Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wasa da So Complete Hausa Novel by Aisha Muhammed Sani

Author :  Aisha Muhammed Sani Category :  Romance

Chapter   7 / 8

18K to 21K   out of 21.4K words

wadda ba ta taba dariya ba arayuwar ta.

"Oh wai har kun gama ne."cewar Adam

Hameeda ta ce, "Daman ina zaka san mun gama tunda ka na waya da wa ta yar iska,ka
manta da mu kaman ka shanya gawar shanu."


Tun da Hameeda ta fara maganar nan Adam kawai ido ya zuba ma ta tsabar mamaki sai
da ya ga ta tsaya sannan ya ce, "Kin gama ko da kari?"

Ta fara un'uni ta na, "A kan wata yar iska kawai........

Adam ya ce, "Hameeda! ina ni bakin ki ke furtawa magana haka?, nagode ba laifin ki
ba ne, huce mu shiga mota."

Auta ta shige A bin ta ita ko Hameeda ta na tsaye ba bu alamar motsi.

Adam ya kara da cewa, "Ba ki ji me nace bane wai?"

Hameeda ta ce, "Na ji Amman kuma bazan shiga ba napep zan hau."


Tsabar bacin rai Adam bai san lokacin da ya kwashe Hameeda da mari ba.

*Ni ko ina gefe nace ana wata ga wataπŸ€”*

Urs xayyeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹
*WASA DA SO*
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*
🀣🀣 _Yau ba kalaman love na kai kasuwa asiyar min_

*PAGE*-25

_Wannan fejin na kune ma su lekye min status🀣mussaman uncle bamai,
shalele,babaxee,fauziya s madaki,kulsum, feedyn bash in ba ku daina kallemin status
ba sai na muku tar gade akumatu😍😍😍ina yin ku yan uwa naπŸ’ƒ_
____________________________________________________________________________

*BEST COMMENTS OF D MONT*

DAGA AYSHA HUMAIRA

Na gode sosai Allah yabat qauna

😑😑😑😑😑😑😑
Amma fa yau Yaya adamu tom ya zafe ni over tayaya zai mare mu bayan ya gama
soyayyar sa bamu ce masa komai ba🀨🀨🀨🀨

Wlh ma ni tausayi take bani yaya zayyi mata haka Dan Allah

🀨🀨🀨🀨🀨🀨
Wacece ma take da suna ku tunamun wan nan mara kamun ka da ita yanzu ko cemata akai
mata an mata kyautar Messi ai yar😎

Dan tasan ba sonta yake ba kawai

Kuma kwaci qwal uwaku idan baku sasanta ba kuka ja aka shiga tsakiyar ku ehe😎

Muna godiya sista Allah ya qara basira da zaqin hannu😘😘

*TO FA KUN DAI JI SAKON NMCY GAREKU ADAMU DA HAMEEDA HAR MA KAWATA NUSAIBA*🀣🀣

Rikye kumatun ta kawai tai sai ga hawaye na kwarara daga idanun ta, ta kasa dago
kai ma bare su hada ido da Adam.

Rai a bace ya kara da cewa, "Wuce ki shiga mota mu ta fi ko?"

Hameeda ba ta ce komai ba illa tafiya da ta fara kamar wadda kwai ya fashewa aciki
har ta isa wajen motar, sannan ta shiga.

Adam kawai cizan harshe ya yi sannan ya shiga motar, Auta ko ta kasa magana domin
duk abin da akai a idanunta a ka yi.


Tuki Adam ya fara kawai gudu ya ke domin zuciyar sa ta fasa ta ke ba abin da ya ke
fadi a zuciyar sa sai, "Me ya sa zan mari Hamee na, mai ya sa hakan?, Na ji haushin
kai na."

Tambayoyi barkatai kawai yake jerowa kan shi wanda ya rasa dalili kuma ya rasa
amsoshin su.


Hameeda kuwa tuni ta fada duniyar tunani, "Wai yau ni Yaya Adam zai mara! ko
mummunan kallo bai tabamin ba bare mari, Amman duk da hakan ni na ja domin kuwa
nasan ban taba ma sa magana cikin tsiwa ba."


