Author : Asmeetah writer Category : Drama
kuliya ce! Mai bakar Aniya!"
Catrina ta kafe shi da ido, ta ɗan saki murmushi, kamar wata jaruma mai raina kowa. Amma bata ce uffan ba. Sai dai cikin zuciya ta tasan cewa Abul ya gane ta! Ya gane asalin ta — Sarauniyar Duhu.
Amma Abul bai faɗi wannan gaskiyar ba, domin yasan dole wata rana asirinta zai tonu, yasan ko zai faɗa musu cewa Catrina ba mutum ba ce, akwai wasu da ba zasu iya jurewa ba. Ya sake juyowa ya ƙara daka wa Abeesh tsawa tare da faɗin
"Ka raina mutuncina kenam? Abeesh.... haƙiƙa na raina tarbiyyar ka, Ka ɗora ma kanka laifi da ba zaka iya ɗauka ba. Ka bar matar aure ka rungumi wata iska..."
---
🔥 Cikin Zuciyar Catrina:
A lokacin da suke zagin ta da fushi da kuma faɗa, Catrina ta rufe idonta, ta furta a zuciyarta:
"Kun yi faɗa da ni amma Sai dai... ku sani, ban zo da niyyar ɗaukar mijin wata ba, na dawo ne don na ɗauki haske daga gare ku."...
Tana kammala maganar zuci ta bar falon tare da nufan ɗakin ta....
Abul ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, a fusace ya bar falon yana mai yin fushi da Abeesh...
A wannan ranar wuni akayi cikin ɓacin rai...
---
A ɗakin Abeesh...
Nasreen na zaune gefen gado, kanta a ƙasa, tana kuka kamar ruwan sama. Abeesh yana tsaye kusa da taga, yana kallon sararin sama. Yayi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce da muryar dake nuna cewa shi ma zuciyarsa cike take:
“Na kasa control zuciyata Nasreen... Ki yarda da ni. Ban taɓa so in cutar da ke ba. Amma bazan iya fitar da Catrina daga zuciyata ba.”
Nasreen ta ɗago kai, idonta jajir ta ce:
“Ka ƙi ka zaɓe ni Abeesh. Na fahimta. Amma bari na faɗa maka abu guda... Duk da cewa zuciyar ka tana tare da ita, ni ce matarka a bisa doka da addini. Ni ce kake da alhaki akai. Kuma wallahi, zan tsaya tsayin daka akan aurena.”
Abeesh ya juyo yana kallonta cikin tsananin damuwa ya ce:
“Na san haka. Amma Catrina... kamar akwai wani abu a tsakanin mu da bana iya bayyana wa. In na kalleta, zuciyata na bugawa...”
“Zuciyar da ta buga shin tana manta ƙauna?” Nasreen ta katse shi, hawaye na gangarowa. “To ka zauna da ita. Amma ka sani, bazan bar aurena haka nan ba.”
---
Washegari da safe...
Falonsu ya lafa, amma ba a cire kayan da suka tarwatse ba. Tasleem ta fito daga ɗakinta cikin riga mai laushi da ɗan gashi a rataye akan wuyanta, tana fitowa ta iske Catrina zaune kan kujera tana shan shayi, cikin fara’a kamar ba ita aka kusan cakawa wuƙa jiya ba.
Tasleem ta tsaya cak tana kallonta, sannan ta ce da ƙarfin zuciya:
“Ke fa baƙuwar da aka ba wurin zama ce. Amma ina sane da niyyarki... Soyayya dai za ta fito da gaskiyar ta, kuma wata rana za a gane wacece ke, Catrina...”
Catrina ta ɗan saki murmushi, tana ɗora kofi a leɓenta sannan ta ce
“Idan zuciyar mutum ta amshi abu, ko wane hali yake ciki, sai ya rasa kwanciyar hankali. Bani ce na tilasta masa soyayya ba. Shi ne yazo gare ni...”
Kafin Tasleem ta bata amsa sai ga Asmeen ta shigo, cikin farin ciki da annashuwa —kamar wata sabuwar wata...
Tasleem ta kalleta da mamaki ta ce:
“Asmeen... me nake gani haka? ke ce yau a part ɗin nan? yau Ango ya barki kenam tin Aure rabon ki danan, ga shi har mun shiga sati na biyu...”
