kwamdon tumatir da buhun albasa daga gona, haba ita bata gajiya, kace nace tadena daurama kanta dawainiya please kaji, niya kamata nabata ba itaba kaji" gyadamata kai yayi kanshi akasa maganan karshe ta mugun mai ciwo wanan kasancewan har ina wai ita yakamata tabata wato ga Mamanshi fatararriya matsiyaciya ko, sukuma masu kudi, hmmm wata rana dagake har danki saina saku kuka wlh, saina muku abinda kudinku bazai taba gyara abinba, tsayar da maganan zucin yayi daidai yar aikin Ammi takawo wani hadadden kula da masa da miya keciki tabashi, karba yayi yace "thank you Ammi" sanan yajuya, tashi Waleed zaiyi Ammi tace "kanacin abinci baka gama bane zakawani tashi" kaman zaiyi kuka yace "nifa Ammi nakoshi, kuma I want to see blood off" "to ai saikaje su mai blood" Ammi tai maganan da zuciyanta daya dariya Waleed yayi yawuce yabi bayan Arham dahar yajuya da sauri yay kofa itakuma Ilham tai kaman ba satan kallon Arham din dataga ko bye baimata ba, yarage dinning din daga ita sai Ammi.
Concentrating Ammi tayi tana cin abinci saikuma chan tadan dago daidai itama Ilham ta dago hada ido sukayi da Ammi, Ammi tai murmushi sanan ta mayarda hankalinta kan abinci cikin seriousness dinan nata da halinta na bawasa tace "Khadija kinyi kyau, you look so fresh Masha Allah, am expecting good news kwanan nan fa daga wurinki" kasa dagokai Ilham tayi tama kasakai abincin baki tana wasada spoon din ahannunta, Ammi ta cigaba. "nasan ku yaran zamani bakusan dazaran kunyi aure ayi aciki a haihu kunfison sai anci soyayya, bakuson ace daga shigowa kunyi tuntube dashi, wasunkuma ma har planning suke, please daughter banda planning take note, I need an heir, inason magaji, inason naji good news daga gareki kwanan nan kinji" gyadama Ammi kai Ilham tayi akunyace tace "in sha Allah Ammi zakiji kwanan nan" murmushi Ammi tayi cikeda gamsuwa tace "sai magana tabiyu, bazaki yi aikiba, am sorry about that I know bazaki so hakan ba, banson kina dauke da jikana a jikinki kije kinama wasu aiki, this magana is between me and you bazakiyi aikiba but every month zan dinga biyanki salary is that okay with you?" gyadama Ammi kai tayi ahankali tace eh, juyowa Ammi tayi ta fuskance ta da kyau tace "sai magana ta karshe ki kulamin da yarona da kyau, Alhamdulillah kinga Waleed yanzu kinyi zama dashi kinsan yanda yake, Waleed is a very sweet calm boy, baida hayaniya ko kadan kuma baidau duniya da zafiba, nasan abinda na haifa nasan, nasan waye shi, nasan Waleed zai kuladake da kyau dan haka kema ki kulada shi da kyau, kome yamiki ki kirani ki fadamin bawai kihau yima d'ana fadaba, ni kadai nakeda wanan ikon na dagama yarona murya da sunan fada duk duniyan nan, ba'a haifi wanda zai ma innocent yarona ihu aka ba koyaci mutuncin shi saidai in ban raye, inko daraina sai inda karfina yakare so ki kula kinji" gyadama Ammi kai tayi gabanta nafaduwa daman tun kafin ayi auren mahaifiyarta ta riga tafadi mata Ammi nada zafi gata kuma da zaki but inhar kanason kaji zakinta kaso danta, akan danta zata iya komi, muryan Ammi ne yadawo da ita daga dogon tunanin dataje kwalama yar aikinta kira tayi. "Huwaile, Huwaile" dagudu yar aikin tazo tarage tsawo agabanta tace "gani Hajiya yakuri banjiki da wuri ba ina baya ina aikin dakika sanine" tabe baki Ammi tayi tace "wuce kije fridge kidauko min magungunan dana bakiyau ki samin a fridge nace miki na matar d'ana ne" da sauri yarinyar ta tashi taje fridge, wasu goruka guda uku ta dauko a basket mai kyau takawo ta ijiye gaban Ammi, daukan gora daya tayi ta jijjiga tareda budewa tamikama Ilham tace "gashi kisha" karba tayi cikeda girmamawa ta kwankwada zata ijiye Ammi tace "shanye duka" kwalkwalewa tayi ta ijiye tana lashe baki dan maganin da dadi, Ammi tace "wanan maganin dakika gani yana wanke ciki tass da mahaifa, inma yarinya tai planning ne kan kartadauki ciki tass saiya wankosu su fito ta fitsari, sanan ya wanke mahaifa koda ya cushe zata wanke tsaf ta yanda once yay releasing zai tafi mahaifarki direct, inhar mace tasha maganin nan akayi batai ciki ba to tanada wata natural condition ne dake hanata haihuwan" faduwa gaban Ilham yahauyi wanan son yara da Ammi kedashi haka na lafiya ne, mika mata sauran gorunan Ammi tayi tace "wayan nan tsumi ne kishanye su" karba tayi tasake gyadamata kai daidai Waleed ya shigo tashi Ammi tayi tace "zonan yallabai" dariya yayi yabita stairs tahau yana biyeda ita abaya, Ammi tace "bakabani labarin excursion dinba, how was it" labari ya shiga bata sunayin sama Ilham tabisu da kallo har suka bace mata wanan wata irin matace, wayarta tadauka data ijiye agefenta tabude da sauri daidai sako na shigo mata, ganin Arham ne yasa tabude dagudu.
_"you are mine, ban yarda wani yatabaki ba, karki yarda ki kwanta da yaron nan, is a warning ā "_
Murmushi tayi tamai reply da.
_" to sarkin kishi, babu wanda zai taba maka ni yallabai, I miss you, sainaji inama bamu dawoba, please kazo da daddare nadan ganka"_
Maido mata da reply yayi da.
_"I don't wanna come, bazan zoba, cus I hate that old witch, she don't like me is obvious babu dai yanda zatai danine sabida tasan danta bazai iya rayuba bani ba, I will see you tommorow"_
Wani iri taji kaman tai kuka, hakan yasa tai reply dinshi da.
_"promise"?_
Dawo mata da reply shima yayi da
_"I promise Lawyer"_
Da sauri ta turamai da.
_"but tayaya bayan gobe kuna orphanage kuna aiki"?_
Sake aiko matada sakon yayi yace.
_"just trust your Arham, ki kawai tabbatar ya maidake gida dasafe kafin yatafi orphanage, you will see me, cus if I didn't have you I might die, I can't go a day without that yummy pus"_
Wani malalacin murmushi tayi tace.
_"I trust you my dirty nigga, gat to go bye_
Tai maza ta tura sakon tareda deleting messages din duka ganin Waleed na saukowa daga stairs daure da alwala zashi masallaci, karasowa yay dinning din ya tsaya daga dan nesada ita yace "har yanzu baki gamacin abincin ba?" murmushi tayi ta kalli plate din gabanta sanan ta kalli fuskarshi saitai shiru kawai ta tsaya tana kallonshi barinma ruwan daya jika pink lips dinshi, bazata iya karyaba tanason Waleed soma mahaukacin so, kodan baimata yanda takeso ne yasa takejin Arham dake yimata yanda takeso oho, sanan tana tausayin Arham sosai saisa take sonshi ko menene oho ita tama rasa, all she knows is takasa tsanan Waleed, and duk in zata kalleshi saitaji wutar sonshi nakara ruruwa aranta to kodai kyanshi da kudinshi ke dibanta ne? Or is it possible kaso MAZA BIYU KUMA ABOKANAN JUNA? Ta tambayi kanta. "Tunanin5 me kike"? Waleed yamata tambayan yana karasowa gabanta a dinning din ya rungume hannayenshi akirji. "wai ni?" ta tambayi kanta tana kallonshi, daga mata gira yayi alamun yes you, murmushi tasake mai tace "kawai tunanin gidan mu nike inaso naje zaka barni?" yana kallonta eyes to eyes ya girgixa mata kai, sanan yace "matar Waleed bata zuwa ganin gida sai bayan ta shekara da aure, I am a well cultured man you know" yasake daga mata gira, samun kanta tayi da kasacemai kala saima wata shegiyar kasala da sha'awan shi dataji ya diran mata all of a sudden, he was so close to her yana mata magana ciki ciki sanan yana wani kashe mata sexy idanun nan nashi yana daga mata gira, ganin ta shagala da kallonshi yasa yajuya kawai yafice daga dakin yace "tashi kije kiyi salla, ankira magrib".
