SANADIN KENAN 1 HAUSA NOVELS BY TAKORI.doc

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   7 / 10

18K to 21K   out of 27.7K words

ta gurfana tana bai wa Goggo hakuri,
 Na yi miki alkawari Goggo, duk wanda ya fara zuwa yanzu zan ba shi dama ya fito ba zan kara korar kowa ba .
Sai a sannan ne Goggo ta sauko, ta daga hannu sama ta ce,
 Ya Allah ka kawo wa Aminatu miji na gari alfarmar Alqur ani .
Wani ikon Allah kuma sai dif! Maneman suka dauke kafa, babu su babu alamarsu, har Amina ta tafi hidimar kasa jihar Gombe..
To duk wanda ya zo, in ya ji cewa Amina cikakkiyar likita ce, sai ya ga ta fi karfinsa ya cika bujensa da iska.

*** *** ***
Bayan Amina ta kammala hidimar kasa, an rarraba su asibitoci da dama, da taimakon Dr. Turaki aka bar Amina a ATBU Teaching Hospital, Dr. Amina Mas ud Shira ta fara aiki a  physiotherapy department cikin kawarewa da sanin makamar aikinta.
****












Maballan  suit din da ta sanya masa ta ke ballewa, a tausashe kuma tana yi masa hira, ta dauko  necktie mai ruwan makuba ta zarga masa ta ja ta matse tana fadin,
 Ba ka ga yadda ash (ruwan toka) ke karbarka ba Baban Amina, ya kamata mu shiga gasar (handsomes) ta duniya, saboda har tafiyarsu ka iya, matsalarka daya rashin fara a, kullum handsome fuskar nan a cikin seriousness, zan yi rantsuwa ban yi kaffara ba, idan nace ban da Amina ba wanda ke ganin dariyarka, ko ni albarka& ...
Bai san sanda ya yi dariyar ba, Aisha will never cease to amuse him (Aisha ba za ta bar sa shi dariya ba kullum), mace ce ta gari da kowanne namiji ke burin samu, idan har samun mace ta gari shi ne cikar rabin addini yana da yakinin cikar nasa rabin addinin. Ya kama karan hancinta ya ja kadan,
 Kin ga malama yi sauri ba na son shirme, flight dina to Abuja karfe sha daya na safe zai tashi, don ba ni da yadda zan yi da ke ne zan barki da Ameena ku taho a mota. Ni rasa me ye abin tsoro a jirgi, matsoraciya kawai .
Aisha ba ta yi magana ba, ta dauko masa (briefcase) dinsa. Ita dai tunda Ubangiji ya halicce ta ta ke tsoron hawa jirgi, ga ta dai ba haihuwar kauye ba, ko wani abu makamancin haka, it happens by nature.
Akwai lokacin da maigidan ya takura mata don ya zama dole, umrah za su je bayan aurensu, zuwa dakin Allah ya kori komai ga kowanne musulmi, don haka Aisha ta yi shahada ta hau jirgi, suka nabba a a mazauninsu, bayan sun sanya  belt . Da jirgin ya yi kururuwa ya karci kasa ya luluka sama, Aisha ta rungume mijinta ta runtse idonta, sai jini ya kece kamar an yanka rago, cikin watanni uku ya fice.
Tun daga lokacin bai kara takurawa Aisha wajen hawa jirgi ba. Shi zai bi jirgin, ita ta bi mota su hade a inda za su je. Fita kasar waje kuwa ba ya daga cikin al adun rayuwarsa, ba ya zuwa kowacce kasa duk da arzikin da Allah ya yi masa ban da Saudi-Arebia. A cewarsa bai ga me zai je ya yo ba ban da asarar dukiya, duk abin da muke nema na jin dadin rayuwa muna da shi a kasarmu mai dumbin albarka.
