Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Malikussaifi IBNI Ziyazzinun Book 1 Complete Hausa Novel by Aliyu Abubakar Sharfad

Author :  Aliyu Abubakar Sharfad Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 5

6K to 9K   out of 12.3K words

daya 5

fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi

rubutawa Mr Hausa Ebooks

"Da WAHASHINFALA yaga haka sai yace ""Baba yanaji kace dani Sarki bayan ba"

"haka bane, kuma ka kirani da wani suna wai MAALIKUS-SAIF bayan ni sunana WAHASHINFALA."

"Tsoho ya dubeshi yayi murmushi yace ""Katahone daga garin DUWAR kuma yau kwananka sittin kana tafiya kafin kazo nan, kuma"

WAHASHINFALA ba sunanka bane sunan ka wanda Allah ya nufa shine

"MAALIKUS-SAIF, mahaifinka kuwa shine Sarki ZIYAZINUN mai mulkin kasar"

"HAMRA'U YAMEN wanda ya rasu, kuma kaine wanda adduar Annabi Nuhu zata fada a kansa zai samu mulkin duniya baki daya, ya kuma tambayarsa ya MAALIKUS-SAIF yanzu mai kake bautawa? Ya amsa masa da cewa ""Eh nidai naga"

"mutanen nahiyar mu suna bautawa rana da wata ne, amman ni bana bauta masu sabo da nasan Allah ne ya halicceni saidai ban samu Wanda zai koya mani yadda zan bauta mashi bashiyasa ni ban bauta wa komai Tsohon yace ""Ka dogara ga Allah yanzu zan musuluntar da kai. MAALIKUS-SAIF yace na dogara ga Allah, Tsohon yace kace na gasgata babu abin bauta sai Allah kuma na gasgata da Annabi Muhammadu Annabi da zaizo a karshen zamani da Annabin wannan zamanin Annabi"

Ibarahim alaihissasatu wassalam.

MAALIKUS-SAIF ya maimaita shahada kamar

"yadda Tsohon nan ya fada masa. Bayan ya gama sai Tsoho yace masa ni sunana Shehu ZAJJADA, yanzu tunda ka musulunta ka zama dan uwana kuma ya zama dole na taimakeka nasan ka fito neman littafin kogin NIL zan fada maka inda yake amman"

inaso kafin ka tafi ka kwana a nan domin inason sanar dakai hanyoyin bautar Allah.

Shehu ZAJJADA ya koya wa MAALIKUS-SAIF alwala da zikirin Allah suka zauna suna ta zikiri har cikin dare sannan shehu ZAJJADA ya mike ya daga hannu ya roki

Allah ya kawo masu abinci daga arzikinsa.

Nan da nan sai ga abinci da abubuwan sha

"iri-iri a gabansu, MAALIKUS-SAIF ya cika da dunbin mamakin ganin wannan abinci saboda baiga yadda ya kawoshi ba. Shehun ya umarceshi da yaci abinci amman kafin ya fara ci yace Bismillah."

MAALIKUS-SAIF ya fadi haka ya fara dibar

"gara abinka da maijin yunwa. Haka yayita ci har saida yaji ya koshi sannan ya sha ruwa, sannan ya kwanta ya huta."

"Kwanciyarshi keda wuya bacci ya kwasheshi, shi"

kuma Shehun ya ci gaba da zikirinsa.

Can da gari ya waye Shehun ya tada MAALIKUS-SAIF yayi masa wa'azi sannan

"ya kuma cewa ka dogara ga Allah, zaka kubuta da duk wani yanayi da ka samu kanka."

Sannan ya zagaya da shi bayan wannan dutsen ya nuna masa yace yanzu

"kabar dokinka anan domin baya da amfanin tafiyar da zakayi dashi, ya nuna masa yace kabi gefen kogin nan kayi dama zakayi tafiyar kwana uku zakaga wani fili, bayan ka wuceshi zaka kuma ganin wani kogin mai matukar girma dan girmansa"

"babu iyaka, to saika tsaya a nan. Akwai wata dabba mai suna HATSHA."

