SANADIN KENAN 1 HAUSA NOVELS BY TAKORI.doc

Author :  sumayya Abdulkadir Takori Category :  Romance

Chapter   2 / 10

3K to 6K   out of 27.7K words

dattijai masu tsoron duniya da abinda ke cikinta ya zo. Itama tana yarda da abinda suke hangowa kawai tana kare kanta ne don tana son yin aikin ko burin data ke dashi akan Goggo ya cika. Ba tana son yin aikin bane don taje taji dadin rayuwa ko makamancin hakan, zata cika alkawarin data taba yiwa Goggo ne tun tana kankanuwa.
Goggon da bata yi karatun zamani ba, amma ta tsaya (against all odds) ta samar dashi gareta, ta cika mata burin ta, har gashi yau al umma na amfana da ita, ya zame mata hanyar samun abinci na har abada, ya zama silar samun hanyar dogaro da kai a gareta.
Kullum ta dauki albashi cikin asusun ta sai ta tuna babanta,
 Ina ma kana raye Baba? In rashin kudi ne yasa ka sha wahalhalun da ka sha a rayuwarka, yau ga kudin na samar maka bani da abinda zanyi dasu. Don haka zanyi komai da gumi na don Goggo taji dadi a karashen rayuwarta.
Ilya ya shigo ya zauna gefe  Wai me kuke tattaunawa ne ana gani na aka yi wani gumm?
Goggo bata tanka ba, don ta san shi sarai, muddin ya ji akan aikin wa ake wannan takaddamar Amina tayi nasara ta gama. Don kaifin bakinsa sai yafi na kowa. Inna Zulai da batasan hakan ba ta soma harhada masa dan abinda ta fahimta.
 wai Gwamna Ji-qas, ke son daukar Amina aiki ta kula da diyar sa mai shanyeyyen jiki, amma dole sai ta koma gidansa don ya rabo yarinyar daga gadon asibiti, zai dinga ninka mata albashin ta na asibiti sau hudu duk wata. Goggo ta kasa amin...... Ilya ya kasa tsayawa yaji karshen zancen nan yayi tsalle ya dire yace  kan uban nan! To shine kuka sa Dr. Amina a tsakiya kuna son yi mana sagegeduwa? To ke Amina yanzu wai me kike ce musu sun ki yarda? Goggo in wannan damar ta wuce Amina anya kin yiwa kanki adalci ganin irin wahalar da kika ci da jikinki, lafiyarki da aljihun ki kamin Amina ta zama likita? In tambaye ku, ina ruwan Ji-kas da Amina don ya dauketa aiki cikin gidansa, ance muku bashi da mata ne ko manemin mata ne? To in silar hakan ne Allah zai baiwa Amina miji sai ku sa kafa ku shure alherin Allah? Kai ban taba jin Goggo kin bani takaici irin na yau ba, kin biyewa Inna Zulai kifin rijiya kuna ta bata yawun bakinku akan alherin da yazo har gida ya same ku.
Shin wai ance muku Amina itace kadai likitar kashi a jihar Bauchi? Don kun samu Allah ya zabo ta cikin dubu ya bata shine zaku tsaya kuna kasa ta akan faranti tana lallashin ku tana muku bayani kuna dojewa? Dr. Amina, adana yawun bakinki zai yi miki amfani a gaba, barni dasu. Ku gayamin duk abinda kuke gujewa na shigar Dr. Amina gidan gwamnati. ..... .
Amina banda dariya ba abinda takeyi, Goggo da Inna sun kirne fuska sai jifansa suke da harara. Shi kuwa ya kai hannuwa ya harde a kirji ya mike kafafu a dole jira yake su bashi amsa. Goggo tace.
 Sannu uban mu. Matse baku nan mu sai mu gaya maka abinda muke gujewa din na zuwan mace babu aure wani waje ta kwana . Ilya ya gyara zama ya gyara murya.
 A inda babu Uba, komai kankantar namiji Uba ne. Don haka ni Ilya uban Amina, na amince diya ta Dr. Amina taje aiki gidan Engnr. Ji-kas.
Da take kwana a asibiti binta kuke? Kai ni ba don kar ace nayi rashin kunya ga Iyaye ba da sai ince ban taba ganin gidadawan mutane irinku ba. Ana kiranku gidan Gwamnati kuna cewa ba zakuje ba.... .
Goggo ta dauki kwanon silva a gefenta ta jefe shi da shi, Inna Zulai data fi kusa dashi ludayi ta kaiwa bakinsa ya kauce. Amina tace  haba Yaya Ilya, maimakon ka gyara ka tayani lallashin su duk ka kara damalmala al amarin. Goggo kuyi hakuri, nidai na gaya muku akan aikina zan je gidan Gwamna don wani kebantaccen uzri dana ke dashi akan ki Goggo. Amma in baki amince ba na hakura Goggo, zan je na samu Dr. Turaki gobe in fada masa ban samu amincewar ki ba .
Jikin Goggo yayi sanyi. Ta san Aminan ta har ga Allah batada kwadayi, bata nemi komai ta rasa ba, Amina gudun maza take ba son kai kanta garesu ba. Amina na son aikinta fiyeda komai a rayuwarta. Ta sha gaya mata yana sanya mata nutsuwa, yana sa ta nishadi, yana sa ta farin  ciki yana rabata da damuwa.
Duk ta yarda da wannan, kawai dai burin ta a yanzu Amina tayi aure shine kwanciyar hankalinta, ba wai bata son ta da aikin ta bane. Kuma ta yarda yanzu Amina bata korar masu son ta sune suka dauke kafa.
Goggo Hauwa ta nisa ta dubi Amina, Zulai da Ilya masoyan su na gaskiya da duk suka zuba mata ido. Kowannensu ta bakinta yake son ji don a yanke maganar haka kowa ya huta.
 Amina, na yarda kije aikin  yar Gwamna amma a bisa alkawari guda daya .
Amina ta dago da nutsuwa akan kyakkyawar fuskarta,  wane alkawari ne Goggo? Insha Allah zan cika miki shi muddin bai fi karfin na ba .
Kije kiyi aikin na amince, amma idan kafin cikar wa adin aikin ya cika Allah ya kawo miki mijin aure zaki bar aikin kiyi aurenki. In yaso idan mijin ya amince sai ki cigaba .
Amina tayi murmushi har gefen kumatunta biyu suka lotsa.
 Ai a bisa wannan alkawarin muke Goggo har gobe. Wallahi ba ni nake korar su ba, su suke korar kansu. Amma na kara yi miki wannan alkawarin. Ko yau na fara aikin gobe mijin ya zo, zan bar aikin nayi aure ko wanene shi.
Da sauri Ilya yace  A ah Dr. Amina, daina cewa ko wanene, idan kuturu ko Gyartai ya zo ba ruwan Goggo fa, ke zaki zauna dashi .
Goggo Hauwa bata san sanda tayi dariya ba, duk zukatansu sukayi dadi, don basa son ganinta cikin damuwa ko yaya, walwalarta itace tasu. Inna Zulai ta mike tayi musu sallama tana fadin
 kin bari sun kalallameki da dadin bakinsu. Ni nayi nan, tunda ko na sake cewa komai ma ba tasiri zaiyi ba .
Ilya yace  haka ne Hajiya Inna, gara ki adana yawun bakinki zai yi miki amfani gobe. Sai Ji-kas! Wallahi sai Ji-kas!! Insha Allahu sai Ji-qas bamu fada a banza ba, bamu sha rana a banza ba!!! Gashi tun ba a je ko ina ba nida Amina mu zamu fara shan inuwar gwamnatin Ji-qas. Mune a cikin gidan gwamnati! .

