Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

HALIN GIRMA Complete Hausa Novel by Hafsat Rano

Author :  hafsat rano Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 13

15K to 18K   out of 38.7K words

sa hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d'aya d'aya.
? Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad'a masa yadda yake abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san ma yana yi ba ma.
?? Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin sa.

***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban, a kan idon sa ya dawo ya tashi da sauri ya tare shi ya bud'e masa kofar mota.

"Sannu da zuwa Abba."

"Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan."

" Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?"

" Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?"

" Alhamdulillah." Yace yana tuna abinda ya faru dashi.

" Allah ya taimaka ya bada sa'a."

" Amin Abba." Yace yana bin sa rik'e da jakar sa a baya.

" Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji."

Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da Babba nan da nan ya gane akwai wani abu.

" Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?"

" Eh Abba." Yace yana sosa kansa

" Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?"

" Toh Abba Nagode." Girgiza kai Abban yayi ya wuce bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi zaman sa anan yana jiran kiran Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi

"Yawwa wai kazo in ji Abba."

Rik'e hannun sa yayi suka koma yana jin wani iri a ransa, bakin sa dauke da addu'a ya shiga falon ya tarar Abban ya chanja kaya yana zaune da alama abinci ya gama ci. A chan gefe ya zauna yana jin kunya.

"Yawwa ina jin ka Ibrahim, ya akayi?"

Shiru yayi yana tsara yadda ya kamata ya ce, sai da ya dau sakanni yana hado maganar kafin yace

"Dama Abba akan maganar Fatima ne."

"Uhum ina jinka. Ya akayi?"

"Dama... Dama so nake dama a bani dama kamar yadda tsarin gidan nan yake."

Murmushi Abba yayi cikin jin dadi yace

"Masha ALLAH naji dadin wannan abu matuka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi kaji? Allah yayi muku albarka."

" Amin Abba." Yace a ciki-ciki farin ciki na kamashi,

" Kaje ku daidaita idan Allah yayi mu haka muke so, an riga an zama daya ai in sha Allah babu wata matsala."

" Nagode Sosai Abba, Allah ya kara girma."

" Amin." Yace yana chanja tasha a tv, shiru Khalil din yayi kafin ya mike

" A huta lafiya Abba."

" Yawwa Ibrahim."

Yana fita ya daka tsalle a wajen yace

"Yes!!"

Da sauri ya bar wajen yana jin kamar ya same ta ya gama ne, zai nuna wa fakirin saurayin ta cewa dan gida yafi bare.

***Sabon yadi ne me saukin kudi sosai, dinkin ma irin dan 1500 din nan ne, a rayuwar sa be taba hasashen saka ire-iren kayan da yake sakawa a yanzu ba, wani kallo Musaddik yake masa yana jin kamar ya kamashi yayi ta bugu.

"Yanzu Moh irin kayan da zaka saka kenan zaka ganin sirikin ka?"

"Wait and see." Yace yana kawo wata leda a kusa dashi, ya wurga masa yana cigaba da kallon kansa a mudubi

"Ka chanja mu tafi idan yaso muyi sallar magriba a hanya sai mu karasa."

"Na saka me?" Musaddik yace da sauri yana bud'e ledar.

"Wait what! Kana nufin ni zan saka wannan kayan."

"Mu nawa ne a dakin nan?"

"You must be kidding me, haba haba an fad'a ma kowa ma irin ka ne."

"Allah su zaka saka mu tafi, kayi sauri karka batan lokaci I'm dying to see my love."

"Aiko sai dai ka tafi kai kadai wannan karyar ba dani ba."

"Da wa toh? Wa nake dashi bayan kai? Kasan da ace ban samu kanta ba dole kaima ka tattaro ka dawo sabon shagon nan dana zauna mu zauna tare. Allah dai ya taimake ka wallahi."

" Ai wallahi babu yarinyar da ta isa nayi mata irin wannan son, the whole you, Captain Muhammad Ahmad Santuraki, dan ga sarki jikin sarki sannan kuma babban soja, ko da yake fa dama ance ku sojoji baku iya soyayya ba, musamman idan allurar ku ta motsa."

