Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HALIN GIRMA Complete Hausa Novel by Hafsat Rano

Author :  hafsat rano Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 38.7K words

huta ko?"

" Tell her Mamma, wallahi kamar na bugeta yau din nan ta bani haushi."

" Kaifa ya sunan ka?" Ta tambaye shi

" Amaan." Amani tayi charaf ta rigashi fad'a sannan ta dora

"Nice hassana, shine husaini, na girme shi so nice babba."
??
Murmushi Iman tayi, so adorable yaran,

"Oya ku wuce kowa ya cire uniform dinsa kuzo muyi dinner, nasan Iman ta gama gajiya tana so ta huta"

Mamma tace tana mikewa

" Zayd, Ya Mubarak dinner na table."

" Ni sai nace gida gaskiya, I'm full."

Ya Mubarak yace yana gyara zama sosai. Kama hannun Iman Mamma tayi, suka wuce dining din tare da Zayd yana mata tambayoyi. Mommy na jinsu bata saka baki ba, dama kuma ita haka take da kara sosai, komai nasu Itace akai amma bata taba nuna musu iyaka akan nata, shiyasa suma duk wani abu da ya shafe ta toh sune a gaba gaba, sai ta koma gefe ta zama yar kallo. Bata da hayaniya kamar dai Iman koman ta a nutse takeyi musamman kuma abun da ya hadu da arziki sannan ga ilimi both boko da islamiyya. Kujera taja gefen Iman din da suka bar mata ta zauna daidai lokacin Amaan da Amaani suka dawo kowa ya sauya kayan sa zuwa na zaman gida. Amaani na kokarin fara surutun ta suka hada ido da Mommy, kallon da tayi mata kadai yasa taja bakin ta tayi shiru har suka gama babu wanda yayi magana.
?? Falon suka dawo, a lokacin Ya Mubarak da Zayd suka yi musu sallama akan zasu dawo gobe kowa da family dinsa, har bakin mota Mommy ta rakasu ta dawo sai kawai ta wuce dakin ta, ta bar Mamma da yaran suna hira, ta lura da yadda Iman din ke jin kunya da rashin sabo amma kuma tasan wace Mamma ba zata taba barin ta ba har sai ta tabbata ta sake dasu, balle uwa uba iyayen magana su Amaani su kadai ma sun isheta.
?? Kwanciya Mommy tayi farin cikin zuwan yarta na ratsa ta, wayar ta ta dauka ta kira number Abba, lokacin ya gama cin abinci kenan yana kokarin duba wasu papers dinsa a computer yaga kiran nata, tsaywa yayi da abinda yake yi ya daga.

"Nagode sosai IB, naga Iman fiye da yadda nayi tunanin ganin ta, hankali na ya kwanta dan na tabbatar da tarbiyyar ta, kayi ma maman tasu godiya dan Allah. "

" 'yaya amana ce a garemu da dole mu kula dasu da tarbiyyar su, domin dole ne Allah ya tambaye mu a ranar gobe kiyama, banyi komai ba face abinda ya zama wajibi na."

Ya fad'a yana jin chan kasa zuciyar sa da zata samu labarin abinda ya faru a zaman Iman din da Maman daku tabbas za'a iya samun matsala, abu daya ya hanata yin wani katabus akan maganar Iman din, tabbatar mata da yayi akan bata da matsalar komai, kuma tana hannu na gari.
? ? Sallama sukayi ta runtse idon ta, hasashen irin shirye shiryen bikin da zatayi kawai take, ba zata bari ta koma ba har sai tayi mata nata kalar gatan da zata tabbatar da ita din yar gata ce.
?? Turo kofar akayi, ta daga kai ta kalli Iman din cikin rakiyar Mamma.

" Sai ki gudo ki bar mu? Gamu toh mun biyo ki."

" Na zata wajen Hajiya kuka yi ai."

" Munje chan din ma."

" Ok." Tace tana mikewa zaune.

" Bari na duba yaran chan, ina ga daga haka zan kwanta, sai da safe Iman."

Murmushi Iman tayi ta amsa sannan mummy tace

"Sai da safe Yaya."

