KIDA A RUWA-1 By Bilyn Abdull

Author :  Bilyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 35

12K to 15K   out of 104.8K words

haka ya tuntu?esa. Babu ko musu Malam Shehu ya amsa da zumu?insa. Abun ya burge sarki a lokacin, domin kuwa da yawan talakawa babu abinda sukafi ?yama kamar batun bokon a wannan lokaci. Saboda kowa na tsoron a ?ata masa al'adar iyalinsa da addininsa. Cike da zumu?i Malam Shehu ya nufi gida, ya tara yaransa da matansa biyu ya gaya musu ?udirinsa da albishir ?in da Sarki ya masa. Ya kuma tabbatar musu zai kai yaransa manya duka uku a sakasu boko. Wato ?a?an Inna kenan uwargida. Amma sai su yaran suka saka masa kuka dan basu da sha'awar hakan. Hakama mahaifiyarsu Inna ta nuna bata so, dan kuka ta saka masa ita bata so akai mata ?a?a su koyi kafirci, lallashin duniya da bayanin gamsuwa Malam Shehu yama Inna amma ta?i saurarensa bare ta fahimceshi. Har takai ransa ya ?aci ma ya fita ya bar musu gidan.
Ê Ê Ê Ê Abdul-rasheed yana cikin yaran tsakkiya, dan a wajen mahaifinsu shine na uku, a ?akinsu kuwa shine na fari da Iya ta haifa. Yana da ?anne uku, mata biyu a tsakkiya sai autansu.Ê ?acin ran da Malam Shehu ya nuna ya dami Iya, duk da kuwa bai ambaci Abdul-rasheed a cikin wanda zai saka makaranta ba, tasan kuma saboda yana ganin shekarunsa basu kai bane. Dan a lokacin shekarar Abdul-rasheed 5 ne kawai. Haka ta yini tana sa?e-sa?e, sai dai batace da kowa komai ba har washe gari Malam Shehu ya dawo ?akinta. (Ranar kwananta kenan).
Ê Ê ÊÊ Bata tada zancen ba ko a ranar sai dare, bayan ta bashi abinci yaci ya gode ALLAH ta kwashe akushin daga gabansa sannan ta dawo ta zauna gefensa cike da ladabi. Da yake lokacin ?ari ne kowa ya shige ?akinsa, baka jin motsin kowa sam. Cikin nutsuwa da girmamawa tace, ÒMalam niko in zaka bani dama ina da shawaraÓ.
Ê Ê Ê Kallonta yayi da dukkan hankalinsa, kafin ya amsa mata da, ÒIna jinki Halimatu, wace shawara ce? Kuma akan minene?Ó.
Ê Ê Ê Ê Iya ta ?ara du?ar da kai irin na girmamawa. ÒMalam akan maganar jiyane na batun makaranta. Naga ranka ya ?aci daga kai har Yaya. Dan ALLAH kayi ha?uri ka fahimceta, kasan batun bokon nan yana bama kowa tsoro, ba kuma kowa ke fahimta ba kai tsaye. Amma tunda kana so, kuma kaji ka gamsu da saka ?a?anka, mizai hana kafin Yaya ta sakko itama ta fahimta ka ?auki shi wannan yaron (haka take kiran Abdul-rasheed saboda karar kasancewarsa ?an fari) ka saka kawai. Daga baya itama nasan idan ta fahimta zata bari a saka su Bilyaminu ?inÓ.
Ê ÊÊ Shiru Malam Shehu yay cike da nazarin maganar Iya. Kafin ya nisa tare da sakin murmushi irin nasu na manya. ÒNagode sosai Halimatu, ALLAH yayi miki albarka. Tabbas naji da?i matu?a akan wannan shawara taki. Duk da da farko ina duba ?an?antar Abdul-rasheed ne shiyyasa ban sakashi a lissafi ba, dama sai gaba nake son kaishi shi bayan su sun fara. To amma maganarki sai ta min da?i, kuma ya bani mafita dan dama a cikin tunanin yanda zan fuskanci mai martaba nake akan hakan. Kinga yanzu dai kawai na kai Abdul-rasheed a sakashi, su kuma tunda basa so bazan matsa musu ba, su cigaba da karatunsu na mahammadiya da noma. ALLAH ya sanya musu albarka gaba ?ayansuÓ.
Ê Ê ÊÊ ÒAmin malam. Idan hakan kayi ma dai-dai ne. Amma zuwa nan gaba ?in dai suma a sake tuntu?arsu ko zasu canja shawara bayan sunga shi wannan yaron ?in ya faraÓ.
Ê Ê Bai musa mata ba akan hakan. Washe gari cike da farin ciki ya kama hannun Abdul-rasheed suka nufi gidan sarki. Wannan shine mafarin fara karatun bokon Abdul-rasheed. A lokacin yana da shekara 5 a duniya, dan an haifesa a 1947 ne. A shekara ta 1953 aka saka shi a makarantar Bauchi Native Authority Primary School (wacce daga baya ta zama Kobi Primary School). Kuma Alhamdullahi sai ya kasance shima yana son karatun kuma yana maida hankali. Malama Shehu yaji matu?ar farin cikin ganin Abdul-rasheed yana da himma akan karatun, dan haka ya ?ara tsayawa a kansa sosai. Ba'a boko Abdul-rasheed ya tsaya kawai ba, har ilimin addinin ma yana ?o?ari akai dan suna zuwa malarantar allo kamar sauran yan uwansa, sa?anin ?an uwan nasa da sunfi maida hankali dai akan ?an abubuwansu na yara na yau da kullum, sai kuma makarantar allo da suma suna zuwa kamar shi.
