Author : Asirin Jiya Category : African Stories & Novels
cikin damuwa. Idan ya tambayeta kuma ta ce ma sa ba matsala.
Yau ma su na cin abincin dare tare amma ya lura a takure ta ke kamar ba ta jin daɗin abincin duk da kuwa ita da kanta ta bada order abinda su Eliza za su girka.
"Mom is there something you are hiding from me?"
"Ofcourse not son, mi ka gani?"
"Mom kamar akwai abinda ke damunki, you always look disturbed. Like you are hiding something very important...."
"Zaid" ta katse shi
"I'm fine son, yes i look worried saboda yanzu ba da bane, but nothing else"
"Mom that night, twenty years ago...."
"Zaid!" Ta faɗa da ƙarfi.
"Shikenan tunda bakyason maganan"
Ajiye cokali ta yi ta ce " I've lost my appetite"
Sai da ta shige ɗaki ya sauke ajiyar zuciya. Ba zai manta abinda ya faru shekara ashirin da su ka wuce ba. He was only eight amma ya na iya tuno komai. Lokacin da Dad ya ɗauke shi daga London kullum sai ya tuna kukan Mom a daren ranar. The screaming, the cries, everything.
Maganan Aaliyah ya tuno da ta ce akwai babban al'amari a rayuwar Mom that he needs to know about. "Could it be related to what happened 20yrs ago?" Ya tambayi kan sa.
He was only eight years lokacin da ya rabu da Mom and ba ta taɓa neman sa ba. She stays in London all the while. Ya tuna lokacin da ta zo Nigeria ya ƙi ya je wajen ta. How she kneel and cried. Hawaye su ka gangaro ma sa. Lallai ne dole ya nemo diary ɗin Mom atleast he will find some answers there...
Ta ya Zaid zai tuno ma ta da abinda ta ke ƙoƙarin ɓoyewa iya tsawon rayuwar ta. This is too much for her.
Ta sa key ta buɗe drawer, ta fidda jakar da ta jima tana adanawa.
"If only you came Saeed, if only you came that day" ta faɗi hawaye na zirya a idon ta.
*"Ke ce zuciya ta Aaliyah, idan na rasa ki na rasa zuciya ta gaba ɗaya" * ta tuna maganganun sa lokacin da ya sanya ma ta zobe a hannun ta. Ta kalli yatsarta da ke ɗauke da tabon ƙuna. Ko ba zoben a wajen akwai shaidar zaman zoben a yatsar.
Gani ta ke kamar yau ne komai ya faru. Da saka zoben da kuma cire shi.
"Makhtub" abinda mai duban ya faɗa kenan lokacin da ta tambayeshi.
"Zan auri Saeed?" Tambayar da ba za ta taɓa mantawa ba kenan.
"Makhtub yarinya, rubutacce ne, ko sama da ƙasa za su haɗu sai kunyi aure. Sai dai....."
Ƙaran wayarta ya fargar da ita ta yi murmushi lokacin da ta ga Aaliyah ce.
Ta ɗauka wayar ta na murmushi, lokaci guda Allah ya haɗata da yarinyar nan amma ba ƙaramin shiga ranta ta yi ba.
...........................
Mom ba ta wajen aka yi zaman saboda Zaid bai ma sanar da ita ba. Idon Hajiya Fatima yai zuru-zuru lokacin da lawyer ya gama bayanin sa. "Wannan gidan da ku ke ciki na Aaliyah ce. Aaliyah, Ahmad ya bawa gidan nan"
Gidan da Aaliyah ba ta zauna a ciki na cikakken shekara ba. Ta ya Ahmad zai ma ta haka? Fatima ta tambayi kanta
"Hajiya Fatima, ina so ku daure ku yi zaman lafiya tsakanin ku. Idan ki ka cire wannan gida da Ahmad yai wa Aaliyah kyautar sa Aaliyah ta yafe gadon Ahmad. Daga ke, 'ya'yan ki sai Zaid ku kuke da wannan dukiya, kuma idan aka ce a raba kowa yai na sa waje ba za ku ji daɗi ba. Zaid shi kaɗai ne ɗa namiji dan haka ki bashi haɗin kai ya kula da ƙannen sa" lawyer ya faɗi ya na harhaɗa takardun da ya nunawa su Hajiyar.
