Author : Asmeetah writer Category : Drama
ido masu tsananin natsuwa da kwanciyar hankali ya ce
“Zuciya tana da hanyar da ba a iya shan kwaya a ɓoye ta ba. Zuciyar Tasleem zata gane ni, amma lokacin da ya dace.”
Daga nan suka yi masa sallama. Nasreen da Asmeen suka kalli Abeesh da idon tausayi, yana so ya zauna da Yayan shi tsawon shekaru basu ga juna ba,
daƙer suka samu ya yadda zasu tafi tare yana kuka, suna kuka..
Suna cikin mota suna tafiya cikin yamma, Asmeen ta ce:
>“Shiyasa Mommy bata taɓa barin mu shiga bedroom ɗinta ba… Ashe akwai wani shirin da take a ɓoye”
Nasreen ta jinjina kai cikin alhini ta ce
“Shiyasa Mommy da Tasleem ba sa shiri,
Tasleem ta taɓa faɗa mun cewa tana mafarki Mommy tana shan jini, amma ban taɓa yarda da ita ba.”
Ta share hawayenta sannan ta ƙara da cewa:
“Tasleem na da baiwa… Zuciyarta na gane gaskiya kafin baki ya furta.”......
ƁANGAREN AMAAR...
Shi kuma Amaar ya zauna shi kaɗai, jikin sa a manne da bandeji babu kaya a jikinsa, idanunsa sun zurfafa cikin tunani. Kallon gilashin taga yake yi, yana hango rana tana faɗuwa ga duhu yana shigowa.
“Tasleem…” ya furta da ƙaramin murya.
Sai ya rufe idanunsa, zuciyarsa ta ɗauko masa shekarun yarinta, lokacin da Tasleem ke masa dariya, suna gudu a ciyawa, tana ce masa
“Kai ne Hasken Ruhi na…”
Sai ga hawayensa sun gangaro Zuciyarsa ta gama raunana Kuma ba wani bandeji da zai warkar da raunin da ke cikin zuciyar sa.....
ƁANGAREN MADAM NABLAH…
A cikin duhun dakin tsafi, hasken wuta mai shuɗi yana walkiya daga wani ƙaramin madubi mai jini a cikin gilashi, wanda aka ɗaure da ruƙon zinariya mai zane-zanen gargajiya. Wurin tsafin ya cika da hayaƙin turare da gurnani na shiru – kamar ana karanta wata duniyar da ba a iya gani da idon duniya.
Madam Nablah na zaune akan tabarma ta zinariya, tana sanye da tufafin bakake masu yalwa, hannayenta a buɗe, dukkan tafin hannunta cike da wuta mai yawo kamar ruwan zafi.
Cikin murya mai sanyi na mugunta, take furta yaren tsafi
“Zaaaa'qil... H'azmaar... Ayyukan da Maruuk!”
Bana hangen zuciyar maƙiyina, Bana gani abinda ke ɓoye.”
Madubin tsafin ne ya fara girgiza. Sai hayaƙi ya shiga zagaye a cikinsa – hayaƙi mai launin jini. A hankali siffar wani fuska ta bayyana… fuskar Amaar.
Madam Nablah ta ɗan motsa daga inda take zaune, ido a zarr kamar ba ta yarda da abinda take gani ba.
“Na tura ka cikin ruwan hallaka! Me yasa kake raye?!”
Waye ya cece ka?! Waye yake baka kariya daga tsafina?!”
Ta miƙe da sauri, ta taka gaba ta danna hannunta a tsakiyar madubin. Sai wani irin zafin wuta ya fesa mata – madubin ya ƙi bada cikakken bayani Ya ɓoye wani bangare.
“Wannan tsafi ba cikakke bane… akwai wani karfi da ya hana ni ganewa...”
A cewar Madam Nablah.
Nan take siffar wasu fuska biyu suka bayyana a gefe:
Nasreen da Asmeen.
A ruɗe ta ce
“Ƴaƴana!” Ta furta da ƙarfi. “Kuna tare da shi? Kuna kusa da mutumin da zai rushe mun mulki?!”
