Author : Aisha Muhammed Sani Category : Romance
"Smile sai ka zo kawai, za ka sha mamaki."
Hirarsu suke cikin nishadi,Wanda duk Wanda ya gansu zai ce Masoyane , A masoyan ma
wa'inda sukai zurfi cikin so.
Amman su kam ba su fahimci hakan ba su dauki kulawar da sukewa juna kawai shakuwa
CE ta yan uwan juna.
In kaga Adam ya wage baki yanata dariya da tsayawa to suna tare da hameeda ko su na
waya,In ba haka ba kana ganinsa kasan miskiline.
Haka kuwa ita ma Hameeda surutun ta agunsa ya tsaya ko ince akanta domin in dai ka
ga ta zakye tana zubar ba da labari to A kan yayanta Adam ne.
Duk da cewa iyayensu sun fahimci cewa akwai soyayya tsakanin su amma hakan bai sa
sun fada musu ko su nuna cewa sun fahimci hakan ba,kawai sun zuba musu idone suna
ganin ikon Allah.
Adam na gama waya da hameeda Mubarak ya ce, "Nikam dai yau ba zanyi shiru ba,Adam
wai mai yasa ka ke *WASA DA SO* ne?,ka son Hameeda Amman ka kasa fahimtar hakan.
Adam ya ce, ............
Urs xayyesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*WASA DA SO*
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE*
whenever U feel Blue,
i will be there for U,
Whenever u are sad'
i will stay by ur side,
whenever U need sumone to love,
i will always be there for u......
*PAGE*-22
____________________________________________________________________________
"Ba ka yi karya ba Ina son hameeda kuma ina son mace mai irin haleyar ta da ma ya
na yin ta gaba daya,Amman abinda ba Ku gane ba shine son da nake ma ta ba irin
Wanda Ku ke tunani ba ne,Hameeda jinjikinace dole na so ta kuma nai kishinta Amman
ba wai so na soyayyar Aure ba,bana tsammanin zan iya rayuwar da Hamee nah." Ya
karasa fadan hakan ya na murmushi tare da kallon hoton Hameeda da ke screem din
wayar sa.
Mubarak ya ce, "Hmm Adam kennan ina ganin ni na San ka fiye yadda kasan kan
ka,Amman A kullum Ina ma fatan alkairy, domin farincikin Aminina shine na wa."
"Godiya na ke Abokina naji dadin jin hakan daga bakin ka."
Washe gari
Hameeda na zaune ta na chating A wayarta sai ga text din Muhsin ya shigo ma ta
kamar haka:
_"Assalamu alkaimu ya ke masoyiya ta,hasken raina,fatan kin tashi lafiya?Allah yasa
haka Ameen,ina so in sanar da ke cewa yau zanbar cikin garin nan zan koma kauyen
kano *gaya* asarin garin mahaifina,Ku ma bazan dawo ba sai har na mallaki Abinda
zan aureki dama Wanda zan ciyar da ke da ikon Allah,Amman ina so kimin alkawari
daya,bazaki taba bawa wani damar shiga zuciyarki ba,ki killacemin kanki kamar yadda
kika saba,daga yau bazan kara kiran ki ba kuma bazan kara miki text ba har sai na
dawo gareki,karki manta ina son ki ,kuma zan cigaba da sonki har bayan raina,na
baki Amanar zuciyata,ZANYI KEWARKI ,daga masoyinki,kuma mijinki in Allah ya yarda
MUHSIN."_
wassalamu alaikum
Hameeda ta na karanta text din ta na kuka ta rasa me ke ma ta dadi Aduniyar nannan.
Haka ta gama kukan ta har tai barci agun.
_________________________________________________________
A kwana atashi har Muhsin ya yi sati biyu da tafiya,Adam kuwa ya gama jarabawar sa
zasu dawo gida .
Adam da Mubarak sun shirya tsaf,hakama Nusaiba wadda ita dai da ka ganta kasan ba
ta son tafiyarnan.
Adam da Mubarak sun rakata har wajen motarta suna Allah ya kiyaye,Nusaiba ko ta
kasa magana banda hawaye ba a binda ke zuba a idonta.
