Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ƴar GOGGO Complete Hausa Novel by Sayyada

Author :  SAYYADA Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 3

3K to 6K   out of 8.1K words

nawani kurma ihu dango dayan karan yayi wani salle da"

"kadan yakamo kafata yadiro dani kasa , sai ga fadawan sarki suka shigo , suna duddubawa hangoni"

"sukayi asaman bishiya duk na rude , sukace kaiii aljana da rana saka !!! Lallai yau munyi gamo aiko da"

"gudu suka ruga sukayi gidan sarki , suka sanar da sarki wai sun kama aljana!!! Abunka da 'yan kauye sai"

"gasu acikin lambur da sarki da dansa yarima wai sunzo ganin aljana. Ina makale asama , su zeenatu ko"

tun yaushe suka ari na kare sukayi gida . Yarima Abdallah yace ke aljana mai bayyanuwa da rana mai sa

"kika zabi zuwa anan amasayin maboya , to kisani yau ni dan sarki yarima Abdallah sai na kasheki !!! Wani"

"uban ihu na daka danaga ansaitamin takobi dai dai kaina , nafado daga saman bishiyar ina 'yan uwan bil"

"adama wlh ni mutum ce kumin rai Gwaggo batasan nazo nan ba ,har kasa na durkusa. SARKI yace ku"

dakata gaskiya ne ba aljana bace kunganta nan . Yarima cikin izza da mulki yace to uban wa yashigo dake

"tanan kuma ta ina kikabi kika shigo ???? Duk da naji ya ambaci uba sai naji soronsa yafita araina nace ,"

kul Yarima akan mongoro zaka zagi ubana mai yamaka ?? Yace eh lallai mutum ce yayi wani sayuwa ya

wankeni da mari Na fadi akasa yace kafff kauyennan har akwai wanda zanmai magana ya

maidamin FADAWA sukace hattara dai yarinya . Sarki ya dakatar da yarima yace ke maisa kika shigo

nan ko dai abinki ne yafado kika biyo ki dauka . Nace karya haramun wlh ba ko daya yunwa nakeji kuma

naga kafin naje gida zan iya galabaita shine na hau ta wannan garun na diro dan insaka abakin

salati .wani kakkarfar ajiyar zuciya sarki yayi yana mamakin yarinyar . Yarima Abdallah yace nayi tunani

ba a hayyacinki kika shigo ba ashe dai mahaukaciya ce !!! Nace Ni ba mahaukaciya bace rasssss nake

"da hankali na gani nayi kun ajiye ku baku ci ba mu bakubamu ba , ga mabukata na so wasu su kwana da"

yunwa amman ku ko ajikinku . Yasake yunkurowa zai sake marina Sarki ya da katar dashi ta hanyar

daga mai hannu. Cikin bakin ciki ya saya yana kallona kamar ya shakoni Sarki yace kintabbata cewa

"mutan gari suna son abinda muka shuka amman basuda hali cira shine suka hakura , bayan ko wane"

karshen wata ina sawa acire buhu hamsin na kowane kayan itatuwa arabawa bayi da kuma mutan gari

"to ina ake kaiwa ?????? Yarima yace baba karka yadda da ita tayo karya take , dan na fuskanci batada"

cikakkiyar lfy . Nace tab lafiya ta lau gaskiyar kawai na fada . Jikin sarki yayi sanyi tabbass ana ha'inci

amman zaisa ido . Yace ke ´ar wacce unguwar anan kauyen? Nace ina layin Sabuwar namba . Yace wa

fadawa su debo min duk wani iya_iyan itatuwan da yakenan asamin a buhu arakani gida dan yamma

tafara . Sukace angama sarki . Haka akayi kuwa har gida suka kawo ni duk da magrib ya gabato amman

layinmu cike yake da mutane dankuwa sunji labari wai sarki ya kama deejee ankaini an kulle !!!! Sai ko

gani da fadawa har kofar gida aka ajiye min sukayi tafiyarsu . Na kwallawa Gwaggo kira tafito duk tashiga

"tashin hankali, tace deejee kece anan nawuni kuka nayi tunanin sun kasheki gashi badaman zuwa,"