Idanunta suka cika da wuta, kamar yadda ƙarfin jikin aljanu ke ƙara ratsa kanta. Tana jin wani mugun zafi yana tashi daga ƙasan cikinta. tana tangaɗi da haka ta zauna a wurin amma bata faɗi ba, sai dai ta farka da sabuwar murya, murya mai haɗe da na wani tsatso daga duniyar tsafi
tana faɗin
“Ba za ku yi nasara ba, Wannan ƙyauren nawa ne. Ruhi ba zai iya haskakawa a cikin duhu ba…”
Madubin ne ya bushe da hayaƙi ya ɓace. Sai wata ƙaramar ƙwarya ta karye a gefe, Hannu biyu suka ɓullo daga ƙasa hannuwan aljanu suna miƙa mata wani baƙin zobe da wasu sabbin kayan tsafi.
Madam Nablah ta ɗauki zoben ta cusa ɗaya a yatsanta, ta ce
“Tasleem zata dawo gare ni… koda da jinin Amaar zan ɗaure zuciyarta!”
Ta sa dariyar mungunta mai amo, ta ɗaga hannunta sama – wutar tsafi ta sake fitowa, tana zagaye dakin da wani sabo, mafi ƙazantar shiri...
ƁANGAREN TASLEEM…
Tana kwance a cikin bedroom ɗinta, tana numfashi da ƙyar. Gumi na keto mata, jikinta yana rawa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar zata fito daga kirjinta. Har yanzu bata manta da abin da ya faru ba, robot ɗin da suka rikide, murya mai ban tsoro, rawar duhu, da faɗuwarta daga saman beni amma abin mamaki ta farka lafiya.
Sai dai akwai wani abu dabam da take ji a jikinta yanzu… wani nauyi a zuciya, kamar an cire mata wani ɓangare na rayuwa amma ta kasa sanin me ke faruwa.
Ta zauna akan gado, ta riƙe kanta da hannaye biyu, tana kuka a hankali.
“Wayyo Allahna… me nayi? Me yasa nake jin kamar akwai wani sirri da ya ɓuya cikin rayuwata? Kuma waye wannan mutumin da na harba? Waye shi a rayuwata?”
Ta tuna fuskarshi, fuskar Amaar, fuskar da ke da wani sanyi da zafi a lokaci guda. Sai zuciyarta ta tsinke da ciwo. Idanunta suka cika da hawaye.
“Na kashe mutum? Na kashe shi? Amma me yasa tun daga ranar dana gan shi nake jin wani abu dabam? Me yasa idan ya kalli idona nake jin tamkar ya san sirrina fiye da yadda ni kaina na sani?”
Tana cikin wannan tunanin ne sai taga kyakkyawan locket (abun wuya) a gefen gadonta. Bata san daga ina ya fito ba. Tana ɗagowa, ta buɗe… hoton wata yarinya ce a ciki da yaro gud, Ita ce – Tasleem ce da wani yaro wanda ya haɗe da ita.
Sai wani irin shocking ya daki zuciyarta. Sai zuciyarta ta fara bugawa da karfi ta ce
“Wannan hoton… me yake nufi?! Wannan yaron…”
Ina tunanin na san fuskar nan... amma ta ina? Me yasa yake min kama da…”
Nan take ta fara jin jiri. Sai ta fadi a saman gadon, tana huci, tana fitar da gumi. Zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Kamar ƙwaƙwalwarta na ƙoƙarin faɗa mata wani abu, amma akwai wani abu da ke hana shi fitowa fili.
A cikin baccin da ya ɗauke ta, ta fara mafarki. A mafarkin, ta tsinci kanta tana gudu a cikin jeji – tana gudu daga wani abu, amma daga can gaba sai taga Amaar tsaye, yana mata murmushi. A bayansa kuma akwai wata mace mai bakaken kaya, idonta jajaye kamar wuta…
“Karki kuskura ki tuna!”
“Kar ki gane waye shi… idan kika gane, rayuwarki zata ɓace!” – Muryar Madam Nablah ce.