Ê Ê ÊÊ Makarantar tana kusa da ?ofar gidan sarki, cikin unguwar da ke cike da yara masu sanya riga doguwa da rawani ?arami, wasu kuma ke tafe da allo. Malamai suna koyar da aji da harshen Hausa a farko, amma daga baya aka fara musu harshen turanci a matsayin harshen karatu. Ya koyi rubutu da karatu, ya kuma fara shaÕawar duniyar da ta wuce yankinsu. A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI. Abdul-rasheed ya kammala primary ?insa aji shida (Standard 6) a 1959, yana ?auke da babban burin samun ilimin da zai sa ya taimaka wa garinsu. A Shekarar 1960 ta kawo masa sabon babi. An tafi da shi Zaria tare da sauran ?a?an manyan Arewa, inda ya shiga Government College Zaria (Barewa College), makarantar da aka san ta fi kowace a Arewa. Ya tafi yana kuka Iya nayi. Yayinda Inna ke dariyar ?eta ita da ?an uwansa, a ganinsu dai ya saka kansa a wani bala'i ne shi da uwarsa. Amma ita Iya addu'a tabishi da shi kawai, sai kewar rashinsa a kusa da ita matsayinsa na babba dake taimaka mata da aike da abubuwa na yau da kullum dake tsakanin uwa da ?a. Zama a boarding school ya koya masa nisa da iyaye da wahalar rabuwa da gida. Ya saba da rana da safiya da bugun ?aho, shiga aji da sautin turanci daga bakin malamai na Ingila, da kuma yin motsa jiki da yamma a filin kwallo. A can ne ya ha?u da wasu ?ananan jaruman Arewa, wa?anda daga baya za su iya zama manyan shugabanni idan UBANGIJI ya ?addara hakan a littafinsu. Tun a zuwa hutunsa na farko ?an uwansa suka fara hango canji a tare da rayuwarsa, sai dai hakan baisa sunji suna son yin karatun boko ba, hasalima babban su ana shirin masa aure ne wato Bilyaminu. Shekaru sun mi?a a rayuwar karatu ta Abdul-rasheed, yana zuwa hutu a duk lokacin da aka basu, yayi kwanaki ya koma cike da kewar gida da ?an uwansa da iyaye. A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gashi ya kammala a 1966, yana da shaidar Cambridge School Certificate, wadda aka fi darajawa sosai a lokacin.ÊYa dawo gida Bauchi cike da farin ciki da nasarori, nasarorin da suka saka iyayensa a farin ciki mara misalin kwatance. Abdul-rasheed ya kammala Secondary school cike da nasarori da suka sake faranta ran mahaifinsa, dan haka ya sake tsaya masa akan cigaba da karatun nasa. Bayan kai kawo da taimakon wani malamin su na Boarding ya samu gurbin shiga jami'a a Kano. A wannan ga?ar ma dai kowa ya bishi da addu'a musamman mahaifinsa da mahaifiyarsa. Yayinda sauran ?an uwansa ke masa dariya da kallonsa a matsayin wahalalle mara aikin yi, hakama Inna mahaifiyarsu kallon abin ta dinga yi kamar wani rashin aikin yi ne, sai dai duk habaicin da take da dariya iya bata kulata ba. Haka akai masa shiri ya taho Kano karatu a shekara ta 1967, ya shiga Ahmadu Bello College a Kano, wanda daga baya aka fi sani da Abdullahi Bayero College, har ya zama Bayero University Kano (BUK) a cikin 1975. Yana karantar History and Political Science, yana ?ara fahimtar tarihin mulkin mallaka da rawar da Arewa ke ciki a Nigeria data samu nasarar ?anci kai a 1962. Cikin makaranta yake zaune, dan basu da kowa da suka sani na dangi a cikin Kano ?in sam, hasali ma a cikin gidansu kaf babu wanda ya ta?a zuwa garin Kano sai shi yau da ALLAH ya kawo matsayin ?alibin ilimi. Zaman Kano ya bu?e masa ido, ya kuma sake koya masa iya zama da mutane, ya kuma ha?ashi da abokai na ?warai na amana...
Rayuwar Abdul-rasheed a Kano wata irin rayuwa ce mai cike da ?alubale da darasin rayuwa. Domin kuwa ba karatu kawai ya maida hankali ayi ba harda koyon ?inki. Ya fara koyon ?inki ne a dalilin abokinsa Nasiru. Wanda suka ha?u acikin makarantar department ?insu ?aya. Da farko dai babu wata abota a tsakaninsu sai gaisuwa, sai da Abdul-rasheed ya fahimci Nasiru ?uru ne dan akwai fahimtar karatu sai dai bashi da hayaniya sam sannan suka fara abota, dan kuwa Abdul-rasheed bashi da girman kai, duk abinda bai iya ba idan ya fahimci wanda ya iya koda mace ce sai ya nema taimakon a nuna masa, ta haka ne ya samu kusanci da Nasiru, a hankali suka zama abokai dan shima dai rashin girman kan Abdul-rasheed ?in ya burge Nasiru sosai. Kamar wasa ya jashi suka je gidansu wani weekend, dan kuwa Nasiru ?an garin Kano ne a anguwar ?ofar mata. A ?ofar gidan su Nasiru kuwa akwai shago da ake ?inki kasancewar a bakin titi suke kusa da kasuwa, shagon kuma na yayansa ne. Tunda Abdul-rasheed ya ?yalla ido yaga shagon sai abin ya bashi sha'awa, baiyi ?auron baki ba da suka shiga gaida yayan Nasiru yay ta yaba abin, shi ko Yayan Nasiru yaji da?i ya kuma fahimci kamar Abdul-rasheed na son harkar, sai yay masa tayi. Babu musu yace aiko yana son koyar kuma ya gode. Daga haka suka saita zai dinga zuwa duk weekend koyon ?inki...........???



