Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HALIN GIRMA Complete Hausa Novel by Hafsat Rano

Author :  hafsat rano Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 38.7K words

ga wanshi ya bani izinin zuwa wajenta."

" Ina jinka."

" Toh nayi magana da Takawa akan idan har zuwa gidan su ya taso ba sai kowa yaje daga royal family ba, a samu wasu cikin mutanen Takawa din da ya aminta dasu suje neman auren."

" A wanne dalilin kenan? Ina ka taba jin anyi irin wannan shirmen Muhammad? Idan ma anyi hakan an fad'a maka ba zasuyi bincike akanka ba kafin su baka izinin ganin yarsu ba? Ai dole ne iyaye na kwarai su yi bincike sosai su san wa zasu bawa yarsu."

" Nafi son duk wannan yazo daga baya Ammi, dama dole su sani amma ba yanzu ba, marikiyar yarinyar ce matsala, idan har taji da wuri zata iya bata abun dan ta jima tana bata wa."

" Idan hakan ne matsala, toh ka bar komai a waje na, karka manta wanne gida kake magana Muhammad, wargi ma ance waje yake samu, bata isa tayi komai ba idan har taji kai din waye, gaba da gabanta fa, ka daina tunanin komai kayi addu'a, har naji inason yarinyar da dukkan zuciya ta, Allah ya sa ta zama abokiyar arzikin ka."

" Amin Ammi, in sha Allah ma ba zata sani ba har sai ranar, zanyi duk yadda zanyi bata sani din ba, yadda abin zai dake ta, kuma nayi alkawarin hukunta ta daidai da abinda tayi."

" Ya sunan diyar tawa?"

"Fatima sunan ta, Iman."

" Masha ALLAH, Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

" Amin."

" Inyeee, lallai babu kunya Babana? Hadda saurin amsawa ko?"

Dariya ya saka sosai,yayi saurin kashe wayar jin Ammin zata yi masa dan biki.
??

Rik'e wayar ya cigaba da yi a hannu yana juyata,maimakon ya kirata sai wata dabara ta fado masa, take yaji wani dadi ya kamashi ganin ya samu hanyar da zai hana Maman sanin komai har sai lokaci ya kure mata.
?? Kwanciya yayi ya ja blanket har saman kansa, sannan ya kirata yana jin ringing din na tafiya daidai bugun zuciyar sa.

***Da safe ya so ya makara bayan ya koma bacci da asubah, kiran Musaddik ya tuna masa abinda suka shirya, a gaggauce ya tashi ya shirya, ya kimtsa kansa cikin shigar Khakin sa, ya fito a sojan sa, kayan sun yi masifar karbar sa, yanayi da tsarin zubin halittar sa sunyi daidai da kayan, shi kansa yana jin sa ontop a duk lokacin da ya samu kansa cikin irin shigar kayan.
?? A hannu ya rik'e wular ya fito suna ganin shi suka taso da sauri, duk suka k'ame su biyun kafin daya ya bud'e masa motar daya kuma ya zagaya mazaunin driver ya tada motar suka fice daga gidan.
?? A chan permanent site din sukayi zasu hadu da Musaddik, yana isa yaga motar sa a waje, be shiga ba ya kirashi a waya ya fito ya same shi. Tare suka fito da Ja'afar, Musaddik ya zura kansa cikin motar yana kallon sa.

"Ya riga yazo, yana reception yana jiran MD ya hada shi da oga at the top"

"Ga kuma Oga kwata-kwata anan ba." Ya kalli Ja'afar suka kwashe da dariya

" Me ka shirya masa Oga?

" Ni na isa Captain? Ai ban isa ba Wallahi. Duk abinda ka shirya min dai, ni ai bani da say."

" Ya akayi be gane ka Musaddik bane wai?"

" Ba zai gane ba ai, I'm not in charge of staff din wajen, wannan aikin admin human resources ne, plus kaga chan sabon branch ne nan kuma main site."

" Haka ne kuma, yanzu zan jira anan."

