Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Duniya BIYU Mabanbanta Complete Complete Hausa Novel by M.shakur

Author :  M.Shakur Category :  Romance

Chapter   22 / 48

63K to 66K   out of 142.7K words

agidan marayu yanzu sun tafi, please kibata I don't want wani abu ya saman mini Hajiya" cikeda tashi hankali Mom tace "karki damu bari na bita" kwana tayi da sauri tabi bayan Ammi itama.



Motar Ammi na zuwa gate kasancewan security sun santa suka fara ihu. "Hajiya Don come Hajiya Don come, open the gate" sukahau jin dadi dan bata cika zuwa gidan marayun ba but duk randa zatazo ruwan kudi take musu, dan yake ta musu ta saka hannunta cikin jakan da yar aikinta tabata rapas din yan dubu sababbi ta dauko guda biyu ta mikama babban su, ihu sukahau yi suna mata godiya direba yaja motar ciki, kafin su rufe gate saiga second Mom, dadi kaman yau ana baki itama kyautan tamusu mai tsoka sanan ta shiga ciki, har gaban office din Waleed inda yake parking motarshi direba yay parking, tsabagen yanda jikin Ammi ke rawa kasa bude kofan tayi saida direba yafito yabude mata tasa kafafunta tafito tana fitowa motar Mom na sawo kai wajen, parking tayo tafito da sauri tai wajen yayanta data tsaya chak tana kallonta tace "Adda meya faru?" kasa magana Ammi tayi tajuya kawai Mom biyeda ita, itama Mom ganin yanda mutane suka taru a tsakar wajen yasa taji gabanta yafara faduwa, ana ganinsu aka fara gaishe dasu. "Barka da zuwa Hajiya, barka da zuwa Hajiya" kasa amsa kowa sukayi Ammi tai gaban asibitin daidai Mama Iyami dake kuka sosai tafito tawani irin zube agaban Ammi tace "Hajiya ku shiga yana ciki, wayyo Allah na mun shiga uku, gatanmu na kwance a asibiti raga raga, rai na hannun Allah" tsallaketa Ammi tayi tasa hannu tabude kofan ta shiga ciki Mom biyeda ita, Nurses din data gani charko charko tsaye agaban reception din tawani irin dakama tsawa. "kuna kallo na bazaku gayamin inda d'ana yakeba" arude duka nurses din suka mata pointing dakin da aka rubuta emergency asama, yanda Ammi ke ihu yasa Mom takama mata kafadar Ammi alamun tai calming down, kabar da hannunta Ammi tayi tai hanyar dakin, tana zuwa batai watawataba tabude kofan tasa kanta ciki, Dr Kemi da Dr Ayo ne akan Waleed din dahar lokacin bai farfado ba, ancire mai riga da singlet, dagashi sai dogon wandon jikinshi da belt anmai dauri akafada ta wajen hammata an hade da hannunshi kaman wanda ya karye, fuskarshi tai jajajir, gefen idon damanshi dama idanun duk sun kumbura, gefen bakinshi ya tsage yanadan jini tsabagen marin dayasha na Arham, wuyan shi tsabagen matsan da riga da necktie din wuyanshi sukamai har ciwo suka jinmai jini nafita wuyan yay jajir kaman an zaneshi da bulalan inji.