Ta kurma ƙara a mafarkin – sannan ta farka da ihu!
Ta miƙe da sauri daga gado, huci na fita daga bakinta, hawaye na gangarowa. Ta dafe ƙirji.
“Zan tafi! Zan tafi inda na bar shi. Ko da kuwa ya mutu ne – sai na tabbatar da hakan da kaina.”
Da sauri ta saka hijabi, ta fice daga gidan zuciyarta cike da rudani da alhini, amma wani ɓangare na zuciyarta na kokarin farka da gaskiyar da aka daɗe ana ɓoye mata…
NEXT NEXT NEXT
SAI DAI KUYI HAƘURI YAU BANYI EDITING BA, KODA ZAKU SAMU TYPING ERROR KU SHARAR KAWAI😃😃....
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 27 to 28
Tasleem na tafe da sauri kamar wadda gobara ke binta. Fuskarta cike da ruɗani da tarin tambayoyi, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Kusan ta yi kamar mai hauka, saboda abinda take ji, abinda take tunani—da kuma abinda take fargaba ta aikata.
A daidai shiga falon gidan nasu kenan, sai taga su Nasreen da Asmeen na shigowa cikin gaggawa daga ƙofar baya.
Da ta hango su, ta nufe su da sauri, jikinta na rawa.
“Ina yake? Ina wannan mutumin? Daman yana raye? Na ji kamar yana kiran sunana… don Allah ku gaya mun gaskiya! Ku gaya mun shi ɗin waye!”
Asmeen ta tsaya cak, tana kallon Tasleem kamar zata yi kuka, amma sai ta haɗiye kukan ta ce
“Ke Tasleem, me kika aikata?! Shin kina da hankali kuwa?!”
“Wato har ke Asmeen?” Tasleem ta furta tana kallon su da kuka,
“Ni fa ban gane ba, kawai na ji wani abu dabam tun da na gan shi! Amma ban san me yasa na harbe shi ba… wallahi bazan iya rayuwa da wannan laifin ba!”
Nasreen ta matso kusa da ita, ta kama hannunta cikin tausayawa domin sun gano yanzu duk abinda Tasleem ta aikata da taimakon tsafin da ya gusar mata da zuciya ne cikin basar wa ta ce
“Laifi ki ka aikata! Kema kin sani. Kuma ki sani wannan mutumin ba kamar kowa bane! Amma ki daina tambaya… idan lokaci yayi, za ki gane shi.”
Tasleem ta girgiza kai da ƙarfi, zuciyarta kamar zata tarwatse.
“Toh gaya mun! Ku gaya mun kawai ko ya mutu ne?!”
Asmeen ta juyo da sauri tare da faɗin
“Ba zai mutu ba insha Allah, amma ki shirya fuskantar abinda kika aikata..."
Tasleem ta sunkuyar da kai tana hawaye, tana jin nauyin abinda ta aikata ba don ta sani ba, sai don wani abu na ciki da ke hura mata wuta.
Nasreen ce ta kalli Asmeen tare da girgiza mata kai alamar tayi shiru da wannan batun.
**
A nan ne ƙarar buɗewar ƙofa ta katse su. Fuskar Madam Nablah ce ta bayyana, tana shigowa falon kamar guguwa Idanuwanta jajaye, fuskarta ba Annuri, kamar wadda ta dawo daga duniyar aljanu.
Nasreen da Asmeen suka tsaya cak, jikinsu ya ɗan yi sanyi. Tasleem ta juyo da sauri, da mamaki a fuskarta ta ce
“Mommy? Ina kika je jiya? Kuma me yasa fuskarki haka?”
Madam Nablah ta wuce su kamar ba ta ji ba, idonta na ɗauke da wata ƙwayar duhu, kamar ba ta cikin hayyacinta, ta tsaya dab da fitilar falon, sai ta juyo a hankali, ta kalle su ɗaya bayan ɗaya.
“Me kuke aiwatar wa a cikin gidan na? Me kuke ɓoye mun?”
