Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DOCTOR ILHAM Ƙauna Duk da Komai By Amira Saminu

Author :  Amira Saminu Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 15

27K to 30K   out of 43K words

gansu suna Tafe jere da juna suna Ido hudu da"

"Ilham ya hade fuska ya koma office din sa ta na ganin Haka ta karfi takkardan ta nufa Office din da sauri tabi bayansa sam bai kulla tana Bayansa ba ya rufo kofar da karfi Hakan ya sa Yatsan hannunta shiga ya dantse ta ,yar kara ta saki dan tsabar zafi har idonta Sun kawo ruwa ,juyowa ya yi Yaga hannunta Yana zubda jini ,a rikice ya ce'' Albi ki yi hakuri ban san kina bayana ba .''"

"Ai kamar jira take abin ka ga shagwafafiya ta fashe da Kuka tana yar fa hannun janyota ya yi , sannan ya rufe kofar ya"

zaunar da ita bi sa chair din dake wajen sannan ya yi tsugunni Irin na Maza ya Kamo hannunta tare da jawo Kayan dressing Yana mata ya ce'' Mon halal ki yi hakuri ban kula kina bayana ba dan Allah ki yafeman sannan ki dai na Kuka kin san na sha fadamaki cewa tadamin da hankali yake kina son na shiga damuwa ne .''

Hawayenta ta share ta ce'' Na daina in dai Hakan zai sakaka damuwa na bazan sake ba .''

Allah ya barmani Mon halal din ta ki zama Mallakina hankalina ya kwanta in san ni naki ne ke dai .''

"To Waya fada?"" cewa ba Kai ka dai ne bane a zuciya ta .''"

"Yanzun fa na ganki da Bashir ,'' Murmushi ta yi, ta ce'' Babu abin da ke tsakanina da D.C Bashir sai mutumci kuma"

wajenka ya ce'' Na zo in baka wanan takardun ka duba zamu shiga wajen wata mai ciki da take Labour .''

Sorry Ilham ban san Haka abin yake ba kishine yakamani amma zan kiyaye gaba kuma yanzu ba gobe ba idan mun

tashi aiki zan je wajen Alhaji in Sanar masa ayi ta ta Kare .''

"Sunkuyar da Kai ta yi , ta ce'' ga takardun sannan ni yau anan zan kwana sai gobe zan sauka daga aiki .''"

Bai ji dadi da ba tare zasu koma gida ba amma ya ce'' babu damuwa Zaki ji sako wajen Dady .''

"Murmushi ta yi , tare da ficewa daga Office din tana cewa Allah ya sa Muji Alkairi.''"

"Girgiza Kai ya yi , ya ce'' amine sannan ya rufe kofar .''"

Dakin da matar take tanu fa sosai ta tausaya mata dan halinda da ta ganta Haka ta yi ta kulla da ita har Allah ya

"sauke matar Lafiya ta santalo beby boy kyaukyauwa Murmushi Ilham ta yi , ta ce'' Ma sha Allah Congrats ta fada tana Mika mata beby din ,'' sai da matar ta kalla abin da ta Haifa sannan Ilham ta karfe sa ta kawo ma jama'ar da Suka yi raki yi sai santin yaron mutanan suke , ita kuma ta koma ciki ta gyara mai jego sannan suka Kai ta dakin hutu ita da beby din ta kafin da safe su sallama me ta dan tun safe fa Suka zo sai wajen karfe 1h30 na dare matar ta haihu tana gamawa ta koma Office din ta sai da ta tabatar ta rufe kofar sannan ta cire rigarta ta likitoci ta kwanta bi sa dan karamin gadon dake dakin.''"

Sai da yamma lis sannan Musa ya Baro Asubitin dan ya so su hadu da Ilham amma ba dama ga shi wayarta a kashe

"dan Haka ya yi hakuri ya tafi gida sai da ya yi , wanka sannan ya nufi part din Ammi tana zaune tana karatun jarida da sallama ya shigo , ciki ciki Ta amsa ta ce'' Har ka Dawo ,'' E'e Ammi .''"

To ka abincin ka tsan a kithchen ka je Ka dauko .''

