Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Malikussaifi IBNI Ziyazzinun Book 1 Complete Hausa Novel by Aliyu Abubakar Sharfad

Author :  Aliyu Abubakar Sharfad Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 5

3K to 6K   out of 12.3K words

ta

"karbeshi, ta rungumeahi tana kuka domin farinciki da murna da suka kamata."

Sannan

ya fada mata duk sharuddan da aljana ta fada masa. Anan Sarki da matarsa suka sama wannan yaro suna WAHASHINFALA.

"Bayan an samu kwananki Kamar kwana Arbain da dawo da WAHASHINFALA wurin Sarki AFARA'U sai matar Sarki ta sami ciki, murna kan murna wurin Sarki AFARA'U da matarsa DAHASHANATU basai an fada ba, gashi suna murna aljana"

ta dawo masu da WAHASHINFALA gakuma DAHASHANATU tana da ciki.

Duk

gari akayita taya Sarki murna. Hakadai lokaci yayita tafiya har lokcin haihuwar DAHASHANATU yyi tahaifo ya mace aka saka wa yarinyar suna SHAMATU.

Ita

"wannan yarinyar farace kuma sai ya zamto Kamarsu daya da WAHASHINFALA. Wannan lamari ya baiwa Sarki AFARA""U tare da duk sauran mutane mamaki saboda sudai gasu bakake amman gashi sun haifi farar mace, balarabiya, kuma gashi tayi kama da wannan yaro WAHASHINFALA, haka dai sukayita manaki."

"A lokacin da WAHASHINFALA yakai shekara bakwai, sai ya bukaci yanason ya fara hawa doki, sarki yasa aka dauko masa wani dan karamin doki, da WAHASHLFALA yaga wannan dokin sai ya rainashi yace shi bazai hau wannan karamin dokin ba, shi babba yake so. Sarki yasa aka mayar da wannan dokin aka"

kawo masa wani baki ingarman doki mai digo-digon fari a wuyansa da kirjinsa.

"WAHASHINFALA yace wannan doki yayi masa, yayi tsalle ya dare kansa yayi"

sukuwa a gaban jama'a yana dawowa gabanSarki yana tirjiya.

Daga nan

WAHASHINFALA ya fara koyon yaki da takobi kuma cikin kankanin lokaci ya

kware a harkar fada da takobi yazama kaf yaran dake sa' anninsa bawanda zai iya ja dashi har manyan ma.

Ganin haka yasa Sarki AFARA'U ya dinga alfahari dashi kuma ya ware masa masu yimasa hidima.

Wata rana Sarki yana zaune a fadarsa da yan majalisarsa ana fadanci can saiga

bokan Babban Sarki mai suna SAKARAJUNA ya shigo fadar sarki da yan majalisa

suka mike domin girmamawa ga wannan boka saboda sanin matsayinsa a gurin Babban Sarki wato SAIFURRA'ADU wato shugaban Sarki AFARA'U.

Boka

"SAKARAJUNA ya zauna, bayan sun gaisa da sarki ne sai boka SAKARAJUNA"

"yace masa yazo kasarsa ne ziyara, daga haka akaci gaba da fadanci daga can sai Boka SAKARAJUNA yaga WAHASHINFALA zaune kusa da Sarki."

Sai Bokan nan ya

"tambayi Sarki cikin rada mai ya kawo wannan farin yaron nan, kuma mai yake yi a"

cikin kasarka? shin baka da labari cewa irinsu ne zasu mulki duniya kuma su maidamu bayinasu bayan sun karkashemu.

Nan take Sarki AFARA'U ya fadawa

"bokan nan maganganu masu sanyaya zuciyar Boka SAKARAJUNA ya yarda, da suka nitsa ne cikin hira sai Sarki AFARA'U yake bawa boka labarin cewa ai matarshi ta haihu shekaru biyar da suka wuce ta haifa masa ""ya mace."

Nan da nan boka ya

"bukaci da akawo masa yarinyar ya ganta, Sarki yasa aka kawo masa SHAMATU dan boka ya samata albarka."

"Da boka ya daga ido ya kalleta sai yaga ai fara ce balarabiya,"

kuma gashi tayi kama da wannan yaro WAHASHINFALA wanda Sarki yace ba dansa bane.