_Zaku sameshi a wa?an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER????- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ?asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya??_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: ??_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number ??_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number??_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ????_*

*_Typing??_*








*_??KI?A A RUWA.....!!??_*




*_Bilyn Abdull ce ????_*


*_?????? ??????? ???????????? ?????????_*
_Da s?nan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._



_Chapter 7_

_Amin afuwa wlhy gaba ?aya banda nutsuwa ne an mana haihu bana yini a gida, jiya ma shaf na manta da batun posting ALLAH ??. Kuyi ha?uri ayi suna gobe idan ALLAH ya kaimu sai na dawo gaba ?aya hankali kwance, ga pages babu nutsuwar editing. Ina ?ara neman afuwa????._
__________________


*_NACE ina kuke ne?!!. Al'ummar Gombawa nake magana ?? fulanin asali ke nan ??._*

*Shin kuna da labarin cewa kuma nesa ta matso kusa gare ku?*

_Maza kuzo ku sha labari da ?umi-?uminsa, domin kuma fa NAKUN ya bu?e muku gidan gyara da ?al?ale jikin mata ?an kwalisa a kusa da ku gabb._

*_Idan kunji ana kiran maida tsohuwa yarinya to wannan katafaren shagon ne na??_*


*ALIYU HAIDAR COSMETICS PLAZA*

_ADDRESS SHOP D80 WOMAN LINE GOMBE MAIN MARKET_

*_Zaku same mu a wannan numbers ?in kamar haka??_*
*07068210505*
*09133081313*

_DEALER IN all kind of skin care products such as:_

moisturizer
Sun screen
Face Toner
Eye cream
Face serum
Face wash
Face scrub
Face cream
Face marsk
Body lotion
Body cream
Shower gel
Body scrub
Tube
Body oil
Body spray
Perfume
Hair crm
Hair spray and many more

