Author : Asirin Jiya Category : African Stories & Novels
lokaci, a kowani hali, duk min rintsi ina son ki Aaliyah, har ƙarshen rayuwata, har ƙarshen numfashina a doron ƙasa. I will forever love you Aaliyah"*
*...........Aaliyah............*
Fear
Ina son Sa'eed sosai, kowacce rana kamar ƙara dasa min son shi a ke a zuciya ta. Sa'eed mutum ne mai karamci, tsaftacecciyar soyayya ya ke gwada min wanda ta ke babu ƙarya a cikin ta. Idan ka cire riƙe hannu ko runguma sau uku Sa'eed ya taɓa kissing ɗi na. Wani lokaci na kan nuna ma sa alamun ba matsala idan ma mun aikata abin da ya fi kiss amma sai ya dinga janye jiki da ni. Akwai lokacin da na fito fili na faɗa ma sa ni da shi ɗaya ne kuma zan mallaka ma sa kai na ba tareda wani tsoro ko fargaba ba. Yai murmushi kawai ya ce "Aaliyah ba jikin ki na ke so ba, haka nan akwai lokacin da za mu kasance tare har abada, ki yi haƙuri kafin nan"...
Saura kwana ɗaya na tafi gida muna zaune da Sa'eed a gida na aka fara ƙwanƙwasa ƙofa. Muna zaune a kujera mu na shan tea ɗin da ya haɗa min wanda har yau na ka sa iya haɗawa kamar yadda ya ke haɗawa. Tunanina pizza da mu ka order ne aka kawo ma na, dan haka na tashi da sauri na je na buɗe ƙofa. Ido na zaro ganin Amma na tsaye.
Na faɗa jikin ta ina murna...
Shigowar da ta yi ta ga Sa'eed ya sa ta haɗe rai tana yiwa Sa'eed kallon tuhuma. Da ƙyar ta amsa gaisuwar da Sa'eed ɗin ya ma ta. Shima ɗin sai na ga tsoro ya bayyana a fiskar sa.
Suna gama gaisawa ya ce zai tafi, na nemi ya tsaya a kawo mana pizzar amma ya ce yana sauri ya tuna zai je ya amso saƙo.
Sa'eed na tafiya Amma ta kalle ni cike da masifa ta ce " mi ya ke yi a nan?"
"Amma ya zo tayani hira mana tunda ba makaranta" na faɗa ba tareda wani fargaba ba.
"Na shiga uku, Aaliyah ba dai anan ya ke kwana ba?"
Duk yadda na faɗawa Amma Sa'eed ba ya kwana a gidana haka nan bai taɓa kwana a gida na ba bata yarda ba sai da ta dudduba gidan ta ga babu kayansa ciki.
"Amma wai miye haka ne? Sa'eed ɗan uwana ne, ko da ya kwana anan mi ye a ciki?"
Amma ta fara min faɗa, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba. Tun ban maida abin komai ba har tsoro ya fara shiga na saboda maganganun da ta ke faɗa. Ba abinda ya fi ɗaga min hankali irin abinda ta ce wai idan ma soyayya mu ke to mu dena dan ba inda zai kai mu.
"Amma miye ne idan mun yi soyayyar? Sa'eed mutumin kirki ne"
"Tsakanin ki da Sa'eed babu soyayya Aaliyah, idan kuma ki ka fara za ki sha baƙar wahala ne dan ba inda zai kai ku. Ki kama kan ki Aaliyah ko kuma na sa Baban ki ya chanja miki makaranta"...
Har mu ka koma gida Nigeria ban ga Sa'eed ba gashi Amma ba ta bari na fita a gidan ba. Dama ta je ganin yayanta da ba lafiya ne ta biyo min akan mu wuce Nigeria tare tunda nima chan na nufa...
Tundaga wannan lokaci na ji tsoro ya shiga rai na. Ina tsoron ka da kashedin Amma ya tabbata, ina tsoron kar wata rana a raba ni da Sa'eed...