Nasreen ta tsaya da ƙarfi, tana fidda numfashi ta ce
“Ba zaki gane ba Mommy… sai ranar da Allah ya nuna miki gaskiya.”
Madam Nablah ta ƙura mata ido, ba tare da tace komai ba. Idanunta sun nuna alamar karin haɗari da bacin rai.
**
Abeesh da yake jin hayaniya a ƙasa tun daga ɗaki, ya leƙo, amma ganin ya hango Madam Nablah ne yasa ya juya da sauri ya koma, Bai taɓa jin zuciyarsa ta ƙone kamar yau ba. duk kyautatawar da aka yi mata amma hakan bai hana ta hallaka mahaifinsa da ɗan uwansa ba.
Tasleem ce ta katse su da kuka tana faɗin "amm inason ganin sa, ba'a son raina na harbe shi ba, Allah yasa bai mutu ba...."
Madam Nablah wacce take shirin barin wurin jin kalaman Tasleem ne yasa ta dakata, a slow ta juyo tana tambayar su "wa kika harba?..."
Da sauri Nasreen da Asmeen suka ce "babu komai"
Madam Nablah hannu tasa ta juyar da Tasleem tana son ganin abinda ya faru ta cikin ƙwayar idanuwan ta, cikin fushi da tashin hankali Tasleem ta hankaɗe mahaifiyar su tana faɗin
"kar ki taɓa ni domin ke Annoba ce, ki fita daga cikin rayuwar ta na tsane ki, ina ji a jikina cewa kin raba ni da abubuwa mafi muhimmanci a cikin zuciyata, ke kika kashe mana mahaifin mu sannan kika ɓoye Abul Abeesh a cikin ɗakin duhu, bai kamata na cigaba da ɓoye waɗannan sirrika a cikin zuciyata ba, ki sani sai na kawo ƙarshen ki...."
Nasreen da Asmeen sumar tsaye suka yi jin mutuwar mahaifinsu da kuma Abul Abeesh yana raye,
Madam Nablah zaro idanu tayi waje tana mamakin jin waɗannan kalamai daga bakin Tasleem....
Tasleem ta cigaba da cewa "sannan akwai abinda kika raba ni dashi wanda yana da matuƙar mahimmanci a rayuwa ta, tabbas na gan shi a cikin mafarki na kuma na ganki kema da wasu rikitattun idanuwa, meye sunan sa? meye sunan sa? sunan sa A.. A.. Am, yana zuwa mun a matsayi spirit, shi ɗin haske ne wanda na tabbata da wannan hasken zai tarwatsa baƙin tsafin ki..."
Madam Nablah kanta ba ƙaramin ɗaukan zafi ya yi ba, cikin fushi ta lumshe idanuwanta lokaci guda ta buɗe su da wani irin jajayen idanuwa, idanuwanta sai farfatsin wuta yake, a tsawa ce ta yi wa su Nasreen magana da cewa "ku fita ku bani wuri yanzun nan"... cikin wata ƙatuwar murya, yanzu ta fito a asalin ta na matsafiya...
Nasreen da Asmeen haka jikin su yake ɓari cikin tsoro da fargaba suka yi waje da gudun gaske...
Itama kuma Tasleem riƙo hannunta tayi tana jan ta har ta kaita can room ɗin su ta wurga ta saman gado...
Madam Nablah tsabar tashin hankalin da ta shiga ta ma rasa abinda zata yi haka tabar ɗakin a fusace tare da rufe ƙofar...
Amaar yana kwance akan gadon sa ba abinda yake tunawa illa Tasleem, ya runtse idanu, yana furta a zuciyarsa
“Tasleem… ki yafe mun. Lokaci yana zuwa. Lokaci da komai zai bayyana. Amma yanzu... Sirrinmu yana da daraja.”
Madam Nablah na zaune a ɗakin tsafinta wanda ke cikin ɗayan ɓangaren gidan da ba kowa ke iya shiga ba. ɗakin duhu ƙirin amma dakin na ɗauke da hasken fitilar tsafi—wato wuta mai shuɗar haske da ke fitowa daga ƙasan wani tafki mai duhun ruwa.
