Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rainon SOJA Book 1 Complete Hausa Novel by Mamanteddy

Author :  MAMANTEDDY Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 11

27K to 30K   out of 31.5K words

yana kan yi. “Hummmm....Dogon Numfashi ta sauke tana maida kallon ta ga Ali Haidar, da yake sakin mata murmushin nan nasa, fuskar sa ya tara ƙasumba tamkar ba Daga Aikin soja yake ba. Duk wata cikar zati na Cikakken Namiji saurayi ya gama bayyana masa, Don a wannan lokaci yakai 27 . Yana sanye cikin ƙananun kaya na Hutawa da shan iska , White t.shirt da boxer wani Black mai yarfin kakin Soja...He looks neat and breathtaking💔 Bin ta yake da innocent face ɗin sa kana taga ya ware hannun sa yana furta “ taho mana Jidder na”.

Murmushi Tayi cike da jin dadin ganin nasu don bata yi tsammanin Dawowan su ba ta nufi Aliyu tana zama tare da shigewa jikin sa tana furta “ Oyoyo Ya Haidar 💃🏻”....Kee ina Ma'eesha ? ” .


Muryar Khalil ya katse su , Wanda a hankali ta ɗago tana kallon sa kana ta kalli Aliyu sai ta fara kame-kame tana cuno bakin ta gaba . Ya Khalil bakayi kyawata ba ne kake tambayar Ma'eesha ita kaɗai? . Zama yayi a kujeran dake fuskantar nasu kana yace“ Nayi kyawar ku duka, yau aka yi Hutu ina result din ki ? Ina kuma nata nasan ta she is talented, Shiyasa na ƙagu naga na nawa tayi ?”. Hummmm Ai ba tare muke ba ....kaman ya ba tare kuke ba ? Yess tana hanya zata shigo yanzu. Kamin Khalil ya ƙara magana tuni ta miƙe tana faɗin “ Lemme go and take shower , idan na dawo sai ka duba result din nawa ”. Bin ta da kallo Khalil yayi , kana ya kalli Aliyu wanda yake shan Lemun tsamin da yasa aka yi masa juise nashi. Shan Lemon sa yake tamkar baya jin mene suke faɗi.

Takaici ne ya kama khalil tabbas shi jikin sa bai bashi ba , Miƙewa yayi yana furta “ Ali baka ji menake cema jidderh ba? Wai kai wannan lemon amfanin me yake maka?. Kallon sa Aliyu yayi a Miskilance kana ya kalli Ruwan lemon hannun sa , motsa laɓɓan sa yayi tare da cewa“ Baka taɓa sanin mene lemon tsami ke sawa ba ko ragewa? , Tsayawa Khalil yayi kana yace “ Ban sani ba ”. Aje cup ɗin yayi yana kallon sa tare da gyara zaman sa kamin yace “Alright rage sha'awa , don Ni fa bana tsammanin Zan koma Bakin Aiki ba tare da Aure ba , da matata zan koma. “Wani irin kallo Khalil yayi masa idan da sabo ya saba da iskancin Aliyu baya ɗaukar sa da mutunci ko yaji kunyar sa na yayan sa ,ya dauke sa tamkar aboki ....mtswwwww Bad behavior, ya furta yana hararan Aliyu tare da Cigaba da cewa “ Na tsani wannan Ɗabi'ar naka Haidar, idan kaso ka Auri Huɗu a lokaci daya.

Wani irin dariya Aliyu yayi wanda sai da na ƙara kallon sa , gaba ɗaya ya sauya ya wani koma Arrogant har a Muryar sa. Dariya yayi irin ta Basawan soja “Hahahaha...”! Ai shikenan Ya Khalil dama na faɗa maka Ni mace ɗaya ba zan iya rayuwa da ita ba ,don ba zan samu biyar buƙatan.......Ɗaga masa hannu khalil yayi yana dakatar dashi kana yace “ Ka bari idan Daddy yazo sai kayi masa bayanin Aure kake buƙata , Ni Bara na leƙa naga Ma'eesha, na ƙosa naga yanda yanzu ta girma shekaru uku bamu ganta ba”.
Ok Ali ya furta yana kauda kan sa gyefe , yayin da Khaleel cikin sauri ya fice daga Falon ”.