Dukkan su ko wa da abinda ya ke ayyanawa acikin ran sa.

Duk da cewa Hameeda tunani ta ke tare da tuhumar kan ta amman hakan bai hana hawaye
fita daga idanuwanta hakan ya sa Auta ma fara kuka.


Adam na kallon su ta mirro hakan yasa shi tsayuwa da tukin sannan ya fara fadin,
"INNALILLAH WA INNA ILAIHIR RAJI'UN."
Azuciyar sa har sai da ya ji zuciyarsa tai sanyi sannan ya fara tukin .

Bai huce da su gida, wani wajen shakatawa da yasaba kawo su kawai ya nu fa.

Su na isa ya fito tare da budewa Hameeda kwofa, ba mu su kuwa ta fito, haka ma Auta
ta fito.

Adam ya ce mu su, "Ku zo muje."

Haka kuwa akayi suka bisa abaya wani gun zama yakai su tare da mu su alama da su
zauna.

Sun fi minti goma da zama amman ba wanda ya ce wa kowa komai.

Adam ne ya durkusa tare rikwo hannun Hameeda kamar yadda ya saba aduk sanda ya gan
ta cikin damuwa.
murya Araunace ya ce, "Hamee na, kin san yau kin batamin rai kuwa."

Daga ma sa kai kawai tai alamar eh.

Ya kara da cewa, "To me ya sa ki kamin rashin kunya?, ko da na mi ki wani abun da
ya bata mi ki rai ta wannan hanyar yakamata ki sanar da ni?"

Kara daga ma sa kai kawai ta yi.

"Kin sa zuciya ta tai zafi har ya kai ga na mare ki, nasan cewa kin ji zafin marin
ajikin ki amman ni na fi ki jin zafin domin kuwa azuciyata na ji sa, ki yi hakuri
ki ya fewa Yayan ki bazan kara ba." yakarasa fadan hakan tare da rikye hannuwan sa
biyu

Alokacin Hameeda ta dago tare da durkusa kamar yadda ya yi ta rikwo hannayensa biyu
tare da fadin, "Yaya ni ce da laifi wallahi duk laifi na ne, domin kuwa nasan da
ban ma haka ba bazaka taba mari na ba, kuma nayi danasanin yi ma rashin kunya, Abun
da ban taba ma ba arayuwa, nasan cewa za kai tunanin cewa na girma ne nafara
hakan."
Ta karasa maganar ta na kuka.

Share ma ta hawaye Adam ya fara yi tare da cewa, "Ki bar kuka Hamee na ni ai nasan
ba haka Hamee na ta ke ba, kin yanzu bari akawo ma na ice cream mu sha sai mu tafi
gida ko." ya fada yana kallon Auta wada tuni ta wage baki domin an ambaci
masoyinta.


Icream Adam ya je yakarbo mu su aiko tuni Hameeda da Auta su ka ware su na sha,
Adam ko sai dariya ya ke mu su.

Da ka gansu kasan cewa su na cikin farinciki kaman ba su ne dazu ba.

Harda rige-rigen shanyewa tuni ko Auta ta riga Hameeda, ai ko Auta ta kwace na gun
Auntyna ta shanye.

Sannan su ka tashi da nufar hanyar gida.



Urs Xayyeesherth.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹
*WASA DA SO*
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

Once in a white, great love comes to your life. it probably wont last but its good
to know that at least once in your life, you had that kind of love

*PAGE*-26

____________________________________________________________________________

A kwana a tashi har lokacin jarabar Hameeds yayi Adam kuma zai koma makaranta.

Ranar da zai koma ranar Su ka fara zana jarabawar su.


Tunda Adam ya koma skul ba su kara waye da Hameeda ba kasancewar exams ya sha ma ta
gaba, kuma Dady ya karbi wayar ta ma.


Adam da Nusaiba sun fara soyayya Amman zan iya cewa ba kamar yadda masoya su ke ba
domin kuwa shi gudun ta ya ke duk da cewa yadage akan sai ya koyawa zuciyarsa son
ta na dole amman hakan ya gagara.

Malamin su kuwa kullum acikin jan sa ya ke ajiki domin komai ya faru sai Adam ya
sanar ma sa.