Daina abinda yake yayi ya matso kusa dashi

" Idan bansa an saka min kai frog jump ba, kace ba suna na Muhammad ba."

Dariya maganar ta bawa Musaddik,

" Ni zaka saka frog jump?"

" Sosai, ka cigaba da batan lokaci kaga."

Tashi Musaddik yayi ya sake daga kayan, kafin ya fara sawa yana cigaba da mita.

" Kanka akeji wallahi." Moh yace yana cire agogon hannun sa.

" Ka cire watch dinka please, anything da zai sa ta zama suspicious, I don't care idan kowa na gidan su yasan ni waye, amma ita? Da marikiyarta will be the last da zasu sani, surprise ne me kyau nake son basu dukka, sai dai kowanne da yadda surprise din zai zo masa."

" Wicked soul." Musaddik yace yana jefar ta watch dinsa akan mirrow

" What ever!" Yace yana yin gaba yabi bayan sa yana jin dadin kayan jikin sa, babu nauyi shawai shawai amma kuma ba zai yarda Moh din yasan ya ji dadin kayan ba.

A daidai shagon aka daajiye su, yace su je chan in da suka saba jiran sa su jirashi zai kirasu. Duk da basu so ba amma haka suka tafi suka barsu, Musaddik ya dinga jan tsaki suna tafiya a k'asa har suka isa kofar gidan. Wayar sa ya ciro ya kira ta, tayi ta ringing bata daga ba,

" Bata daga ba."

" Da ka kirata tun kafin muzo ai."

" Wannan ba matsala bace, bari kaga."

Ya kwankwasa gate din kafin ya dan tura shi suka shiga, dai-dai lokacin Khalil ya taho zai fita sukayi kichibis, wani kallo ya bisu dashi irin na sama da k'asan nan, kafin ya tuntsure da dariya sosai, hakan yayi bala'in bata ran Musaddik da dama chan baya daukar nonsense.

" Malam lafiya zaka kalle mu kayi dariya?"

" Lafiyar kenan, sai dai kun makara, dan gida ya shiga ya fita ya gama tabbatar da komai akansa, sai abi wani sarkin dan an riga an gama magana kuma su din ba kananan mutane bane da zasu sauya maganar su."

" Kana nufin?" Musaddik yace a zafafe

" Ina nufin kamar yadda na fada mishi ne a baya, Iman matata ce an riga an gama magana rana kawai ake jira a saka mana."

Wani kallo Moh yayi masa da ya saka Khalil shan jinin jikin sa, amma sai ya dake ya cigaba da gaggayawa musu magana. Muhammad be ce komai ba har ya gama, ya juya ya fice ya barsu a tsaye kamar mutum mutumi.

" I have no option than to show him my real identify, idan yaso duk abinda ya biyo baya yayi kuka da kansa ba da kowa ba, karfe nawa ne appointment dinsa?"

" Da safe ne, goma kamar."

" Owk Allah ya kaimu."

" Amin." Musaddik ya amsa ransa na sake baci akan abinda Khalil din yayi musu


HALIN GIRMA

Hafsat Rano

WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR =?%?=?%?=?%?=?%?sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ?WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL=?I?
*_HALIN GIRMA=?I?
*_TAKUN SA?A=?I?
*_SO DA ZUCIYA=?I?
*_?ABI'AR ZUCIYA=?I?
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ?AI ?AI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2=?I? 3=?I? 4=?I? 5=?I?
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*>?????????? #team zafafa biyar .

___________

*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*

*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*

*_za'a fara posting in sha Allah 1st January da yardar Allah_*

*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*

*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

SAIKU TURA SHAIDAR BIYA[1/5, 10:07 PM] Sakaba: *HALIN GIRMA*

? ? ? ? ? ? 8
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*?