Ita wannan

"dabba tunda Allah ya halicceta idan rana ta fito daga gabas tana daga tsakiyar wannan kogin sai tayita tsalle wai sai ta kamo rana, idan rana ta tsaya daidai a sama sai bakinciki ya kamata, sai ta fito da kanta daga bangaren gabas tayita turmutsa kanta a cikin yashi dan hushi, haka kuma idan rana ta koma gabas sai tayita tsalle da niyyar"

"ta kamota har rana ta fadi, idan ta fadi nan ma sai ta fito da kanta a bangaren yamma"

ta rinka turmutsa kanta a yashi nan ma dan haushi.

To idan kaga wannan dabba tana

"tumurmusa kanta a cikin wannan yashi to kar kaji tsoro ka kana gashin wuyan wannan dabbar ka dafeta, bazataji komai ba saboda girmanta, kai koda cikin idanunta zaka shiga bazataji komai ba. Ka zauna kana makale a kanta har ta maida kanta yamma, bayan ka sauka zakaga wani mutum, to ta dalilin wannan mutumin zaka"

samu wannan littafin.

Daya gama wannan bayanin sai MAALIKUS-SAIF yayi

"godiya Sannan yabi wannan hanyar da Shehun ya nuna masa, ya shafe kwana uku yana wannan tafiyar har ya isa wannan filin da Shehun ya fada masa...."

Anan zan dakata

Zamu cigaba zuwa Gobe Ana yin comment yan uwa

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN

littafi na daya 1 part 6

post by Shuraih 99%

.

Isar sa keda wuya kuwa yaga wannan dabbar tanata tumurmusa kanta a cikin yashi kamar dai yadda Shehun ya sanar dashi.

Nan da nan sai yayi maza ya dane kanta har

"rana ta fadi,takai bakin gabar daga bangaren yamma, koda MAALIKUS-SAIF yaga haka sai ya fado daga kanta ji kake tik!. Ya tashi ya fara tafiya."

"Can yana cikin yafiya sai yaga wani mahayin doki a sukwane ya yi yo kanshi, koda mahayin yazo gab da MAALIKUS-SAIF da niyyar bankeshi sai MAALIKUS-SAIF"

"yayi sauri ya banke dokin, haka suka rinka yi har sau shidda ko da mahayin dokinnan yaga haka sai ya zare takobinsa ya kaiwa MAALIKUS-SAIF Sara da suka shi kuma yana gocewa, hardai ya harzuqa MAALIKUS-SAIF, MAALIKUS-SAIF ya dubi"

"mayin sai yace kaidai Allah wadaranka ragon banza, ai ba haka ake gwanimtar yaki ba, haka kawai mutum yana tafiya ka tasar masa dan ganin yana kasa Kai kana doki,"

"kuma ga makami a hannunka, bari in nuna maka yadda sadaukai suke nasu sha'anin."

"MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya damki wuyan dokinnan da hannun dama, ya kuma sake yin wif! Ya shaqo Wuyan mahayin da hannun hagu ya daga sama ya jinjina shi sannan ya saukeshi a hankal1 ya ce ""Kaga yadda sadaukai suke nasu"

"lamarin""."

"Da ganin haka sai wannan mahayim dokin ya sakko daga bisa dokinsa ya tsaya gaban MAALIKUS-SAIF ya yaye kyallen dake rufe a fuskarshi koda ya yaye sai MAALIKUS-SAIF yaga shema mace ce ba namiji ba ne ya dubeta yaga kyakkyawa ce, sai tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN koda yaji ta kira"

sunansa sai yace kekuwa yaya akayi har kika san suna na? bani labari mana.

"Yarinya ta fara da cewa ""Suna na DAMATU, na samu labarin kane a wajen"

"mahaifiyata wacce itace Sarauniyar bokayen birni KAIMARA, sunan ta Bokanya AKILA."