_________________________

sai da su Hameeda su ka kammala jarabawar su sannan su ka fara waya da Adam suna
dan gaisawa amman ba kamar yadda su ka saba ba.

Muhsin kuwa yadawo daga neman kudi kuma ya samu ba laifi domin kuwa aiki ya yi
tukuru domin ya ga ya mallaki abar kaunar sa.
Yau kwanan sa uku da dawo ya zo falo domin magana da iyayen sa.

"Abba nadawo nace ko za akarama iyayen Hameeda magana tun da dai yanzu ta gama
makaranta."

Abba bai ce komai ba har sai da Mama ta kara da ce wa, "Haba Alhaji ba ki mai yaron
nan ya ke cewa va ne."

Murmushi Abba ya yi tare da fadin, "Ko kun man ta da maganar da nai a bayane?, ni
bazan hanasa auren Hameeda ba amman na cire hannuna dashi kuma bazan fasa ma sa
fatan alkairi tare da sa albarka ba.


Tun da Abba yagama jawabin sa ya tashi tare fadin, "To ni dai natafi office sai
nadawo.'

Muhsin Da Mama su ka ce , "Adawo Lafiya."

Ya amsa da, "Ameen." sannan ya fita.


Mama ce ta juyo ga Muhsin ta ce, "To dai ka ji amman a ganina hakan ba matsala ba
ne kaje ka sammi Alhaji Ahmad."


*Babban Aminin Abban muhsin kennan*

Muhsin ya ce, "Ai kuwa Mama shikennan, nasan ina zuwa gun Baba Alhaji magana ta
kare."

Muhsin ya fita cikin farinciki domin yasan cewa kaman ya Auri Hameeda ne da yardar
Allah.


Aikuwa ya na zuwa yasanar da shi bai bata lokaci ba ya nufi gidansu Hameeda.

Bayan ya je sunyi magana sosai sannan Dadyn Hameeda ya nuna ma sa ce wa ba komai
tare da sa ranar Aure nan da wata daya .


Tunda Muhsin ya ji wannan lamari farinciki ya kasa gushewa azuciyarsa,Hameeda ko
ita ji tai kamar kullum abun bai dameta ba ko ajikin ta.


Ta fannin gidaje biyun nan kowanne kawai shirye-shiryen biki ake.

Adam ko ya na makaranta bai ma san me ke faruwa ba,Amman wani lokacin ya kan tsinci
kan sa cikin damuwa,duk da cewa sun gama makaranta saura kwanaki kadan su dawo gida
amman ji ya ke kaman shekaru zai kara, kawai damuwar sa bai wuce ace ya dawo gida
ba.


****************************

A kwana atashi yau Adam ya kammala makaranta zai dawo gida kamar yadda saura
kwana bakwai bikin Hameeda ka na ganinta kasan cewa ta tana da damuwa domin ku duk
ta rame ta yi baki.

Adam ya ki fadawa kowa zai dawo wai shi adole surprise zai mu su mussaman ma
Hameeda.


Gidan su Hameeda yafara zuwa a ka ce ma sa ai suna family HOuse gaba daya harda su
Momynsa Domin za ai bikin Hameeda.

Abin ya matukar bawa Adam mamaki duk da cewa yasan maganar Muhsin da Hameeda.

Ba inda ya nufa sai Family house din su banda bugu ba abinda zuciyarsa ke ma sa.


Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹
*WASA DA SO*
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

❀❀❀ when you love someone is not special
but when you are loved by every one is the most special thing in life.
*PAGE*-27

____________________________________________________________________________


Ya na zuwa ku ya iski gida ya cika tam, dan haka kuwa ba tantama Auren Hameeda za
ayi.
"Subhannallah."kalmar da ya ke iya furtawa kennan.

Jan kafar sa ya ke da kyar har ya shiga ciki Auntyce ta tawo da sauri tare fadin,
"Oyoyo Son Amman gaskiya ka shammace mu fa, da har ina gobe azo adauke ka ka zo ayi
biki da kai."

Murmushi kawai Adam ya kewa Auntyn nasa domin maganar ma ya kasa.