**
Bayan mami sun fita ba daɗewa ruwan ya fara tsagaitawa, Ya zama sai dai yayyafi irin mai ƙarfin nan. Titin babu kowa kaman an share ko abun hawa babu masu wucewa kowa ya fake a mafakarsa. Ma'eesha ta hanga ita kaɗai tana tafiya tana rungume da hannayen ta alamar sanyi na kaɗata. Gaba ɗaya ta jiƙe sharɓammm sai tafiya take , komai nata a salɓi take yin shi alamu har ta gaji da tafiya. Fitowa Mami tayi daga moton jikin ta a mace zuciyar ta na kuka ta fara takawa ixuwa inda Ma'eesha take. Ɗan nesa da ita ta tsaya tana ƙare ma kyaƙyƙyawar fuskar ta kallo wanda kan ta ke ƙasa sam bata lura da Mami ba , har ta tako zuwa gaban ta .

Ƙafafun mami ta gani a gaban ta ,wannan yasa ma'eesha saurin Ɗagowa suna haɗa ido da Mami dake zubda Wasu irin ƙwallah...Cikin Sanyin murya tana Wangale mata baki cike da fara'ar nan nata ta furta “ Mami...”! Lumshe ido Mami tayi wasu hawayen na sauko mata kana cikin sauri ta furta “ Na'am Babyn Mami taho gare ni”. Da gudu Ma'eesha ta faɗa jikin mami data rage Tsawon ta itama tana Rungume Ta tsammmmm....Ina sonki Ma'eesha na , tayi maganan tana ƙara mannata da jikin ta . Ina sonki Nima mami. Caaakkk ta ɗauki Ma'eesha tana murmushi tare da cewa“ Yau Ali da Khalil sun dawo fa😄”.

Yeeeeee Mami muyi sauri Uncle sun dawo? Daddy fa? Moton suka shige kana Mami tace “ Jidderh ce tace ki fita ? Me Yasa baki fake a wani wurin ba? Yau sai na hukunta Jidder, yanzu zan kira Doctor Isma'il ya taho ya duba ki , za kisha magani ko Ma'eesha na?

Murmushi Ma'eesha tayi kana ta gyaɗa mata kai cike da yarinta ta furta “Eh mami amma kar ki ma Anti jidderh komai , laifi nayi mata ” . A'a nafa sanki bakya laifi Ma'eesha . To mami na kiyi Haƙuri ki yafe ma Anti Jidder.

Tsayawa Mami tayi tana kallon ta kana ta kai hannu tana kwantota bisa ƙirjin ta . A hankali take shafa bayan Ma'eesha tana cije laɓɓanta ita kaɗai tasan halin baƙin cikin da zuciyar ta ke ciki a halin yanzu .

**
Fitowa tayi daga Bedroom ɗin ta tare da isowa tsakiyar falon, sai ƙamshi take yi tana hura hanci .....Sanye take cikin rigar Atampha doguwa mai ƙaramar hannu an mata ɗinkin da ya kama jikin ta sosai . Dama ba gwanar saka Kallabi Bace haka ta fito Attachment ɗin kan ta na reto har tsakiyar baya , Wanda yake ɗauke da launin milk don ba bama baƙi ta sanya ba . Kunnen ta ɗaya cikin ear phone yayin da hannun ta ke ɗauke da Wayar ta. Plate shoe ta sanya tana mai isowa zuwa Tsakiyar falon Nasreen tayi tana wannan yauƙi tare da caɓe baki tana bin Ma'aikatan dake falon da Wani irin wulaƙantaccen kallo . “Barka da wannan lokaci Hajiya ”.

Muryar Ma'aikatan ya katse ta inda ta ƙara ƙare masu kallo a ciki ta amsa su da “ yauwa, tana wuce su tare da fitowa falon zuwa wajen farfajiyar gidan.....Babban magana gida ne na gani wani irin mahaukacin gida mai girman gaske wanda ya ƙayatu har ya gaji da ƙayatuwa. Gida ne zaka rantse da Allah unguwace guda ,don yafi girman wasu unguwan....Part part ne sun kai 7 amma ko wanne da bene bisa kan part ɗin , Benen ma biyu aka ɗaura ba Ɗaya ba. Gida ce da ka gani kasan na wani attajirin me kudin ne wanda irin su ma baka ganin su a gida Nigeria.....Abu ɗaya ya bani mamaki shine Yanda naga duk Girman gidan da kuɗin dake cikin ta ba'a Aje wasu masu tsoron gidan birjik kaman na gidan General Saleh Yelwa ba . Wannan ya sani tunani da kuma ƙaguwa na son ganin mamallakin wannan gida. Gani nayi Nasreen ta kai hannun ta tana bi ta lifta kamin tayi sama tana hayewa ixuwa wani irin falo mai ɗauke da Adon Golden komai na wurin .

“Hello , Hello babe ...” Maganan take jikin ta ko ina rawa yake yi kar-kar-kar tamkar zata kifa saboda tsoron wanda take wayar dashi . Al...Aliyu ina hanya don Allah mu haɗu kaji? Kasan ba zan iya rintsawa ba idan ban sanyaka cikin idanuwata ba......Yanzu Ruwan ya ɗauke zan taho guest house ɗin ka yanzu.