Washegari Amina da kwarin gwiwar ta ta doshi ofishin consultant dinta Dr. Usman Turaki. Saidai kash! Ofishin Turaki a kulle. Wani masinja ke gaya mata ai Dr. Turaki an bashi appointment na kwamishinan lafiya. Ya bar asibiti sai nan da shekaru hudu.
Allah ya so tanada lambar wayarsa a lokacin waya ta fara a cika duniya. Duk wani babban ma aikaci yanada ita.
Ta kira shi ya kwatatanta mata sabon ofishinsa, sai yace ta jira a office dinta zai turo direba ya kaita yanzun nan.
A wata sassanyar mota da Amina bata taba shiga irinta ba, aka kaita (ministry of health) inda ofis din kwamishina Turaki yake.
Amina bata bi dogon layin da ake bi wajen ganin kwamishinan ba, kai tsaye aka sada da ita gareshi.
Amina ta shiga da nutsuwar ta kamar yadda take ciki kullum, irin wadda zuzzurfan ilmin boko ke gadarwa mai shi.
Ta gaisheshi, ta kuma yi masa murnar sabuwar kujerarsa. Yayi godiya, sannan ya tambayeta ta yi shawarar? Iyayenta sun amince?
Amina ta ce  Goggo ta amince. Amma a bisa sharadin in miji ya zo kafin lokacin kwangila ya cika zan bar aikin in yi aure .
Dr. Turaki yayi murmushi mai kama da dariya.  That s good . Wani dan tunani ya darsu a zuciyar sa akan Ma arouf da Amina. Amma daya tuna halin mutumin nasa sai yayi gaggawar goge tunanin daga zuciyarsa ya janyo na abinda ya tara su.
 kiyi parking yau. Duk da mai girma gwamna ya gayamin bakya bukatar zuwa da komai, amma mutum baya rasa abin amfanin sa. Kayan sanyawa ne bakya bukatarsu. Yau za a maida takwararki gidan daga kauyen Ji-qas. Don Allah Amina ki kula da ita yadda ya kamata. As a doctor nasan bakya bukatar a tuna miki yadda zakiyi da patient dinki. But wannan patient din need extra-more saboda marainiya ce, sannan lafiyarta (matters a lot to her Dad). Zai nutsu ne kadai wajen aikin al ummar sa in ya tabbatar Amina tana a kyakkyawan hannu kuma tana cikin koshin lafiya koda bata taka kasa.
Daga yau zan bar zama jakada a tsakaninku, kai tsaye zaki dinga magana da His Excellency in kuna bukatar wani abu ko sanar dashi wani abu na cigaba ko na ci baya da ya danganci lafiyar diyarsa. Be the best doctor and the best physiotherapist as we know. Kawo wayarki in sanya miki lambar tasa .
Amina ta mika masa, ya sanya tayi saving. A ranta ta san ta karba ne kawai amma bazata taba iya kiran MA AROUF JI-KAS ba! Wani kwayan mutum guda daya da ko sunansa bata taba kwatanta fada ko da a zuciyarta ba, duk da zasu kasance gida daya, shi din dai (Turakin), zata cigaba da baiwa jakadancin ko yana so ko baya so.
Su wanene wadannan gwarazan Ma arouf da Amina? Daga ina suke? Menene asalinsu? Ga dai kaddarar rayuwa ta hadasu bayan kowannensu alamu sun nuna duniyar sa daban ce data dan uwansa??? Mu waiwaya baya.
****