Asmeen tana dariya ta ce
"wallahi nazo ziyara ne, nayi farin cikin ganin ki sosai...."
Tasleem ta ce "Asmeen ya dai nake ganin ki cikin farin ciki kodai yanzu ba wata matsala tsakanin ki da Shaprees?..."
Asmeen rungumar Tasleem ta yi tare da faɗin
"yanzu mijina bashi da wata matsala, ya zamo tamkar waliyi, shiyasa kika ganni cikin farin ciki, mu da duhu har abada munyi hannun riga...."
Tasleem cikin farin ciki ta ce "Alhamdulillah Ƴar uwata haka nake son ji..."
Catrina tana kallo Asmeen da mamaki, amma bata ce komai ba. Amma wannan haske da ke dawowa cikin Asmeen, wani sabon babi ne da zai iya karya ƙa’idar da Madam Nablah ta kafa.
---
Kiyi shiri...
Madam Nablah na gab da dawowa daga tafiyarta. Kuma za ta dawo ta tarar da gidan nata yana karkarwa da rudani—soyayya da ƙiyayya, barazana da mafita suna yaki a cikin gida guda.
Catrina na zaune tana maganar zuci....
Suna cikin wannan halin sai ga Nasreen ta shigo falo, ganin Asmeen yasa ta tafo da gudu suka rungumi juna, haka suke farin cikin ganin juna...
Su uku sun haɗa kayuwansu guda suna farin cikin kasance da juna... Yayin da
Catrina na zaune cikin izza kamar itace uwar gidan. tana gyara yatsun kafarta da reza tare da tauna cingam tana ƙararas...
Su ma duk zama suka yi...a falon.
Nasreen tana kallon Catrina cikin kishi da zafi kamar zuciyarta na tafasa da ruwan zãfi.
Asmeen tana kallon su cikin fara'a, tana riƙe da wani ƙaramin ledar kayan zaƙi domin tasan ƴan uwanta suna matuƙar son kayan zaƙi na ƙwaɗayi...
Ta ce:
“Tasleem! Nasreen yau na ce bari in zagaya na gaishe ku… Amma… kamar sabuwar fuska nake gani…”
ta kalli Catrina sannan ta dawo da kallon ta ga Tasleem da Nasreen ta kuma cewa
“Wacece wannan baƙuwa muka yi ne? Ban taɓa ganinta ba.”...
Tasleem ta lumshe idonta, zuciyarta na ƙoƙarin kwantar da kai, kafin ta ɗan jinjina kai sannan ta ce:
“Ƴar baƙunci ce daga can waje. Tazo gaisuwa ne ga Momy, sai ta tsaya.”...
Catrina ta saki murmushin da babu laifi amma akwai shashanci a ciki ta ce:
“Ni kuwa sai dai in ce nazo sadaukar da zuciya… Gidan da na samu kulawa da kwanciyar hankali. Ina jin kamar nan ne nawa gidan.”...
Asmeen ta ƙara kallonta, cikin nazari da tsananin shakku, tace:
“Kwanciyar hankali da kulawa…? Hmm, an ci sa’a. Sai dai kamar kin fi dacewa da ɗakin baƙi, ko ba haka ba?”
Catrina ta ɗan kwashe da dariya, tana ɗan karkada gashinta ta ce:
“Wani lokacin zuciya ta fi gini zama gida, Asmeen…”
Nasreen ta miƙe tsaye, tana tafa hannunta kamar wacce ta gaji tare da faɗin:
“Kina nufin zuciyar mijin wasu? Tunda ai kin sami sabuwar matsuguni, ko ba haka ba?”
Asmeen ta kallesu duka biyu cikin mamaki, bata fahimci inda zancen ya dosa ba. Amma kafin tayi magana, sai wayar Catrina ta yi ƙara. Ta ɗauka, ta yi wata hira da ba a ji ba, sannan ta miƙe kamar wacce zata bar falon.
Ta ce da su .
“Zan wuce yanzu. Sai an jima...”