Fita tayi ta ja musu kofa cike da farin cikin kwanan da ya da uwar zasuyi yau.

"Dawo kusa dani."

Dawowa tayi ta zauna daf da Mummy din, ta jawota ta dora kanta a saman cinyar ta, cikin tattausan lafazi tace

"Kin girma sosai Iman, nayi mamakin yadda kika kara chanjawa akan last da Dr. Ya tura min hoton ki, amma kuma naga baki da walwala sosai, ko rashin sabo ne? Ko kuma hakan halitta ne?"

Murmushi tayi me sauti, nutsuwa ta saukar mata, taji da gaske she's safe fiye da yadda ta taba ji a rayuwa ta, a hankali ta furta

"Babu komai Mummy."

"Shikenan, ki kwanta idan kika huta duk maganar da zamuyi sai muyi kinji?"

Ta shafa kanta tana murmushin. Daga kan ta tayi ta ajiye a saman gadon ta fita daga dakin. Wajen kayan ta, ta nufa ta ciro wayar ta, tasan ya mata magana a WhatsApp bata samu sukunin dubawa ba. Misscalls ta gani ta whatspp call sai messages dinsa da ya turo mata. Sakon ta fara dubawa ta,tabi kowanne tayi reply ta bar daya da yake tambayar ta size din undies dinta kunya na kamata. Godiyar kudin da ya bata tayi masa hade da addu'a tana turawa sai gashi yazo online, maimakon ya amsa sai taga yana kiranta, kasa dagawa tayi kunyar tambayar da yayi mata na dawo mata

_" Baby menene size din B da P?"_

Haka ya rubuto mata fa, kin dagawa tayi har ta katse ya sake kira ta kara bari ta katse,

_" Please dan Allah ki daga, kwana nawa banji muryarki ba? Sam na manta zan iya kiran ki ta whatspp call sai daxu, please ki taimaka ki daga inaso naji muryar ki wallahi."_

_" Ni dai muyi chatting."_

_" Ni dai ki daga, zan sake kira. "_

Kafin tayi reply sai ga kiran sa, ta daga da k'yar tanayin nesa da wayar. Ajiyar zuciya ya sauke da karfi

" Kin iya rigima wallahi, haka kawai sai anyi punishing dina ko? "

" Um um. "

"Toh naji, ya hanya? Ya me ya faru?"

Cikin zumudi tace

" Ina cikin farin ciki yau, komai ya tafi yadda ya kamata, kowa so na yake kamar zai goya ni. "

"Mum fa? "

" She's just like me, kamar ni take har I don't care attitude dinta, amma deep down she's super happy, na gani a idon ta. "

Dariya ya saka

" Alhamdulillah, nayi miki murna sosai sosai, Alhamdulillah. "

" Nagode sosai. "

" Yau kwana zakuyi nasan da Mum kuna magana. "

" Anya? Kila ko sai an kwana biyu. "

" Bari ki gani dai. "

" Uhum tohm shikenan. "

" Baki min replying dayan chat din ba, abinda na tambaye ki. "

Dauke wuta tayi gaba daya kamar bata ji ba, ya sake maimaitawa yana rik'e dariyar sa, ya gano kunya taji tunda taki daga wayar sa, bata san halin sa ba lallai, rage murya yayi sosai yace

" Dan Allah ki fad'a min Aunty zata yi min fad'a gobe idan nace ban tambaye ki ba, dan Allah. " Shiru tayi masa

" Please ki fad'a min, ko da yake ma zan iya chanka ai, bari muga... zasu kai size..."

" Innalillahi. " Tace tana zare wayar gaba daya ta kashe ta. Tuntsurewa yayi da dariya kamar zai fado daga gado, yayi saurin komawa chat din ya hau rubuta mata

"Sorry matar Muhammad, daga wasa sai ki yanke min waya? Toh ai ban gama jin muryar ki ba wallahi."

Tick daya ya gani alamar ta ma kashe datan gaba daya, gwada kiran ta yayi aikuwa yaji switch off.

Tsaki taja ta wurgar da wayar , ta rasa me yasa me maxa sam basu da ta ido, zata dade kuwa bata yi waya dashi ba. Samun kanta tayi da yin murmushi sai kuma ta hade fuska ta sake jan tsaki. Ya ma bata haushi gaba daya.