Duk maganan da take zuba shi take ba tare da ta jira jin mene Ali zai ce mata ba , Murmushi tayi tana datse kiran tare da furta “ Ohhh mah Handsome....Nayi kyawarka sosai. Ta furta zancen tana kutsa kan ta ixuwa Ƙaramin falon dake cikin babban falon da ta baro.


Wani attajirin Alhaji na gani sanye cikin shigar sa ta manyan mutane cikin faran shadda fari ƙal wanda tsadarta ma ƙwaƙwalwa ba zata ɗauka ba . A shekaru yakai 65 a duniya haka zaliƙa kan sa babu ɗigon farin gashi . Kallon sa tayi a kaikaice tana ɗan ƙasa da murya tare da cewa “ Abba nazo ne amsan Kuɗin Yes da No😱” .........................!






Masoyana free page zai ƙare a next page me kuka gani a wannan salon tafiyar 💃🏻tun a yanzu nasan abubuwan sun fara sauya maku😄badaƙalar na gaba ....shin waye wannan Abban da bai san Meye Yes da No ba😹? Ku Cigaba da biyo alƙalamin Aysha mmnteddy.

*Littafin na kudi ne book 1 zai ƙare a next page book 2 Kuma sai a fara payment nashi..... regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN.*
[12/15, 2:00 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*




Last free page
12
______________________

*Daga Wannan page din free page ya ƙare masu bin shafin kyauta wannan shine na karshe . Ga masu ɓukatar shiga group na rainon soja Regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN yan Niger zaku Turo katin Artel na 500f.*
______________________

Maman-teddy
Marubuciyar
My Lady boss
Walijaam
Siyasata
The Sexy Boss
Yar Aikina
Bafullatanan Ruga
Gidan Ƙwarata
The virgin maid
Ƙwarton manya
Ƴar maula
Sexxies House
Duniyar shahara x world
Mr romantic
Ƴar Waye?
Dijama yar Fulani
Habibi da'iman
Taɓarah
Ƴar tsakar gida
Da sauran su .
________________________

“Hidima ce ta makarantar ya taso Nasreena? . Muryar Dattijon mai cike da kamala ya katse Nasreen dake tsaye cike da rashin tarbiyya akan sa . Eh zaka bani kuɗin Yes and No. 😱 Kuma Abba kuɗi ne masu yawa Wallahi duka semestern nan babu littafi Mai tsadar shi. “To to badamuwa , kije Wurin baƙo ya baki kuɗin ,Allah yayi miki Albarka ” . Amin Abba ....ta furta tana Gimtse Dariya tana ficewa daga Falon . Mtswww Ɗan Rainin hankali, Wallahi Allah ɗaya kenan da ina da gado akan tsohon nan babu yanda za'a yi ba zan kashe shi kowa ya huta ba . Ai kashe shi kawai xanyi mu ƙwashi wannan ƙazamin Dukiyar da tayi masa yawa. Wai dama kuɗi na zama hannun jihili mara ilimin boko ɗan ƙauye irin wannan ? . Babu damuwa ko ba komai Ai Umma na tare dashi , idan ya mutu koda bata da ɗa bare jika dole zata samu wani Abun...Bagidajen banza kaxo duniya a asara babu ɗa bare jika sai tara mata har uku duka kuma babu wacce Allah ya bata ɗa ko ƴa da kai . Ni wallahi lamarin arziƙin sa da kuɗin sa har mamaki nake yi , mutum ya kusa rami amma sai long plans da yake dashi yau yana kasuwancin kaza ba tare da kin yi wani tunani ba zaki ji ya matsa to the next step tirrrr” . Duka Maganan take yi tana ficewa daga part ɗin tare da nufar ɓangaren Hajiya Falmata wato mahaifiyar nata.

**
#General Saleh Yelwa's estate.
Wallahi yau sai nayi ƙasa-ƙasa dake a cikin gidan , Mara kunya Shashashan yarinya , lallai kin manta Wacece Ni , Kin manta .....Mami don Allah kiyi haƙuri. Muryar Aliyu ya katse Mami dake mawa Jidder faɗa. Daddy kuwa Wani irin huci yake saukewa yana zaune don baya son ya motsa daga inda yake ran kowa ne zai ɓaci don General bai iya fushi ba sam . Yana riƙe da Ma'eesha dake ta ɗigar ruwa , Khalil ne ya katse Aliyu da cewa “ Wannan yarinyar Jidder muguwa ce ,bata da imani yanda take baƙa haka zuciyar ta yake baƙi,shi yasa Allah yayo ki baƙa a cikin mu . Daga yau duk ranan da kika ƙara wallahi kema sai kin bar cikin gidan nan ,yanda kika barta a ruwa kema sai kin zauna a ruwa . Don ko ruwan ta ɗauki duk inda rijiya take sai na sakaki na mintoci.