Nan da nan boka yayi tsafinsa ya gani cewa lallai wannan yarin ya

SHAMATU yar Sarki AFARA'U ce kuma wannan yaro ba dansa bane. Sai ya umarci daya mayar da wannan yaran cikin gida.

Sarki ya tura SHAMATU da WAHASHINFALA suka koma cikin gida. Nan dai

"Boka ya sake buka rairayi sai yaga ita wannan yarinya wanda zai aureta farin mutum ne, kuma shine wanda zai mulki duniya, sai ya zaci ko WAHASHINFALA ne, sai ya fusata yace wa Sarki ya zama dole ya kashe wannan yaron WAHASHINFALA in kuma yaki to zai aika wa Dan uwansa Boka SAKARADUSA, ya fadawa Sarki SAIF ce wa ""Sarki AFARA'U ya ajiye wani farin yaro kuma idan ya taso to duk zai"

"halakar damu ne, sannan kuma ya mayar da wasun mu bayi."

Boka SAKARAJUNA

"ya kare da cewa kaga kuwa idan Sarki SAIF yaji wannan batu to labudda zai halaka ka da ki da jamaaar taka baki daya."""

"Koda Sarki AFARA'U yaji wannan magana daga bakin Boka SAKARAJUNA, sai hankalinsa yayi kololuwar tashi saboda yasan indai har wannan magana taje kunnen"

Sarki SAIFIRRA'ADU to kashinsa ya bushe.

Koda gama wannan tunani sai yace da

"boka SAKARAJUNA daya bashi nan da kwana biyar zaiyi shawara, boka ya yarda da hakan."

"Boka yayi wa Sarki sallama ya nufi masaukinsa, yayin da shikuma a"

"bangaren Sarki AFARA'U ya zurfufa kogin tunani na neman mafita, yana cikin wannan haline na tunani Wazirin sa mai suna HARISU ya fado masa arai."

Waziri

"HARISU ya kasance mutum ne mai hangen nesa, saboda sanin yakamata da kuma hangen nesashi ne yasa Sarki AFARA'U ya nadashi Wazirinsa."

Wanda ada yake da

mukamin Sarkin gida.

"Koda Sarki AFARA'U yazo nan a tunaninsa, sai ya kira wani barde yace yayi"

maza gidan Waziri HARISU ya kirashi yanzu yanzu.

Bardennan ya amsa da angama

ya shugabana. Ya haye dokinsa ya sukwaneshi. Lokacin da barden nan ya dawo shida Wazirin HARISU Sarki yana cikin turakarasa.

Saboda haka shima Waziri sai ya

"zarce inda turakarsa Sarkin take. Bayan ya nemi izini Sarki ya bashi, ya kunna kai cikin dakin. Koda shigar sa sai Sarki ya bashi labarin duk yadda sukayi Boka SAKARAJUNA akan WAHASHINFALA. Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron numfashi ya aiye yace ""abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan..."

Zamu cigaba

MALUKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN

littafi na daya 1 part 3

posted by Shuraih Usman

@ https://dlhausanovels.com.ng

Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi

na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron

"numfashi ya aiye yace ""abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan wannan lamari tunda kaidai kanason yaron nan bakason rabuwa dashi ko kadan."

"Mezai hana mu jewa da wannan boka kalamai masu sanyaya rai da kwantar da hankali, muyi masa alkawarin cewa Indai har wannan yaro ya girma mukaga"

take taken shi nason rushe mana masarauta da kuma hanamu bautar zahalu to sai mu

"kashehi."""

"Koda Sarki AFARA'U yaji wannan zance sai yace ""Maraba da fasihin"

"Waziri, hakika hakan za'ayi"".Da haka Waziri yayi wa Sarki sallama ya tafi gida."

Bayan kwana biyar Kamar yadda Waziri HARISU yayi wa Sarki AFARA'Uu

"bayani, cikin sa'a kuwa suka shawo kan boka SAKARAJUNA."

Sannu a hankali soyayyaya mai karti ta kullu tsakanin WAHASHINFALA da

SHAMATU ba tare da Sarki AFARA'U ko boka SAKARAJUNA sun sani ba.