***

Sake kiranta yayi a karo na biyu, ta daga tana goge ruwan da yake hannun ta, tana ciki tana wankewa Gaji toilet shi yasa bataji kiran farko ba, sai da ta fito wanda yayi daidai da sake kiran.

"Assalamu alaikum." Tayi sallama cikin muryar da ta saka Moh sallama duk bacin ran Khalil da ya kwasa yanzu.

"Wa alaikisalam, kina lafiya?"

"Lafiya lou wallahi, ya aiki?"

"Alhamdulillah, ina waje nazo ganin Abba."

"Owk tam gani nan."

Tace sannan ta ajiye wayar, ta fito tana tunanin yadda zata sanar wa Abban, a harabar gidan ta hangi motar sa, alamun ya dawo kenan, karasawa tayi wajen su tun kan ta isa Moh yake sake admiring kyawun ta, koman ta very simple hatta da tafiyar ta kamar ba zata taka k'asa ba, a matukar nutse take komai hakan yake sake dulmiyashi a kogin soyayyar ta.
?? Taba shi Musaddik yayi, ya dan yi firgigit sannan ya saki murmushi

"Allah zaka bada maza, kamar ba soja ba?" Yayi whispering maganar yadda Moh din ne kawai zaiji, banza yayi masa ya rigata karasowa wajen suka hadu a hanya. Kamshin turaren sa me dadi ya rigashi karasawa

"Sannu da zuwa." Tace tana shakar kamshin da ta kasa tantance shi

"Yawwa Dear, kina lafiya?"

"Alhamdulillah, lafiya lou."

"Masha ALLAH, gani nazo neman izini wajen Abban mu, ina fatan ban makara ba."

Girgiza masa kai tayi

" Masha ALLAH, yanzu ya za'a yi, shige mana gaba zakiyi muje ko?"

Da sauri ta kalle shi, idanun ta suka haska cikin nasa sai a lokacin taga ya rage kasumbar fuskar sa sosai kamar ya aske, fuskar sa ta fito sosai idanun sa da suka fi kama da a lumshe suke sun fito sosai, saurin dauke kanta tayi tana jin wani irin faduwar gaba

" Tunda ba zaka yi introducing dina ba, bari nayi da kaina." Musaddik da ya karaso wajen ya harare shi yana murmushi

" Sannu malama Fatima, sunana Musaddik kuma ni ogan sa ne a komai, ina fatan zaki karbi aboki na hannu bibbiyu dan da gaske yake ba da wasa ba."

" Sannu da zuwa,? Ina wuni?" Ta gaishe shi tana sauke kanta kasa har yanzu bata daina jin faduwar gaban ba

" Lafiya lou, ya komai da komai?"

" Alhamdulillah." Tace

" Bari na duba Marwan sai yazo ya yi wa Abban magana."

" Owk."

Ta juya zuwa part din su tana addu'ar kar su hadu da khalil, a falo ta tarar da su dukka Zeenat na danna wayarta, Maama na zaune Marwan yayi filo da kafarta yana kallon Disney World, shigowar ta ya saka suka maido hankalin su kanta

" Sannu da gida Mama."

Kin amsawa tayi, ta gimtse fuskar ta ta muskuta tana cigaba da kallon TV.

" Mama dama Muhammad ne yazo wajen Abban."

Da sauri Zeenat ta mike, ta hau kyalkyala dariya kamar wata sabuwar tababbiya, kawai sai Maman ma ta hau tayata, suka sakata a gaba da dariya abinda ya bata mata rai har taji kuka na neman xuwar mata

" Su Malam ne anzo za'a Abba kenan, ya kyauta miki ai ya taimaka da yazo, dan Khalil yafi karfin ki, shi din dai shine daidai da me bakin hali irin naki, me kike so nayi yanzu."

Daidaita muryar ta tayi, tace

"Dama so nake Marwan yayi musu iso wajen ..." Da sauri ta katse numfashin ta

"Tashi maza maza Marwan, je kace wa Abban gidan su Aliyu yana da baki, yi masa kar ya gaji da jira yace ya fasa."