Wata rana muna zaune da ita sai nace mata ta buga mani qasa taga waye

"wanda zai aureni, sai ta amsa mani da cewar Wanda zai aureki sunansa MAALIKUS-"

"SAIF na ainahi amman yanzu ana kiransa da suna WAHASHINFALA, kuna asalinsa"

"dan wani Sarki ne mai suna ZIYAZINUN Sarkin kasar hamra'u yemen amman yanzu yana qasar wani sarki mai suna AFARA'U, bayan an kwana biyu, sai tace mani shi"

wannan wanda zaki aura ya nemi auran wata yar Sarki aka nemi ya kawo kan wani

dan fashi kuma gashi can ya dawo.

To a wannan lokaci sai na rinka damunta da

"yaushe zai zo garin nan? Sai ta rinka ce mani ai ya kusa Zuwa, sai yau kuma dana sake tamayarta sai tace dani inyu maza ai gakacan ma ka iso, amman ta fada mani cewa inyi qoqarin yaqarka, indan naga baka da niyyar cutar dani sannan ka kama"

"wuyan dokina sannan ya dagani daga ni har dokin, sannan ya saukemu a hankali to"

"Wannan shine wanda zan aura, saboda haka kaji na kira sunanka kada kayi mamaki."

"Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan yarinya ta fadi wadannan batutuwa a kansa sai ya gasgata zancenta, amman a fili sai yace da ita ""Ke kuwa wannan da qaryar tsiya kike, sannan kin iya shirya batu, domin wannan mutumin da ki ke fada to ni ba ni bane, kedai kawai kinyi niyyar ki yaqeni kikaga babu nasara shine kika shirya"

"wannan zantuka""."

"Koda 'DAMATU taji haka sai tayi murmushi sannan tace ""Daman"

"uwata ta fada mani cewa kona fada maka bazaka gasgata ba, kuma kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin NIL, kuma babata itace zata taimaka maka ka"

dauko wannan littafin.

Tana gama wannan bayani sai ta yaye lullubin dake a fuskarta.

"MAALIKUS-SAIF ya dubeta ido cikin ido yace yanzu ina babar taki take? Tace tana gida, yace to mu tafi izuwa gareta."

"Sai DAMATU tace ""A'a ai a kaidar wannan garin bako baya shiga, domin kuwa tarihi ya nuna wa mutanen wannan garin cewa wani"

"bako ne zai zo ya sace shi wannan littafin tarihin NIL wanda ka fito nema, su kuma wadannan mutanen tun kaka da kakanni wannan littafin shine abin bautarsu, tun lokacin da suka samu labarin cewa wani bako ne zai zo ya sace wannan littafin sai suka tsafe garin, suka sana' anta wani gunki mai suna GAMMAZI wanda duk lokacin da bako ya shigo zai dinga îhu yana Ga... Bako! Ga Bako! Daga nan sai a kama bakon a yankashi wannan dalilin ne yasa bako baya shiga, amman duk da haka, babata ta fada mani cewa idan kazo qofofin shiga garinmu ka lissafa qofa ta tara sai ka duba zakaga wata bishiya a kusa da wannan qofar zakaga akwatu ka shiga ciki sannan ka girgiza igiyar sai mu jawo dakai daga cikin kwatun mu shiga dakai cikin"

garin.

Koda DAMATU ta gama bashi wannan labarin sai ta haye dokinta ta tunkari

qofar birnin nasu.

Shi kuwa MAALIKUS-SAIF sai ya dinga bin sawun dokinta har ya fara hango

katangar birnin KAIMARA.

Daga nan sai ya juya bangaren gabas ya fara qirga

"qofofin shiga garin koda ya qirga ta tara, da ya hango kofa ta goma sai ya dosheta, Kamar yadda 'DAMATU ta fada masa, to daya isa bakin qofar nan sai ya boye ajikin wannan bishiyar da yake duhun dare ne ba wanda zai iya ganinsa, can yana tsaye jikin bishiyar nan sai yaga ana sako akwatu daga kan katangar, koda ya sakko qasa sai yaje ya shiga cikin wannan akwatu, sannan yaja murfin akwatin ya rufe ya girgiza"

igiyar sau uku.