Har suka shige motar da a kazo dauka Kansu tana kallon su sai da motarsu ta tashi
kan itama fara tafiya.
Hameeda tun safe ta tafi gidan Su Adam domin tarar yayanta Adam.
Ita da Aunty ne suka shiga kichin sai girke-girke su ke kala-kala,Mama in tazo
hucewa sai dai ta CE aiki bai isheku ba ne,sai ka ce Abban Autane zai dawo kun
wani zakye sai girki Ku ke kun cika ma na gida da kamshi."
Aunty ce tai murmushi ta na fadin, "Haba ke kuwa Mama D'a na ne fa daya tillo ke
hanya ai dole na dage Dan wallahi ni na zaku ma ya yi ya dawo da,da yarda zanyi
yadawo karatu agarinnan ai da na yi wallahi,gidan ba shi ba dadi."
Mama ta ce, "Oh wannan inaga to in kuma yayi AURE agidannan za ki ce ya tare."
Aunty tana dariya tana fadin , "Ai kin San ma wannan dole ne."
Duk da cewa Aunty ba ita ta haifi Adam ba Amman ta dauki soyayyar duniyar nan ta
daura a kan sa,tun ya na karami ta ke wahalarsa har yau kuwa ba ta taba nuna
gazawarta ba,ko yarta da ta Haifa ba ta nuna ma ta so kamar yadda ta nunawa Adam
ba.
Hakan yasa kullum suke kara samun zaman lafiya da farinciki a cikn gidan su.
Auta kuwa ranar tak'i zuwa skul wai ita A dole sai yayanta ya dawo shi zai
kaita,da kyar Mama ta lallabata sannan ta yarda aka kai ta tana dawowa kuma ta fara
murna bai dawo ba ita zata fara ganinsa tuni ita da Hameeda suka je kwofar gida su
ka tsaya.
Misalin karfe 3 na rana su Adam su ka iso.
Da gudu Auta ta karasa wajensa tare da rungume yayan na ta, ita kuwa Hameeda ta na
ganinsa taji wani sabon lamari jikinta duk ya mutu,kawai kunyarsa ta ke ji,da Dane
da tuni ta karasa ta na ma sa oyoyo Amman yau ta kasa.
Shi ko yadau Auta Amman hankalinsa na kan Hameeda kawai ita ya zubawa ido,ya ga ta
kasa karasowa garesa.
Ba ta rai ya yi tare da fadin, "Ke ba za ki karaso ba ne?"
Urs XAYYEESHERTH
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*WASA DA SO*
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE*
My love for you knows no bounds, itβs timeless and endless. You can enrich my life
in more ways then I could ever express in words. I felt strongly connected to you
the moment I looked into your eyes. I was drawn to your soul in a way I have never
experienced before. You are the only one can see the door to my soul.
*PAGE*-23
____________________________________________________________________________
A shagwabe Hameeda ta ce, "To bayan Auta ce ta rigani." Zuwa ta ke ta na fadin
hakan.
Adam ya yi murmushi ya na, "Ai na zata zaki nunamin kin girma ne an dai na min
Oyoyo."
Dariya kawai Hameeda ta yi tare da karban jakar hannun sa su ka shige gida.
Su na shiga Aunty ta tawo ta rungeme D'an ta tare da fadin, "Barka da dawowa my
son."
Murmushi Adam ya yi tare da durkusawa kasa yana, "Nagode Aunty na na same Ku
lafiya."
Dago dashi Aunty tayi tare da fadin, "Smile lafiyan mu lau,ma za jekayi wanka ka yi
sallah sannan ka zo ga abincin ka nan komai ya na shirye."
Adam ya ce , "Ok Aunty ina Mama tsohuwa ne wa to ita ko murnar dawowa ta ma bata
yi."
Mama ta fito tana, "Yoo ni ina ruwana da dawowarka ka dawo ka ishemu dai."
Aunty ta ce, "Eh munji son bar tsohuwar nan je kayi abinda ke gaban ka."