Cike da Mamaki yake kallonta dan tunda yake da Ammi bai taba tafiya ya dauko abinci ba sai de ta kahomasa cike da

sanyin jiki ya nufa kithchen ta dauko sannan ya fito har zai fita ya tsinci Murya ta tana fadin in dai har zaka din ga kin bin umarni na baka gaji da mamaki ba .''

Bai ce da ita komai ba ya fita sai da ya ci abinci sannan ya nufa bangaren Alhaji Yana kwance yana kallon T .V d

"sallama ya shiga Bayan Sun gaisa ya ce'' Alhaji wajenka nazo ?"""

Ta shi ya yi daga kwancen da yake ya ce'' lafiya dai ko .''

"To lafiya lau Amma ba sosai ba?"" Har sai na ji amsarka ka dai zan warke .''"

"Fadi ina jinka?"" Hmm dama bisa kan maganar Ilham ce ina son ka je Ka nema mani izinin auren ta .''"

Ya fada Yana sunkuyar da Kai kamar tsohon farawo .''

To Musa gaskiya na yi farin ciki da haduwark da yarinyar nan sannan ko ba komai zata kulla da Kai sosai .''

"Cike da kunya yake kallon Alhaji amma bai ce komai ba ,shi kuma ya ci gaba da cewa kar ka damu tufa azakare"

wanansa adakidwaya hura banne ( gobe zan je in nema maka aurenta ) .''

To Baba na Na gode ni zan tafi gyare muzai ( sai an jima ) .''

Fitowar sa Kenan ya hango Safiya ta shigo daga ne sa Ya kirata ta tsaya kamar munafika sai da ya kariso har inda take

"ya ce'' daga ina kike?"" ."

Gidan Amarya na je zamu yi mata girkin sati .''

Ke baki gajiya da yawo ne kamar wacce ta ci kafar Kura Karna sa ki naga gobe kin bar gidan nan .''

"To ai Ammi ta sani kuma ita ta ce naje ai?"" Ni kuma na ce kar ki kuskura kibar gidan nan .''"

"Turo baki gaba ta yi ,ta huce ciki tana magana kasa kasa har ta shige ciki da sallama a bakin ta .''"

"Amsawa Ammi ta yi , ta ce'' Har kin Dawo yane an da ce ne .''"

A'a Ammi wai sai banda gobe zamu kara ta fiya dan ni na sare tun da na fita sai wajen karfe uku wai muyi hakuri Sun

tashi shi yasa na huce gidan Amarya da naga karfe biyar nace bara na Dawo gida .''

"To ki shiga ki huta ga abinci sai kice?"" Wallahi kamar kin san ina jin yunwa .''"

Tafada tana shigewa dakin ta .''

Ilham na bacci aka Budé kofar da yake tana kulle kofar ta cire makullin shi yasa Aka shigar mata Office jin ana shafata

"ya sa ta gyara kwanciyarta dan a tunaninta mafarki take yi , jin ana daga mata Riga ya sa ta bude idon ta suka yi Ido hudu da shi ,a tsora ce ta tashi zaune gabanta na dukan sha tara tara jikinta na rawa ta ce''"

.........................................................................

....................................

Comment

25/03/2022 à 09:25 - Mom Star :

*DOCTOR ILHAM*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS
'<Øüß*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

"```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al™alaminmu ´ancinmu.```"

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*Na*

*Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

28/29

"Jikinta na rawa cikin rawar murya tace'' Fa..ruk ,'' wani uban mari ya sharara mata Wanda ya sa sai da taga star uku"