Da Hajiya Fatima da Inna duk ba wanda ya ce wani abu har Zaid da lawyer su ka fita a falon.
...........................
Sai da aka yi sati biyu da dawowar su sannan Mom ta shirya ta tafi Maiduguri. A wannan lokacin Zaid ya samu damar bincika ɗakin Mom. Ya jima ya na dube-dube a ɗakin amma shiru bai ga diary ba.
Ya zauna akan gadon ta ya na haki.
"Kodai Mom ta tafi da shi Maiduguri ne ko kuma Mom ba ta da diary?"
Zuciyar sa ne ya tuno ma sa ɗaya daga cikin drawers ɗin a kulle ya ke da key. Ya tashi da sauri. Ya nemi key ɗin wajen bai gani ba. It's obvious duk sauran wajen ba a sa key ba sai last drawer ɗin definitely akwai abu mai muhimmanci a ciki.
Ganin neman key ɗin zai ɓata ma sa lokaci ya sa ya fita dan ya nemo guduma ya kwaɗe, ya san duk rintsi kafin Mom ta dawo zai sa a gyara ba za ta ma ganeba...
To his surprise wata jaka ya gani a cikin drawer ɗin. Tsohuwar jaka ce wanda aka yi yayinsu a irin 80's ɗin nan. Ya sa hannu ya ɗau ko jakar tsaftsaf ta ke ba ƙura ko dauɗa a jiki. Sai da ya zauna da kyau a tsakiyar ɗakin sannan ya buɗe jakar. Diary guda biyu ne a ciki sai album. Album ɗin ya fara buɗewa yana ganin hotunan da ke ciki. Hoton farko na Mom ne lokacin tana jaririya sai da ya jima yana kallon hoton kafin ya cigaba da kallon sauran, cikin hotunan da ya ke dubawa ya ga harda wanda Aaliyah ta bashi. Sai daya gama kallon hotunan sannan ya jawo ɗaya daga cikin diary ɗin ya buɗe date ya gani a sama sannan aka rubuta *The beginning*
Rufe diary ɗin yai ya kwashe komai ya maida cikin jakan sannan ya ɗau jakar ya fita daga ɗakin...
Tana kitchen tareda Abba su na girki ƙaninta Abdul ya shigo ɗauke da wayarta da ke ringing.
"Z Wamako na kiran ki Anty"
"Abdul ka maida wayar ka ga aiki mu ke zan kira daga baya" ta faɗi tana ƙoƙarin saita nitsuwarta.
"Tun ɗazu fa ake kira" Abdul ya faɗi yana miƙa ma ta wayar. Tana amsar wayar kiran ya kuma shigowa. Abba ya ce " ki je ki amsa wayar ki"
Haɗiye miyau ta yi ta amsa wayar tareda ficewa daga kitchen ɗin da sauri.
Minti biyar sai ga ta ta dawo fiskarta ɗauke da farin ciki. Abba ya kalleta ya ce " waye *Z Wamako*?"
"Ehm. Abba ƙawata ce da mukayi makaranta ɗaya. Zainab....Zainab Wamako sunan ta"
Kamar faɗin Wamako ya tsikareshi lokaci guda ya furta *Wamako*
"Abba ka san wani mai irin sunan ne?"
Ya jima bai ce komai ba, hankalinsa ma ba ya wajenta. Sunan Wamako ya taɓo ma sa wani tabo da ke zuciyansa tsawon shekaru.
"Abba are you Ok?"'
Yai firgigit ya ce " yes, yes princess"...
..............................
Ba ta sha mamaki ba da Abba ya amince da tafiyarta amma da sharaɗin za ta dawo kafin ƙarfe shida na yamma. Ko ba komai za ta samu ta yi abinda za ta yi kafin nan.
Driver ne ya kaita har gidan su Nawal. Kamar yadda ta tsara. Da dreban su ya tafi sai ta kira Nawal ta fito da motar ta su ka fita. Har cikin compound ɗin gidan su Zaid Wamako ta shiga da ita, su ka rabu akan za ta kirata.
Kiran Zaid ta yi akan ta iso ya ce ta shigo ɓangaren Mom.
A zaune ta sameshi yana karanta jarida.
"Wamako da gaske ka samu diary ɗin?"
Hararanta yai ya ce "idan ban samu ba zan kira ki ne"
"Oh. Ina diary ɗin? Ka karanta?"