Har ta gama shiryawa ta jona wayar a charge amma bata kunna ba har lokacin Mum din bata shigo ba, gefen gadon ta kwanta cikin lallausan zanin gadon da yake kamshi sak irin kamshin da mummy din take, tana rufe idon ta, ta shigo rik'e da cup a hannun ta.

" Iman, kinyi bacci?"

" A ah." Tace tana mikewa zaune

" Yawwa ungo karbi kisha, fresh milk ce nayi miki warming dinta."

Karba tayi, tayi godiya ta kafa kai ta shanye tas, ta tashi da cup din rik'e a hannun ta

" Ajiye shi anan zan kira azo a fita dashi."

A saman fridge din jikin kofar ta ajiye ta dawo ta zauna tana so abinda tasha ya dan yi settling a cikin ta.

"Zo ki tayani duba wannan kayan."

Tayi maganar tana bud'e profile dinsu a cikin system din, gefenta Iman ta zauna suka hau duba wasu jewelries, duk wanda Iman din tace yayi kyau sai tayi starring dinsu, sai da suka gama tsaf sannan suka dawo kan wanda akayi starring din suka sake fidda guda biyar masu kyau sosai, biyu gold biyu azurfa sai daya fashion ne daga wani babban company, a take mummy tayi payment din da komai sannan tace Iman din taje ta kwanta zata karasa wani aiki.??
? ? Tana kwanciya bacci ya dauke?ta? dama ta gama kurewa sosai tana lura da Mummy din bata so ta matsa daga kusa da ita ne. Cikin bacci tayi juyi ta jita a bayan ta, daga nan bata sake farkawa ba sai da aka kira sallah.

***Gaba yayo ya bar su a chan su karasa siyayyar abinda zasu siya dan yaga abin nasu bana kare bane, a Kano ya dira domin su karasa abinda zasu karasa da Bashir saboda yadda lokacin yazo sosai. A gidan sa ya same shi, suka jira Musaddik ya karaso suka fita zuwa wata unguwa da tafi kama da a kirata da unguwar talakawa kai tsaye, tunda suka shigo layin Moh ya tabbatar da zai samu yadda yake so, lallai Musaddik mugu ne na gaske, idan ba haka ba ya rasa unguwar da zai samo ya siya gida sai irin wannan unguwar. A daidai wani kofar gida karamin gaske suka tsaya, suka fito a tare wanda zasu gani yana tsaye yana jiran su, yana ganin su ya karaso bakin sa cike da murna ya gaishe su, sannan ya bud'e musu gidan yace su shigo.
?? Siminti ne gaba daya tsakar gidan sabo yana ta kamshi, bashi da girma tsakar gidan sosai dan be fi yaci tabarma days da rabi ba, a gefe yar karamar rijiya ce saboda rashin ruwan unguwar.
?? Dakunan guda biyu da suka kasance falle-falle ya bud'e musu suka shiga nan ma ko ina an masa fenti yana ta kamshi, babu abinda ba'a saka ba hatta karamin gado da kujeru an saka,da yar karamar tv babu batun fridge ko cooker gas balle azo maganar su AC da sauran kayan more rayuwa, kitchen din babu komai dama sunyi da nufin daga gida sai a kawo mata kayan kitchen suyi amfani dashi. Kitchen din karamin gaske ne dan mutum biyu ba zasu iya aiki a ciki ba saboda kankantar sa, balle a samu sukunin cika shi da kaya.
?? Fitowa sukayi ya rufe gidan yana sake washe baki

"Ranka ya dade gidan yayi ko?"

"Yayi sosai yadda nake so, sai ka sanar musu ba sai an kawo kayan gida ba ,iya kitchen ya isa shima karsu matsawa kansu duk abinda babu zaka saka musu."

"An gama ranka ya dade, sai maganar lefe."

"Ana gobe daurin aure za'a kai, an gama hada komai ina tunani."

" Nagode Allah ya kara arziki."