Adam kawai murmushi ya yi yatafi yana murnar kasancewa D'a ga Mama da Aunty DOMIN
akullum kara birgesa su ke yadda suka hada Kansu su ke zaman lafiya tsakanin su.
Hameeda ce ta bi bayansa da jakarsa,su na shiga Adam ya kulle kwofar tare da fadin,
"Hamee nah da alama kina cikin damuwa Dan ban sa ba ganinki cikin ya nayi haka ba."
Murmushi Hameeda ta yi tare da fadin, "Smile yayana ka yi wanka kai sallah in kaci
abinci za muyi magana."
Adam ya ce , "Oh shikenan sai na fito."
Hameeda ta fita tana, "Adai yi wanka mai kyau kar ai jika-jika."
Adam kawai dariya yayi yana, "za ki sa ni zan fito ai."
A nutse Adam ya yi wanka ya gabatar da farilarsa sannan ya shirya cikin Kananun
kaya,bluen Riga da farin wando,tare da Glass din sa Wanda ya saba sawa,da ka gansa
kai kace wani babban taro za shi.
Aunty da Mama ne Afalo su na zaune.
Ya na fitowa Mama ta ce, " Ai mun za ta sai an shigo an janyo ka za ka fito ne."
Aunty ta ce, "Umm su Tsohuwa dai an cika sa ido,son rabu da ita ka je ga abincin ka
chan Hameeda ta shirya."
Adam ya ce, "Aunty na rabu da Mama nasan damuwarta bai huce goro ta ke bukata ba."
Mama ta ce, "Dukkan su zaku sani ne Bari Abban Auta yadawo."
Dariya dukansu suke sannan Adam ya nufi wajen Hameeda.
Ya na zuwa ta ce, "Wooo yaya Messi na gaskiya turaran kan nan kamshinsa dadi dole
in sace."
Adam ya tabu ne fuska, "Tab yasin ba ki isa ba budurwa ta ce fa ta siyamin ."
Hameeda ta ce, "Oh ka ce yan karya ne su ka siyama ba ma wannan ba ga food din ka
nan bismillah."
"Woooo Amman dai Auntyce ta yi girkin nan daga jin kamshin,Dan nasan ita kadai za
ta iya."
Cewar Adam
Hameeda ta ce, "Ohooo dai ni kaci abinci."
Adam ko ya yi shiru sai afa abinci ya ke abin sa, Hameeda ko ta zuba masa ido ta na
ta kallon sa.
Sai da Adam ya ji cikin sa yadauka dam sannan ya ce, "HAMEEDA ki nutsu muyi magana
ba na son ki boyemin komai ki fadamin komai,me ke damunki? Miye damuwarki? Kar kiji
tsoro ko shakkar fada min duk abin da ke faruwa."
Hawaye ne ya fara zubowa a idanun Hameeda ta rasa me ma zata CE da yayan na ta.
Adam ne ya fara goge ma ta hawayen da ke kwarara afuskarta ya ce , "Hamee na please
ki nutsu mu yi magana."
Hameeda ta ce, "Yaya ......
Urs xayyeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*WASA DA SO*
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE*
You're Always On My Mind, Day And Night
When I Think Of You, All Feels So Right
Need To Have You, Need To Hold You
And Tell You That I Love You.
My Dear, I Don't Want To See Us Apart
This Separation Just Tears Away My Heart
I Miss You, Oh, I Really Miss You
Will Need You More And More Each Day
I Know I Cannot Live Without You
I Miss You, More Than Words Can Say.
*PAGE*-24
____________________________________________________________________________
*WANNAN SHAFIN NA KU NE YAN GRP DIN BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION mussaman ku
Aisha humaira da AG ina yin ku irin sosai dinnan comments din ku na bani nishadiππ
ππ*
Sai tai shiru, Adam ya ce, "Ina jin ki Hamee."
A nan Hameeda ta kwashe duk abin da ya faru tsakanin ta da Muhsin da ma na Abban
Muhsin da Dadynta ta fada ma sa.