Har hutu na ya ƙare ban ji daɗin hutun ba saboda kewar Sa'eed da na ke yi. Sai da na koma Cambridge na samu nitsuwa. Kwanaki kaɗan da komawata na fara ganin chanji tattare da Sa'eed kamar ƙoƙarin ja baya ya ke da ni, gashi ya daina zuwa gidana. Da na tuhumeshi sai ya ce karatu ne ya ke riƙe shi wanda na san ba haka ba ne. A hankali na gane Amma ce ta gargaɗe shi a kai na. Ranan na ma sa kuka sosai na kuma nuna ma sa soyayyar sa ƙarya ne indai zai ji tsoron Amma. Abin ya ma sa ciwo, hakan ya sa ya dena baya-baya da ni ya kuma nuna mini duk rintsi muna tare. Muka cigaba da soyayyar mu kawai mu ka manta da komai...
A shekara na biyu da na zo gida hutu na tuhumi Amma akan dalilin son rabani da Sa'eed da ta ke yi. Ranan ne na ji tsanar gidan mu, na ji a raina ina ma ni ba 'ya ce a gidan Alhaji Badamasi Bulama ba, na ji inama ni 'yar wata maigadi ne ko dreba. Amma ƙiri-ƙiri ta faɗa mini babu aure tsakanina da Sa'eed idan ma zan bar shirmen da na ke yi to na bari. Domin makaranta kawai ake jira na ƙare amin aure domin an min miji.
Ban san ya na ƙare satuttukan da na yi a Nigeria ba domin na kasance tamkar mara lafiya ba na fita ko'ina kuma ba na shiga cikin 'yan gidan mu. Jiji ma dana samu da maganar sai ta tabbatar min da maganar Amma, 'Yar mai kuɗi sai ɗan mai kuɗi...
Ranan da na koma makaranta ina zuwa gida na kira Sa'eed akan ya zo ina neman sa. Tun a Nigeria na riga na yanke wa kai na shawara kuma ko sama da ƙasa za su haɗu ba zan fasa abinda na yi niyya ba...
Yana zuwa na rungumeshi saboda ba ƙaramin missing ɗin sa na yi ba.
"Sa'eed ka min ciki" abinda na faɗa ma sa kenan kuma har zuciya ta abinda na ke so kenan.
Ya janye ni a jikin sa yana faɗin "ciki kuma? Why? Miya kawo wannan maganar?"
"Amma ta ce ba za mu yi aure ba, Jiji ta ce ba za mu yi aure ba. Sun ce wai ba mu dace ba. Sa'eed idan na rasa ka mutuwa zan yi. Dan Allah ka sadu da ni na samu ciki ko za su bari mu yi aure"
"Kwantar da hankalin ki Aaliyah, da sauran lokaci har yanzu saura miki shekara biyu ki ƙare ƙaratun ki. Kafin nan za su amince mana"
Wannan karan cikin kuka na ce " ba za su taɓa amincewa ba Sa'eed. Amma ta ce ina gama karatu za su min aure, wai anriga an min miji"
Na fara ƙoƙarin cire kayan jikina.
"Aaliyah stop this nonsense, ki bar cire kayan nan"
Ban saurareshi ba na yi tsirara gaban sa.
Ya daka min tsawa akan na maida kaya na. Amma ba abinda na yi sai ma na fara ƙoƙarin cire ma sa belt ɗin wandon sa.
"Ba ka sha'awata ne, kai ba namiji ba ne, ka yi duk abinda ka ga dama dani ni Aaliyah ta ka ce"
"Stop Aaliyah" ya faɗa yana tureni amma ban daddara ba na sake matsowa kusa da shi zan cire ma sa riga.
Saukar mari na ji a fiskata wanda ya sa na tsaya da abinda na ke shirin yi.
"Ke mahaukaciya ce Aaliyah, i said akwai lokaci. Ba zan taɓa ɓata miki rayuwa saboda wani dalili marar kan gado ba. Yes I love you amma ba irin wannan soyayyar na ke miki ba, what i feel for you is beyond this"
Har ya je ya ɗauko bargo ya zo ya rufa min ina tsaye ina zubda hawaye.
"Ki je ki sa kayan Ki" ya faɗa a hankali...