Ta juya cikin izzarta, tana tafiya kamar sarauniya, gashinta yana kyalli kamar zinariya. Bayan ta fita, Asmeen ta juya ga Tasleem cikin damuwa tana kallon Nasreen da Tasleem ta ce
“ Ku gaya min gaskiya, wacece wannan? Kuma me take nema a gidan nan?”
Nasreen ta ja numfashi, idonta na ƙoƙarin cikowa da ƙwalla ta ce:
“Ta karɓe zuciyar Abeesh, Asmeen. ita ɗin kamar mayya ce… Ba a san asalinta ba, ba a san inda ta fito ba, amma ya kasa rabuwa da ita.”...
Asmeen ta ɗauki salati, ta dafe goshi tare da faɗin
“Innalillahi... yanzu ita ce wannan ke jefa ki Nasreen cikin damuwa? Kuma Momy bata san komai ba?”...
Tasleem ta girgiza kai sannan ta ce:
“Momy tayi tafiya, kuma kamar da gangan take gujewa auren mu ni da Amaar. Ba komai Asmeen, komai sai dai muyi addu’a… Amma ke fa? Shaprees yana kula dake kuwa?”
Asmeen ta yi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta ce da sanyi:
“E… Yana kokari. Kullum sai ya tambayi yadda nake ji, yana kula da Ni, Na fara jin kwanciyar hankali tare da shi, duk da zuciyata bata gama buɗewa ba.”
Tasleem ta riƙo hannunta cikin nata, tace:
“Ina fatan ke zaki samu farin ciki, Asmeen. mu cigaba da addu'a sauƙi na nan tafe Insha Allahu..."
Suka rungume juna a hankali. Amma a bayan labulen falon, wata inuwa ce ta ke kallon su — Catrina — ta dawo, ba tare da su ankara ba. Idonta ya ƙanƙance, kamar wacce ta ji wani abu da bai mata daɗi ba.
“Soyayya ba ta da sauƙi ...”
ta furta da siririyar murya.
“...amma bazan bar shi ba. Ko da kuwa sai nayi amfani da zuciyarsa gaba ɗaya...”
Bayan Sallar Isha’i
Shapreen ne yazo ya ɗauki Asmeen suka tafi can part ɗin su...
Daren ya zo da natsuwa,
Kowa ya shiga sashi-sashinsa,
Amma zuciyar Nasreen cike da raɗaɗi kamar zuciyar mace da take numfashi a cikin wuta.
Abeesh yana ɗakin Catrina. A cewar shi, “zai je ɗan gaishe da ita ne” — amma Nasreen ta san cewa wannan ƙarairayi ne, domin sau nawa yanzu da take tsintar sa a ɗakin Catrina cikin dare?
Ta zauna a gefen gado tana danna wayarta amma kallo ɗaya zaka mata kasan ba duba wayar take ba — zuciyarta na ambaliya da hawaye ne kawai.
Sai taji numfashinta yana ƙoƙarin ɗagewa....
Tasleem ne ta shigo ɗakin cikin gajiya, tana ɗauke da wata ruwan zafi da lemon zaki. Ganin Nasreen a ɗakin ta cikin damuwa yasa ta ajiye kofin a gefe saman frig sannan ta zauna kusa da ita tana faɗin
"Nasreen, wallahi ni ba zan ci gaba da kallon wannan halin da kike shiga ba. Wannan ba aure bane, wannan azaba ce."
Nasreen ta girgiza kai da hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskar ta. Ta ce
"Na haƙura Tasleem... Na ce da kaina kowa na fuskantar jarabawa a cikin aure. Amma har yau kwana na na uku, mijina yana dakin wata na gaji Tasleem......."
*NEXT NEXT NEXT NEXT*
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
47 to 48
Nasreen tana kuka tana riƙe da hannun Tasleem tana faɗin:
"Kiyi haƙuri da abin da zance Tasleem, zaman gidan nan ya isheni haka, ina zaune ne tamkar gawa, idan na cigaba da zama a gidan nan wata rana zuciyata zata buga ne gaba ɗaya ku rasa ni har abada, bazan iya juran wannan wulaƙanci da tozarci ba, zan tafi Tasleem! zan bar gidan ko hankali na zai samu kwanciya..."