Hawaye ne suka cika idanun Ammi takasa rikesu suka shiga zubowa har zafin dukan takeji ajikinta tsabagen tashin hankali, tunda ta haifi danta incident makamancin hakama baitaba samun dantaba, daidai Dr Ayo yagama gyara jinin wuyan yajuyo ganin Maman Waleed yanda jikinta ke rawa tana kuka yasa yace "calm down ma, bawani abu babba bane kashin kafadarshi tadan goce ta sanadiyan buga bayanshi da akayi da bango, saikuma bruises din wuyan nan dakuma na ido, dan jini yataru acikin idanunshi but with time zai washe, calm down Hajiya, nan da dan anjima kadan danki zai farfado" da sauri Dr Kemi data karaso wurinsu itama ta gyada kai tace "yes ma calm down please Ma" sukabi ta gefensu suka fita daga dakin, wani irin juyowa Ammi tayi cikeda wutan bala'i, da kunan rai da tsantsan bakin ciki ta kalli Mom sanan tanuna mata Waleed dake kwance kan gado da hannu tace "kinga abinda Arham yama d'ana ko? Kinga abinda Arham yama d'ana ko, kina gani daiko, yaron da dama kece tun day one kikai approving friendship dinshi da yaron, left to me yarona ya rayu ahaka baida aboki I his mother can be his best friend and his everthing aman kika nace saina barsu sunyi abota, dan haka karma naji kinhanani dauka hukunci dan wlh wlh bazan yarda ba" tai maganan tana dauko wayanta daga cikin jaka da sauri Mom tace "Adda kinga calm down yanda kike tafarfasan nan bai kamata kidau hukunci ba, dan Allah kiyakuri Adda" da wayan hannunta tanuna Mom tace "Zainab ki shiga taitayin ki, na rantse miki da Allah yanda Arham ya jima d'ana rauni ko kwana baza'ai ba shima sai anjimai, wlh saiyasan ya buganmini d'a, shidan ubanshi ubanwa yataba dukanshi haka? Waleed dakoni bantaba daga hannu na daka bane wani kato zai dokanmin wlh wlh saina ramamai, wlh kuwa kinji na rantse miki" Ammi tai maganan tana bude kofa tafita daga dakin tana dailing number Maman Arham.






Ringing daya Mama tai picking call din ganin kira daga Ammin Waleed, kafin ma Ammi tai magana cikeda fara'a tace "Assalamu Alaykum, barka da yamma Hajiya" ko amsa sallamarta Ammi batayi ba cikeda bacin rai tace " please kome kikeyi kibarshi kisamemu a orphanage na Waleed yanzun nan kizo, ina jiranki yanzun nan" tana kaiwa nan ta katse wayan jikinta na vibrating, Mom ma takasa cewa komi tazama yar kallo matsalan yayarta kenan intai fushi batada hankali, kuma bataji bata gani barin ma when it comes to Waleed matter.


Gaban Mama ne ya yanke lokaci guda ya fadi, tunda tasan Ammi tsawon shekaru kenan bata taba tamata irin wanan kiran ba saiyau, tomeya faru? Allah yasa alkhairi ne, ahankali tafara karanto innalillahi wa innailaihi raji'un kota samu natsuwa cikin zuciyarta, dan batada natsuwa ko kadan sabida zuciyarta wani irin mummunan faduwa kawai yake.





Hijabi kawai ta dauka ta zira akan kayan dake jikinta, ta kwalama diyar kanwanta kira tace "nafita yar albarka saina dawo, ki daura abincin dare" daga ciki yarinyar ta amsa da "saikin dawo Mama" fita tayi daga dakin ta kwalama driban ta kira yafito, mota ta shiga tace yakaita orphanage dinsu Waleed ya amsa mata da to, yatada motar yafita daga gidan.