Sai ta sake tuntsurewa da dariya Zeenat na tayata. Hawayen da take ta rikewa ne suka shiga sakkowa a fuskar ta,

"Kadan kenan kika gani in dai junan mutum bakin ciki toh wallahi shine a ciki." Zeenat tace tana jan tsaki. Juyawa tayi zata fita Maman ta tsaida ta

"Zo ki wuce ki wanke kanukan da aka bata."

Bata ce komai ba, tayi hanyar kitchen din zuciyar ta na kunci sosai. Wanke wanken take tana kuka sosai, irin wand a ta jima batayi ba, tana da masifar dauriya akan duk abinda za'a yi mata, amma kuma a wannan bangaren ta rasa me yasa ta kasa jurewa, wulakanci bashi da dadi kuma yanaa da ciwo musamman a tasaka gaba ana dariyar shakiyan ci da wulakanci.
?? Adadin lokacin da ta saba dauka tana wanke wanken sai data ninka shi saboda damuwar da take ciki. Ta baya ta fice ta koma bangaren Gaji tana jin kamar ta tattara komai ta bar musu gidan. Sau daya a cikin ranaku masu yawa yau ta tuna mahaifiyar ta, shiyasa bahaushe yace wanda ya rasa uwa yayi kuka.

***Da kallo Abba ya bisu har suka zauna suna masu nuna jin nauyi da kunyar sa. Bayan sun gaisa yace

"Gashi kuma ban shaida ku ba."

"Dama Fatima ce ta sanar mishi da Abban yace yazo ya nemi izini a wajenka, toh shine dama dalilin zuwan namu." Musaddik yayi maganar yana addu'ar Allah yasa be kwafsa ba.

"Toh toh..." Abban yace yana tunanin yadda al'amarin yake, musamman maganar Khalil da ya riga ya karbe ta

"Ita Ummin ce tace kuzo ko?" Yayi tambayar yana kallon su

" Ummi?" Suka Hada baki

" Auw Fatima toh, sunan Uwata ne ni ummi nake kiran ta."

"Masha ALLAH, Eh Itace ta turo mu."

"Toh shikenan, ina zuwa."

Tashi yayi ya shiga?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ciki, ya kira wayan Abban su Fatiman dan yasan be kai ga dawowa gidan ba

"Yaya barka da warhaka."

"Barka dai, ya aiki?"

"Alhamdulillah mun gode Allah."

"Allah ya bada sa'a, kana ji, dama akan maganar Ummi ne, yaron nan Ibrahim yazo da maganar sa jiya har ma na bashi izinin daidaitawa da ita ganin shi din na gida ne, yau kuma kwatsam sai ga wani yazo shi kuma wai Ummin ce ta turo shi."

" Ibrahim Kuma?

"Eh shifa."

"Amma da kaina na tuntubi Hajara da maganar sa, amma ta nuna min sam ba da gaske yake ba, hakan ya saka na ce Ummin ta sanar wa wannan din yazo ya ganka."

"Ibrahim kam yazo jiya ya same ni, ga wannan kuma shima."

"Allah ya kyauta."

"Zamu duba muyi bincike, idan yaso sai a bashi dama shima, wanda suka daidaita shikenan, bamu san me Allah ya boye ba, kar muyi gagagwa."

"Shikenan Yaya, duk yadda akayi yayi."

"Madallah."

Fitowa yayi ya tarar dasu a zaune, ya zauna yana fuskantar su

"Kace sunan ka?"

"Muhammad."

"Toh Muhammad daga ina?"

"Adamawa-Yola, amma mahaifiya ta yar Kano ce, nima kuma kaso me yawa na rayuwa ta nayi shi ne a Kanon."

"Toh toh Masha ALLAH, Anyi karatu Muhammad?"

"Eh Abba, nayi karatu."

" Aiki fa?"

" Soja ne ni."