Mutum ne mai girmama kasarsa da son yankinsa (Arewa) kwarai da gaske. Bai yi kowanne irin karatunsa a kasar waje ba. Bayan kammala sakandirensa a (Science College D/Tofa) ya wuce jami ar Ahmadu Bello, inda ya nazarci  Civil Engineering .
Ya fita da digiri mai daraja ta farko, bayan kammala hidimar kasa bai bata lokaci ba ya koma jami ar ya hado digiri na biyu..

Bai fito daga gidan masu hannu da shuni ba, ko gidan wasu masu fada-a-ji, dan talakawa ne likis, mahaifinsa Malamin makaranta ne, inda mahaifiyarsa ta kasance mai sana ar kiwon dabbobi. A haka ya rayu cikin wahalar karatu. Da ta abin amfani har Allah ya sa ya kammala.
A wancan lokacin, karatun boko bai zama yadda ya zama yanzu ba, gwamnati neman masu zuciyar yin karatun ta ke kawai ta tallafa musu. Don haka zai iya cewa matsalolin da ya ci karo da su a zamanin karatunsa ba masu yawa ba ne, ban da nisan gari da gari da yake a tsakani. Amma har alawus na abinci iyaye ba su faya wahala a kai ba, gwamnati na yi musu.
Yana dan shekaru uku mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa, a dalilin ya auro wata, don haka ba ta barshi a hannun matar Babansa ba ta dauke shi ta tafi da shi wani kauye a Jihar Jigawa, inda kanwar mahaifiyarta ke aure. A can ya yi firamare ya gama, da ya isa shiga sakandire ta samu miji a can ta yi aure, shi kuma ta maido shi hannun mahaifinsa, ya dauke shi ya kai shi makarantar sakandire ta kimiyya da ke Dawakin Tofa, daga wancan lokacin ya ci gaba da zama hannun mahaifinsa har ya shiga jami a.
Matar da yake aure din mai suna Luba, ta dauki tsangwamar duniya ta dora masa saboda ita Allah bai ba ta haihuwa ba, tana kishin kaunar da mahaifinsa ke yi masa, komai ya samo a kansa yake karewa.
To zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ga muzuru, ana ga shaho sai ya yi. Bayan kammala digirinsa na biyu ya ci gaba da zama da mahaifinsa, har ya samar masa aikin koyarwa a sakandiren da yake aiki.
Watarana da yamma yana karanta jaridar (Daily Trust) ya ga wani kamfani na cigiyar (Civil Engineers) masu matakin digiri na biyu. Kamfani ne da ke karbar kwangilar ginin tituna, gidaje, asibitoci, gadoji, Dam, titin jirgin kasa da sauransu. Ya dauki adireshinsu na (Fax) da (post office) wadanda da su ne ake amfani wajen sadarwa a wancan lokacin. Ya rubuta (application) ya hada da photocopy na takardunsa ya aika musu. Ya ci gaba da harkar koyarwarsa bai kara tunawa da zancen ba.
Kusa da gidansu da ke unguwar Yelwa gidan Alh. Mansur Maifata ne, mutumin yana da rufin asiri sosai, don duk unguwar babu mai sukuninsa, duk  ya yansa mata ne ta ukun ita ce Aisha, ya sha ganinta tana wucewa in yana kofar gida yana karatun jaridar da ya zame masa taba, in bai karanta  Daily Trust kullum ba, ya ji halin da kasarsa ke ciki ba, jinsa yake kamar mara lafiya.
Kullum yarinyar ta wuce sai ya bi ta da kallo, shi ba ma abocin kula mata ba ne duk da dalibai mata yake koyarwa, amma bai san me ya sa duk ranar da bai ga wucewar Aisha ta gabansa ba, sai ya ji wata irin kewa. Ya kura wa kofar gidansu ido ya yi ta Allah-Allah ya ga giftawarta.
Aisha Mansur, ba wata kyakkyawa ba ce fiye da  yan uwanta ba, amma duk ta fi su nutsuwa da kwarjini. Bai taba ganin ta tsaya da wani namiji a kofar gidansu ba kamar sauran  yan u??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wanta, abin da bai sani ba shi ne, ko an aika ba ta fitowa sai dai saurayi ya gaji da tsayuwarsa ya tafi.