Gwaggo harda kwalla !!!! Wani dariya na kece dashi nace kai Gwaggo mutuwa kuma ai da saurana dubi

"kiga ´ar yarinya dani , kingafa abinda sarki yaban . Gwoggo ta ce sarki usmanu ne yabaki deejee? Nace"

eh fah harda fadawansa suka rakoni . Yan gulmako sai zuwa suke wai ah deejee ta dawo innabasu lbr

"abinda yafaru sai su tsoke baki , zeenatu ma sunzo mukasha dariya abinmu nace musu kai wani nagani"

"wai shi yarima wlh kamar balarabi sai shegen mugunta , sukayi ta dariya har suka tafi ... ! Ina kwance da"

daddare kawai nayi mafarki ga wannan karnukan lambun mai gari sunyo kaina wani ihu na kurma !

"Agigice na farka na lallbo na kwanta kusa da Gwaggo, ashe dai tana jina tace"""" deejee yakamata yanzu"

kinutsu ita wannan rayuwar asannu ake binta kuma bakisan watarana a hannun wa danda zaki faWa ba

"tayo ki faWa a hannun muggan mutane , zasu iya cutar da ke . Nace Gwaggo ba abinda zaifaru amman"

bazan sakeyi ba .bayan sati da faruwar haka sarki ya aiko da kayan lambu arabawa kowa kuma abi har

cikin gida araba . Mutane sai sa masa albarka suke kuma har gida akazo ana jinjina min wai nayi kokari .

Haka dai rayuwa taci gaba komai yayi farko yana da karshe munkammala primary school namu

akaturamu Junior secondary School acen birni makarantar kwanace da gangan headmaster yayi

haka !kasa muka duka muna bashi hakuri ya janye amman fir yaki sauraronmu . Ina kuka na iso gida na

zube agaban Gwaggo inata zabga kuka harda burgima sai tambayata take amman naki shuru ballantana

"na bata amsa sai da tadau bulala na yi shuru na koramata bayani aiko tafini shiga tashin hankali, tace """""""

wai shi shugaban makarantar taku anya baya shaye shaye !! Ta yaya zai dau yarinya danya kamar haka

"ya kaita birnin kuma makarantar kwana ai bazata sakuba !! """" Bindiga a ruwa gobe zani wajensa sai ya"

jenye zacennan

"Washe gari sai ga Gwoggo a makarantar su deejee har office na head master ta shiga , tace hedmasti"

"wato wai sotake tace ( headmaster) kaiko me jikata tayi wanda yasa kayanke mata hukunci haka har gidan yari na shekara uku . Headmaster cikin soro da mamaki yace hala dai baki fahimci inda kike ba koh to nan makaranta tace ba office na yansanda ba ne . Tace eh nasani amman abinda kake shirya yinsa tamkar a offishin iyan sanda ne ..!! Yarasa abin fada kawai yayi shuru . Tace ya kai shuru ? Aransa yace this old woman she always disturb me ... Yayi ajiyar zuciya yace ummm mama what I mean wannan cigabane yazowa dalibanmu , a da makarantar wuni akeyi kuma hakan takurace ga dalibai saboda bamuna secondary School anan sai anje birni , ganesa ga kashe kudin mota shine gomnati ta taimaka akayi makarantar kwana ka ita ta dauki duk nawinsu ba abinda zaki siya komai ta tanadeshi harda gurin kwana kuma kowa da katifarsa sannan bangaren abinci , ana dafamusu sau biyu a rana kuma duk da haka ko wane karshen mako gomnati zata dinga kamusu abin makulashe da dai sauransu. !!!! Cikin jin"

farin cikin zancensa Gwaggo ta washe baki tace hedmasti har da kati fa kace dai jikata ta huta abinta .