Sai wuraren 9 bayan anyi isha'i yamayi magana da wasu naroka yan anguwanni haka dasukazo neman taimako ya sallame su sanan ya shigo cikin gidan, maida kofar falo yayi yarufe yana kallon Ammi data zauna kan kujera tana aiki da laptop dinta duba sales din da aka mata a campanonin ta take, is a normal thing kullum around that time zata saka fararen glasses sanan ta zauna tana aikin sai wajen 11 na dare sanan zata gama taje ta kwanta, zama kusada ita yayi ahankali yace "sannu da aiki Ammi" kanshi ta shafa tace "kadawo son" gyada mata kai yayi ya jingina da kujera yana zaro wayanshi daga aljihu yarike wayan yana kallo saikuma ya shiga daddanna wayan yanemo number Dr Kemi yay dialing, ringing daya kaman wayan na hannunta ne daman ta dauka.
"Hello Dr Warbai, good evening" kafin ma yay magana yaji karan kuka sosai a background din wayan, ahankali yace "who is crying?" "your patient" tabashi amsa da sauri, tashi yayi yazauna dukya damu, ahankali yace "what about medication dinta danace a dinga bata dakesata bacci" cikeda damuwa tace "Sir wlh na bata tun bayan ta farka da magrib dinan but taki bacci, daidai da ruwa takisha, inta ganmu ma ihu take, taki yarda damu kwata kwata jikinta ma yadau zafi, tun dazu ina kanta sai yanzu nafito daman nazo nakira kane saigashi kiranka ya shigo kaman kaji ajikinta tana kuka" shiru yayi yana rasa mezaiyi saikuma ya kalli Ammi dake aikinta hankali kwance gabanshi nafaduwa yasan yanzu yana fadimata orphanage zashi saita balbaleshi da bala'i, katse wayan yayi yamaida wayan aljihu ya ijiye yay shiru gabaki daya jin karan kukanta yasa yakasa natsuwa mikewa yayi zumbur kaman an dagashi yazuri key motar Ammi dake Centre table da sauri Ammi ta kallai tace "ina zaka?" "orphanage Ammi, emergency case gareni, I have to go" shiru Ammi tayi tana kallonshi kaman zaiyi kuka yace "please Ammi dazaran nagama zan dawo" yanda yayi yasa tace "saika dawo" da sauri yafita daga gidan, motar Ammi ya shiga yay horn gateman yabudemai gate yawuce yafita ya shiga titi yaba sharara gudu, wani super market yawuce akan hanya hakanan saiya sami kanshi dayin reverse back yadawo parking yayi agaban super market din ya shiga, yau kusan 3days kenan bata sakashi a ido ba, wata Teddy babba yasaya, saikuma yasai su snacks da chocolate da ice-cream yabiya kudi yafito ya shiga motar yaja, ko minti 15 baidauka ahanya yakai orphanage din, parking motarshi yayi agaban clinic din yafito lokacin 10 harda kusan minti 15 but yana iyajin ihunta daga wajen, daukan Teddy din yayi da sauri yama manta da sauran abubuwan saya sayo tsabagen yanda kukanta ke rudeshi ya shige cikin, ward din datake ciki yayi agaban dakin datake yaga Dr Kemi da nurses dukansu tsaye sunyi charko charko, babu wanda kukanta the bai dagawa hankali ba, Dr Kemi na ganinshi ta sauke ajiyan zuciya tace "thank God you are here, bari naje nahuta ba'a taba kawo mana patient data taba bamu wuyaba irin wanan yarinyar" wucewa suma nurses din sukayi suka tafi bayan sun gaidashi, ahankali yake daga kafanshi haryakai gaban dakin, kukanta dake tsuma zuciya nakara tashi yana kururuwa, daura hannunshi yayi kan door handle din kafin ya murda yatura kofan ahankali yana kallon dakin, tana zaune akasa kusada kofan ta tankwashe kafa kanta sauke tana rusa uban kuka dakowani gaba na jikinta ke amsawa, bama tadago kaiba balle tasan waye yashigo ba, maida