Su kuma can bokanyanya AKILA da DAMATU da sukaji an girgiza

wannan igiyar sau uku sai suka jawoshi suka shiga dashi cikin birnin.

"Da suka isa gida, sai bokanya AKILA ta kawo masa abinci da ruwan sha, bayan ya gama sai ya kwanta, bayan ya huta sosai bokanya AKILA tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN.MAALIKUS-SAIF ya amsa mata da cewa yawwa, kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin kogin NIL, kuma nice"

zan taimakeka saka makon auren yata da zakayi.

Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka

"sai yace wai meye amfanin wannan littafin da har jama'ar wannan gari suke bashi tsaro sosai kuma har suke bauta mashi? bokanya AKILA tace shi wannan littafin a cikinsa ne akayi bayani yadda za'a zuqo kogin NIL, kuma duk kasar data mallaki wannan littafin to fari na rashin ruwa bazata samesu ba, kuma qasar zata samu arziki da yalwa na albarkacin qasa, haka kuma duk mutumin da wannan littafin ya zamto a"

hannun sa to shi zai mallaki duniya.

Saboda haka tin iyaye da kakanni mutanen

wannan qasa suke girmamashi kuma suke bautamashi.

Kuma tarihi ya nuna cewa

"wani baqo zaizo ya dauke shi wannan littafin, saboda haka ake bawa wannan littafin kyakkyawan tsaro."

A wannan lokaci sai mutanen birnin KAIMARA sukaji gunki

"GAMMAZI yana cewa ""Yaku mutane birnin KAIMARA ga bako ya shigo maku wannan birn?"", ya fadi haka har sau uku nan da nan Sarki.. Ya fito shida tawagarsa aka rinka bincike lungu-lungu, sako-sako har dare yayi amman basuga wannan bakon ba."

"A can cikin gidan bokanyanya AKILA kuwa, MAALIKUS-SAIF yaji hayaniya ta"

"yawaita sai yace da bokanya AKILA ""Amman dai bazasu shigo nan ba ko?"", sai bokanyanya tace ""Kada ka damu bazasu shigo nan ba ya kuma tambayarta yace meyasa kikace"

bazasu shigo ba? bokanyanya tace ai duk manyan bokayen Sarki KABRUNU su dari

"uku da cittin (360) nice shugabarsu, a karkashina suke kuma su waddan nan bokaye sune suke tsaron wannan littafi dan haka ba yadda za' ayi su shigo wannan gida."

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN

littafi na daya 1 part 7

post by Shuraih 99%

.

"Da gari ya waye, Bokanya AKILA ta aika DAMATU gidan makwaftansu da yake masunci ne ta siya masu wani katon kifi, da DAMATU ta kawo sai Bokanya AKILA ta yanka kifin ta kwashe duka kayan cikin kifin ta saka qafafun MAALIKUS-SAIF a cikin kifin ta mayar da dinke cikin kifin; sannan ta dauko wani qaton tsutsu ta daura"

"masa a wuya, sannan ta daura mashi igiya a girji, Sannan ta sakashu cikin rijiya, tace kada ka damu nayi maka wannan ne domin na bata hankalin bokaye ma' abota tsafi da"

Sarki zai sasu bincenka.

Bokanya AKILA ta shirya ta tafi fada da zuwanta fada ta

"iske fada ta cika makil, ta fadi gaban Sarki tayi gaisuwa takoma mazauninta ta zauna."

"Zaman ta keda wuya sai Sarki KAMARUNU yace da ita daman ke muke jira, domin jiya GAMMAZI yayi mana kuwwa cewa wani bako ya shigo mana birni, to inaso ki"

sa yaranki su binciko mana inda wannan bako yake.

Nan da nan Bokanya AKILA ta

umarci wadannan bokayen dari uku da cittin (360) dasu buncika qasa su gamo inda wannan baqon yake.