ASALIN LABARIN
Goggo Hauwa na zaune a madafi tana kullin zobo da kunun Aya, wanda ya kasance sana a a gare ta mai albarka. Ta kwala wa Amina kira daga nan inda ta ke zaune a kujera  yar tsugune cikin tsaftataccen madafinta.
 Me ki ke yi wa tantabarun nan ne haka Amina? Ki fito ki sa hannu mu yi mu gama kullin nan .
Daga can dakin tantabarun Amina ta amsa,
 Dan bebina ne ba lafiya, ya kasa cin abinci shi ne nake dura masa dawar. Amma ga ni nan .
Ta ajiye dan tattabarar a cikin tukunyarsa, ta fito ta tadda Goggo.
Wata kujerar ta jawo ta zauna tana fuskantar Goggon, suka ci gaba da aikin; in Goggo ta zuba sai ta bata ta kulla. Suna yi suna hira irin ta Da da mahaifi.
 Goggo in kin dauki adashen wannan watan ne zan koma makaranta ko?
Amina ta fada cikin murya mai ban tausayi, wadda daga ji za ka fahimci rashin komawa makarantar yana damunta. Cikin muryar tausasawa Goggo Hauwa ta ce,
 Insha Allahu Aminatu, saura kwana biyar ma in dauki dashin. Insha Allahu in dai ina raye Allah zai nuna min cikar burinki. Ga ki can na hango ki cikin farar rigar likitoci kina tsira wa mutane allura& 
Nan da nan Amina ta washe baki, farin ciki mara misaltuwa ya bayyana a kyakkyawar fuskarta.
 Da yardar Allah kina raye Goggo, kuma da na fara daukar albashi kin bar sana ar lemon Aya da Zobo, Cincin da meat pie. Ni zan saya miki duk abinda kike so, in kai ki Makkah, in saya miki mota, ki kwanta a gida ki huta.
Allah ya jikan Baba, da yana raye da karfinsa kafin ciwo ya kwantar da shi ina za ki rinka wannan wahalar? Dubi fa in kin tashi da asuba bakya kara komawa bacci, sannan in dare ya yi ba za ki kwanta a kan lokaci ba sai kin gama hada kayan aikin gobe.
Ina tausaya miki Goggo, har wani lokacin in ji bana son komawa makaranta saboda wahalar da nake barinki a ciki .
Goggo Hauwa ta yi murmushi.
 Amina ke nan, ko Babanki yana raye ba na zama babu sana a, ba don komai ba sai don in tallafa masa, kasancewarsa mai karamin karfi. Da kuma ciwo ya kwantar da shi dole na ci gaba da sana a saboda kudaden magani.
Rayuwa ta canza yanzu kowa ya dogara da kansa shi ya fi, kada ki yi la akari da abin da ki ka yi wa mutane ki ce za su rama miki. Dubi dai yadda kanne da yayyen mahaifinki suka yasar da mu saboda kasa ta rufe idanunsa. Don haka Amina na hore ki da sana a komai kankantarta, ko da ta kiwon Tantabarun nan da ki ka kwallafa wa rai ne watarana za su yi miki amfani .
Amina ta girgiza kai,  Abin yana ba ni mamaki Goggo, wai har Kawu Sule shi ma ya watsar da mu, duk irin taimakon da Baba ya yi masa, ya dauko shi daga kauye ya rike ya samar masa sana a, dubi albarkar da ya samu a ciki, amma wai ko (school fees) ba zai iya biya min ba .
Goggo ta ce,  Kada ki kullace shi, duk lalacewar shi ubanki ne. ba ki da wanda ya fi shi, kuma ba dolensa ba ne ya dauki nauyin karatunki don babu mahaifinki, kada ki dogara da kowa ki dogara ga Allah sai Ya iya miki .
Amina ta girgiza kai,  To ke Goggo ba ki da dangi ne? tunda na taso na yi wayo ban taba ganin wani ya ziyarce ki da sunan dan uwanki na jini ba sai abokan arziki .
Goggo ta yi murmushi,  Ba irin dangin da ba ni da su Amina. Ba zan je ko ina ba ne sai ranar da Allah ya cika miki burinki, na aurar da ke a hannu na gari, sannan ne zan koma gare su Amina .
Aminan ba ta kara magana ba, saboda sun gama aikin. Can kuma ta ce,
 Allah ya yarda Goggo .
Ta mike ta jawo manyan kuloli tana shirya lemukan a ciki. Ta bude (freezer) dinsu ta soma ciro kankara tana zubawa a kai.
Daga can soro suka tsinkayi sallamar Ilya mai kura, wanda ke daukan kayan sana ar yana kai wa makarantu da asibitoci, kura uku suka shigo da ita da samari biyu a bayansa bayan Goggo ta amsa sallamarsu, ta kuma yi musu izinin shigowa. Suka dauki manyan kulolin da bokitan da aka shirya meat pie da cake suka zuzzuba a kura suka yi waje kamar kullum.
Shi Ilyasu dan makotansu ne da yake kula da sana ar Goggon cikin amana, tana biyansa duk wata. Katangarsu daya da gidan Goggon. Amma yanzu a dakin soron gidan yake zaune tun bayan tashin Sule kanin Baban Amina.
Amina ta cire hitar ruwan zafi daga bokiti da ta jona don ruwan wankanta ya yi zafi, ta dauka ta nufi bayan gida. Saboda dadi da tsaftar lemon Goggo Hauwa, da an fita da shi karfe takwas zuwa la asar sai kudinta a hannu. Wasu kuwa gida suke zuwa saya, sana ar Goggon sai masha Allahu domin tana da nasibi a ciki.