Bayan wasu yan shekaru kowa a cikin wannan garin saida ya fahimci soyayyayar dake tsakanin WAHASHINFALA da SHAMATU saboda haka boka SAKARAJUNA ya fara kokarin rabasu ta hanyar alqalaman tsafi amman abu ya

farkara.

Ganin haka ya shirya mashi makirci ta qarkashin kasa.

"Sannu a hankali manema suka fara fitowa neman auren SHAMATU, cikinsu kuwa harda WAHASHINFALA wanda shine kan gaba."

Saboda haka Sarki AFARA'U ya

"nemi shawarar boka SAKARAJUNA, koda boka yaji harda WAHASHINFALA sai yayi dariyar qeta yace ""Inaso gobe a tattatara mani manemanta a kofar fada""."

Daga

"haka Sarki AFARA'U yasa aka rubuta takardu zuwa ga masu neman auren ""Yarsa SHAMATU. Yakira wani bafadensa ya aikesa."

"Washe gari tunda sanyin safiya masu neman auren SHAMATU suka fara bayyana,"

"bayan wani lokaci, suka gama bayyana a bakin fada, cikin mutanen nan kuwa harda"

WAHASHINFALA dashima ya shiga layin manenan SHAMATU.

Bayan wani

"lokaci suka fara jin bugun tabura gami da busar algaita hakan ya tabbatar masu da cewa Sarki yana tafe. Haka kuwa akayi Sarki AFARA'U ne sanye cikin alkebba, daga damansa Wazirin sa ne mai suna HARISU Sannan daga hagunsa kuma boka"

SAKARAJUNA.

"Koda ya karaso bakin fadar, bayan yayi masu barka da zuwa saiya"

umarci boka SAKARAJUNA daya fada masu abinda ake buqata ga duk wanda yakeson SHAMATU.

"Boka SAKARAJUNA ya fara magana kamar haka ""inayi wa"

"bakinmu barka da zuwa, dalilin dayasa muka taraku anan shine, duk wanda yake son auren SHAMATU to sadakinta shine zai kawo mana kan Shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI, koda wadannan jaruman da yayan attajirai dake neman auren SHAMATU sukaji haka sai suka fara sulalewa, cikin kankanin lokaci wajen ya"

zama fetal ba kowa sa WAHASHINFALA.

Koda ganin haka sai boka yayi

murmushin keta yace da WAHASHINFALA jarumtarka ta burgeni sai ka shirya nanda jibi ka kama hanya.

Daga haka suka juya izuwa cikin gidan sarautar.

"Bayan kwana biyu WAHASHINFALA ya shirya cikin bakin sulke, yayi wa"

SHAMATU da Sarki AFARA'U sallama y kama hanya cike da kewar garinshi da kuma masoyiyarshi SHAMATU.

Alamarin SHAMATU kuwa tunda masoyinta WAHASHINFALA ya tafi ta shiga

damuwa kasancewar bata da tabbacin cewa ko zai dawo da rai.

Ahaka ta kwana ta

"wuni a rana ta biyune tana bacci tayi mafarki da annabi HALLIRU alaihissasatu, yace mata ai ita taimakon WAHASHINFALA yana hannunta."

Cike da mamaki ta kalleshi tace taya ya? Sai yace da ita a gidan akwai wata matattala ita wannan matattalar ta

"kasance idan ka taka ta farko lafiya ta biyu bazakata lafiya, yacigaba da cewa saboda"

haka ya zama maki dole kije ki sanar dashi.

Koda SHAMATU ta farka cikin dare

"bata zame ko ina ba, sai bargar dawakai, cikin sanda ta kanto doki ta haye cikin sa'a kuwa ta tadda masu gadin kofar sunata sheka baccisu."

Ba tare da tsoron komai ba ta

bude kofar ta fice.

"Kasancewar WAHASHINFALA be dade da lafiya ba ita ta bi bayansa koma dokin data dauko irin na musammanne wanda ba koda wane lokaci ake fani da suba,"

tadauki lokaci tana tafiya cikin kurmumun daji ba tare da tsoron komai ba.

Aiko cikin

"sa'a ta fara hango WAHASHINFALA wanda yana gab da shiga cikin gidan shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI ta kwala masa kira, koda yaji ankwala masa kira sai yayi turus yaja ya tsaya ba tare daya waiwayo ba."

