija amma shiru baya shiga..
Abun wuyar nashi ta soka a cikin purse din ta ta adana shi da kyau.
Tana shiga gidan ta fada wanka..hjy indirah da murja sunje lagos on one day visit so evrywher was queit.
Haka junnut taxo ta cika mata kirji da nata magiyan akan kaamil,duk dama bahin taki sam tace komai amma gaba daya zuciyan ta sai ya cunkushe
Daga sallah sai sallah Sam ta kasa cin abinci ko zama
idan tagaji da kwanciya sai dai tayi ta zaga site din tana neman taimakon ubangiji trou tasbihi
, .ga yamma ya doso sosai duk sai taji duniyan ya mata daci
Ana shirin kiran magrib Ta fito zata shiga dakin khal sai ga tex din sadat ya shigo wayarta. . cewa yake ya isa kano,kuma subaya ta damka masa sauran dukiyar ta..
Wani irin faduwar gaba taji ya taso mata..ahalin yanzu bata masan me zatayi tunani akai ba...kawai sai ta tura kofar dakin ta shiga ta maida makullin ta rufe.
Data kare ma dakin kallo wani karayar xuciya da gabobin jiki su suka mamaye ta ..
Kuka ta fashe da shi mai sauti kaman wacce ake dukan ta..
A hankali ta sulale kasa ta dafe kirjin ta har tana jan shessheka,bata ma san ya zatayi ta rabu da su din ba..
Familyn Jahan Aarah,subaya junnut kaaamil and khal dukan su farincikin su ayanzu yana hannun ta ne
What if she is gone?will thy be happy!...a tunanin ta tana ganin ita ce matsalar rayuwar su a baki daya.
Kai dole ne ma tabi shi yakaita duk inda zai kaita ya kashe ta ma ayanzu ji take kamar bata damu ba
Wannan shine da sadukarwan da har ta mutu bazata manta da shi ba.
Kuka taci sosai kamar wanda take ganin mutuwar ta har sanda aka kira ishai kafin ta tsagaita
..,jiki ba kwari ta mike ta dauro alwala tayi ishai..few minutes tana kwance akan gadon shi fuskansa ne yake mata gizo'...ita har yau bata san meya sa take mutuwar son sa'ood ba..tun daga ranan da suka fara haduwa ta fara tunowa har ila yau tana hawaye...gaba daya pillow case din data lafe ya jike da tears zuciyan ta na mata wani irin zafi but dan tayi saurin dawo wa cikin hankalin ta sai ta dan ja drawer sa,batare d tasan dalilin yin haka ba
...babu komi aciki sai hard cover joter mai kyau bold and calm handwriting dinshi ne akai an rubuta the devil dog...
She stare at it for a while,cahn ta mike ta zauna da shi a hannu tana budewa saiga wani hoto ya fado a ciki da sauri ta daga.,murmushin bazata ne ya kufce mata data ga hoton ta ne na tun lokacin da sukaje programe din shahrul ya yaga fuskan sauran ya aje nata ita kadai.
Bude diaryn tayi taga babu komai aciki...biron dake jiki ta zare with much insanity ta rubuta masa summaryn duk abunda ke faruwa da itaTare da yadda take matukar kaunar shi aranta,..knocking yasa ta aje book din a gurguje bata rufe shi ba ma ta fice ta amsa door din
maid ce a bakin door ta kawo mata sakon cewa ana neman ta a waya achan side din hjy indira..
Batayi kasa a gwuwa ba ta dauko mayafin ta ta isa,fitar ta ke dawuya kaamil ya shigo dakin after 20minutes baigan ta ba sai ya dauki joter ya bude ya shiga karantawa cikin nitsuwa..
dama junnut ta gaya mashi sunyi magana da bahiyya,so yazo ne ya sake gwadawa da niyyar idan bazata fada mashi waye mijin ta ba zai mata sallama a goben zai tafi bazai sake dawowa nigeria ba har abada...
Sai dai abun da yake gani ayanzu ya zaca masa kwakwalwa ya ruda masa tunani
Bahiyya and his sa'ood?Sadat and bahiyya?
Ji yayi kamar wani iirin labarin tatsuniya yake karantawa musamman ma na wasan yara...yanzu abu daya kawai yake so yaji ya tabbatar da zancen
Shin dagaske ne khaldun ya aure ta kamar yadda yagano a rubuce tana refering dinsa da husband?..
Shin meyasata ki fada masa?wai har saood zaiyi aure bai sani ba?
..Sannan wannan sirrin subayan daya gani bayajin zai iya yin shiru akai mikewa tsaye yayi da joter a hannu yana mai sauke ajiyan zuciya
Tuni ya mance da hrtbreak dinsa ya shiga jigila yana nazari..
.. shikam dama basu ko ga maciji da sadat jinin su sam bai hadu ba....
Yana cikin haka sai ga budewar door din, data ganshi sanda ta tsorata bude baki tayi kamar zatayi magana data ga joter ahannun sa sai da taji gaban ta yayi mumunan faduwa
Turus tayi abakin door tana rau rau da