*TSOHUWAR💖SOYAYYA*
*©Azizat*
Wattpad @000Azee
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
1️⃣0️⃣
Free page
*za'a samu cigaban wannan labari a 200, idan kuma ka biya kuɗin Sakatariyata to 100 za ka biya. Domin ƙarin bayani 08137311900*
Wayar Zaid da ke ringing ne ya katse shi daga karatun da ya ke yi. Ya ɗaga ido ya kalli Aaliyah da idon ta ya cicciko da hawaye.
"Mi ya same ki kike kuka?" Ya tambaya yana ƙura ma ta idanun sa.
Ta girgiza kai kawai tana matse hawaye da gefen gyalenta.
Cigaba da kiran da aka yi ne ya sa yai tsaki tareda jawo wayar da ke kan gado.
Kafin ya swiping ya ɗauka kiran ta ga sunan da ke jikin screen ɗin *Zahra* babu tantama ta san Zahra MCcollins ce ke kiran sa. Waye bai san Zaid Ahmad Wamako da Zahra MCcollins su na soyayya ba.
Zahran da ta ke da over 2million followers a instagram da twitter. Manyan mutane da 'ya'yan manya sun yi chaa a kanta amma ba wanda ta damu da shi kamar Zaid. Shekara ɗaya da ya wuce ta tabbatar da zargin da ake ma ta kan soyayyar su da Zaid ɗin, inda ta bi duk shafukan ta na sada zumunta ta posting hoton ta da Zaid da su ka yi a Dubai ta rubuta *my man* a ƙasan hoton. Ba dan rasuwan mahaifin Zaid ɗin bama ƙila da anyi auren Zaid da Zahra tuntuni...
Arnold MCcollins shine kakan Zahra ta wajen Uba. Baturen ƙasar Ingila ne wanda ya zo Nigeria lokacin turawan mulkin mallaka. Kusan shekaran sa shabakwai a Nigeria kafin Allah ya sa yana da rabon musulunci ya musulunta. Kasancewa matar sa Rebecca ta daɗe da mutuwa ya sa bayan musuluntar sa aka bashi mata a Niger state inda ya ke da zama.
Hadiza Mamman Kankana 'ya ce a gidan Alhaji Mamman Kankana ɗaya daga cikin masu kuɗi kuma jigajigan ƙasa 'yan asalin Minna.
Auren Abubakar Arnold MCcollins da Hadiza Mamman Kankana sun haifi yara biyu, mace da namiji. Muhammad da Aisha.
Shekaran su goma shabiyar da aure Abubakar ya rasu yana mai shekaru sittin da ɗaya.
Muhammad da Aisha ba ƙaramin gado su ka samu ba saboda dukiyar da wannan baturen ya mutu ya bar mu su.
Muhammad A.A MCcolllins fitaccen mutum ne a ƙasar Nigeria da ma duniya gaba ɗaya. Ya riƙe muƙamai da dama kafin ya koma aiki da United Nations. Matar sa ɗaya Hajiya Maryam Tambuwal wanda itama 'yar babban gida ce. Allah ya azurta su da yara uku.
Hanifa Mccollins ita ce 'yar fari, wacce ta ke auren ɗan sarkin Sokoto. Sai Anwar MCcollins wanda ke auren 'yar shugaban ƙasa. Sai autar su Zahra wanda ta ke cin karenta ba babbaka a ciki da wajen ƙasar.
A shekarunta ashirin da biyar ta na da kwalin degree uku a ɓangare daban-daban. Tana da Kamfani da ta buɗe shekaru uku da su ka wuce, Zahra MCcollins brand ce. Tana da kyau, kuɗi, asali da nagarta. Yarinya ce da ta ke da girman kai da jiji da kai, ba da kowa ta ke harka ba, iya matsayin ka iya kusancin ka da ita.
Za ta iya walaƙanta kowa indai ka shiga gabanta. Ta samu tayin soyayya da ga wajen 'ya'yan manya da dama, sai dai da mutum biyu ta taɓa soyayya ko kuma na ce ta amince da soyayyar su. Masoyinta na farko cousin ɗin ta ne Junaid, ɗa a wajen ƙanwar Baban ta wato Aisha MCcollins. Ba su jima tare ba su ka rabu dan yanzu haka shekarar sa uku da aure. Zahra na masifar son Zaid, duk girman kan ta ba ƙaramin walaƙanci ta sha a wajen Zaid ba kafin su ka zo su ka zama masoya...