Tasleem rungumar ta tayi tana rarrashin ta tare da faɗin "wait Nasreen....kina maganar zaki tafi shin ina zaki je? gidan nan fa shine dolen ki koda bakya Auren Abeesh, bakida yanda ya fi nan gidan..."
Cikin kuka Nasreen ta ce "ko ina zan je, kuma zan rayu a ko ina...."
Tasleem ta ce:
"To yanzu dai dare ya yi kiyi haƙuri zuwa gobe da safe, ki kwanta kiyi bacci dan Allah...."
Daƙer Tasleem ta rarrashe ta tukun ta kwanta, a tare suka kwana a ɗakin, gari yana waye wa Nasreen ta fara shirya kayanta, tasa a ranta ita tafiya zata yi....
Har ta gama shirya komai tana zaune, cikin shirin ta....
Tasleem ta ce:
"Ki yi haƙuri Nasreen, komai ya yi farko zai yi ƙarshe, wata rana sai labari da yardar Ubangiji, bamu da kowa kin sani, bamu san wasu dangin mahaifin mu ba sai Abul dake Tare da mu, sannan tin da muka zo duniya Mommy bata kaimu gun wajen dangin ta ba, mun sha tambaya har mun gaji, ta ƙi bayyanar mana su, to ya zamu yi...."
Girgiza kai Nasreen tayi tare da miƙe wa tsaye tana faɗin
"Ki yi haƙuri kawai domin tafiya ba fa shi, dan Allah ki kula mun da Asmeen, sannan ki bawa Abul haƙuri domin bazan masa sallama ba, idan Mommy ta dawo itama ki bata haƙuri, zan tafi...."
Ɗaukan mayafin ta tayi ta yafa daman da akwatin ta take tafe, ta gama shirya komai.....
Tasleem riƙo hannun ta tayi tana faɗin:
"Nasreen meyasa bakya jin magana ne kam?...."
Nasreen tana kuka mai zafi, hawaye na gudu kamar ruwan sama, tana girgiza kai tana faɗin:
"Na gaji! Bazan iya ba! Wallahi bazan iya zama da mijin da yake da yake kwana da wata mace a gidana ba!"....
Tasleem ta ƙwantar da murya tana riƙe da hannunta ta ce
"Dan Allah Nasreen ki zauna, wannan gida naki ne, kar ki bar shi haka!"
Nasreen janye hannunta tayi da ƙarfi tare da faɗin:
"A'a Tasleem! Ki bar ni na tafi. Ki bar ni da hukuncin da na yanke wa kaina dan Allah...!"
Tana kuka ta fizge hannunta daga riƙon da Tasleem tayi mata, cikin sauri ta fito falo da akwatinta a hannu, tana fitowa ta ci karo da Abeesh da Catrina, sun fito daga ɗaki suna murmushi kamar babu wani abu da ke faruwa...
Itama Tasleem da sauri ta biyo bayan ta, ganin su Abeesh yasa itama ta tsaya cike da mamaki tana kallon Abeesh domin shine abun ji, ba Catrina ba...
Abeesh idonsa ne ya sauƙa akan Nasreen tana riƙe da akwati, zuciyarsa ce tayi wani irin bugu ganin a halin da take ciki, da sauri ya ƙarasa shigowa falon yazo ya tsaya a gaban Nasreen, cikin rashin fahimta yake kallon ta daga bisani ya ce:
"Ina zaki je da akwati?..."
Nasreen tana hawaye ta ce "zan tafi inda bazaka ƙara gani na ba, ina haka kake so ko? ka zaɓi budurwarka sama da ni matarka ta Aure...."
zuciyarsa ce ta ɗauki sautin bugu jin abinda ta faɗa....
Ya riƙo hannunta cikin firgici yana faɗin:
"Nasreen ki tsaya, ki saurare ni. Dan Allah, ki zauna mu warware komai."
Nasreen ta ce:
"Uhmmm! Lokaci ya ƙure Ya Abeesh, a yanda na ƙudurta a raina cewa a yau zan bar gidan nan kuma a yanzu to babu wanda zai dakatar da ni akan hanyata, sai dai kawai kayi haƙuri amma tafiya dole ne, bana buƙatar ƙara ganin fuskar wannan baƙar munafuka...."