Ko cikakken 15min direban bai daukaba yakaita orphanage din, tana fadin mahaifiyar Arham ce ita aka barta ta shiga dan ta taba zuwa sau daya suka shiga ciki, kirjinta bai kara faduwaba sai dataga ma'aikatan orphanage din carko carko a tsaitsaye ana tattaunawa agaban clinic, parking direba yayi tabude kofa tafito daga motar kirjinta na bugawa, wayarta dake hannunta taciro tanemo layin Arham ta hau kiranshi danta tambayeshi maiya faru, wani abu yafaru ne amman har wayan ya katse bai dauka ba, hakan yasa tai dialing number Ammi, ringing daya Ammi ta dauka, ahankali Mama tace "Hajiya na iso" cikin muryan Ammi dabata fita sosai tace "kishigo asibitin muna emergency" shine kawai abunda Ammi tafadi mata ta katse wayan, sosai Mama taji kirjinta na bugawa yanda Ammi kemata magana, hakan yasa ta daga kafarta tana kallon mutane ta shiga tafiya harta karasa gaban asibitin tasa hannu ta bude kofar ta shiga ciki, kasan cewan emergency din asibiti bata boyuwa yasa tana ganin dakin tagane batare datama tambayi nurses din dake wurin ba tai wajen kofan, ahankali ta murza hannun kofan dakin tashiga ciki, Ammi da Mom tagani zazzaune, Mom kan kujera Ammi kuma kan gado gefen kafar Waleed, Waleed kuma kwance kan gadon asibiti, ansa mishi drip, fuskarshi tai jajir ta kumbura wuyanshi ma haka, hannunshi adaure daurewan irin na karaya dinan, wani irin mummunan faduwa gabanta yayi karfin hali tayi tadaga kafarta ta karaso cikin dakin ta tsaya gefen Waleed, bakinta har rawa yake tace "Ha....Hajiya meya sami Waleed? Meya faru? Meyasame shi"? muryanta na breaking sosai tayi maganar hankalinta a mugun tashe, dagokai Ammi tayi tazuba mata jajayen idanunta sanan ta tashi daga kan gadon tace "biyoni" da sauri Mom ta tashi tana girgiza ma yayarta kai amman Ammi ta dauke kai kaman bata ganta ba tabude kofa tafita Mama biyeda ita, itama Mom tabisu wajen, tsayawa sukayi a reception premises din cikin fushi Ammi tamata pointing dakin da Waleed yake ciki tace "wlh mutuncin ki danake ganine yasa nakiraki dan kizo kiga abinda yafaru da idanun ki, kinga Waleed dina, kinga yanda yake akwance agadon asibiti, kinga yanda yadawo, dan iskan danki ne ya mishi haka, Arham ne yama Waleed dina haka, jibi yanda yama d'ana dukan dakoni dana tsugunna na haifeshi bantaba mai irinshi ba, kitayani tambayan Arham da ina labo yazo yatayani nakudar d'ana ne dazai kamamin shi ya daddaka haka"? mamaki ne ya mugun cika Mama kaman wacce ke koyan magana tadafa kirjinta tace "Arham! " tana kwalalo idanunta waje tsabagen mamaki, cikeda masifa Ammi tace "duk abunda Waleed yama Arham da abunda zai saka mishi kenan, Waleed ko agogo nasaimai bayi karba saina sayo biyu nashi dana Arham, komi shida Arham, amman yau Arham ne zai kamashi yama wanan shegen dukan toh wallahi bazan yarda ba, wlh, bazanji kunyarki na cuci kaina ba, wlh wlh bazan yarda ba yanda yama yaron nan shegen dukan nan sai shima anmai irin ta, mai rabani da Arham sai Allah don saina yagashi, saina sa anmishi x10 abunda yama Waleed wallahi wallahi bazan yarda ba" Mom dai batace komai ba kuma batayi yunkurin hana Ammi fadan ba saboda zata iya komawa kanta, ita kanta abin ya daure mata kai har lokacin yanda Arham yakama Waleed ya daka haka. Numfasawa Mama tayi ta goge hawayen daya zubo mata tace "Hajiya kima Arham kome kikaga dama, karki barshi kisa shima amishi fin haka, fin dukan dayama Waleed ma dan abinda yayi bai daceba nabaki goyon bayan nan dan inbama kisa amai hukunci ba ni wlh sainasa" wayan dake hannun Ammi tabude takira inspector general of police na tafada mishi komai sannan tace mishi atabbatar ankarya ma Arham hannu da kafa kafin dare da toture na police, tana katse wayan ta shiga turama inspector address din gidansu Arham.


ā¤ā¤ā¤
[11/1, 11:47 PM] Re@lšŸ–¤ K@usy šŸ”: šŸ’« _TWO DIFFERENT WORLD_ šŸ’«



šŸ’«šŸ’« _*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_šŸ’« šŸ’«





āœļø M SHAKUR





2ļøāƒ£6ļøāƒ£ & 2ļøāƒ£7ļøāƒ£




FREE PAGE
Komawa falo sukayi duk suka zauna Anty Hussai da Yakolo sukahau hira banda Anty Hassu datai shiru tana tunani ko kadan bata yarda da Ilham ba, but still batason tama Ilham tunanin datake yi, duka duka yaushe Ilham ta girma hartai wayon da da aurenta zata dingabin wasu mazan, ta tambayi kanta saikuma tai shiru, duka duka yaushe akai auren Ilham dake mugun son Waleed kaman zatai haukane zatabi wani namijin? Ajiyan zuciya ta sauke tana kokarin kawar da tunanin daga zuciyanta dan bamata fatan abinda take tunani shike faruwa.