"suna yawo a saman kanta sannan ya fincikota da sauri ta gantsara masa cizo tayi wajen wayarta ta dannan lambar Abul Khair ,da sauri ya kwace Wayar Yana buga mata Kai ga bango aiko hannunta ya danna karaurawar dake Nuna a kwaye matsala ,dan ita tama manta da ita tsabar firgici jin ana nufo dakin yasa ta kwarara ihu Hakan Yaba mutanan damar shiga Kai tsaye ,da mamaki kowa yake kallon Faruk Ilham Na ganin ta nufa wajen fa'iza tana Kuka ,'' d.c Bashir ne yanufa wajen Faruk tareda shako huyansa yayi hurgi dashi kamar Kayan wanki ya Kai masa naushi a Ido cike da facin rai dan ubanka iskancin da kake a waje bai isheka ba har sai kazo dan ka batamin sunan asubiti ko asarare kawai Kai de anyi dan iska kuma kasani daga yau Wallahi bazaka kara sha'awar lalata Yan mata ba dan uwarka kallon sécurité din dake wajen yayi yace'' ku fitarmin dashi kuci ubanshi ,cike da girmama umarni suka sungume shi sukayi waje da shi suka fara dumarshi kamar an Sun samu Banza sai da sukayi masa jina jina sannan suka barshi sannan suka daure shi da igiya a wajen asubiti suka koma ciki ,'' kallon Ilham ,Bashir ya yi, ya ce'' babu wata damuwa dai ko"

",'' gyada masa Kai ta yi alamar e'e ,'' to ke ?"" Fa'iza ki zauna anan idan Allah ya kaimu da safe zai ga abin da zan masa.''"

Cike da jin kunya ta ce'' D.C na gode sosai .''

Karki damu babu komai ?.

Ficewa ya yi Ita kuma ta koma ta kwanta amma baccin Yaki daukarta sai de ma Hana fa'iza baccin da ta yi dan sai

"tafara bacci sai ta ce'' fa'iza bacci kike ne ,'' ita kuma sai ta ce'' A'a a Haka har Asuba ta yi ,Mikewa ta yi, duk da kanta Yana saramata amma Haka ta daure ta shiga toilet ta dora Alawa tafito tareda Tashin Fa'iza ita ma taje ta yi alawa a tare sukayi sallah sannan Ilham tafara har hada Kayanta ,''kallonta Fa'iza ta yi ,ta ce'' Ranki shi dade ina kuma zuwa yanzu .''"

"A takaice ta ce'' gida zan je mana?"""

To amma ai nake ganin gari bai yi hasken da Zaki fita yanzu ba kuma gashi motarki Batanan .''

Ajiyar zuciya ta sauke dan sai yanzu ma ta tuna cewa Abul Khair ya tafi da ita zaune tayi tareda dafe Kai dan sosai

"kanta ya bugu ga rashin bacci da Bata samu ba Wayar ta janyo tareda Kiran wayar Abul Khair ,sai da ta yi ringing hudu a na biyar ya dauka tareda da sallama a bakinsa amsawa ta yi ta ce''Mn halal dan Allah in ba damuwa kazo yanzu a asubiti ina son ganinka .''"

"Lafiya dai ko Ilham Me ya faru ?"""

"Sai kazo tafada tareda kashe Wayar ta ajiye ta gefe, jin Hakan yasa shi dauko makullin motarta yafito zai fita suka"

"hadu da Alhaji a hanya ,sai da ya gaida shi ,ya amsa Yana fadin ina kuma zaka je yanzu.''"

Wajen aiki ne aka kirani amma yanzu zan Dawo .''

"To ba damuwa ?""ka kula da hanya sai Dawo ko ."""

Insha Allah Baba.''

Baba Yana shiga ciki shima ya yi wajen motarsa ya shige sannan get man ya Budé masa kofa yafice daga gidan sai

Asubiti .''

Yana isa ya sauko ko kulle motar bai yi ba ya fito yanufa office din Ilham dan a yanayin da tayi masa magana zaka san

"tana cikin damuwa ,'' Yana kaiwa ya yi , fa'iza ta Mike tareda Budé kofar da Aka saka ta kullawa da Key ,'' bai tsaya Wata wata ba yanufa inda take tareda ajiye hannunsa a kafadarta ya ce'' rayuwa ta lafiya kike me yasa meki hakane"

.''

"kallonsa ta yi , da idonta da Suka cika kwalla ta ce'' Babu komai .''"

"Ya Zaki ce babu komai ?"" Kin ga tell me hankali duk a tashe yake Waye ta jimaki ciwon nan .''"

Fa'iza ce ta ce'' Kar ku na tsoma baki Akan abin da bai shafeni amma jiya kadan ya rage yallabai Faruk ya mata fyade

.''