"Aaliyah ki ke ko wace, I dont trust you. Ki faɗamin miyasa ki ke bibiyar Mom ɗina"
Ba ta bashi amsa ba sai ta buɗe jakarta ta fitar da wani diary daga ciki ta ce "wannan diary ɗin shi ya sa na san wacece Mom kuma shine dalilin da ya sa na ke bibiyarta"
Kallonta yai na wasu daƙiƙai sannan ya ce biyoni.
Ɗakin Mom su ka shiga inda ya fito da jakar da ya gani a drawer.
Lokacin da ya fitar da abinda ke ciki Aaliyah harda ɗan ihunta.
Zaid ya ce "lafiyar ki kuwa"
Aaliyah ta ɗan yi gyaran murya ta ce "duk farin ciki ne ya jawo haka"...
A ƙasa su ka zauna bayansu na jingine da gado. Nan su ka fara karanta diary ɗin Mom...
*TSOHUWAR💖SOYAYYA*
*©Azizat*
Wattpad @000Azee
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Free page
0️⃣4️⃣
*...........AALIYAH.............*
The begining
Suna na *Aaliyah Badamasi Bulama*. A faɗin garin Maiduguri suna Bulama suna ne da yai ƙaurin suna, gida ne da ya gaji dukiya da arziƙi tun Iyaye da Kakanni.
Mahaifina Alhaji Badamasi Aliyu Bulama ya fito daga wannan gida mai daraja, ya fito gidan kuɗi kuma ya nemi kuɗi ya samu. A wannan lokaci Alhaji Badamasi yana ɗaya daga cikin wanda su ka ƙara ɗaukaka sunan gidan su saboda yadda Allah ya buɗa ma sa arziƙinsa ya haɓaka sosai.
Mahaifina matan sa biyu, da farko ya auri 'yar dangi wato Hajiya Yana sai daga baya ya auri Mariyatou. A lokacin da ya auri Mariyatou yaran su huɗu da Hajiya Yana. Akwai Bukar, Falmata, Aliyu sai Sanah wacce ta ke 'yar shekara ɗaya a lokacin.
Mariyatou wadda kowa ke kira da Amma ƙanwa ce ga Alhaji Aliyu Sise Idrissa wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi a garin Agadez da ke ƙasar Niger, asalin su Buzaye ne.
A yadda labari ya zo mana Mahaifina ya je Niger biki ya haɗu da mahaifiya ta. Kyawunta ne ya ja hankalinsa farat ɗaya. Wadda a take ya sa a nema ma sa ko ita wacece. Kasancewarta ƙanwa ga Alhaji Sise sai abin ya zo ma sa da sauƙi saboda Alhaji Sise abokin sa ne.
Wata goma da auren Mariyatou aka haifeni. Kyau da farin fata ta duk daga mahaifiya ta ce. Tun da aka haifeni kuwa Amma ba ta sake haihuwa ba sai dana shekara biyar kafin ta haifi ƙanina Muhammad sannan Usman, Yahya da Musa su ka biyo baya.
Mu shabiyu ne a wajen Mahaifinmu. Hajiya Yana na da 'ya'ya bakwai Amma na kuma biyar.
Tun tasowata na ke cikin gata, daga wajen Amma har zuwa wajen Baba. Yadda na ke da kyau ya sa kowa ke son ɗauka ta, haka nan koyaushe akayi baƙi Baba zai sa a kawo ni, ina maƙale da shi.
Yawan surutu da tambayoyi su ne ɗabi'un da su ka bayyana min tun a ƙarancin shekaruna. Ba na taɓa gani na yi shiru.
Hajiya da Amma su na zaune lafiya, Hajiya ta riƙe girmanta a matsayinta na babba hakan ya sa Amma ta kwantar da kai su ke zaman su lafiya tamkar ya da ƙanwa.
Babban gida Baban mu ya gina a Maiduguri. A lokacin gidan mu na ɗaya daga cikin gidajen da ake kwatance da su saboda girma da kyau. An wadata cikin gidan da kayan alatu na more rayuwa kuma tsarin ginin gini ne mai tafiya da zamani saboda wasu ƙwararrun turawa ne su ka zana gidan.