" Yes Sir!" Ya Sara masa suka kwashe da dariya

Khalil na zaune cikin zulumi yana fatan haduwar da zasuyi da shugaban wajen ya zama alkhairi, yana so ya dawo da aikinsa as soon as possible yadda zaifi jin dadin kwace Iman da karfin ikon sa, da yan kudaden sa a aljihu. Fitowar MD ya saka shi tashi da sauri

" Yawwa Ibrahim, yazo yana parking lot, sai kaje ka same shi, best of luck."

" Nagode sir, Allah ya kara girma."

" Amin."

Saurin fita yayi, ya tarar da motoci biyu a wajen, duk da bakin glass, tunanin wacce a ciki ya bi numbers din motar da kallo. _Royalty_ aka rubuta a jikin plate din babbar da tafi kyau da sheki, wajen ya nufa kirjin sa na dukan tara tara, kafin ya karasa yaga murfin bayan motar ya bud'e, anyi masa fitala. Kofar ya nufa ya zura jikin sa bakin sa dauke da sallama, sai da ya zauna ya daidaita a ciki, kofar ta rufe ruf ya shaki kamshin motar me dadin gaske, ya juyo sukayi ido hudu da wanda ko a mafarki be taba hasashe ko tunanin gani ba.

"Hello Ibrahim."

Moh yace yana sakar masa wani irin murmushi me dauke da ma'anoni masu yawan gaske

"Me... Me ban gane ba?" Ya hau k'inkina ya ma kasa daidaita maganar sa.

"Sunana Muhammad Ahmad Santuraki, Also known as Captain Moh, shugaban wajen nan gaba daya, nice to meet you."

" Nooo! Impossible! This most be a joke, Kai din? Kai din? Kai... Kai Kai din?"

" Calm down and take a deep breath, karka hargitsa kanka dan akwai sauran surprises, na farko karka taba wulakanta mutum baka san shi din waye ba."

" Innalillah wa inna ilaihi rajiun."

Ya shiga maimaitawa ba kakkautawa, gaban motar ya kalla yaga sojoji ne su biyu majiya karfin gaske, kowannen su fuskar sa murtuke take babu alamun dariya, jiran umarni kawai suke kamar mayunwatan zakuna, hadiye wani mugun yawo yayi yana jin sanda Muhammad din ya bada umarnin tada motar ,be iya bud'e baki ya hanashi ba, yana jin sanda motar ta soma tafiya a hankali har ta daidaita akan babban titi, kafin me tuka motar ya kara taka motar da gudun gaske

"Shikenan na gama yawo." Ya furta a zuciyar sa be san maganar ta fito fili ba.

Murmushi Muhammad yayi ya taune gefen lips dinsa yana ayyana kalar rashin m din da zai masa.
[1/7, 9:40 AM] Sakaba: Halin Girma
? ? 9

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*?

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb



***
Yana jin sanda motar ta tsaya, ya juyo da sauri ya kalle shi, hankalin sa na kan wayar sa yana dannawa, fuskar sa a hade tsaf babu alamun wasa ko kadan, tsoro ne ya sake shigar Khalil din sosai, yaji kamar yayi ta kurma ihu yana neman taimako, amma kuma ya san babu wanda zai taimaka masa musamman idan aka zo aka ga wanda yake tare dasu.
? Ji yayi an murda handle din bangaren sa, yayi saurin matsowa sai gashi a tsakiyar motar, daf da Moh, wani banzan kallo ya watsa masa da ya sakashi saurin komawa inda yake zaune.

"Come ou!" Wani murdadden soja yace matsa bayan kofar ta gama budewa, idanu ya soma rabawa tsakanin Moh da sojan fuskar sa ta nuna matukar tashin hankalin da ya shiga

"I said come out!" Ya daka masa tsawa da ta saka shi saurin fitowa

"Dan Allah Oga kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da rashin hankali, duk abinda na farfada ba wai har zuciya ta bane wallahi."

Ya hau magiya yana kallon Moh da yayi kamar baya wajen, damtsen hannun sa sojan ya kama ya shiga jan sa har zuwa wata kofa in da ya hangi sojoji sun fi su ashirin suna tsalle tsalle a wajen.