" Ah Masha ALLAH, soja ga wuta ga yaki, soja marmari daga nesa. Hakan yayi kyau a cigaba da samar mana da tsaro a k'asar mu, Allah ya yaye mana abubuwan da suke damun mu suka hanamu zaman lafiya a k'asar, Allah kuma ya cigaba da dafa muku."

" Amin." Suka amsa cikin jin dadin yadda Abban ya sake dasu

" Shikenan Muhammad, ka bani number wayar ka da address din ka, zan neme ka in sha Allah."

Hannu Musaddik yasa a aljihun sa zai ciro wallet dinsa ya dauko complimentary card din Moh din yayi sauri fara karantowa Abba number, yace kuma zai masa text message na address din in sha Allah. Godiya sukayi masa suka fito yana jin tsoro na shigar sa, tsoron kar Abban yayi rejecting dinsa, tsoron yadda zai yi komai ya tafi yadda yake so.
? Kiranta ya sake yi ta fito bayan ta wanke fuskar ta sosai dan kar ya gane, duk da haka sai da ya gane kuwa,ya kafe ta da ido yana jin babu dadi.

"Me ya samu idon ki?" Ya tambaye ta dan ba zai iya hakuri ba,

"Ba komai."

"Ban yarda ba, kalli idon ki, Dan Allah ki fad'a min me ya faru?"

"Abu ne ya fad'a mina idon dazu, amma ya fita ma."

"Ban yarda ba, ki fad'a min waya bata miki rai? Waye ya saka ki zubar da hawayenki masu tsada?"

Ji tayi kukan na sake taso mata, dan dama idan kana cikin halin kuka aka matsa maka da tambaya ko ana so ka maida zance sai kaji sabon kuka ya taho maka,

"Ba komai da gaske ba komai."

"Dan Allah ki fad'a min menene?"

"Mamana na tuna." Ta fad'a masa saboda kawai ya kyale ta da tambayar

"Kiyi hakuri, akwai abubuwa da yawa da nake son sani, I ll call you idan na koma, ki daina kuka kinji? Komai zai wuce in sha Allah."

"In Sha Allah." Tace tana daidaita kanta.

"Kinyi alkawari kin daina kukan ko?"

"Nayi."

"Nagode, zan kiraki."

"Shkenan ka gaida gida.". Juyawa tayi ta koma ciki shi kuma ya fita ya tarar da Musaddik ya cika yayi fam kamar zai fashe.

"Muje ko?"

"Allah iyakata wajen bishiyar chan, ka kirasu suzo su dauke mu wahalar tayi yawa ai."

"Naji muji toh."

Ya ciro wayar sa ya kirasu cikin kankanin lokaci suka karaso, har suka isa babu wata magana tsakani Musaddik ya sauka su kuma suka wuce.
? A gaggauce ya gama komai ya shirya cikin kayan sa masu kauri, ya zauna yana jawo wayar sa, kafin ya kirata ya samu kiran DG, yayi saurin dagawa yana karawa a kunne. Gaisuwa sukayi ya bukaci ganin sa a Abuja idan an shiga working days, da toh ya amsa masa sukayi sallama ya juya akalar kiran zuwa number Ammin sa.

"Ammi na barka da dare."

Yace sanda ta daga wayar

"Barka dai yarona, kana lafiya?"

"Lafiya lou Ammi, ya gida da kowa da kowa."

"Kowa lafiya, ya aikin naka?"

"Alhamdulillah Ammi, babu dadi gashi ina missing dinki sosai."

"Ban yarda da wannan zancen naka ba, idan da gaske ne ai kasan in da nake."

" Ina na zuwa ai, ranar ma wani aikin ne ya taso urgent shiyasa na tafi."

" Ku kenan aiki, Allah ya taimaka ya bada sa'a."

" Amin Ammi, naje naga Takawa ai, har munyi magana ma akan maganar da Bubu yayi min."

" Eh naji kuwa suna waya jiya, sai dai bamu zauna munyi maganar ba, me yace maka?"

" Akan yarinyar ne dama Ammi, mahaifin ta yace nazo na

6 / 13