*_Harma da abinda bamu lissafo ba anan. Ku dai kawai karku bari a yi babu ku. Domin kayanmu garanti ne kuma dahir ne ??_*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/HCLn6awOrmP5WJmO9jPrgK?mode=ems_wa_t


__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Haka kuwa akayi, kamar wasa Abdul-rasheed ya fara zuwa koyon ?inki, kasancewar yana son abun dan danan sai ga sakamako ya fara bayyana. Baya gajiya duk asabar da Lahadi sai yazo. Da Nasiru yaga yana wahala da kashe ku?a?ensa ga ?an makaranta komai nasa a ?a'ide yake, ga nisa Abdul-rasheed yana jimawa baije gida Bauchi ba sai yace mizai hana duk juma'a ya dinga biyoshi sai Monday su dinga shiga makaranta tare, ya dinga weekend dai a gidansu. Da farko Abdul-rasheed yaso turjewa, sai da Nasiru ya nuna masa fushinsa sannan ya amince amma yana ?ar-?ar dai, duk da kuwa kowa ya sanshi a gidan su Nasiru zuwa yanzu, kuma suna nuna masa so da kulawa. Amma shi dai baya son takura musu, yana kuma tsoron kar mahaifinsa yay fa?an barinsa makaranta harna kwana uku a kowane mako batare da saninsu ba. Tun dai yana ?ari-?ari har ya saki jikinsa.
Ê Ê Ê ÊÊ Tun a farko fara koyon ?inkin Abdul-rasheed akwai wata yarinya a ma?waftan su Nasiru da kullum takan wuce da safe da allo zata makaranta. Takan gaishesu idan zata wuce, hakama idan ta dawo da takan gaishesu ta shige gida. Shi dai bai ta?a tambayar sunanta ba, bai kuma ta?a magana da ita ba bayan gaisuwar nan da take musu a tare. Sai dai a kwana a tashi har ya haddace muryarta mai cike da nutsuwa da rashin hayaniya.
Ê Ê Ê Ê Ranar wata Lahadi da yamma yana a shagon shi ka?ai yana ?inki ogansa Yaya Zubair yaje sayen kayan ?inki zazza?ar muryar yarinyar nan ta ratsa kunnensa. ?agowa yay da sauri tare da take keke ya tsayar daga takun da yake masa. Tana tsaye daga wajen shagon ta rissina ta gaisheshi kanta a ?asa. Amsa mata yay da kulawa, kafin ya furta, ÒKina son wani abu ne ?anwata?Ó.
Ê ÊÊ Kanta a ?asa ta ce, ÒEh Yaya, dama kayan ?inki na kawo ma Yaya Zubairu, naga kuma baya nan ma kamarÓ.
Ê ÊÊ Cike da zolaya ya ce, ÒOh dan Yaya Zubairu baya nan kin fasa ?inkin?Ó.
Ê ÊÊ Da sauri ta ce, ÒA'a zan baka ka ajiye masa damanÓ.
Ê ÊÊ Murmushi yayi a karo na farko, ya ce, ÒTo shike nanÓ. Yay maganar yana tasowa yazo bakin ?ofar dan ita tana daga waje har yanzu. Mi?a masa ledar tayi kanta a ?asa. Karo na farko a rayuwarsa ya zubama hannunta ido. Fara ce sol, hannunta da ?unshin jan lalli da yay mata shegen ?yau. Harga ALLAH sai da gabansa ya fa?i, mazantakar ta motsa amma sai ya kauda kansa kawai ya amsa yana ?an murmushi da duba kayan ledar. Yadi ne irin nasu na maza. ?agowa yay ya sake ?an kallonta. ÒA ajiye kawai kenan zaki dawo ki masa bayani?Ó.
Ê Ê ÊÊ ÒA'a basai na dawo ba. ?inkin Bashir da Tasi'u ne daman. Inna tace dan ALLAH idan bata takura masa ba zuwa jibi a ?inka. Dan zamuyi tafiya ne bikiÓ.
Ê Ê Ê ÒIn sha ALLAHU za'a ?inka, nima zan ?inka musu da kaina. Idan kin shiga ki turo min su yanzu naga girmansu a daren nan zan yishi dan da safe zan wuce makarantaÓ.