Bokaye suka dukufa suka zana alkalaman duba bisa rairayi suka

"shiga aiki, haka sukayita yu har tsawon wani lokaci, su zana su goge su sake zanawa su kuma gogewa su shafe... Can sai suka tsaya da wannan duban sukace munga wannan baqon."

Koda Sarki KAMARUNU yaji wannan bokayen sunce haka sai yayi

farat! Yace a ina kuka ganshi maza ku gaya mani.

Can sukace shidai wannan bako

"gashi mun ganshi cikin duhu kuma kifi ya hadiyeshi, ga kuma wani tsuntsu ya ratayoshi, da sarki yaji haka sai yace wannan wace iriyar maganar banza ce kuke fada haka mara ma'ana."

Sai Bokanya AKILA tayi farat ta rufesu da fada tace na fada

maku cewa ku daina cin abinci da yawa domin yana hanaku kuyi aikin ku yanda ya kamata amman kunqiji ai ga irinta nan yanzu kun binciko wa Sarki shirme.

Koda

"Sarki yaji haka sai ya fusata yasa hauni ya sare wa Bokaye biyar kawuna, sannan aka tashi daga fadanci."

Koda Bokanya AKILA ta koma gida sai ta fito da MAALIKUS-

"SAIF daga cikin rijiya ta fito dashi daga cikin kifin sannan ta kwance mashi tsutsun data daura masa, kana ta kwashe duk abinda ya wakana a fada ta fada mashi."

"MAALIKUS-SAIF yace lallai kina da yawan hikima, badan kinyu mani haka ba da"

"da tuni bokayen nan sun gano ni, haka sukayita fira da Bokanya AKILA tare da yarta DAMATU har dare ya raba sannan suka kwanta bacci."

"Da gari ya waye a rana ta biyu, Bokanya AKLA ta samo wata barewa ta daura mata fuka-fukan tsuntsu, sannan ta sa MAALIKUS-SAIF ya durkusa"

gaban

"barewar ta daura mashi ita ta kuma daura wata igiyar ta raba qafafun barewa da qasa, ta shirya ta yafi fada."

Da zuwan ta fada sarki ya umarce ta data sa bokayen nan da su

buga gasa su nemo inda baqo yake.

"Nan da nan bokayen nan suka tsundum aik1, can"

sai bokayen nan suka dago sukace sun ganshi.

Cike da zumudi Sarki ya tambayesu

"yana ina? suka kada baki sukace ai gashi can wata barewa ta tashi sama dashi, nan da nan Sarki ranshi ya qara baci yace me yasa kuke kawo mani wasa ne? Kun tabajin ance yau ga barewa da fuka-fukai?, wannan ai rainin hankali ne yasa aka kuma yanka"

bokaye biyar nan dai fada ta tashi.

"Bokanya AKILA ta tafi gida tana dariya, taje ta kwance MAALIKUS-SAIF suka"

cigaba da hira.

"A rana ta uku Bokanya AKLA ta samo wata babbar tasa, ta yanka wata dabba ta juye jinin a cikin wannan tasar, ta kuma samun wata tasar da dora a cikin tasar da ta zuba jinin, Sannan ta umarci MAALIKUS-SAIF daya shiga cikin tasarnan zauna,"

bayan ya shiga ya zauna.

"Sai ta kama hanya ta nufi fada, isarta keda wuya ta umarci"

"bokayen dake karkashinta akan su fara aiki. Nan suka dukufa, bayan wani dan lokaci suka dago sukace munga wannan baqon a cikin wani kogi na jini, sannan banda wannan kogin da yake ciki akwai wani kogin wanda shi babu komai a cikinsa, jin haka sarki ranshi ya qara baci ya umarci hauni daya kara sare kawunan bokaye goma, sannan yace da bokanya AKILA ke ya kamata ki duba mana inda wannan"

"baqon yake tunda su sun kasa,"

bokanua AKILA tace to tunda yau saura kwana biyar

"bikin mu na shekara to a ranar zan kawo maka wannan baqo, koda jin haka sai fuskar Sarki ta fadada da murshi a haka aka tashi daga fada."