Baban su Aisha na matukar kokari a kan tarbiyyarsu. Shi dai bai taba yi mata magana ba, haka ita ma. Amma ya lura in ta dawo daga islamiyya ta wuce shi, ya bi ta da kallon da ya saba binta da shi, in ta kai kofar gidansu sai ta juyo cikin dabara ta kalle shi, sannan ta wuce. Sai ya yi murmushi ya maida kai ga jaridarsa.
Ranar da ta lura ya kamata tana kallon inda yake, da gudu ta shige gidansu.
Murmushi ya yi, ya ci gaba da karatun jaridarsa, ya rasa me ya sa yake jin yarinyar a ransa. Ko sunanta bai sani ba.
Ranar wata juma a suna zaune a kan tabarma a kofar gida shi da Babansa, suna cin tuwon dare a kwano daya, daya daga cikin ma aikatan gidan Alh. Mansur ya zo ya gaida Baban, ya kuma sanar da shi Alh. Mansur ne ya aiko shi ya sanar da shi zai zo ganinsa karfe tara na dare.
Baban ya ce,  Allah ya kawo shi lafiya .
Bayan sun gama cin abinci sun wanke hannu da ruwan butar alwala, Baban yake janshi da hira, don ya san in ta dan nasa ne, to a zauna a haka awa uku baki a rufe, ko kowa ya dauki jarida ya karanta.
 Ni wai cewa nake wata mai zuwa za ka cika shekaru ashirin da bakwai ne?
Ya yi dan lissafi, ya ce,  Eh, Fabrairu insha Allahu .
 Kuma ba ka da niyyar aure ko? A da in an yi magana ka ce karatu, hidimar kasa, aiki, yanzu wanne ne ya saura?
Ya yi dan murmushi bai ce komai ba.
 Daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri, ba za mu kasa rike mata ba. Albashinka ya isa ka ciyar da iyali, ga gidan nan babba ne na ja maka katanga na ware maka muhalli, me kuma ya rage?
Ya yi  yan mutsu-mutsu na rashin abin cewa, domin ba shi da hujjar da zai bayar, kuma ba zai iya fada wa Babansa abin da ke ransa ba, ganin abin ba mai yiwuwa ba ne.
Inda Allah ya kwace shi daga titsiyen Baba shi ne, isowar Alhaji Mansur Maifata. Turarensa mai dadin kamshi ya baibaye su, shaddarsa har walkiya ta ke. Ga damanga ya kafa, wadda a da babu masu sanya ta sai masu hannu da shuni. Ya ba su hannu dukkaninsu, Baba ya ba shi wurin zama, shi kuma ya yi musu sallama ya tashi ya ba su waje.
Bayan gaisuwa da tambayar iyali, Alhaji Mansur ya gyara murya,
 Wato Malam Habibu, abin da ya kawo ni neman alfarma ne, na neman iri. A zaman shekaru ashirin da muka yi tare na yaba da halayenka, da tarbiyyar da ka ba wa yaron wajenka. Ga ilimi mai kyau da ka tsaya tsayin daka ya samu, ban taba jin an ce yau ga abokin fadansa ko ga wani hali na banza da aka same shi da shi ba. Wannan ne ya kawadaitar da ni in neme ka mu hada iri, in har ka amince.
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya hore mu da mu nema wa  ya yanmu mazan aure na gari a aurensu na fari. Duka yarana na ba su dama su zabi mazan aure da kansu su uku manyan, Aisha ce kadai ban bai wa wannan damar ba, a dalilin ita marainiya ce, mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwarta, ta sha wahala a hannun matana, ina so ta samu kwanciyar hankali da sukunin zuciya a gidan aurenta.