Parts huɗu ne a gidan na mu, akwai ɓangaren Baba wanda ya fi ko'ina girma, yana amfani da ƙasa wajen ƙarɓan baƙinsa wanda ke ƙunshe da falo biyu da ɗakuna uku, akwai babban dining room da ke ɗaukan kujeru ashirin, sai sama inda ya ke kwana falo da ɗakuna biyu da ɗakin karatu. Akwai ɓangaren Hajiya da ke ɗauke da falo da ɗakuna huɗu da kitchen, dining da store sai na Amma na ma haka. Bangaren ƙarshe kuma na yara maza ne falo ne da ɗakuna huɗu shima. Chan ta bayan gidan kuma an gina quaters na ma su aiki, sannan akwai garden a gidan wanda aka wadata da rumfuna guda huɗu domin zaman shaƙatawa.
Lokacin da aka haifeni da 'yan watanni kaɗan Amma na ta koma makaranta dan haka rainona kwacokam ya koma hannun Jijiɗo matar ɗaya daga cikin masu gadin gidan mu.
Jiji kamar yadda na ke kiranta ita ta raine ni kuma ita na fi gani a matsayin uwa, saboda na taso na ga ita ke min duk wata ɗawainiya da uwa ke wa ɗiyar ta. Sabo mai tsanani ne ya shiga tsakanina da wannan salihar mata. Lokacin da aka yayeni kam daina damuwa ma na yi da Amma na, domin hatta 'yan gidan mu kirana su ke da 'yar gidan Jiji.
Lokacin da aka sa ni a makaranta kuwa, a kullum idan na tashi Jiji ce za ta zo ta shirya ni ta bani abinci sannan ta ɗauke ni ta kaini wajen mota inda direba ke jiran mu. Da na dawo kuwa ita za ta cire min kaya ta min wanka ta bani abinci, wani lokaci idan na dawo ban ganta a ɓangaren mu ba to gidan su zan wuce da gudu kamar yadda na ke kiran quarters ɗin su. Ba na taɓa yarda na dawo wani ya min hidima idan ba Jiji ba, duk ranan da Amma ta yi yunƙurin kula da ni sai na fara kuka, wani lokaci har da birgima akan dole Jiji ce za ta cire min kaya ko Jiji ce za ta min wanka ko bani abinci, randa na ishi Amma kuwa har mangareni ta ke yi.
Akwai wani lokaci ina shekara shida Jiji ta tafi ƙauyensu lokacin za a yi bikin 'yarta Nana, sati biyu su ka yi achan ba su dawo ba. Cikin sati biyun nan kuwa sai da nayi rashin lafiya mai tsanani, ta kai sai da na kwana uku ma a asibiti.
Harta Baba da bai cika zama a gida ba saboda yawan tafiye-tafiye sai da yai kwana biyar a gida yana kula da ni, hakan ya rage min kewar Jiji. Ranan da Jiji su ka dawo kuwa ai a gidan su na kwana na ƙi komawa ɓangaren Amma na. Jiji Allah bai ba ta yawan haihuwa ba, yaranta mata biyu. Lokacin da aka aurar da 'yarta ta fari ba ni da wayo gaskiya, dan Jiji ta ce lokacin ina shekara uku ne. Ina shekara shida kuma aka aurar da autar ta Nana. Abinka da fulani auren wuri duk aka mu su. Asma'u tana shekara shabiyu aka aurar da ita Nana kuma shauku, duk cikin su ba wanda yai makarantar boko.
Bayan bikin 'ya'yanta sai ya zamana ni ne kaɗai 'ya a wajen Jiji, tana sona sosai kamar 'yar da ta haifa a cikinta, hakanan nima ina sonta sosai.
.....................
Bazan taɓa mantawa da wannan rana a tarihin rayuwata ba, wata ranar jumu'ah a shekarar 1975 lokacin ina shekara bakwai a duniya. Na dawo daga makaranta ko cire uniform ban yi ba na yiwo gidan su Jiji saboda ban ga Jiji a sashen mu ba.