"Oga dan Allah ka bawa oganku hakuri Dan Allah!"

"Kasan waye oga kuwa?"

Da sauri ya girgiza kansa

"Ban sani ba wallahi, rashin sani ya jawo nayi masa abinda nayi amsa amma dan Allah na tuba yayi hakuri."

Dariya sojan ya saka sosai

" Baka da hankali amma, ka zo har nan wajen kayi tunanin zamu kyale ka, ka tafi free? Nah sai mun dan sassamaka yadda gobe ba zaka kara ba. "

" Dan Allah nace fa? Ka tayani bawa ogan hakuri. "

" Naka wasa ne. "

Yayi gaba yana rik'e dashi, yanayin rikon da yayi masa da yanayin jikin Khalil din zai baka dariya sosai, dama bashi da wani jiki sosai gashi kuma a hannun manyan maza, wani daki ya kaishi sannan ya sake shi yana masa dariyar mugunta

"Zaka kwashi kashin ka hannu yau, wallahi Oga zai iya sawa a batar da kai a k'asar nan, kasan waye kuwa? Tab."

Jawo masa kofar yayi ya rufe ta har da key yana kwasar dariya.
? Chan karshen dakin yaje ya tsugunna yana jin dana sanin barin zancen da yayi, dama a maida baya da ya goge duk abun da yace ma Muhammad din cikin rashin sani. Ji yayi cikin sa na kara alamar ya lalace, ya tabbatar bala'in tsoro da firgicin da ya shiga ne ya saka cikin nasa lalacewa. Mikewa yayi da sauri ya hau zagaye a dakin yana maimaita

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun."

Ji yayi ana murda key din dakin, ya tsaya yana kallon kofar cikin tsoro. Captain Moh ne ya shigo sojoji biyu na biye dashi a bayan sa, daya rik'e da kujera yazo ya ajiye masa ya zauna yana wa Khalil murmush

"Alhaji Khalil barka da warhaka."

"Dan Allah dan Allah kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da yarinta wallahi amma ba zan sake ba."

"Haba Khalil, so soon haka? Ka sani ko sojan gona ne ni, kasan fa talaka da samun wuri."

"Wallahi ni dai ba zan sake ba, kayi min rai, mahaifiyta da ni ta dogara, dan Allah."

"Calm down magana zamuyi, ka nutsu ka saurare ni, warning ne me hade da dokoki, ina fatan zaka bud'e kunnuwan ka kaji ni sosai."

"Ina ji wallahi."

"Babu kai babu abinda ya zama mallaki na, Ina nufin Fatima, ko a hanya ka hadu karka taba nuna ka santa balle har magana ta hada ku, a da nayi niyyar barka ka gwada sa'ar ka akanta, amma kuma a yanzu na gama yanke wa, baka kai na nemi abu tare da kai ba, dan haka ko son ta zai kashe ka sai dai ka hakura... "

" Na biyu, a yau ba sai gobe ba zaka wuce in da ka fito, ba tare da ka bud'e bakin ka kace wa kowa komai ba, ina nufin, bakin ka ya zama kanin kafar ka, kar naji zancen a wajen kowa ciki har da ita yayarta ka da bata tsoron Allah. "

" Last but not the list ka koma bakin aikin ka, ka rik'e mutuncin ka sannan bakai ba wulakanta kowa. "

" Duk abinda ka fad'a wallahi zanyi, nayi alkawari, ni dai kar ka raba ni da mahaifiyata wallahi bata da kowa sai ni. "

" I'm done with you, gashi nan take him back, ku tabbatar ya bar Kano kafin karfe shida na yamma. "

Juyawa yayi cikin wani irin taku ya fice daga wajen, yana fita sukayi kansa

" Ai wallahi ba zaka shigo nan a banza ka fita bamu ci ladan ka ba. "

Wani soja yace yana kai masa rankwashi.

" Tashi kayi frog jump. " Dayan ya daka masa tsawa yana zaro belt dinsa. Da sauri ya hau yi yana hada zufa su kuma suna tuntsura dariya, sai da suka gajiyar dashi sosai sannan suka fito dashi suka sashi a mota suka maidashi har kofar gidan suka ajiye sannan suka tafi.