Ganin shirun

yayi yawa yasashi ya waiwayo koda ganin wadda ta kirasa sai fuskarshi ta fadada da murmushi.

Ya tabayeta keko meya sa kika biyoni? SHAMATU tace Zan baka labari amman ba yanzi ba.

WAHASHINFALA shida SHAMATU sukayi kokari suka shiga cikin gidan

"kasurgumin dan fashin nan SA'ADUNUJJANJI can suka hango wata matattakala,"

nan take WAHASHINFALA ya doshi inda matattalar nan take ya mika kafa ya taka ta farko ya kuma taka matattala ta biyu daga takawarshi sai ya rufta ciki wasu

"wukake guda biyu masu matukar kaifi, da tsini tare da suka nufoshi zasu rabashi biyu"

cikin azababben sauri SHAMATU ta rugo da gudu ta rikeshi sannan tayi wuf ta jawoshi waje.

Ai koda ya ganta sai ya cika da matukar mamaki ya tambayeta ya akayi

kikasan haka? Nan ta kwashe labari kaf ta fada masa.

Da yaji haka sai yace gashi

"yanzu adduarki taci. Nan dai SHAMATU ta ci gaba da bashi labarin wannan matattala tace Ita wannan matattalar idan ka taka ta farko lafiya to tabiyu ta Sharri ce dan haka idan ka taka ta farko to saidai ka tsallake ta biyu ka taka ta uku. To haka sukayi har suka isa can sama da suka isa sai suka riski wata katuwar kofa ta baki karfe saboda haka sai MALUKUSSAIF ya leka ya hango wani mutum baki, kato,"

"mai manyan idanuwa gasu jajaje tamkar garwashin wuta, gashi da katon hanci kamar"

"gwangwani, ga katon kai Kamar mangala Sannan ga manyan labba kai kace fata aka"

shinfida.

"Daga gefen damansa mutane arbain ne haka ma bangaren hagunsa. Koda WAHASHINFALA yaga haka sai ya dawo bayan wannan kofar ya labe, koda ganin haka sai SHAMATU tace da WAHASHINFALA shi wannan mutumin na tsaki baki"

"mummunan shine SA""'ADUNUJJANJI."

Suna zaune can sai SA'ADUNUJJANJI yace

"da mutanensa kai kutsaya nifa kamar motsi nake ji fa? Inaga daya daga cikin mutanen da kuka kamo ya kwance, daya daga cikin ku ya tashi ya duba."

Yana gama rufe

"bakinsa, daya daga cikin Sadaukan nan ya tashi domin ya dubo yana zuwa daidai inda kofar nan WAHASHINFALA yayi wuf ya sare masa kai, ita kuma SHAMATU ta janyeshi ta boye gawar, da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yaji shiru sai ya kuma turo wani barden nan ma dai WAHASHINFALA ya sare masa kai kamar yadda yayi wana farko, haka SA'ADUNUJJANJI yayi ta aiko da mutane har akazo kan na biyar nan fa kowa tsoro ya darsu a zuciyarsu aka rasa Wanda zai tashi shikuma WAHASHINFALA dayaga anjima babu wanda ya sake fitowa sai ya kutsa kai ya shiga cikin dakin ya tsaya gabansu koda SA'ADUNUJJANJI yaga WAHASHINFALA sai yace kai kuma wannan karamar halitta daga ina haka? Kuma"

maiya kawoka nan harka halaka mani mutane?

WAHASHINFALA ya amsa masa da

"cewa babu ruwanka daga inda najo, kuma dalilina na zuwa na wajenka shine nazo ne na kasheka, Sannan na tafi da kanka a matsayin sadaki."

Koda SA'ADUNUJJANJI

yaji wannan magana sai ya bushe da dari sannan yace kai yanzu wannan yaro har

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN

littafi na daya 1 part 4

post by Shuraih 99%

"zaka iya fada dani? Dubeka fa ka dubeni na ninka ka sau goma, yanzu kaiko wannan saurauyin wane ne ya turoka ka aikata wannan abu gareni? WAHASHINFALA"

cikin bacinrai yace ba'a sani ba idan zakayi shirin yaki kayi.