Gaba daya jikin Adam ya yi sanyi domin ga dukkan Alamu Hameeda ta Amince da Muhsin,
duk da cewa ya na jin kishin kanwar ta sa, to Amma fa wannan karon ya zama dole ya
taimaka ma ta wajen cimma burin ta, domin farin cikin ta.
Murmushi Adam ya yi tare da riko hannun kanwar ta sa ya ce, "Haba Hamee na, A kan
wannan karamin abun ki ka shiga damuwa?,indai wannnan ne na mi ki alkawarin duk
ranar da Muhsin ya dawo, ni zan jagoranci maganar Auren."
Hameeda ta kasa d'ago kai ta kalli Yayan nata.
Adam ya d'ago ma ta da fuska ya k'ara da cewa, "Haba Amaryar Dan Shila Abokina
Smile mana kinsan fa bana son ganin ki cikin damuwa."
Tuni Hameeda ta fara dariya ta na dukan yayan na ta wai a dole ya ce wa mijin ta
d'an shila.
Aunty ta nunawa Mama tana, "Ni ko Mama Anya ba soyayya tsakanin Son da Hameeda
kuwa?"
Murmushi Mama ta yi tana, "Ai indai Adam da Hameeda ne ni na ka sa gane mu su kawai
mu zubawa sarautar Allah ido."
Aunty ta ce, "Haka ne Amman dai zan yi farinciki in son ya sami Hameeda A matsayin
Mata, barin yadda ta san halin sa shi ma ya san na ta."
Mama ta ce, "Haka ne kam."
Ranar kuwa Hameeda ta k'i tafiya gida Anan ta kwana ban da labaran
makaranta ba a bin ya ke ba wa kanwar ta sa har ma da labarin Nusaiba da dramar da
su kai A wajen cin abinci, ban da dariya ba abin da Hameeda ta ke mussaman in ta
tuna gun cin abincin nan.
Karfe 11:00 Hameeda ta ce, "Umm good night yaya Adamu gwanda kai, ku ma kar ka man
ta gobe da sassafe za ka ta shi mu fara karatu."
Adam ya ce, "Ok night sweetie saura ku ma ki zo ki isheni tun A suba."
Dariya kawai Hameeda ta yi ta tafi dakin ta.
Ta na zuwa tai alwala ta yi sallah sai da ta yi karatun QUR'ANI sannan ta yi
Addu'ah ta kwanta.
Haka ma Adam domin sun saba haka iyayen su su ka nu na mu su tun su na k'anana.
Washe-gari
Bayan sun yi sallar Asuba duk sun koma barci, Hameeda har ta kwanta ta tashi tuni
taje ta tashi Auta da ya ke yau weekend ne su ka nufi d'akin Adam da ruwan sanyi su
aboye.
Su na shiga Auta ta fara mintsinin Adam ta na, " yaya ka tashi safiya ta yi."
Ita ku ma Hameeda na ta watsa ma sa ruwan .
Adam ya na, "Haba Auta ku barni na yi barci na mana dan Allah na gaji fa."
Ya gyara kwanciyar sa kawai ya cigaba da barcin sa.
Hameeda ta fadawa Auta abu a kunne .
Ai ko tuni Auta ta gantsarawa yayan na su cizo a kumatu.
Da ihu Adam ya tashi ya na, "Auta wallahi yau sai na zane ki A gidan nan."
Kan ya ta so Hameeda ta dau Auta sun bar d'akin da gudu.
Adam ma gudu ya ke ya na bin su a baya.
Su na zuwa falo su ka zaune ku sa da Abba.
Abba ya na , "An fara ko?"
Auta ta ce, "Umm ba Yaya ba ne ya ki tashi mun tashe sa, shi ne wai sai ya da ke
mu."
Abba ya ce, "Ah to ba abin da zai mu ku, ku zauna anan abin ku."
Ai ko sai ga Adam ya shigo ya na, "Allah yau Auta da Hameeda sai na zane ku a gidan
nan."
Abba ya ce, "A'a fa ni na ce su ta so min kai."
"Allah fa Abba wallahi yaran nan sun raina ni ka bari in zane su."