***Abba na zaune yaji text message ya shigo wayar sa, tunanin sa ma ko alert ne ya bud'e sai yaga sako daga bakuwar number da be sani ba, bud'e message din yayi ya soma karantawa

_" Dr. barka da warhaka, ya aiki? Allah ya taimaka. Dama wata magana nake son yi akan fatima, ina rokon alfarmar daka saka ido sosai akan abinda yake faruwa a cikin gidan, in sha Allah zaka gano wani abu da ya dade yana faruwa ba tare da sanin ka ba. Sai anjima a huta lafiya. "_
?? maimaita karanta sakon ya dinga yi yana kokarin daidaita tunanin sa waje guda, waye ko wace wannan? Me sakon yake nufi? Me ya faru da Fatima din? Duk wadannan tambayoyin ne suka shiga yi masa yawo aka, be san me yasa ba, kawai sai yaji hankalin sa ya kasa kwanciya da abinda ya karanta. Tashi yayi ya fito zuwa falon gidan, ya k'wala kiran Iman din. Zeenat ce ta fito

" Ina Ummi? "

" Ina ga tana wajen Gaji. "

" Je ki kira min ita. "

Fita tayi shi kuma ya cigaba da tsaiwa awajen har suka shigo a tare.

" Ki same ni a daki na. " Yace yana juyawa tabi bayanshi, dariyar mugunta Zeenat tayi a tunanin ta wani laifin Iman din tayi dan sosai yanayin Abban ya nuna bacin rai.

A gefen gadon sa ya zauna, ta samu chan gefe daga kasa ta rakube tana tunanin dalilin kiran.

" Kina jina Uwata? Kina da wata matsala wacce ban sani ba? "

Girgiza kanta tayi

" A ah Abba babu. "

" Kalle ni nan, ni ne mahaifin ki, baki da wanda yafi ni bayan mahaifiyar ki, ki fad'a min gaskiya idan akwai wani abu da yake damunki."

Zuciyar ta ce tayi rauni, taji kuka na taho mata, ta k'asa rike shi kawai ta fashe da kuka. Dafe kansa Abban yayi, ya shiga tunanin me yake faruwa? Wanne irin abu ne haka da har shi ya kasa ganewa?

"Fatima..." Ya kira ainihin sunan ta a karo na farko a rayuwar ta

"Na'am." Ta amsa cikin muryar kuka

"Kowanne bawa da irin yadda rayuwa take zuwar masa, kiyi hakuri zanyi bincike, sannan akwai shiri da nake yi na kaiki wajen mahaifiyar ki da zarar maganar bikin ku ta tabbata, nayi mata alkawarin kai mata ke da zarar lokacin auren ki yayi, mahaifiyar ki na son ki fiye da yadda take son kanta, ki rik'e wannan."

" Tashi kije kinji, ki daina kukan haka."

Tashi tayi bayan tace

" Nagode Abba." Ta fice ya bita da kallo yana jin kamar be kyauta mata ba.

Dakin su ta wuce ta tarar da Zeenat na waya har da shewa, juyawa tayi zuwa store ta zauna a gefen katifar ta, tayi kuka sosai har sai da taji babu abinda yayi saura a zuciyar ta. Tsawon lokaci ta sauka a ciki har sai da taji maganar Mama tana fad'a a waya anan ta gane ta dawo dan dazu bata gidan. Tashi tayi ta fice ta kofar baya bayan ta gyara fuskar ta a sink din kitchen.

***Zama Mama tayi tana sababi akan tafiyar Khalil din babu sanarwa, sai dai a k'asan zuciyar ta taji dadin hakan domin a kalla hankalin sa zai dauke daga kan Iman din har a gama magana da shi dayan da yazo. Abba ne ya shigo ya sameta tana zaune , ya zauna a gefenta sai tasha jinin jikin ta musamman da ta gama sanin halin sa tsaf.