Bayan ya gama wayar da Zahra ya kashe wayar gaba ɗaya ya ajiyeta gefe. Sannan ya juyo ya kalli Aaliyah da har lokacin tana ƙoƙarin goge hawaye ya ce " a ina ki ka samu diary ɗin Sa'eed?"
"Wamako mu cigaba da karatun za ka gane daga baya"
Kallon ta yai na ɗan wasu daƙiƙu kafin ya buɗe diary ɗin Mom ya cigaba da karatu.
*..........Aaliyah...........*
Ahmad Wamako
Tun daga ranan hankalina bai kwanta ba, amma Sa'eed bai wani nuna damuwa ba. Koyaushe ce mini ya ke na kwantar da hankalina na cigaba da addu'a komai zai zo da sauƙi. Sai da aka ɗau lokaci mai tsayi kafin na cire damuwa a raina na, koyaushe Sa'eed nuna min ya ke akwai nasara a tattare da soyayyar mu...
Wata ranan Alhamis na dawo daga aji zan shiga gida sai na ji kamar ana kuka, na kasa kunne sosai sai na ji kaman daga ɓangaren Cassy maƙociyata ake kukan. Da farko na yi niyyar na share ta sai kuma na ga hakan bai dace ba, maimakon na shiga ɓangarena sai na je ɓangaren Cassy na fara buga ƙofar ta. Ba ta buɗe da wuri ba sai da na yi ta mata magiya kafin ta zo ta buɗe. Ganin yadda idon ta ya koma saboda kuka ya sa na shiga tambayarta miya faru. Da farko ma na ɗauka ko faɗa su ka yi da saurayin ta dan na san tana son Damien sosai. Sai da ta faɗa min asalin abinda ya faru sai jikina yai sanyi.
Saurayin ta Damien yai hatsari ya mutu. Abinda ya ƙara ɗaga ma ta hankali shi ne sati biyu da su ka wuce wata ƙawarta ta ma ta kwatancen wani mai duba. Out of curiosity sai ta je, da ta je mutumin ya gaya ma ta Damien zai mutu. Ta harzuƙa da wannan zance ta zage shi tatas, ta kirashi da maƙaryaci. Sai ga shi da safiya aka kirata akan Damien yai hatsari, bai jima da kawoshi asibitin ba ya mutu. Ba shiga rarrashin Cassy ina nuna ma ta lokacin Damien ne yai...
Bayan kwana huɗu da mutuwar Damien na je na samu Cassy akan ta kai ni wajen mai duban nan, ina so nima ya min duba. Da farko ta ƙi saboda tana tunanin kar na je a gaya min abinda zai ɗaga min hankali amma da na nuna ma ta koma minene zan jure ba zan tada hankali ba sai ta yarda...
Mutumin da mu ka je irin sufi ɗin nan ne, yana yin sa da kuma turancin sa ya daɗa tabbatar min da ba zai wuce ɗan ƙasar India ba ne.
Muna zuwa ya kalleni ya ce *Aashiƙan* yai murmushi wanda na rasa gane murmushin ko na minene. Tun kafin na ma sa bayanin mi ya kawo ni ya ce ya sani na zo ne akan maganar soyayya na gyaɗa ma sa kai ina sawa a raina wannan mutumin da gaske yana duba ɗin.
Na miƙa ma sa hannun dama na bayan ya buƙaci hakan. Ya sa yatsar sa yana bin zanen hannuna kafin ya ce *Makhtub* ya cigaba da cewa "ko sama da ƙasa za su haɗu sai kun yi aure" ya kalli ƙwayar idon na ya ce "sai dai za ku yi shekaru talatin kuna kewar junan ku" ba tareda na gama gane ma'anar maganar sa ba na ce "ka ce ni da Sa'eed za mu yi aure?"
Sai da yai dariya kafin ya ce "za ku yi aure"
Kalmar za mu yi aure kaɗai ya wadatar da ni duk wani bayani da ya ɗaura akai duk shirme ne a waje na.
Na ɗau maƙudan kuɗi na bashi sannan mu ka bar wajen sa zuciya ta cike da farin ciki.