Abba ya ce, "To ku bashi hakuri dan bakuda gaskiya."
Kunnuwansu su ka kama su na "sorry Yaya bazamu sake ba."
Abba ya yi murmushi ya na, "Yauwa yaran kirki."
Adam ya ce, "Umm za ku sa ni ne."
Hameeda ta kalle sa ta ma sa gwalo
"Abba ka ga yarinyar nan har gwalo ta ke min fa?"
Urs xayyeesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*WASA DA SO*
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE*
when you wait for someone for few mintues-its need
for few hours-its trust
for few weeks-its friendship but when you know the person will not come and still
wait-its love.
*PAGE*-25
*Sorry for d late wishes br amman duk da haka vazan yi kasa agwiwa ba domin kuwa
wannan shifin na ka ne kai kadai*
Wishing you all the fun and excitement that only birthdays can bring. Happy
birthday yaya hayat admin of Adminsπππππ,Allah ya karo shekaru masu albarka.
____________________________________________________________________________
Murmushi Abba ya yi tare da fadin, "Ai kannen ka ne ka yi sorry kawai."
"Umm wai bako ya zo a na nu na ma sa banbanci yasin tafiya ta ma zan."cewar Adam
kenan dai-dai da shigowar Aunty.
Ta ce, "Wa ya isa ya koran min d'a na a gidan nan ai sai dai ku, ku fita."
Dariya dukan su, su kayi Adam ya na, "Yauwa daz my lovely Aunty."
Bayan yan wasu kwanaki.
Adam ne da Hameeda Tare da Auta sun fito za aja shoppin.
Dukkan su Anko su kayi na bluen shadda, Adam ya sa farar hula da farin takalmi,haka
ma Auta da Hameeda farin gyale tare da farin takalmi, Mama ce ta fito ta na
murmushi tare da fadin, "Ah yaran kirki kun sha kyau Adawo lafiya a dai kula."
Hameeda ta ce, "Ameen Mama sai mun dawo."
Suna isa kuwa Auta ce kan gaba wajen shiga,da gudun ta.
Adam ya kalli Hameeda tare da fadin, "Ke ba kya yi gudun ba ne?"
Murmushi Hameeda ta yi sannan ta ce, "Ai in ka ga na yi gudu to kai ma ka yi ne."
" kut wato ka sa'an ki nan, lallai yar nan kin ga ma rainani wallahi."cewar Adam.
Hameeda ta ce, "Haba yaya Adamu na."
Tuni ya bata rai zai yi magana sai ga kiran ya shigo wayar sa, dagowan da zai yi
sai ko ya ga lambar Nusy, murmushi ya yi tare da cewa Hameeda, "Ki shiga ki fara
zaba ina zuwa."
Ba karamin bacin rai Hameeda ta ji ba kawai tafiya ta yi batare da ta kara furta
komai ba.
Kara wayar ya yi a kunnen sa tare da fadin, "Amincin Allah ya tabbata ga saurauniya
ta."
"Tare da sarkin da ya fi kowani sarki adalci." cewar Nusaiba.
Waya su ka yi sosai ta masoya domin zallar soyayya kawai su ke ginawa, a bisa
tsarin da ya dace.
Tun daga ranar da Hameeda ta nunawa Adam cewa ta na son Muhsin shima ya kudiri
niyar koyawa kan sa son Nusaiba, ko da kuwa zuciyar sa taki amincewa da hakan zai
daure domin ya kawar da soyayyar Hameeda da ke son shiga zuciyarsa, *shi a gun sa
soyayyar Hameedan ma ba ta shiga zuciyar sa ba wai so ta ke ta shiga, fans shin kun
yarda wannan hasashen na Adam ku wa?*
Sai da ya gama iya kwokarin sa dan nunawa Nusaiba soyayya sannan ya bi bayan
Hameeda da Auta wa'in da tuni sun gama siyayyarsu shi kawai su ke jira.
Tun daga nesa ya ke murmushi da ka gansa kasan cewa An faranta ma sa rai.
Hameeda na ganin sa kuwa ta bata rai kamar