Gidan marigayi Malam Mas udu gini ne na talakawa masu rufin asiri. Dakali biyu sun sa kofar gidan a tsakiya, da ka sanya kai zaure (soro) za ka tadda, a cikin soron akwai daki falle daya wanda marigayin ya mayar dakin hutawarsa da karbar bakinsa masu zuwa daga kauyensu wyin kwanaki a wajensu. Daga baya da ya dauko kaninsa Sule a dakin ya zauna ya yi samartakarsa har ya yi masa aure.
A halin yanzu Ilya dan makotansu shi ke zaune a dakin wanda ya zama kamar Da ga Goggo, saboda maraya ne kamar Amina shi ma mahaifinsa ya rasu tun yana karami.
Da ka wuce zauren za ka tadda tsakar gida madaidaici. A tsakar gidan, dakuna ciki dai-dai ne guda uku, madafi a gabas, bayan gida a kudu. A tsakiyar filin tsakar gidan bishiyar umbrella ce wacce ta bude ganyayyakinta sosai ta ba da duhuwa mai sanyi.
Daki falle daya na maigidan ne Malam Mas ud, kafin Allah ya dau ransa, daya na Goggo da Aminatu, tare suke kwana ba sa raba shimfida, yayin da daya dakin Tantabaru ne fal kala-kala maza da mata, sabuwar haihuwa da masu tashi, kowanne aure cikin tukunyarsa.
Sana ar Baban Amina kenan, ya kiwata Tattabaru in sun girma ya kai kasuwa ya sayar. Wani zubin kananan ma ana saye. Da wannan sana ar ya rike iyalinsa, suka rayu cikin rufin asirin Allah. Duk da matarsa Hauwa tana gwada sana o in hannu iri-iri.