SA'ADUNUJJANJI

yace zo mu shiga cikin gidana akwai fili isasshe wanda zai ishemu ni da kai.

"SA'ADUNUJJANJI ya tashi yaransa suka biyoshi a baya, WAHASHINFALA ma"

"ya biyo shi a baya, suka shige wasu manyan soraye guda uku suka riski wani fili, da suka isa wannan fili sai SA'ADUNUJJANJI ya juyo wajen mutanen sa yace idan muna yaki da wannan yaro kar wanda ya kawo mani dauki koda kuwa kunga yana"

"kokarin samu galaba a kaina ne, ku tsaya kawai kuyi kallo."

Koda yaran

"SA' ADUNUJJANJI sukaji haka sai su dukansu suka babbake da wata mahaukaciyar dariya, domin sun san cewa ba ta yadda za' ayi wannan karamar halittar ya iya kai"

shugaban nasu kasa ko yazo da matemaka bare ya zo shi kadai.

Suka amsa da sunji sun yarda.

"Can kuma SHAMATU data ga sun shiga wannan gida, sai ta fito daga inda take boye ta hau kan wani dutse inda zata iya ganin karawar da za'ayi tsakanin"

SA'ADUNUJANJI da saurayinta.

SA'ADUNUJJANJII ya yiwo kan WAHASHINFALA yana gurnani tamkar zakin

"dakejin yunwa ya hango nama, WAHASHINFALA shima ya zare tashi takobin yayi dauki kan sa suka kaure da yaki bají-ba-gani har dare yayi rana ta take."

Can suna

cikin wannan dauki ba dadi dine sai WAHASHINFALA ya taka wani karamin dutse ya durkushe kasa.

SA'ADUNUJJANJI ya daga takobinsa ya kawo wa

WAHASHINFALA wani wawan sara koda SHAMATU taga haka sai ta tabbatar da cewa indai har saran nan ya dira a kan masoyinta to saidai wani bashi ba.

Sai tayi

wuf! Ta zaro wani gariyo daga cikin sulkenta ta wulwuloshi ta jefi

"SA'ADUNUJJANJI dashi, sao gariyon ya sare shi a hannu wanda hakan yayi sanadin faduwar takobin dake hannunsa."

WAHASHINFALA ya rike takobinsa a hannu yayi

"niyyar sarewa SA'ADUNUJJANJI kai amman sai ya fasa yace tashi ka dauki takobinka muci gaba da yaki, domin bazan kasheka ta hanyar yaudara ba, sai kuma ya juya ya fuskanci dutsen da SHAMATU take tsaye yace jinjina gareki ya"

ma'abociyar bege.

Koda SA'ADUNUJJANJIl yaji haka sai ya tashi ya dauki takobinsa

"suka ci gaba da yaki, haka suka cigaba da wannan gwabzawar har tsawon kwana uku a rana ta ukun ne shuka tsaya domin su huta, ko wannensu ya samu guri ya zauna yana haki."

Su kuma yaran SA'ADUNUJJANJI sun cika da mamaki ganin irin

jarumta da kuma sadaukartaka ta WAHASHINFALA.

"Can da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yace ""Yaro me yasa lokacin da takobina"

ta fadi ka samu damar kasheni amman kaki kace bazaka kasheni da yaudara ba? kuma naji kamar kana magana da wani.

WAHASHINFALA yace wannan yarinyar

"da zan aura itace ta cillo mani wuka, kuma da ita nake magana shiyasa nace bazan kasheka da yaudara ba."

WAHASHINFALA ya sakko da SHAMATU daga kan dutsen nan ya shigo da ita

cikin wannan filin ta zauna kusa da shi.

SA'ADUNUJJANJI yace lallai yau zan shayar da ku gidauniyar mutuwa daga kai har ita sannan naje har kasarku na kashe

"uban wannan yarinya na fatattaka garin gaba daya, na kwashe dukiyoyinsu sannan na"

koro bayi.

"Koda sukaji haka sai suka zabura suka cigaba da sara da suka, a takaice dai saida WAHASHINFALA da SA'ADUNUJJAN.JI suka shafe tsawon mako duga cir"

"suna gwabza yaki amman babu wanda ya samu nasara a kan dan uwansa, har saida"

makamansu suka lalace nan take kowa ya yada nashi suka tsaya sukayi cirko-cirko kamar zakaru suna kallon juna suna muzurai.