Be amsa ba, yayi gaba ya fad'a motar yana kallon tsarin gidan, murmushi ne ya kwace masa, ya girgiza kansa yana ayyana yadda zuciyar Mama zata buga ko kuma ta kusan bugawa,yayi alkawarin shayar da ita mamaki irin wanda bata taba tunani ko hasashe ba.

? Kai tsaye wajen gym suka wuce, ya kwana biyu be motsa jikin sa ba, yana bukatar hakan saboda tafiyar da sukayi be samu lokaci ba. Dariyar shakiyanci Musaddik ya dinga yi masa, ya tsaya daga abinda yake yana hararar sa

"wai dariyar menene haka? Uhum?"

" Naga yadda ka dage kake ta faman daga karafu nan nan ne wallahi, kar dai ka illata musu yarinya wallahi, kasan dai kai din tsohon tuzuru ne da yaki auruwa. "

Robar ruwan da ya gama sha ya jefe shi dashi, ya goce ta fadi kasa yana sake tuntsurewa

" Ka kiyaye ni wallahi. "

" Anki din, daga fadar gaskiya?"

" Zan kamaka ne, naga kafarka a gida na wallahi. "

" Gidanmu dai. "

Towel ya ja ya goge gumin fuskar sa, ya biye wa Musaddik zai dauke hankalin sa ne ga abinda yake shirin yi. Wayar sa ya dauka akan dan table din wajen yayi dialing number ta, sai da ta kusan katsewa sannan ta daga.


"Huh!" Ya furzar da iska yana jan numfashin

"Ranki ya dade an gama jamin ajin ne?"

"Ina wuni?" Ta kautar da maganar ta hanyar gaishe shi

"Lafiya lou, ya gida ya kowa da kowa?"

"Alhamdulillah."

"Masha ALLAH, yaushe Abba yace zaki dawo?"

"Be fad'a ba, amma naji Mummy tace ba zan dawo ba sai ranar."

"Ranar? Yaushe kenan?"

" Ka cika tsokana wallahi, nima ban sani ba."

"Ke kuma kin cika kunya ba, sai kici sai ranar auren mu kawai."

" Allah zan kashe wayar." Ta fad'a tana turo baki, dariya yayi yace da sauri

" Allah ya baki hakuri Matata."

Shiru tayi tana wasa da album din hotunan da Mamma ta bata bayan ta mata bayanin kowa da yake jiki.

"In sha Allah ana gobe za'a kai lefe, kinsan sha'anin rayuwar, Allah yasa be makara ba."

" Be makara ba, Allah ya saka musu albarka."

"Amin Matata, nagode sosai da bani dama da kikayi, in sha Allah ba zaki yi Dana sani ba."

"Kullum godiya? Ni me nayi?"

"Ai wai kinga dai yanayin yadda abubuwan suke."

"Babu komai Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

"Amin Amin amarya ta."

Yar karamar dariya tayi, shima ya tayata kafin suyi sallama. Mamma ce ta shigo dakin rik'e da jaka babba, sai me aikin gidan dake biye da ita da wasu kayan suma da yawa, ajiye su sukayi a gefe me aikin ta fita kafin ta sake dawowa ciki dauke da tray da aka doro chicken pepper soup da wani cup shima cike da abu kamar kunu, sai wani da akayi ma hadin fruits aka saka madara. Dora shi tayi a saman drawer ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? fita ta barsu.
Da hannu Mamma tayi mata alamar ta taso, ta taso ta zauna a k'asa in da Mamma din ta nuna mata, tray din ta sakko mata dashi tace maza ta cinye naman tas, idan ta gama akwai bakuwar da zata shigo wajenta, Itace me jakar chan. Tun zuwan ta gidan take faman shan abubuwa, a dan lokacin tayi masifar chanjawa, tayi kara fari da kiba jikinta ya sake murjewa sosai. Ita kanta tana jin da gaske ta kai mace, tana jin zata iya karawa da ko ma wace amma a dah, bata da wannan confidence din.
Bata kyuwar cin duk abinda aka bata dan da bata samu wanda zai dubeta ba balle har ya bata abinda yasan zai amfane ta. Shiyasa ta bada himma take yin duk abinda za'a sata.