Ina shiga falon su na fara ƙwala sunan Jiji. Sai ganin wani yaro na yi ya fito daga ɗakin su Jijin ɗauke da radion Baffa Manu. Na ƙwalla ƙara na fara cewa "ɓayawo, ɓayawo,...Jiji ɓayawo a gidan ku" na fita da gudu na yi hanyar gate, ban tsaya ko ina ba sai gaban Baffa Manu. Ina haki na fara ce ma sa ga wani yaro ya shiga gidan su ya sace mu su radio. Da farko Baffa Manu bai gane ba sai daga baya ya gane ya fara dariya. Ina cikin yi ma sa bayani sai ga yaron yana tahowa inda mu ke. Na nuna shi da yatsa na ce "Baffa ga ɓayawon nan, ga shi chan da radiyon ka Baffa"
Baffa ya kalleshi yai dariya ya ce " ba ɓarawo bane Aaliyah, ɗa na ne"
"Ƙarya ne Baffa, ɓayawon radio ne fa"
Sai da Baffa ya jima yana min bayani kafin na gamsu ba ɓayawo ba ne musamman ma da na ga wannan yaron da ya zo miƙawa Baffa Radiyon ya yi.
Abinda ban sani ba alokacin shine, wannan yaron ba radiyo ya zo sata ba, ba kuma wani abin daban zai sace ba illa zuciyar Aaliyah. Wannan fari dogo siriri kuma yanƙwanannen yaron ba radiyo ya zo sata ba illa Zuciya ta....
*..............SA'EED...........*
Fulani boy
Ƙauyen Durum shi ne asalina. Inda aka haife ni, iyaye da kuma Kakanni na.
Baffa na ya rasu ina shekara biyu a duniya hakan ya sa lokacin da Inna ta ta sake wani auren aka maidani gaban kaka na Modibbo.
Suna na Sa'eed Aliyu Modibbo amma kasancewar sunan Harɗon ƙauyen mu ne da ni shi ya sa ake kirana da Harɗo ko kuma Lamiɗo, yawanci ma anfi kira na da Lamiɗon.
Mahaifiyata ba a Durum ta sake aure ba, a Lame mijin da ta aura ya ke, shi ya sa na tashi ba uba ba uwa sai kakanni.
A shekarar 1975 Kakana Modibbo ya rasu lokacin ina da shekaru shabiyu a duniya. Kaka na bai haihu dayawa ba, yaran sa biyar, biyu maza uku mata.
Baffa Manu shi ne ɗan fari sai Goggo Ma'u, Baffa na sannan Goggo Sadiya da Goggo Aminah.
Da farko an shirya zan koma wajen Inna ta a Lame sai kuma Dadda wato Kakata ta nuna hakan bai dace ba kasancewa Innata ba ishashshen lafiya gareta ba, dan tunda ta yi haihuwarta na uku ta ke jinya. Ƙarshe Baffa Manu ya zo ya ɗauke ni ya tafi da ni Maiduguri inda ya ke aiki a chan.
Baffa Manu bai da niyyar yin nisa da Durum, sai dai auren sa da Hafsatu (Jijiɗo) shi ya sa ya tattara iyalinsa yai nisa da gida.
Baffa Manu ya taso gida ɗaya da 'yar ƙanwar Dadda wacce ake kira da Hebbini. Hebbini ta so Baffa Manu sosai hakanan Dadda ma ta nuna ita ta ke so ya aura. Sai dai shi kam ya jima da fara son Hafsatu kuma baida niyyar auren wata ba ita ba. Da ƙyar da siɗin goshi Dadda ta amince ya auri Hafsatu, sai dai tunda ta shigo gidan Dadda ta ke takura ma ta. Zagi da habaici ga uwa uba mugunta Dadda ke wa Hafsatu, wanda ko lokacin da ta fara samun ciki sai da ta yi ɓari saboda rashin kwanciyar hankali. Cikin shekara ɗaya da auren Jijiɗo sai da ta yi ɓari sau biyu. Nan Dadda ta fara ƙorafi akan dole Baffa Manu ya auri Hebbini. Shi kam harga Allah ba zai iya ba dan yana son Hafsatun sa sosai. Daga ƙarshe da takura yai yawa ya nemi izini a wajen Modibbo ya ɗauki Hafsatu su ka bar Durum, bai tsaya a Jama'a ba ko Toro ko Bauchi sai ya lula har Maiduguri.
Tunda ya tafi sai da ya shekara uku kafin ya zo gida lokacin Baffa na zai yi aure. Da farko Dadda ta yi fishi da shi ta ƙi ma sa magana amma daga baya ta haƙura dan zuri'a ta shiga tsakaninsa da Jijiɗo dan 'yar su tana shekara biyu a lokacin...
..................
Wata Ranan Jumu'ah a shekarar 1975 kwana na ɗaya a garin Maiduguri ina