"Bayan kwana biyar yaune Bokanya AKLA tayiwa Sarki KAMARUNU alqawarin kawo masa baqon daya shigo wannan gari nasu. Tunda sanyin safiya MAALIKUUS- SAIF ya fara jin hayaniyar mutanen wannan gari, cikin firci ya tashi yace mekuma yake faruwa ne tace ai na manta ban fada maka ba yaune muke bikin shekarar mu kuma a cikin dakin da wannan littafin yake anan muke bikinmu, saboda haka kayi"

zamanka acikin gida nida hannuna zan kawo maka wannan littafin.

Nan fa

"MAALIKUS-SAIF yanuna shi sam baiyarda ba saidai ta tafi tare dashi, dole kuwa hakan tayi tatafi tare dashi amman kafin haka saida ta bashi wani bakin ruwa na tsafi"

"tace ya watsa qa jikinsa, watsarshi keda wuya yaga ilahirin jikinsa ya zama baki"

"kamar yadda fatar 'yan garin suke, Bokanya AKILA ta bashi jakarta ta bokanci ya rike, tana tafe yana binta a baya har suka fito daga cikin gidan."

Fitowarsu keda wuya

"suka tadda bokayen nan dake qarqashin Bokanya AKILA a bakin gidanta suna jiranta tana qarasawa inda suke suka dunguma sai dakin bauta,"

koda suka kusa shiga sai

"MAALIKUS-SAIF ya qarasa kusa da Bokanya AKILA ya miqa mata jakarta, ita"

kuma cikin rada ta qara jadda mashi kan cewa kada ya kuskura yayi yunqurin daukar littafin nan ya amsa mata da to amman badan ya yarda da shawararta ba.

"Koda Bokanya AKILA ta isa cikin dakin bautar sai gaba daya mutanen dake dakin bautar sukayi wa littafin sujjada bayan Sarki KAMARUNU ya fito dashi daga maboyarsa ya dorashi bisa wani taburi, ganin sunyi sujjada ga wannan littafin yasa MAALIKUS-SAIF ya taho a hankali cikin sanda, yazo inda littafin nan yake ya miqa hannu da niyyar ya dauko shi sai kawai yaga littafin ya fado qasa tim! Ya fara"

zagayeshi.

Jin qarar fadowarshi yasa Bokanya AKILA; Sarki KAMARUNU da

"sauran jama'ar dake wannan dakin bautar suka dago daga sujjadar da suka yi, aiko sukayi ido biyu da MAALIKUS-SAIF, nan fa suka hau dukansa baji ba gani, MAALIKUS-SAIF shima ya hau dukansu,"

kasancewarsu suna da matukar yawa sai

"wani daga cikin.dakarun ya zagayo ta bayan MAALIKUS-SAIF ya sammaceshi ya bugesa a tsakiyar kai, nan take MAALIKUS-SAIF ya baje a kasa baiko shura ba, koda ganin haka sai Sarki KAMARUNU yayi godiya ga wannan littafi sannan ya umarci wasu dakarunsa dasu je su jefa MAALIKUS-SAIF cikin wata tsohuwar rijiya"

dake a bayan gari.

Bayan sun dauki gawar sun jefata a wannan rijiyar ne suka dawo

suka sanar da Sarki KAMARUNU. Sannan Sarki KAMARUNU yace da jama'a aci gaba da shagalin biki.

Ita kuwa Bokanya AKILA koda taga an kashe MAALIKUS-

"SAIF sai hankalita yayi mugun tashi kasancewar tasan irin son da yarta ""DAMATU takewa MAALIKUS-SAIF saboda haka ta sulale ta koma gida ba tare da sanin kowaba."

"Koda tafada wa DAMATU abinda ya faru a dakin bauta, kuka °DAMATU ta dinga yi da qyar Bokanya AKILA

3 / 5