She dai headmaster dariyar kawai yakema sai sambutu take Yace nan da sati biyu zasu tafi anan

makarantar zasu hadu da sauran daliban dankuwa motace zatazo ta kwashesu . Dajin haka Gwaggo tayo

gida cikin jin dadi Ina kwance naji Gwaggo na kwallamin kira nafito na taddata azaune akan taburma

tana dama fura tana cewa kaiii madallah . Nace Gwaggo incedai ya hakura da zancen tafiya karatu birni ? Tace a'a deejee tafiya ai tazama dole danko abin daga gwamnati ne ba daga shiba Ta kwashe duk

yadda sukayi da headmaster ta fadawa deejee duk da haka deejee batayi wani farin ciki ba dan bataso tayi nesa da Gwoggo dan babu mai taimaka mata tace shikenan tunda haka abin yake. Gwoggo

tazubamin damammiyar fura nafarasha ina santi !!!!!

Ana washegari su deejee zasu je birni ! Gwoggo taje kasuwa ta sayo dutsen goge kaushe da wata sabulu

"HALA SOAP ita wannan hala soap a KUKAWA amarene maso anfani da ita dun suyi kyau wato dai ita HALAN . Acwar Gwaggo kar gomnati ta gane mata deejee da dauWa ta koraota! Aiko su deejee anyi awa uku ana goge kafa !! Gwoggo na saye akanta tana gani intakamama ta tayata ! Saida kafar tayi wani ja dan durza sannan aka kyaleta. Gwoggo tace to sai kuma wanka ki tabbata kinyi da kyau ! Awankanma anyi kusa awa 2 harda omo akayi wankan da tayi kyau ... Tunda deejee tafito Gwaggo tazuba mata idanuwa tana tuna abunda yafaru shekaru goma sha 12;da suka shuWe !! Irin mummunar ta addin da akaso aikatawa ... Wasu kwallane suka ciga idon Gwoggo! Deejee tace lfy kuwa Gwaggo kamar kwalla kike shirin zubdawa ko dai tafiya ce baki so ? Gwoggo tayi murmushi tana karewa jikar tata kallo tayi wani haske da tayi wankan Amare dama deejee farace kal , tana da dan sawo bata da jiki , gashi kam har yaimata yawa duk da ba wani samun gyara ake ba , hancinnan kamar zai shige baka ! Gwoggo tace kawai dai mamaki nake ashe dai deejee tawa kyakkyawace... Deejee sabar dariya da jin dadi ta kusa faduwa kasa . Tace kai Gwaggo ai wannan sabulunce da omo yasa nayi haske .. wasu kayantan ta nasallah tasaka acewarta daga gobe na daina sanyaku , har bacci ya dauketa . !!! Gari yana wayewa ko karin kummallo basu saya yiba sukai gidansu zeenatu dan suwuce har makaranta Gwoggo ta rakota tananan saye sai da"

"taga tashin motarsu kamin ta koma gida ! Gwoggo har da zubda kwalla gani take anrabata da deejee. !!!!! Nima ( Sayyada) harda iyar kwallata narasa wazabi deejee ko Gwaggo!!! Kai garadai nabi deejee birni , wata mota nagani irin na masu saidai itace na haura nace mubi bayan motarsu deeje dankar suSacemin da gani mukayo birnin amman kashh na nemi motarsu DEEJEE na rasa sana diyar wata motar"

da tayo kanmu kamar zata bigemu ta wuce nace kai mubi waccan motor sai naga waye aciki .

BIRNI

Dai dan wani katafaren shop motar tasaya !!!! Wani hadadWen saurayi nagani wanda bai wuce 27yrs ba

"yafito daga mota farine kal , da wani kwantaccen gashi kansa kamarna larabawa yana da sawo bashi da kiSa , sanye yake da wata shadda kana ganinta kasan ta taci NAIRA dankin have jampa akayi wani farin glass ne a idonsa , daga gani dai kasan wannan daga cikin daula yafito .mabiya bayansa nagani sunshige cikin shop din suka sanar Ga YARIMA MAHEER yashigo kowa yafita zaiyi siyayya!!! Bai fi mintina ba sai naga kowa fitowa yake jiki na kyarma akasaya daga gefe ... Sannan yafara takunsa cikin izza da takama dan MAHEER akwai ji da kai baison raini Yashiga shop din sai da yagama siyayyar yafito kaminnan"

naga mutanen da suke waje suka fara kusa kai cikin shop din dan su kammala nasu siyayyar. Inanan

MAHEER yaja motarsa da masu mara masa baya sukabar haraban wajen ... ( Nace tab baza abarni

abayaba sai naga ina MAHEER zaije sannan dan wani hamshakin mai kudine haka . Wani dan sahu na hau nafara binsu MAHEER abaya. ) To kuma kubiyoni danjin wai maike faruwane abirni sannan waye

wannan MAHEER din da alamu dan masu fada ajine tunda har zai iya fidda wasu yayi uzurinsa.