Wani Irin garam gabansa ya buga da karfi idonsa sukayi jajir jijiyoyin Kanchi suka taso ya ce'' ina yake ne .''

A tsora ce Fa'iza ta ce'' Yana Bayan Asubitin nan an jima za'a fito dashi dan nunawa Al'umma sannan a huce da shi

police station .''

"Fitowa ya yi ,yanufa Bayan Yana isa bai tsaya Wata wata ba yashiga kaima Faruk mazga sosai yake ihu har muryarsa"

"ta dusashe ,da gudu sécurité din dake wajen suka yo kansa da kyar Aka kwace Faruk a hannun abul Khair da sai sauke ajiyar zuciya yake .''"

"Safiya nayi Alhaji yatafi gidansu Ilham nan ya saka mai gani ya masa magana ,bai wani jima ba yafito nan suka gaisa"

"cike da mutumtawa , Alhaji ne ya ce'' Muhamed dan Allah nazo ne Akan maganar yaron wajena da yar ka Ilham .''"

"Lafiya dai ko ?"" Alhamdulilah dama nazo nema masa auren tane idan Allah ya sa ba'ayi mata mijiba .''"

"Washe baki Dady ya yi , ya ce'' Masha Allah to ai Ilham yarka ce babu damawa fairakat ( na baka ita).''"

Kai amma Naji dadi sosai nagode Allah ya saka da alkairi ya basu Zaman Lafiya .''

"Amine fairaturage ( Allah yasa Alkairi)."""

To Na gode Muhamed Inde gyara muzai .''

"Nan sukayi sallama sannan kowan nansu suka koma gida ,alhaji Na shiga Kai tsaye part din Ammi yanufa da sallama"

"a bakinsa ,amsawa sukayi dama ita da Safiya ce zaune a falo suna jan tarbi ,'' Baba ina kwana ?"""

Lafiya lau Safiya ana zaune .''

E'e baba .''

"Baice da ita komai ba ya duba Ammi ya ce'' Hajiya Ta yau nazo maki da baban Albushir ,'' Murmushi ta yi , ta ce'' To"

Bani labari in sha .''

Dazun munyi magana da Muhamed Bisa kan maganar Ilham da Musa Abul Khair sosai yafini murna ya ce'' yabamu

ita .''

Tunda yafara maganar Ammi ta hade fuska kamar ta makure huyansa ta ce'' bangane me kake nufi ba Kana nufin

wanan karuwar yarinyar zata zama Sakakuwa ta Allah ya sauwake kaga Alhaji ni wanan shedaniyar yarinya bazan taba laminta ta shigo mani gida ba Wallahi .''

Kallon bakida hankali ya mata ya ce'' nawa Kika kashe wajen gina wanan gidan ne to ni bazan kaminci wanan

iskancin banzan naki ba Wallahi idan har baki dai na abin da kike ba to da alama wata zata shigo wata kuma ta kama hanya dan ni bazaki mai dani karamin mutume ba .''

"Yana gama fadan Hakan yafice daga part din ,a hasale Ammi ta ce'' ko da za'a yi auren nan Wallahi sai de wani gidan"

amma ba nawa tafada tana kallon Safiya taci gaba da cewa munafika ai duk kune Kuka jawo za'a kawo mani diyar watsan mutumniyar banzan ta kara she tana bankada mata Harare .''

Allah yabaki hakuri Ammi .'' tafada tana shigewa daki sabida Kiran wayarta da ake yi .''

Tana shiga ta fada kan bed tareda amsa Wayar tana fadin Hello Kitty na ya kake .''

Lafiya lau Cutie ke jiya kike gudu ba ko sallama .''

"Murmushi ta yi, ta ce'' ba doli ba ai naga baka da niyar sallama ta shiyasa gashi mangari ba ta Kurato so kake yau a"

Hanani zuwa ne.''

Haba in sa Raina ina bacin Baki kusana ni dama Kira nayi inji Zaki zo yau ne .''

"Me zai Hana sosai ma zan zo ?"" Dan farincikin ka mana .''"

"Idan fa Amma ta Hanaki ?"".."

Haba ina ji koda satan hanya ne sai na fita dan nayi tauri bazan tankwasu yanzu ba .''