Ta durƙusa gaban madubin tsafi wanda yake rataye cikin iska, ba tare da ya taɓa wani bango ba. Duhu ne ya mamaye zagayen madubin, sai hayaƙin da ke fitowa daga hanci da bakinsa yana motsi kamar numfashi.
Madam Nablah ta daura hannunta biyu a saman madubin, ta lumshe ido, sannan ta fara karanto wani irin yare da ba a saba jin shi ba tana furta
“Naqaatu-t-Tilum... Sarwaqeen Al Jabaroot... Izran Tumma... Qadhaab!”
Sai wani ƙarin hayaki mai ƙanshi irin na jikin bil’adama ya turnuƙe madubin. A take, madubin ya fara juyawa, yana haska launuka dabam-dabam.
**
“Na ce ku bani haske... Ku bani abin hangowa! Ina son ganin wanda ya juya tsarina, wanda ya tsallake mutuwa! Waye wannan mutumin? Waye wannan da ke ɗauke da ikon da bai kamata ya rayu ba?”
A cewar Madam Nablah.
A hankali, madubin ya fara nuna hoton Amaar a kwance, yana magana a cikin zuciyar sa. Amma fuskar Amaar ta bayyana ne cikin duhu—madubin na ƙoƙarin hana Madam Nablah ganin cikakken fuskar sa.
Madam Nablah ta ƙara daka ƙara da cewa
“Ku buɗa min! Na mallaki ikonku! Na rage rayuka fiye da dubu, ba ku isa ku ɓoye min ba!”
Sai kuma wani murya mai zurfi ya fito daga cikin madubin, murya mai girgiza ƙwaƙwalwa ya furta
“Ba komai zaki gani ba… yana da kariya, wanda ba za ki iya keta ba.”
Madam Nablah ta ja da baya da sauri, hannunta na rawa, idanuwanta na ƙara huda da baƙin iska.
Ta ce
“Kariya? Waye zai iya kare wanda na hallaka?”
Madubin ya koma duhu, ya ɓoye komai. A take, idon Madam Nablah ya fara kadawa da alamar fushi. Ta juyo daga gaban madubin, ta buge wani kwano da ke gefenta.
“Wannan kuwa… bai mutu ba! Wannan mutumin da Tasleem ta harba… akwai wani abu da ban gane ba!”
Ta fara kaiwa da komowa a dakin, tana saƙar zare a cikin zuciyarta.
“Tasleem! Yarinyar nan fa ta fara juya ni. Sannu a hankali mafarkinta na zama gaskiya. Idan ba a hanzarta ba, zata zama babban barazana gare ni!”
Ta tsaya cak. Wani aljanin gefenta ya bayyana daga ƙungurmin inuwa. Ba shi da fuska mai bayyana kamar wata inuwa ce dake numfashi.
“Me kike so mu yi da ita?” – in ji muryar aljanin.
Madam Nablah ta kalli inuwar da ƙyam, sannan ta ce:
“Na shirya. Lokaci yayi da zan sake haɗa wani tsafi—wanda zai mantar da Tasleem komai. Sai dai kafin nan, dole na fara da wanda ya juya makirci na… duk da ban gane waye bane tukuna.”
Ta juyo gaban madubin tsafi, ta ce da ƙarfi:
“Zan tono shi da hannuna! Ko da kuwa daga ƙasan ƙasa yake…”
**
A wannan lokaci, Madam Nablah bata san cewa ƴaƴanta suna kusa da tono sirrinta ba. Amma sai dai wani abu yana yawo a zuciyarta—ana matsa mata daga wani ɓangaren da ba ta fahimta ba. Kuma ita kanta tana fara jin tsoron wani abu: ta fara jin ƙyamar zuciyar Tasleem.
Madam Nablah ta fito daga dakin tsafinta da takalman ta masu tsini suna kara-kara akan tiles din gidan. Fuskar ta cike da damuwa da kulle-kullen mugunta. Duk da bata iya ganin fuskar Amaar ba a cikin madubin tsafi, amma zuciyarta na kara tabbatar mata da cewa akwai wani