Tundaga wannan rana na sawa kai na salama domin ance ni da Sa'eed za mu yi aure. Ko gayawa Sa'eed ban yi ba dan na san zai mun faɗa. Na riƙe abin a raina ni kaɗai...
Saboda ni Bayan Sa'eed ya kammala degree ɗin sa ya ɗora da masters domin mu samu mu gama makaranta tare. Wannan karan tun kafin ayi hutu na kira Baba na ce ba zan zo Nigeria ba saboda zan tsaya yin project ɗi na. Bai musa min ba ya amince kai tsaye. Da na kira Amma na gaya ma ta sai ta dinga mun faɗa domin ta san saboda Sa'eed ne na ƙi dawowa gida. Ni dai ban damu ba tunda Baba ya amince...
Kwamci tashi har Allah ya kawo mu ƙarshen karatuna inda ni Aaliyah Badamasi Bulama na kammala degree ɗina yayinda shi kuma masoyina Sa'eed Aliyu Modibbo ya kammala masters na shi.
Mun sa dogon buri a zukatan mu. Da mun dawo Nigeria kafin mu tafi bautar ƙasa zan sanar da Baba maganar Sa'eed saboda muna gamawa sai a mana aure. Kasancewa an tabbatar min ni da Sa'eed za mu yi aure sai ban sa a raina za a samu matsala ba musamman idan na tuna cewa Baba yana so na ba zai min auren dole ba sai dai...
........................
Cikin ikon Allah ba mu jima da dawowa ba aka tura Sa'eed bautar ƙasa chan Minna. Ni kuma Borno, ban ji daɗi ba dan ina so mu tafi bautar ƙasa tare. Na je na samu Baba a falon sa da letter ɗin da niyyar ya min hanya a maida ni Minna sai na tarar da wani zance marar daɗin ji.
Baba shi ya sa aka posting nawa Maiduguri saboda yana so na zauna kusa da gida.
"Baba na yi karatu a ƙasar waje ma balle kuma bautar ƙasa a chan wani state, za ku iya ganina duk lokacin da ku ke so fa" na faɗa da sigar sakalci.
"Aaliyah ki zauna a gida, ba na son ƙananun maganganu da na ke ji ana faɗa a kan ki"
"Baba wani magana kenan?" Na faɗa cike da tsoron tambayar da na yi da kuma amsar da zan iya samu.
"Aaliyah ba na son kusancin ki da Sa'eed. Dan kun yi makaranta ɗaya ba yana nufin ɗaya ku ke ba. Ki riƙe matsayin ki shima ya riƙe na sa"
Baki na rawa na ce " Baba ina son Sa'eed"
Bai yi mamakin kalamai na ba dan ya san da hakan tuntuni.
"Ko ma mi ki ke ji game da shi ki yakice shi. Na riga na miki miji"
Na fashe da kuka ina bashi haƙuri amma ko saurarata bai yi ba ƙarshe ma ya tashi ya bar min falon...
Kalmar an min miji yana da girma a wajena, hakan na nuna ba ni da 'yan ci kwata-kwata. Ya kuma nuna cewa banida ikon zaɓar mijin da na ke so sai dai a zaɓa min.
Sa'eed yana Minna bai san miya ke faruwa ba ni kuma ina Maiduguri ina fama da ƙunci. Wasa-wasa fa Baba ya ɗauke min wuta, yai biris da lamarina ya nuna matuƙar na cigaba da maganar Sa'eed a gidan nan zai aurar da ni tun ma kafin na gama bautar ƙasa na. Babu wanda ya damu da halin da na ke ciki, kowa nuna min ya ke bamu da ce da Sa'eed ba. Harta Jiji abinda ta ke nanata min kullum kenan. Sanah ce kaɗai ta yarda da soyayyata ta kuma supporting ɗi na...
Na turawa Sa'eed wasiƙa akan halin da na ke ciki amma har yau bai tura mini amsa ba. Ina kwance a ɗakina ina duba tsoffin wasiƙun Sa'eed Amma ta shigo ɗakina.
Na ɗaga ido na kalleta na kau da kai. Ta ajiye min wassu kaya a gabana ta ce,