"Dariya ya yi, ya ce'' my Cutie love kin fa iya soyaya ba dama .''"

Ai ban kaika ba ko Kitty na.''

Babu gwani dai to da wane lokacin Zaki zo ne .''

Bayan sallah La'asar in sha Allah .''

To Allah ya kahomani ke lafiya ta kirkin .''

Amine ta fada nan sukayi sallama ta katse kiran .''

25/03/2022 à 09:25 - Mom Star :

*DOCTOR ILHAM*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS
'<Øüß*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

"```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al™alaminmu ´ancinmu.```"

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

*Na*

*Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

30/31

Da kyar suka samu abul Khair ya kwantar da hankalinsa Hakan yasa yayi hakuri ya koma ciki wajenta yanufa ya ce ''

"rayuwa ta garin yaya wanan dan Iskan ya samu damar shigowa wajenki ,'' nan ta fadamasa abin da ta sani ,iska mai zafi ya fizgar ya ce'' Muje gida ko ?"""

Babu musa ta Mike suka yi hanyar gida babu mai magana kowa da abinda yake sakawa a ransa har suka iso sai da ya

shiga da ita har cikin gida sannan suka yi sallama ya tafi gidansu Ilham Na shiga ta tarar dasu Mama suna breakfast Inteesar ta kalleta da karkatacen kanta tana zubar da yawu ta ce'' Aunty na har kin Dawo .''

"E'e ?"" Kawai ta fada tareda gaishe da su Mama ,'' suma suka amsa sannan ta huce daki babu Wanda ta saké yima"

magana .''

"Tana shiga ta fada toilet wanka ta yi , ta saka Kaya Marasa nauyi sannan ta bi lafiyar gado sai bacci .''"

Dady ne da sai da Ilham ta shigo ya tuna da maganar Alhaji ya ce'' Maryam dama dazun ban Sanar dake ba yau da

sasafen nan Alhaji yazo gidan nan neman auren Ilham .''

A'a Masha Allah gaskiya nayi farinciki sosai .''

Amma Maryam Ilham ta san abin da ke tsakaninku da Murja ne .''

A'a Bata sani ba kuma Bana fatan ta sani tunda babu anfani Hakan .''

Hakane nasan wata rana dole ne ta sani in dai ana tare kuma ana raye .''

To banki idan lokaci ya yi Sata sani ai .''

Allah yasa Alkairi a cikin wanan hadin da mukayi .''

Amine .''

Safiya ce ta fito cikin shirinta Irin na isanan tana taunar shiwgom ta ce'' Ammi na shirya ni zan fita ko .''

"Da Mamaki take kallon Safiya wanan kuma wace Iriyar shiga tayi wai tana nufin a Haka zata fita,'' katse mata tunani"

ta yi tana fadin sai na Dawo Ammi .''

"Fita ta yi , batare da taji cewar ta ba ,dan tsabar Mamaki sosai Ammi take kallonta har ta bacewa ganinta Anya kuwa"

Safiya ce wanan.''

Da wann tunanin ne Abul Khair ya shigo tareda gaishe da Amma ko kallonsa Bata yi bare yasama ran zata amsa .''

Ina kwana Ammi? ''

Bansani ba tunda kaine mai Bada lafiyar .''

"Shiru ya yi ,n'a dan lokaci dan Yaga yau abin ba sauki Mikewa ya yi ,ya ce'' Ammi zan fita babu abin da kike da bukata"

ne .''

"Ko hmm Bata ce masa ba bare kallon arziki ,'' fita ya yi ,ya koma part din sa Ya kwanta nan ya Kira Wayar Ilham"

amma ba'a daga ba sai da ya jera mata miss call 3 sannan ya shafamata lafiya tashi yayi ya shirya dan zai fita .''

Janye suke da shi saman jaki Sun Rataya masa takalmi a huya ko Riga babu a jikinsa sai zagaye gari suke yi da shi

kowa ya gansa ya san me ya aika ta Haka sukai ta yawo da Faruk tun safe har yamma sannan suka Dawo da shi nan

D.C ya Kira Yan Sanda suka yi gaba dashi.''

"Ilham na tashi ta

10 / 15