***A bangaren gidan su Iman kuwa, bayan dawowar Abba sai da suka sake wani rikicin da Mama, wanda ya saka kowa ji har aka dinga ganin baiken Maman, amma kishi ya rufe mata ido matar Abba Musa na zugata tayi masa tijara son ranta, be kula ta ba don a yanzu baya sakata cikin jerin masu hankali, yana mata uzurin kishi ne ya sakata yin wasu abubuwan. Bayan kamar kwana biyu da dawowar sa ta same shi har daki ta bashi hakuri abinda ya bashi mamaki sosai, hakura yayi ya sakko amma ba wai don ya hakura da maganar Iman ba, yana nan sai ya yi mata hukunci daida abinda ta aikatawa yar sa.
Shirye shirye ya kankama sosai, mama babu zama kullum tana hanyar kasuwa tun da ta samu labarin cewa Bashir yace iya kitchen kawai zasuyi, hakan yayi mata dadi shine ta maida hankalinta sosai wajen kawata kitchen din dan ta tabbata gidan ba karamin gida bane, dole ne su fita kunya ta hanyar hada mata kitchen din yayi sosai.
Duk abinda ta tambaya Abba bata yake dan baya son wata doguwar magana, hankalin sa gaba daya yana kan maganar auren Iman, da yadda daurin auren zai kasance domin yasan za'a yi taro ne irin wanda ba'a taba yi ba, manyan mutane zasu halarta da yan siyasa da manyan sarakunan k'asar nan da ma na ketare. Duk abin nan Mama bata san komai akai ba, bata taba tambayar shi game da Iman din ba ko yadda nata tsarin yake, shiyasa kawai shima ya rufe ta ruf ya barta da abinda take yi.
A yadda tsarin bikin yake, alhamis za'a yi kamu, juma'a a daura aure sai asabar dinner kamar yadda Zeenat din suka zauna suka tsara ita da Bashir bayan ya sanarwa Moh da tsarin ya kuma bashi go ahead.
Tsarin bikin da su kuma chan masarauta suke shirya wa biki ne gagarumi za'a yi a Kano da Adamawa, kowanne kuma kwanaki za'a dauka anayi tun daga asabar din washegarin bikin, na Kano za'a fara kafin a koma adamawa in da za'a kai amarya.
Kamar yadda yake a tsari, ranar alhamis za'a karbi lefe, lefen Zeenat da Iman, wanda Mama tayi gayya, gayya irin ta ban mamaki, tana Kuma sanarwa mutane suzo suga lfen Zeenat dan ta tabbatar za'a ga kayan da baa taba gani ba.
Yan uwa da abokkan arzikin Mama su suka cika gidan, aka shirya kaya na mamaki, aka gyara gidan. Wata sister Mama ce tazo ta sameta tana zaune cikin kawayenta ana shewa, ta jata gefe hankali a tashe tace

"Yaya, wani labari naji fa, dangin mijinki na hirar basu san Ina wajen ba, naji suna cewa Iman tayi goshi ta samo jinin sarauta, ana ma tunanin dan sarki ne duk da Basu tabbatar ba ana boye zancen ne amma kamar hakan ne."

Wata irin dariya Maman ta saka, har da hawaye

" Kinji ki Fatima da wani zance, su fa basu san kan zancen ba, maganar Zeenat ake ba Iman ba, na ji wannan zancen tun bayan zu ba ai, kawai na kyale mutane ne yadda abun zai kada su, ba dai anjima kadan zasu iso ba? Zamu gani ai."

" Allah yaya? Kin Kuma tabbatar da hakan ne?"

" Zaki gani ai."

Tayi gaba tana murmushin mugunta, ba karamar kunya tasan za'a sha ba a lefen Iman din ba.


Hmmm






***Assalamu alaikum sisters fatan alkhairi ga kowa da kowa. In Sha Allah hutun mu zai kama asabar da lahadi, domin kowa ya samu damar aiwatar da wani abu me muhimmanci a rayuwar sa, sannan mu kula da gidajen mu da iyalan mu dukka, mu bawa yaranmu da mazajenmu lokacin da suke bukata daga garemu. In Sha Allah Monday to Friday za'a samu posting in sha

12 / 13