Wuraren 4 na yamma ya shigo gidan marayun yay parking motarshi yana tattaro wasu uban takardu daya ijiyesu a kujeran gefen direba ya kwasa dayawa yarike sanan yabude motan yafito daidai Waleed yakaraso wajen dan daga masallaci yake, wani iri Arham yaji dayaga Waleed kaman zai maida takardun cikin motarshi saikuma yarike hannunshi, karasawa wurin shi Waleed yayi hannunshi zube cikin aljihu yace "kadawo blood" gyadamai kai Arham yayi yace "yes nadawo blood, Mama ta iya saka mutum aiki, iyaye sai ahankali" zaro hannu Waleed yayi daga aljihu yamika Arham din yana kallon uban papers din hannunshi yace "what are those blood mugani"









Da sauri Arham ya kalli papers din gabanshi nafaduwa Saikuma yakara linkesu yana lankwdhesu da kyau gudun karyaga mainene su yace "they're not mine, nawani dan anguwan mu" saikuma yabude mota da sauri ya zubasu ciki sanan yamaida kofar motar yarufe yajuyo ya kalli Waleed dahar lokacin kallonshi yake, sanan yace "muje daman akwai maganan danake so namaka" juyawa Waleed yayi yace "am going to the clinic now to check my patient nafito mayi maganan" ganin kaman ran Waleed din yabaci yasa yace "muje to naraka ka clinic din" yabi bayan Waleed din, clinic din suka shiga da basuda much patient that are on admission saidai out patient wayanda kawai zasuzo suyi complain kazakaza na damunsu adubasu abasu magani sutafi, dakin da Widad take direct Waleed yayi Arham biyeda shi suka ya shiga, tana kwance akan gadon an lullubeta da bargo fuskarta ne kawai awaje da gashinta da akai parking tana bacci, idanunta har wani nama nama sukayi tsabagen bacci, karasawa gaban gadon yayi Arham biyeda shi, Arham yace "for the past 3month now kullum yarinyar nan nazo dakin nan bacci take saikace wacce take a coma" stethoscope yadauka yana makalawa a kunne yace "she's not in a coma, babu ranan duniyan dabata tashi, yawanci sau daya take tashi, amata brush abata abinci suma duk tanaci tana gyangyadi tasha magungunan ta, I was the one that increase her dose, duk wanda yakeda damage a brain need absolute rest, yesterday nakara mata MRI da CT scan I was happy with the result, fluid din yaragu sosai wanda yarage baifi an atom size ba, yanzu shi nabashi 4days, dazaran kwanakin sun cika zan sake running test din inhar babu saina godema Allah, tagama da magungunan zan mata transfer zatabar hospital takoma hostel, dudda haka I will be monitoring her ina bata magungunan that help with the memory lost" yay maganan yana zare, stethoscope din daya daura kan kirjinta duk Arham na kallonshi, dan tabe baki yayi yace "tamayi kokari kusan watan ta 9 akan gadon asibiti, sai yanzu ma nake dana sani daban karanci medicine ba nima nadawo likita kaman kai nawani kama ina karanta engineering, kumako kasan inda na karanta medicine dafa nafika kwarewa" yay maganan ahankali hankalin shi nakan wayanshi dayake dannawa yana kokarin turawa Ilham message kartace baikara nemanta ba, dan juyowa Waleed yayi ya kallai jin maganan yamai wani iri aka, ganin wayama Arham din ke dannawa yasa yagyara mata bargon yace "let's go" yay gaba shikuma Arham yamaida wayan aljihunshi da sauri yabishi suka fita, office din Waleed suka shiga, Arham yaja kujera ya zauna Waleed ma yazauna yana gyara zaman takardun kan table dinshi sanan yace "yes ina jinka kace akwai maganan da kakeso kamin blood"