kofan yayi yarufe ahankali, sanan yadago kafanshi yazo har gabanta, ijiye mata Teddy yayi akasa agabanta sanan ya zaga ta gefenta ya tsugunna ahankali yana kallon yanda tsabagen bala'in kuka kandaya kulle mata ta wargajeshi yama rufe mata fuska da baya, cikin wata irin karaman tattausan murya yace "Sabeeha" har kasan kwakwalwanta taji kiran sunanta dayayi dawani irin sauri ta dago kanta takai hannayenta ta gyara gashin gaban fuskarta ta hanyar waresu kyakkyawar fuskarta ya bayyana ta kallai suka hada ido, wani irin fashewa da kuka tayi saikuma tasa hannayenta biyu ta tureshi tana ihu da kuka. "ahhhhh ammmm" saikuma tajuya da sauri ganin Teddy daya ijiye mata awurin yasa tai grabbing nashi da sauri ta daga ta shiga kwadamai tana mugun kuka jikinta na rawa ranta ya bala'in baci, saida ta kwalamai Teddy iya son ranta sanan ta jefar dashi akasa ta tattaka tana kuka saikuma ta dauka ta mike tsaye tana tafiya tana dingishi tai wajen gadonta tahau ahankali ta kwanta ta rungume Teddy tana sauke ijiyan zuciya.
[11/1, 11:47 PM] Re@lš¤ K@usy š: š« _TWO DIFFERENT WORLD_ š«
š«š« _*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_š« š«
āļø M SHAKUR
2ļøā£3ļøā£
FREE PAGE
Yadade atsugunne yanda ta barshi, zai iya cewa tunda Allah ya halltoshi duniya da dai wayanshi aka bai taba ganin mutumin daya daga hannu da sunan zai dakeshi ba aduniyan nan ballema har ya dakan sai akan yarinyar nan, bude idanunshi da tuntuni suke alumshe yayi yadan juya ya kalleta, sai ajiyan zuciya take irin na wanda yay kuka dinan ta kankame Teddy tana jikinta har bari bari yake, ahankali ya furta zuciya! Mikewa tsaye yayi ahankali yafara tafiya batare daya waigo ya kalleta ba yay kofa, hannunshi yadaura zai bude kofan yaji tawani irin fasheda kuka da sauri yajuyo, ganin yayi ta tashi daga kan gadon tana kokarin saukowa daga gadon, saukowa tayi tana kuka ta taho har gabanshi tana dingishi, rungume hannayenshi yayi yanabin gashinta dake lilo da kallo yace "you just finshi beating me, why are you crying again? Ba bakison ganina ba?" yay maganan gabaki dayanta cikin harshen turenci, cigaba da kukan tayi batare data cemai kalaba, sosai yaje yanason yay training nata yabata tarbiya mai kyau, ahankali yace "you don't beat your elder koma mesuka miki, is wrong, now say sorry" dago jajayen kumburarrun rinannun idanunta tayi ta kallai kaman yanda shima ya tsare mata ido, ahankali cikin dishashiyar muryanta dabata fita sosai tace "so...rry" yanda tafadi sorry was so cute da saida yasashi murmushi, handky aljihunshi yaciro yazo har gabanta ya tsaya sanan ahankali yadaura left hand dinshi kanta sanan yakai right hand dinshi dake rike da hanky din kan fuskarta wani irin wawan ajiyan zuciya ta sauke da saida yasa ya kalli fuskarta kafin ahankali yashiga goge mata hawayen dayay chaba chaba a fuskarta, sanan ya share mata hancin daya baci da majina, sanan yawuce cikin dakin zuwa gaban gadonta, pink bathroom slippers din da aka bata na sawanta yadauko ya ijiye agabanta yace "put on the slippers" sakawa tayi da sauri tana kallonshi shikuma ya tsaya yana kallon cute yatsun kafarta fararen da zai iya cewa baitaba ganin yatsun kafan mace kai kyau hakaba kodan baya kallon yatsun ne oho, dago kanshi yayi ya kalleta yace "let's go" yay maganan yana bude kofa yafito yajuyo ya kalleta, da sauri itama tafito tana kara rungume Teddy dinta ta