Ta ƙarasa maganar tana kallon Catrina....
Abeesh ya ce "ki saurare ni mana Nasreen, yaushe kika koyi taurin kai ne?..."
Nasreen ta ce:
"Zaman duniya koya maka ake don haka don na koyi taurin kai wannan ga donsa nayi, idan kana so na cigaba da zama da kai to sai dai a yanzu ka kori Catrina daga gidan nan, sannan ka fita hanyar ta tinda ba Auren ta zaka yi ba...."
Abeesh ya ce:
"Gaskiya Nasreen bazan iya koran ta ba domin ba ni na kawota gidan ba....."
Jinjina kai Nasreen ta yi sannan ta furta "gaskiya ne! Amma zaka iya juran rashin ganina ko?...."
Ta fizge hannunta daga riƙon da ya yi mata sannan ta nufi yanda Catrina take tsaye a gefen su tana sauraron tattaunawar da suke....
Nasreen tana iskota ta shaƙo wuyan ta da ƙarfi, tana faɗin:
"Zan bar miki shi! Ki cinye shi nama ɗanye idan kina so! Shashasha! Ƙaruwar banza!"...
Catrina kuwa bata ce uffan ba, sai shu’umin murmushi da take yi, kamar tana jin daɗin ruɗanin da ta jefa su a ciki.
Nasreen ta juyo da ƙarfi tana jan akwatin ta tayi hanyar waje tare da faɗin:
"Duk wanda ya biyo bayana, wallahi ban yafe masa ba!"....
Ta fice da hanzari. Kowa ya tsaya kamar babu rai a jikin su...
Catrina maganar zuci take tana faɗin:
"Na fara cin nasara. Amma ba zai tsaya a nan ba... Nasreen, ba barin gidan zaki yi kawai ba — zaki bar duniyar gaba ɗaya ne ...."
Cikin takaici Tasleem ta juyo tana kallon Abeesh, wanda ya zauna a kujera cikin tagumi ya rasa mai yake masa ciwo a jiki,
Cikin ɗaga murya ta ce:
"Shikenan. Hankalinka ya kwanta ko? Matarka ta bar maka gida saboda wata ƙazamar banzar Catrina. Wallahi ka bani kunya!"...
Abeesh a firgice ya miƙe da fushi yana daka mata yatsa cikin nuna yatsa yake faɗin:
"Dakata Tasleem! Kar ki kuskura ki zage ta a gabana!"...
Tasleem ta ɗan zaro ido, hawaye na gangarowa ta ce:
"Saboda na faɗi gaskiya? Kenam tafi Nasreen a wurin ka? tabbas abun nakan ya fara wuce gona da iri, dole akwai wani abu a ƙasa ba baka kawai aka barka ba, amma zan binciko koma menene...!"
A fusace Abeesh ya nufi ɗakinsa a ruɗe, ba tare da ya furta komai ba...
Catrina ma ta shige nata ɗakin ba tare da wata magana ba...
Tasleem ta zauna a kan kujera, tana kuka mai zafi, tana tunanin wani irin hali ƴar uwarta zata shiga..
_____________🚗💥
Nasreen tana tuƙi cikin gudu, zuciyarta cike da takaici da ciwon zuciya tana faɗin:
"Me yasa Abeesh ya zama haka? Me yasa ya canza lokaci guda kamar ba Abeesh ɗina ba? Me yasa zan zauna da mijin da bai girmama ni ba?"...
Tana cikin maganar zuci
Kwatsam — wani duhu ya bayyana a gaban motarta, glass ɗin gaba ya rufe da baƙin hayaki. Nasreen ta firgita tana ƙoƙarin danna birki, domin ba wani ganin hanya take ba, ga shi ba dare bane balle ace dare ne ya yi, misalin ƙarfe 8 na safe ne yanzun....
Cikin baƙin wannan duhu, Catrina ta bayyana a siffar iska, tana murmurshi cikin mugunta tare da faɗin:
"Kin fice da kafafunki… amma ba zaki koma da su ba, Nasreen."...
A ruɗe Nasreen ta dakatar da tuƙin ba tare da ta ga a yanda take ba, ta tsaya ne