Ahankali Arham yasake jawo kujeranshi gaban table din sosai yasauke ijiyan zuciya ahankali sanan yace "I need a favour blood, kaima kasan you've been my ride, my backbone my everything, u are my only friend I come to you in every situation" yadanyi shiru sanan yace "I need money blood, I need money sosai" ahankali Waleed yace "for what?" ahankali yace "kaga na farko, Maman su yarinyar nan da Mama tace na aura, kanwar Mama gidansu ya rushe, ruwa yamusu gyara, sanan inaso nasaya ma mijinta shanu da gona su dinga sana'a, sanan inaso nakaisu Umara harda Mama and many other thing, please kabani 10m blood" yakarshe maganan ahankali shiru Waleed yayi yana kallonshi, arayuwanshi baida mutum daya keso kaman Arham, saisa kome zaimai baya taba sa ido koyaga mezaiyi da kudin kowani abu baruwan shi, in yabashi kudi yabashi ne so badamuwarshi bane abinda zaiyi da itaba, baitaba cire kudinshi yasai kaya ma shi kadaiba bazaima iyabane inhar shi zai cire kudi yasai sitira to nashi dana Arham zaisaya, duk wani abu dazaisa ajikinshi inhar Arham baidashi to iyayen shi ne ko uncle dinshi suka siyamai, yana bama Arham kudi sosai excluding kudin albashin shi, lokacin bikinshi yabashi dollars da Ammi tabashi baimasan yawansu ba, ko last 2weeks saida yamai kyautan 3M cikin kudaden sa gwamnati takawo ma gidan marayu tallafi dan he don't really needs government money kafin su kawo yay amfani da kudinshi yayi abinda ya kamata, abincin Mama da supplement dinta yana kanshi kowani wata saiya saya yakaimata yabata kudin kashewa amatsayinta na maman abokinshi, yabada kudin man motan ta dakudin man generator na gida, banda inverter dayasa aka saka agida saisa 247 duk lokacin dazaka gidan Mama nada wuta, Arham baya komi danta ko'ina ya tare mai wata dawainiyar shi to'ina yake kai kudin shi? Abin yadade yana damunshi bawai dan sa ido kowani abuba just amatsayin shi na abokinshi na gaskiya zaiso yasan inda yake kai kudaden shi karyazo yana wulakanta kudinshi koyana saka kudinshi awani abu na haram ne, yariga yasaimai dankareren gida a anguwan da gidanshi yake da Ilham keciki, incase inya tashi aure yasa matanshi ciki ballema yace gini yake da kudin ina Arham yake kai kudi, kowani bad abu yake da kudi? No hakkinshi ne amatsayin shi na abokinshi na gaskiya ya tambayeshi yaji. "X-man kayi shiru kobaza kabani bane?" Arham yatambaye shi, dan nisawa Waleed yayi yace "no bahaka bane, actually I've been wanting to ask you this question also, I think today is the right day, Arham" Waleed yakirashi anatse, zubamai idanu Arham yayi irin ina jinka dinan batare daya amsaba, ahankali Waleed yace "Arham banso kamin karya, tell me please mekake yi da kudi"? Dawani irin sauri har yana neman taran numfashin shi yace "kaman ya menake yi da kudi" dan jim Waleed yayi yana kallonshi saikuma yace "okay lemme do it like this kafahimce ni, blood duk wata dawainiya dazata sa ka kashe kudinka na dauke makashi yet kullum bakada kudi, me kakeyi da kudi"? Wani irin zabura Arham yayi yamike tsaye daga kan kujeran dayake kai yana kallon Waleed din yace "mekake nufi da duk wata dawainiyar dazata sa na kashe kudi ka daukemin ita yet kullum banida kudi, Waleed gori kakemin sabida kana siyama mahaifiyata yar buhun shinkafa duk wata kana kaimata"? Waleed was still seated akan kujeran shi ya girgiza kai yace "uhm'uhn that's not wat I meant Arham, calm down and sit let's talk please, banga abin zafin nanb......" wani irin buga table dinshi Arham yayi da hannu yay kara yace "don't fucking tell me to calm down, on what account zaka dinga tambayana menake da kudi sabida ka daukemin dawainiyar kaina kana saima mamana yar buhun shinkafa da wake, Waleed ni kakema gori sabida kaga Allah bai horemana kaman kuba eh? Ni kake ma gori Waleed, am talking to you kamin shiru are you stupid"? Arham yadakama Waleed tsawa dayasa Waleed yaji ranshi yabaci dan ba'amai tsawa koda yana yaro baima sababa, tashi kawai yayi dan baiso yabiye mai suyi fada yay wajen hanger dayake makala suit dinshi yaja yadauka zai saka, wani irin shan gabanshi Arham yayi da jajayen idanunshi ya kalli Waleed yanuna kanshi da hannu yace "ni kakema gori Waleed, sanan inamaka magana kamin banza ni kake ma gori"?

22 / 48