"Can sai SA'ADUNUJJANJI yace ""Kai"

"yaro! Yanzu tunda makamanmu sun gaza yanzu sai mu fidda sharadi, WAHASHINFALA yace wane sharadi? SA' ADUNUJJANJI yace sharadin shine yanzu zamuyi kokawa nida kai duk wanda ya kada wani sau uku to shi ya cinye"

"wannan gasar, idan kai ka kadani sau uku to kai ka cinye wannan gasa sai kayi yanda"

"kakeso dani, haka zalika idan ni na kadakai sau uku to sai nayi yanda nakeso dakai."

"Koda WAHASHINFALA yaji haka sai ya yarda da wannan sharadin, suka fara kokawa kici-kici, can sai SA'ADUNUJJANJI yayi wuf! Ya suri WAHASHINFALA ya daga sama zai fyada da kasa, kawai sai WAHASHINFALA ya Kama kunnen SA'ADUNUJJANJI ya murda cikin ikon Allah sai ga SA'ADUNUJJANJI ya fadi"

kasa tim!.

Haka dai WAHASHINFALA yayi ta kada SA'ADUNUJJANJI har sau

"uku, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro kayi nasara aikata abinda kakeso dani ya durkusa bisa gwiywoyinsa."

Da WAHASHINFALA yaga haka sai ya

"dauko gariyonsa yayi niyyar sare kansa, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro amman da zaka kyaleni, da raina, ka kuma riqeni na zama bawanka domin kila wata rana zan maka amfani."

Da WAHASHINFALA yaji haka sai ya ajiye wannan

gariyon yace gaskiya ne na yarda da maganarka.

SA'ADUNUJJANJI da kaf yaransa suka jinjina ga WAHASHINFALA sukace

"""Gaisuwa gareka ya shugabanmu"" anan suka kwana."

Da gari ya waye

SA'ADUNUJJANJI da yaransa suka zo gurin WAHASHINFALA suka kwashi gaisuwa Sannan suka zauna daga gefen WAHASHINFALA.

WAHASHINFALA

yace da SA' ADUNUJJANJI da mutanen sa to ai saiku tashi mu tafi kasar DUWAR domin kuwa nasan Sarki AFARAU yanacan yaba jirana.

"Nan da nan SA'ADUNUJJANJI suka dora wa giwayensu sirdi, shi kuma WAHASHINFALA da SHAMATU suka haye kan dawakansu suka kamo kan"

hanyarsu ta dawowa kasar DUWAR.

Bayan sun samu Kamar kwanaki uku suna

"tafiya sai suka fara hango katangar birnin DUWAR, anan sai shamatu ta rigasu shiga"

"cikin birnin dankada a gane cewar tare suke, takoma gida ba tare da wani ya ganta ba."

"A wannan lokacin kuma sai akayi sa'a boka SAKARAJUNA yace da Sarki AFARA'U cikin gatse zomu je bayan gari muga ko wannan yaron zai dawo, Sarki,"

Waziri da sauran fadawa suka fito bayan gari suna diban hanya.

Can sai suka hango

"WAHASHINFALA ga kuma SA'ADUNUJJAN.JI da yaran sa bisa giwaye, ""kagani ko gashinan abinda kaja mana kasa wannan yaron ya tsokano mana"

"SA'ADUNUJJANJI, ya matsa mashi ya sanar dashi cewa mu muka turo shi, gashinan"

"sun sakoshi a gaba suzo su halakamu""."

"Koda jin haka sai Sarki, boka da jama'ar gari"

"suka ruga da gudu cikin gari suka rurrufe kofofin gari, da suka karaso sai WAHASHINFALA yasa daya daga cikin yaran nan ya bubbuga kofar amman ba'a bude ba."

Koda WAHASHINFALA yaga haka sai yayi tsawa ya umarci

SA'ADUNUJJANJI daya karya kofar birnin.

Nan da nan SA'ADUNUJJANJI yayi

"wa toron giwarsa qaimi ya bangaji kofar garin ta karye, suka kutsa kai izuwa cikin"

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN

littafi na daya 1 kashi na

2 / 5