REST HOUSE nasa yawuce yana shigowa kai saye dakinsa yawuce ya tadda ta akwance da ita sai wani

"have_vest da gajeren wando iya cinya bai kulata ba yayi toilet ya wasa ruwa, yafito daure da towel a kugu da wani ™aramin ahannunsa yana goge jikinsa da shi tasowa tayi cikin tata salon ya rungume sa ta baya , cikin hanzari ya da katar da ita yace bana sallameki ba ! Mesa baki tafi ba cikin cool voice yake maga danshi baya son hayaniya..... Tace I need Yadakatar da ita dacewa get out kinsan ni bana sex sai"

romance So is better for you ki tafi sai na nemeki . Sayawa tayi tana kallonsa da kananun idanuwanta wanda suka cika da sha'awar sa tarasa yadda zatayi kuma tasan halinsa abinda take nema bazata samuba . Yakammala shirinsa yajefa mata bounch na kudi yace kada na sake kallonki ! Tadau kayanta tamaidasu jikinta tai gaba . Waya yadauka yace kashigomin da ita Wata kyakkyawar budurwa akashigo

"da ita yasaya yana kare mata kallo """" cikin soro tace dan Allah kabarni intafi """" taku yayi a hankali har zuwa kusa da ita yace na kiraki shene kika gudu amman danasa yarana suka daukoki ta karfi shine zaki ban hakuri to kisani sai nagama duk abinda zanyi zaki tafi inkuma bansami yadda nakeso ba anan zaki kwana """" jikinta yafara k´arma cikin e""e""na tace ka. kaaa rufamin asiri wlh bansani bane na hankadeka"

"kamin rai Sai ta fara kuka """" cikin Cool voice nashi yayi murmushi irinma mugunta yace kina tunanin"

zan kyaleki ne ? Gyallenta ya zame daga jikinta yafara shafa gashin kanta yace ummm you look pretty but bakya kamshi jikinta sai rawa yake aranta ta ce yau ba mai kwatanta ahannun sa kayanta yafara

cire mata amman tayi saurin dakatar dashi ta hanyar masawa baya da taiyi Yasakeyin murmushi ya ce

"ummm da alamu anan zaki kwana ko """" cikin rawar murya ta ce a'a ka kyaleni intafi janyota yayi suka fada kangado cikin karfi yarabada da kayan jikinta , ganin surar jikinta yasa ya fara fita daga hayyacinsa, murya na rawa yace Do you need money ? zanbaki duk abinda kikeso . Kuka tafara tace a'a banason komai ni kabarni intafi . Yaga dai zata bata masa lokaci yafara luguigitata iyanson ransa . Da farko yarinya ta sorata a tunaninta fyade zai mata amman sai taga shi nema kawai yake yasami nutsuwa da ita ! Yaringa wasa da ita har yasami nutsuwa , ya mirgina gefe yana haki kamar wanda ya nome rabin gona . Yace ga kudi agaban mirror ki dauka ki tafi , cikin sauri ta maida kayanta ta dau kudin ta fice . Yaci gaba da baccinsa . Yana farkawa ya tuna kiranda mahaifinsa ya masa ya hanzarta ya shirya yafito yace wa driver ka kaini gida .... Bai bata wani lokaci ba sai gasu a wani haWaWWen gidan sarauta , wani babban gate akabude WOW ( abinda nace Ni Sayyada ya zanyi inshige ? Nayi dabara na kwanta ta karkashin mota akashige dani cikin dan baku lbr ) dafarko nace anya a duniya nake sai da na nutsu kamin na fahimci ashe dai a duniyar nake """""""" MAHEER ne ya fito daga mota bayan masu saronsa sunbude masa murfin muta cikin tafiyarsa ta jinin sarauta yake taku Kai saye fadar mahaifinsa ya nufa , yanashiga"

"fadawan sarki suka mike saye suna BARKA DAI YARIMA!! Hannu kawai ya daga musu ya durkusa har kasa yana gaida maimartaba sarki Ahmadu . Sarki yace MAHEER ankamin labarin unguwar da suke nan gabas damu suna cikin mawuyancin halin rashin ruwa, dan haka kai zan daura akan kula da harkokin wajen sai"

"ayi abinda yadace , cikin girmamawa yace insha Allahu baza asami masalaba za ayi komai akan lokaci."