"Me yasa kika ce min Ibrahim ba da gaske yake akan maganar Ummi ba, sannan shi kuma yaje ya samu Yaya da maganar."

Yadda ta zabura yaso bawa Abban mamaki.

"Khalil din ne yaje wajen Yaya? Yaushe akayi haka? Me yayan yace masa?"

"Duk ba wannan na tambaye ki ba, baki bani amsa ta ba."

"Toh toh ai gani nayi shi Khalil ba yanzu zai yi aure ba, su kuma yaran nan yanzu ne muke so mu aurar dasu, bana so Zeenat ta tafi da bar Iman tunda kaga tare suke komai, shiyasa nace gwara wanda ya shirya."

"Haka ne kuma." Yace yana mata wani irin kallo da ya sakata tunani sosai

"Toh hakan yayi ai, Ina fatan dai zeenatu ta sallami yaron nan Bashir ko? Dan ina nan akan bakana ba zan bashi ba."

"Dan Allah Dr ka bar wannan maganar, tunda tana son shi kayi hakuri kawai ayi tunda an wuce zamanin da za'a yi wa yara auren dole."

Girgiza mata kai yayi yana dakatar da ita

"Wannan maganar taki shirme ce, musulunci mu ya bawa damar zaba wa yayanmu mazaje na gari, dan haka ban yarda da Bashir ba, idan akwai wani ta kawo shi."

Ya tashi ya fice ransa na baci da yadda maganar Bashir din taki karewa, sam Hajara bata shirya gane abunda yake hango musu ba, eh hango musu tunda duk in da aka je aka jawo ita uwa sai tafi cutuwa da abinda zai samu yarta.

***Text message biyu ya tura a lokaci daya, address din sa da Abba yace ya tura masa ta message sai kuma message din da yayi wa Abban Iman din, wanda yake ganin shine kadai hanyar da zai bi wajen hana Maman sanin duk wani abu akan Iman din, ya tabbata daga lokacin Abban zai saka ido sosai, ba kuma za'a dau lokaci ba zai gano komai, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar ya nemi alfarmar barin komai ya zama sirri a tsakanin su iyaye maza, domin dama su iyaye maza baa sansu da ratatin zance ba, ba kasafai ma suke zama suyi ta magana anyhow ba, ya tabbata idan har hakan ta yiwu toh zai samu abinda yake so, zai kuma tabbatar da Fatiman sa ta samu gatan da bata taba tunani ko hasashen samun sa ba.

***Tunani Abba ya fad'a ganin address din da Muhammad ya turo masa a matsayin in da yake,Emir Palace Kano, Emir Palace Adamawa-Yola, me hakan ke nufi? Kiran Abban su Fatiman yayi yazo ya same shi a part din sa, ya nuna masa message din sannan ya kira sauran yan uwan su Abba Musa suka hau tattaunawa akan abinda ya kamata su yi. Dama chan Abba Musan yana siyasa sosai, sai sukayi shawara akan shi ne zai wuce gaba wajen binciken waye Muhammad din a cikin kwana uku kachal. Haka kuwa akayi, washegari ya same su da maganar da ta yi matukar basu mamaki. A yadda suka sani idan wani daga cikin irin wannan yaga yarinya yana so, kawai aikawa ake iyayenta suzo ayi magana a fadar sarkin, a matsayin shi sarki dama uban kowa ne, sai suga ga banbanci inda Muhammad din yazo kai tsaye ba tare da ya nuna shi din waye ba, ba kuma tare da ya nuna karfin iko na mulki ba, hanyar da ta dace da kowa yake bi wajen neman aure shima ita yabi.
? A cikin su babu wanda be yi amanna da maganar ba, musamman binciken da Abba Musan yayi da irin yabon da Muhammad din ya samu daga wajen mutane da dama musamman mazauna masarautar.
? ? Shiru Abba yayi bayan kowa ya gama tofa albarkacin bakin sa, aka bashi dama a matsayin sa na mahaifin Iman din,

"Bakwa ganin idan iyayen yaron nan suka san in da yazo neman aure zasu kyale shi, duba da mu din ba wasu bane

7 / 13