Garin Bauchin Yakubu shi ne asalin garin Malam Mas ud na haihuwa, sun fito daga kauyen Shira. A kauyensu tun yana yaro kiwon Tattabaru yake yi, wani ne ya ba shi shawarar ya dinga shigo da su maraya ana sayensu da daraja, da haka ya fara, ya yi keji babba ya zuba su a kasuwar Wunti, Allah kuma ya sanya masa albarka a ciki, ya koma gida Shira ya sayar da katuwar gonarsa ta gado ya dawo ya sayi gidan da suke ciki a yanzun.
Hauwa u mahaifiyar Amina, asalinsu  yan kasar Sirrleone ne. Kasuwanci ne ya kawo iyayenta Bauchi har ta zame musu gida. Rannan ta shiga kasuwar Wunti wajen Babanta kai masa abinci kamar yadda ta saba kullum karfe biyu na rana, tana  yar shekara goma sha uku, ta ga Tantabaru guda biyu a hannun wani abokin cinikin Babanta. Cikin sha awa ta soma tattaba su, ta ce,  Baba, don Allah ni ma ka sayo min in yi kiwonsu, ina son Tantabaru .
Babanta Malam Hadi wanda shi kuma sana ar saida kaji yake yi ba su da nisa da Mas ud, wanda a lokacin saurayi ne mai tashen kuruciya, ya yi dariya ya ce,  Ba na son rigima Hauwa u, ina za ki iya wani kiwon Tattabaru ke da ko kajin da nake bari a gida ba iya kula da su ki ke yi ba, ina za ki iya wani kiwon Tantabaru?
 Wallahi Baba zan iya, don Allah ka saya mani .
Hauwa ta dage, Malam Hadi yana matukar son Hauwa, don ita kadai Allah ya ba shi, tare da maidakinsa Aishatu.
Ya ce,  Tunda kin dage bari in sallami wannan mu je in saya miki

2 / 10