tsaya kusadashi, hannunshi yasa yajawo kofar yarufe sanan yafara tafiya ahankali sabida ita, kallonsu nurses din suka tsaya sunayi da mamaki yarinyar daketa uban kuka, tana ganinsu tadaga Teddy ta sama tai gaban counter dinsu da gudu zata rafka musu da sauri Waleed ya daka mata tsawa. "Saheeba" tsayawa chak tayi bata rafka musu ba tajuyo kaman zatai kuka ta kallai, daure fuska yayi tamau yace "come here" tahowa tayi ahankali sukuma nurses din na dariya kasa kasa, hannunta yakama yarike sanan yay wajen kofar fita daga clinic din da ita, security yabude musu kofan suka fito, tunda aka kawota bata taba fitowa ga wuta ko ina a premises din kaman ba dare ba, ga hadaddun flowers ga few cars dake pake a filin, tsalle tahau yi tana kara kankame Teddy ta kana ganinta kasan she's very very happy, tai wajen flowers tana tattabawa saikuma ta daura Teddy ta akan flower tana tsalle, murmushi yayi yawuce ta yace "lets go" daga Teddy ta tayi ta dauka tabishi da sauri tana dingishi har zuwa inda yay parking motarshi, bude mata gidan gaba yayi yace "seat" shiga tayi ta zauna ahankali sanan yazaga mazaunin direba tana binshi da kallo kaman zai gudu saida yabude motan ya shigo sanan ta sauke ajiyan zuciya ta shiga tattaba motan tana yan surutai kaman yanda yara keyi in sukaga kayan barna, wajen radio mota ta shiga tattabawa da sauri yace "stop" denawa tayi ta hade hannayen takai dukansu baki tana kallonshi da kwala kwalan idanunta, dan ajiyan zuciya yayi yahanata wanan takoma wanan, ahankali yamika hannunshi baya yadauko jakan desert da snacks din daya siyo mata ya daura kan jikinshi ice cream yaciro yabude yasaka spoon yamika mata yace "ice cream" tsayawa tayi tana kallon ice cream din dabai wani narkeba da kallo dan da kankaramshi aka bashi, kwanto da kanta tayi tana leka ice cream din kaman wata matsoraciya spoon din yazaro ya lakato ice cream din yakai bakinshi yasha ya lumshe ido yace "is sweet, ice cream" karban duka ice cream din tayi daga hannunshi zata sha saikuma ta dago takai hannunta ta fizge spoon dinta shiga shan ice cream din kaman zata hada da roban cikin 2min ta shanye tass tamikamai spoon da roban ice cream din, murmushi yayi yaciro muffin daga ledan yabata kaiwa baki tayi taci taci ye tasake mikamai hannu alamun yakara mata saida tacinye duka guda biyar din dayasa yo sanan yabata ruwan sanyi ba sosai ba tasha tai gyatsa da karfi dayasa yatabe fuska yana kallonta yace "yanyanyaa, don't do that again" gyadamai kai tayi hankalinta yakoma kan yan littatafai data gani kan saman motan, da sauri tamika hannu zata dauka kafin ta dauka ya dauke yace "stop is not mine na Ammi ne" ahankali tana kallon fuskarshi tace "Am....mi?" gyadamata kai yayi yace "yes Ammi Saheeba" saita shiru ta tsaya kallonshi, murya chan kasa yace "now listen kinsan me yasa nakawo kinsan nabaki kayan dadi"? Yay maganan da turenci dan turenci kadai ya lura tanaji inya mata hausa bata ganewa, turencin ma yawanci bata cikamai reply ba, badaita wani maganan kirki dan baitabajin tamai full sentence da turenci ba, ahankali yace "you see am a very busy person, I work in this orphanage, and I am a Dr, bakoda yaushe zaki dinga ganina ba, kinsan menene banso inhar kinayi zanyi fushi dake?" da sauri ta girgiza mai kai yace "banso kina kuka, kobaki ganni ba karki kara kuka do you know why? Because am going to make you a promise