Ê ÊÊ Godiya tai masa cike da girmamawa, sannan ya wuce kanta a ?asa. Samun kansa yay da binta da kallo. Doguwa ce sosai masha ALLAH, shekarunta bazasu wuce 14 ba, tana da ?an jiki, hakan ya nuna ne kuwa sakamakon kayan dake jikinta, zani da riga t-shirt sai kallabi disko, Tayi ?ammara da gyale a ?ugunta, kasa ?auke idonsa yay harta shige gidansu, a mamakinsa ya ?an juya zai koma yana sauke ajiyar zuciyar da tazo masa a bazata kamar ance sake waigawa sai ya ganta tana le?ensa. Wuff ta shige kamar wal?iya kuwa, tana turo ?yauren zauren gidansu na katako burum. ?an tsai yay yana kallon ?ofar kamar mai tunani, sai kuma yay murmushi ya juya ya koma cikin shagon.
Ê Ê Ê Yana zama su Tasi'u ?annenta sukai sallama. Yara ne matasa da bazasu wuce 9/7years ba. Sun gaishesa da girmamawa, ya amsa musu da kulawa yana musu murmushi. Dan sun sanshi ya sansu tunda yanzu ya zama ?an anguwar duk da kwana 3 kawai yake a duk sati. Amma sau?in kansa da son kula yara yasa duk suka sanshi. A karo na farko a rayuwarsa ya tambaye su miye sunan yayarsu?. Caraf Bashir dake matsayin ?arami ya ce, ÒIndoÓ.
Ê Ê Ê Ê Samun kansa yay da fa?in, ÒMasha ALLAH A'ishatu kenan. Wace makarantar kuke zuwa?Ó.
Ê Ê Ê Yanzu kam Tasi'u ne ya ce, ÒMuna zuwa makarantar Malam Sallau. Yaya Indo nada ?o?ari sosai, dan duk wata tana wanke allon ta sau biyu, yanzu haka tana izu kusan ashirin.
Ê Ê Ê ÊÊ ÒKai kai kuce dai yayarku Malama ce kawai?Ó.
Ê Ê Wannan kalma ta saka Bashir da Tasi'u tsuge masa da surutu akan yayarsu Indo. Abu kamar wasa hirar yaran ta dinga masa tasiri a zuciya, yana tare da su har akai kiran magriba, shi ya jasu suka je massalaci.Ê An idar da salla sun dawo sai ga Indo tana nemansu. Karo na farko da Abdul-rasheed ya samu kansa da yima Indo kallon ?urulla sosai. ?ya?y?yawar yarinya mai cikar zatin fuska da hasken fata. Suna ha?a ido tai saurin juyawa zata shige gida. Amma sai ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta.
Ê Ê ÊÊ ÒA'ishah!Ó.
ÊÊ Cak ta tsaya amma ta kasa juyowa, dan haka ya ?arasa inda take ri?e da hannun su Bashir. Sai da ya ?an ?ara kallon fuskarta sannan ya furta, ÒAmin afuwa nine na ri?esu a shago suna tayani ta?i, Inna ma ki bata ha?uriÓ.
Ê ÊÊ Batare data ?ago ba ta jinjina masa kai tana kama hannunsu suka shige. Yanzu ma sai ta juyo da tunanin yabar wajan zata saci kallonsa suka ha?a ido. Da sauri ta shige. Murmushi yayi yana girgiza kansa ya koma shago yana yaba halittar UBANGIJI a ransa, dan tabbas A'isha kyakkyawar yarinya ce kam. Kyawunta a bayyane yake ga mai kallonta kuma.

Ê ÊÊ?Tun daga wannan rana al'amarin Indo ya fara sa?ar zare a zuciyar Abdul-rasheed, har takai Nasiru ya fara harbo jirginsa. Haka ma Yaya Zubairu ya fara fahimta halin da Abdul-rasheed yake ciki akan Indo da yanda itama in zata wuce yanzu takan saci kallon cikin shagon bakamar da da zata wuce kanta a ?asa ba koda zata gaishesu. ?annent kuwa koda yaushe suna manne da Abdul-rasheed, tun mahaifiyarsu na jin sunansa a labarinsu ko idan ya saya musu abu irin na yara sun kai gida har dai ranar ta nema

5 / 35