Hameeda ce ta fito da murmushin ta tare da fadin, "Yaya messi welcome ai na zata ma
bazaka zo ba." a shagwabe ta ke maganar kamar yadda ta saba.


Aunty da ta fahimci d'an na ta cewa akwai matsala ce wa tai, "Son zo mu shiga daga
ciki, ke kuma Hameeda ki je ki karbo mana dinkin."


Aunty kawai jan Adam ta ke domin tafiyar ma da kyar ya ke.

bayan sun zauna ne Aunty ta ce, "Son me ke damunka ne?"

Dauriya Adam ya yi tare da fadin, "Bakomai Auntyna kawai dai ba na jin dadin jiki
na ne."

Aunty ta tashi tare da fadin, "To jirani ina zuwa."

Alokacin Adam ya ji wani abu ya tarnake masa azuciya "Aunty, Aunty ki tsaya zan
mutu."

Ahankali ya ke maganar domin kuwa zuciyon ya fara cinsa.

Da sauri Aunty ta karasa waje ta sanar da su Mama da driver domin aje asibiti.


Kan su karasa asibi Adam ya dai na motsi kwata-kwata.


Aunty ta na kuka tana fadin, "Son kar kamin haka dan Allah kar ka tafi ka barni."

A haka har su ka isa asibitin, likitoci suka taru akan Adam kowa ya na iyaka bakin
kokarinsa.


Tun safe har dare yayi ba likitoci Ba Adam.


Sai kusan asuba su ka fito tare da musu albishir cewa an samu damar ceto rayuwar
Adam da kyar.

Ba karamin murna dukka family su ka yi ba kasancewa Adam ya na daga daga cikin
wanda aka fi ji da shi a family.
Bayan su Dady sun zo sun gansa sun tabbatar da cewa jikin da sauki sannan su ka
koma gida akabar Hameeda Akan Aunty zataje tai wanka inta dawo sai Hameeda ta koma.


Hameeda na shiga dakin Adam ya kalleta da murmushi tare da fadin , "Hamee na."

Hameeda ta ce, "Sannu Yaya Messi wai Muhsin na gaishe ka anjima zai zo."

Adam ya riko hannun kanwar ta sa tare da fadin, "Hameeda,yanzu nasan cewa na yi kai
na babban illar ta dalilin *Wasa da so* ban san cewa ina mi ki so na Aure ba sai
ayanzu,Hameeda dan Allah kar ki gujeni akan ki zan iya rasa rayuwata,Hameeda ina
son ki wallahi da gaske na ke ina sonki, sonki ne ya kai ni cikin wannan halin,ki
aminta da ni mu rayu dan Allah."


Tunda ya fara maganar nan Hameeda kawai kallon mamaki ta ke masa sai da ta ga yayi
shiru ta ce, "A'a A'a Yaya Adam ba na son wannan wasan ka bari karka kara bana so
ni Muhsin zan Aure,ka dai na min haka wasan ka ya yi yawa,ka bari dan Allah."karasa
maganar tai tana kuka tare da fincike hannun ta, ta fita daga dakin.

Adam kuwa banda hawaye ba abinda ke kwarara a idanunsa azuciyarsa ko sai fadi ya
ke, "Ni na cuci kai na daman nasan Hameeda ba za ta taba yarda da ni ba wallahi
nayi dana sanin *Wasa da so* sai ayau nasan me nene so."

_Ni xayyeesher na ce ko ya abun zai kasance? ku biyo ni domin ganin Ya zata
kaya......._

Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹
*WASA DA SO*
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

*PAGE*-28

____________________________________________________________________________


Hameeda na fita kuwa ta ci karo da Aunty, tuni ta goge hawayenta kan ta karasa,
Aunty ta ce, "Fatan dai ba jikin Yayan na ki ba nE?"


kawai girgiza ma ta kai Hameeda ta yi alamar Aa, ita ko Aunty ba ta tsaya ba ta
amsa ba ta shige ciki.

Ta na shiga ta tarar da Adam ban da hawaye ba abin da kwarara daga idanun sa, da
sauri Aunty ta kasara tare da fadin, "Menene kuma son ko dai jikin ne a kira
likata."

Rikwo ma ta hannu ya yi tare da fadin, "Aa Aunty ki zauna ba komai."