Ba wanda zuciyata ke kawo min kullum, sai hoton MA AROUF dan wajenka, shi ne na yo tattaki in nemi wannan iri mai albarka. Ba na bukatar komai sai sadaq (sadaki) da Allah Ubangiji ya yi umarni. Amma idan Ma arouf bai amince ba, don Allah kada hakan ya yi sanadiyyar da gaisuwar makwabtakar da muke yi da juna za ta tawaya, kuma kada a takura masa. Abu ne dai da nake da yakini a kai ba zai samu matsalar komai da Aisha ba, saboda ko cikin  yan uwanta ta fita daban wajen hankali da kyakkyawar tarbiyya .
Malam Habib ya ja numfashi ya sauke, ya dubi Alhaji Mansur cikin murmushi.
 Wato dauki ne Allah ya kawo mini ina zaune a kan tabarma ta. Wallahi Alhaji tashin nan da ka ga ya yi zancen da nake yi masa ke nan, a da in na yi ya ce karatu, hidimar kasa, project, masters. Amma a yanzu babu ko daya, bai dai kai ga ba ni amsa ba ka zo, amma na san ba zai ki abin da na yi masa umarni ba. Sai dai kamar yadda ka ce, ba zan tursasa shi ba, zan ba shi zabi ba umarni ba.
Duk da haka wani hanzari ba gudu ba,  yar wajenka Aishatu ka ce sunanta ko? Za ta iya zama a wannan muhalli da Allah ya hore mana? Domin dai yatsun ba daya ba ne, kuma babu karya ko yaudara a tsakaninmu .
Alhaji Mansur ya yi murmushi,  Ko a bukka ne cikin jeji na yi wa Aisha aure za ta zauna. Ina tabbatar maka da wannan. Tana da gida nata na kanta da ta gada daga mahaifiyarta, amma a gidan mijinta za ta zauna ko ya ya yake. Don haka kada ka kara wannan tunanin .
Suka yi musabaha suka yi sallama, cike da aminci ga juna, Alhaji Mansur ya tafi.
Saboda farin ciki Malam Habibu da kyar ya bari garin Allah ya waye suka tafi masallaci sallar asubahi, da suka fito tun a hanya yake gaya masa yadda suka yi daren jiya da Alhaji Mansur.
Shiru ya yi kamar mai tunani, jinsa yake kamar a kan gajimare, yana shawagi don farin ciki. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, bai tabbatar cewa ita ba ce. Su hudu ne kuma bai san sunan kowacce ba. Baba ma bai sani ba, balle ya tambaye shi, yadda Baba yake murnar nan ba zai iya tula masa kasa a ido ba, kawai sai ya yi kundumbala ya ce,  Idan ita yarinyar ta amince ni ma na amince .
Baba ya kama hannayensa ya rike cikin nasa, yana ta sanya masa albarka.
Baba da kansa ba aike ba, ya je ya sanar da Alhaji Mansur amincewar Ma arouf wa auren Aisha. Gadan-gadan suka shiga shirye-shiryen auren shi da Alhaji Mansur. Ta fannin Baba, ya sa an yi fenti na farar kasa a sassan da ya ware wa dan tilon dan nasa, aka yi shafe na sumunti, daki ne ciki da falo matsakaita sai wani falle daya a gefe. Falle dayan Ma arouf ke zaune ciki matsayin nasa, ciki da falo aka bar wa amaryar, sai makewayi guda biyu, na wanka daban, na bayan gida daban, sai  yar rumfar kwano da aka bari matsayin madafi. Tsakar gidan ya sha sumunti fes gwanin sha awa. Gidan sai kamshin sabon fenti yake yi mai dadi.
 Yan uwanta uku Khalisa, Halima da Zainab sai rawar kai suke wajen hidimdimun biki, ita kam a sanyaye ta ke, ko can ba shiga sha aninsu ta ke ba saboda ba ta da wannan kuzarin (power). Ban da iya shege ba abin da suke mata, wai Baba ya ba da sadakarta wa malamin makaranta. Ko lefe ba a yi mata ba. A zuciyarta cewa ta ke,  Ai gara zama da malamin makarantar da zama a gidan da ko dariya ban isa in yi ba, gara zama da malamin makaranta da zaman gidan da ban taba farin ciki a cikinsa ba, tunda aka haife ni. Gara zama da malamin makaranta da zaman gidan da ba ni da  yanci. Ya Allah ka sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ni .