"Tashiwa yayi dakin kakarsu yanufa , tanajin motsi tafara magana waye wannan sandarta ta dauko tana"

"nunasa dashi alamun kar acutar da ita , yace kai tsohuwa akwai ki da soro to nine MAHEER jikanki . Tace lah kacemin marajinnan to kashiga taitayinka dama kamin laifi , ka hanani waccan turaren mai dadi da naji ka fesa . Yace kai diddi ke da kika kusa gangarawa kuma wane turare za'a siyamin sai dai ko na shafawa a likkafani ? Haba ´ar sohuwa harda kuka , ni zakace zanmu to ja'iri sai dai kai kamutum mara mutunci . Yace haba diddi wasa da nake . Tace sam sai yafita hakanan yafita a hanyarsa ta wucewa dakinsane yayi arba da dan' uwansa Abdul Malik wanda MAHEER yafishi da watanni bakwai. Kuma dan kishiyar mamarsace wani harara Abdul Malik yayiwa MAHEER ya wuce . Murmushi kawai yarima MAHEER yayi yashiga dakin Hajjiya umma mahaifiyar Abdul Malik har kasa ya duka ya gaidata amman ko kallo bai ishetaba ballantana ta amsa cikin sanyin jiki yafice inda sabo ai yasa tunda mahaiyarsa ta rasu"

yarasa gatan uwa .

"Kai saye motar ta dire dukkanin dalibai a farfajiyan makaranta deejee na hango , deejee nafito sai murna"

"nake nazo birni , wani hoste aka kaimu ! Ba laifi dakin yayi kyau babban dakine maidauke da gado mai hawa uku har guda hudu abinda baimin dadiba shine rabani da akayi da su zeenatu dan a dakin ba wacce nasani . Kayana nafara jerawa a lokata ina kammalawa nahau lafiyayyen gadona na kwanta ni ce ta hawa na biyu na kwanta abina . Wani bacci nadingayi harda munshari abinka da babu a house. Jinayi an makeni a bayana har sau uku ina tashiwa cikin gigin bacci nima na wanketa da mari !! Wasu nagani atare da wanda na mara sukace keee headgirl kika mara yau zakici kol ubanki ! Wacce suka kira da headgirl danni bansanma me ake nufi da hakanba dan turanci ba sonsa nakeba , tace kufitomin da ita ku kaita daning nidai ina biye dasu har daning mukashiga wani babban madafar abinci nagani tukunyar sai mushigeta da gani har headgirl nasu ciki . Tace inwanke tunkunyar kuma yanzu za a daura abincin dare kuma intabbatar tafita tayi kyau ko tabbare karta gani . Sayuwa nayi nace tabbbb tukunyar da ko iya sauketa ba ayi da alamuma amanne take tab bazanyi ba kuma wama yace mata bauta nazo yi ni"

"karatune , duk wannan zancen zucine !!!"

"Taku nafara da nufin barin wajen sai suka jawoni na dawo da baya , wai sai na wanke zanbar wajen ,"

"nace bayin Allah!! bansanku ba , bansan daga ina kukeba , sannan ba wata alaka asakanina daku yau fa na fara ganinku amman sai kudauki kiyayya ™arara ku nunamin . Yanzu sakaninku da Allah ko ku akasa ku wanke wannan jibgegiyar tukunyar nan ba iyata za ku ba dan haka nima bazan iya ba . Wacce ake kira da headgirl ce ta dau hannu zata mareni na rike nace kuttt wlh ba'ayi kiba sabo da cin zali hadda mari , dambe muka fara yi na zage dantsibsai nausansu nake , wai akace gidan yawa yafi

2 / 3