Aunty ta ce, "Indai zan zauna sai ka min alkawarin za ka fadamin abun da ke damun
ka."

kawai zub da kwalla Adam ya cigaba da yi domin kuwa in bai manta ba Aunty ma ta ta
ba fada ma sa cewa ya na *wasa da so* da kyar kuwa ta shawo kan sa, sannan ya fada
ma ta komai abin da ke faruwa tun ya na makaranta kawo yanzu.

Ba karamin tausayin Adam ya ba wa Auntyn sa ba domin tun tuni ta ke guje ma sa
wannan ranar.


A karshe ya kara da cewa , "Aunty Dan Allah kimin Alkawarin cewa wannan maganar ta
zama sirri, ni zan iya jure komai indai Hameeda za tai farinciki a gidan Auren ta."

Aunty ta ce, "To kai kuma lafiyar ka fa son, kennan farincikinta ya fi lafiyar ka
da farincikin ka."

Murmushi kawai Adam Yayi sannan ya ce, "Bakomai Auntyna ai kanwatace."

Duk da haka dai Aunty ta kasa walwala a asibitin nan sai ya kasance Adam ya zama
kaman shi je jinyar ta sai ma ta wasa da dariya ya ke duk dan abun ya bar ran
ta,duk da cewa kuwa shi ya san mai ke damunsa azuci.

Daga karshe dai likita ya zo ya Domin sallamar su tare da ba wa Aunty shawara akan
cewa, "Duk abin da Adam ya ke so amasa indai ana son rayuwarsa."

To fa anan hankalin Aunty ya kara tashi, Adam kuwa ya nuna ma ta cewa ko ajikinsa,
Gashi ba ta da damar fada domin tq dau masa alkawari.


Tunda suka koma gida Hameeda ke gudun Adam , shiyasa da ya fahimci hakan ya ma dai
na fitowa kullum ya na daki.


Muhsin kuwa Mubarak ya sanar dashi komai akan yq taimaka ya barwa Adam Hameeda Amma
ya yi burus tare da da fadin ai shima son tq ya ke kuma ma yq fi Adam son ta.


Akwana atashi yau saura kwana daya bikin Muhsin da Hameeda.

Sun shirya tsaf domin tafiya kamu.

Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹
*WASA DA SO*
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*
*PAGE*-29/30

____________________________________________________________________________

_SADAUKARWA GAREKU YAYUNA HASSAN ATK$HUSSAINI ATK ALLAH YAKARA RAYUWA MAI ABARKAπŸ™_

*Godiya ta mussaman gareka YAYA Mubarak Allah ya kara basira da daukakaπŸ™ALLAH YA
BAKA ABIDILLEπŸ₯°*


*FEjin yau dai ba editing kuyi hkr da typing erorrs*


Fitowar da Adam zai yi domin tafiya ganin Muhsin da Hameeda ne ya rikita ma sa
zuciya tuni ya fadi akasa,Hameeda ko na hango hakan tuni ta tawo da gudu tare da
zuwa wajen yayan na ta,kan ta karasa har numfashin sa yadauke.

Kuka ta fara tare da kiran su Mama,Momy da Aunty,ai ko tuni aka dau hanyar asibiti.



Su na zuwa aka fara Adam taimakon gaggawa , anyi sa'a wannan karan bai kai na
wancen jimawa ba amman wannan din ya fi hatsari domin kuwa ya na dab da rasa
rayuwar sa,Hameeda na dakin ta ki fita rikye ta ke da hannun Yayan na ta, ai ko ya
na farkawa murmushi ya yi tare da fadin, "Hamee na bakuje gun kamun ba ne, ku ta fi
nima zan zo."

Hameeda ta ce, "Aa ai an ma fasa."

Adam zai yi magana kennan sai ga likita ya shigo.

"Barkan ka dai Adam ya karfin jiki?"

Murmushi ya yi tare fadin , "Jiki Alhamdulillah likita."

Likata ya kara da cewa, "Ka na dai daurewa ne kawai, amman dole akwai abun da ka ke
so kuma in baka samu yanzu ba ina da tabbacin ka kara faduwa irin ta yau

7 / 8