Duk abinda Alhaji Mansur ya yi wa sauran  yan uwanta shi ya yi mata a dakunanta, amma dole aka koma da wasu kayan saboda babu wajen sanyawa.
Aka daura aure lafiya da mafi kankantar sadaki, kafin nan ya je sau biyu domin su fahimci juna a bisa umarnin iyayen, sam ta ki yarda ya ga fuskarta, cikin hijabin islamiyyarta ta ke daga sama har kasa. Ta dai gaishe shi da  yar siririyar muryarta, shi kuma ya rasa me zai ce mata. Sai suka zauna shiru. Da shirun ya ishe shi ya bude jarida wadda ke tule a kan wani tebir na falon kala-kala, hakan ya sa ya gane falon Babansu ne. Da ya ga dare ya yi, sai ya yi mata sallama ya tafi. A ransa ya kudurce ko kuturwa ce zai zauna da ita a haka, in har hakan zai sa Babansa farin ciki. Wanda ba abinda bai yi masa ba a rayuwa.
An yi biki lafiya aka kai amare dakunansu.

*** *** ***
Wani irin zama ake yi tsakanin Ma arouf da mai dakinsa Aisha, kowa na dakinsa, ko da ta fito yin wata sabgar ta ji motsinsa zai shigo, ko zai fito daga dakinsa komawa daki ta ke sai ya fita, ko ya shigo ya shige nasa dakin. Ga shi an kawo ta da gara don haka ba ta bukatar komai daga gare shi, shi kuma kullum zai tafi aikin koyarwarsa sai ya ajiye mata kudin cefane a kasan kofar dakinta yadda tana budewa za ta gani.
Baba ne ya samar mata almajiri kullum yake zuwa ya yo mata cefane, da aike in ta yi girki ta zuba masa. Amma ko sharar tsakar gida ba ya yi mata, ita ta ke tsabtace abinta ciki da bai dinsa.
Aisha ta samu kanta cikin wani irin kwanciyar hankali wanda ba ta taba samu a gidansu ba, sai tsangwamar matan uba da  yan uba, kawai don Babanta ba ya iya boye kaunar da yake mata. Tuni ta murmure, kyanta ya soma fitowa. Ta yi kiba, ta yi (fresh) da ita cikin watanni uku. Da kuwa kamar sillen kara aka kawo ta, ga cima mai kyau da tafi ta gidansu. Sammata abinci ake a gidansu kamar an zuba wa karamin yaro, a nan kuwa ita ta ke dafa abin da ta ke so ya ji kifi ko nama, saboda kudin da Ma arouf ke ajiye mata kullum ya fi karfin cefanen rana daya, haka ta ke ta tara ragowar a ranta ta ce, banki zan saya in yi ta tara masa abinsa.
Wani sabon salo, sai Inna Luba matar Baba ta soma zagayowa wajen Aisha in sun fita aiki. Ita Aisha ba ta san halin Inna Luba ba, da zuciyarta daya ta ke girmamata, in ta yi girki kullum sai ta zuba ta ba wa almajirinta ya kai mata, tunda mijinta bai ba ta iznin ta dinga fita ba.
Ta zauna ta sa Aisha a gaba ta yi ta surutun banza da wofi tana bata Ma arouf a idonta, tana fadin ba abin da ba ta yi masa a rayuwa ba tun yana jariri, amma ko gaisuwa ba ta isa ya yi mata ba. Musamman da ta lura ba abin da ya taba shiga tsakaninsu. Tana tsoratar da ita akul ta shiga turakarsa ko ta bari ya

7 / 10