General ne ya Girgiza kai tabbas yasan Halin sojojin nasa zasu aikata abin da yafi wannan , don basu ɗauki hakan ma a babban hukunci ba . A'a duk abun bata kai haka ba , ku barni Ni da kaina zan mata hukunci kuma ko yanzu ai ba ƙyaleta nayi ba . Muryar Mami ya katse su.....wanke irin zafi zuciyar Jidder keyi ji take tamkar tayi kukan kura ta shaƙe Ma'eesha ta kashe ta sai suyi mata hukunci da zasu yi.

Cike da Tsananin ɓacin rai ta kai hannun ta tana dukan Table ɗin dake a gaban ta tana fashewa da kuka tare da miƙewa tsaye. Kallon ma'eesha tayi tana cewa “ To me zai hana ku kashe Ni saboda Ita! Ku kashe Ni ba bar duniya saboda tsintacciyar da ba'a san Asalin ta ba! Ɗifffff.............wurin duka suka ɗauke wuta da jin kalaman Jidder. Cigaba tayi da cewa“keeee Ma'eesha Bara kiji Mami Daddy Duka basu ne iyayen ki ba ,basu ne suka haife ki tsintar ki Yah Aliyu Yayi ya kawoki cikin gidan nan tun kina jaririya shine ya raine ki na tsawon shekaru kana Mami ta amshe ki ta.......Tas-tas-tssss-taasssss ,saukar marin da Khalil ke yi ma kuncinta ya yi sanadin dakatar da ita daga maganganun da take yi . Mari ne ya wanke ta dasu a lokaci ɗaya sunfi huɗu . Mahaukaciya kaiiiii Jidderrrrrr.......Yayi magana yana ƙara idanun shi sun kaɗa sunyi jaa a lokaci guda ya rasa wani irin Abu zai ma jidder .


Da Sauri Aliyu ya kai hannun sa yana dakatar dashi tare da taro shi yana furta “ Wannan duka ba abun ɗaga hankali ba ne? Take it easy please ” . Kuka mami ta fashe dashi mai tsuma zuciya da Sauri tana nufar inda janar yake da Ma'eesha hannun ta takai tana rungume Ma'eesha wacce ta tsaya duka tana bin su da kallo , ƙwaƙwalwarta na wani irin juyawa ta bakin ta na don furta kalma ko da ɗaya ce amma kuma ta kasa ” . Taho baby na ... Mami ta furta tana ƙara manna Ma'eesha daga jikin ta wanda sai a yanzu hawaye suka fara bin kuncinta. Kuka suke yi sosai ita da Mami yayin da Muryar Khalil ya katse su mai cike da Amo, kar ki kirani yayan ki inadai baki kira Ma'eesha ƙanwarki ba , wannan shine final say daga gare Ni . Kar ki ƙara nuna kin Sanni indai kin cire Ma'eesha daga cikin Ahalin mu. No.....” Jidder tayi maganan tana Cigaba da kukan ta don marin da Khalil yayi mata sai da ta zube a ƙasa don azaba. Akan ta yau ka dukeni abun da baka taɓa ba , Wallahi tsanarta na ƙaraji kuma dole ba zata zauna cikin gidan matsayin ƴa ba sai dai ƴar Aiki . Baki isa ba! Zan saka a karairaya ki jidder sai dai daga baya mahaifiyar ki tayi jinya! Muryar General Saleh Yelwa ya katse su cikin tsananin bayyanar ɓacin Ransa. Har wani gumi ke tsatstsafo masa ya rasa da wani ido zai kalli Ma'eesha wacce a yanzu babu sauran Alayen da ɓoye-ɓoye da zasu yi mata ”.

Mami da Gaske ne ke ba Mamana Bace, Haka Daddy Uncle Haidar shima....... Saurin saka hannu Mami tayi tana rufe mata baki kana tace “A'aaaa ....mami da gaske ne just say the truth a shirye nake da ko wacce irin ƙaddara , ko da na rasaki na rasa Daddy duka I will take it as my life destination Mami...Zubewa Mami tayi a ƙasa kalaman Ta suke tsinkar mata da zuciya wani irin kuka mami keyi mai tada hankali ji take ina ma zata mutu duka ta huta don bata da baki da idon da zata kalli Ma'eesha ta sanar mata da gaskiyar Al'amarin. Matsawa Jikin ta Ma'eesha tayi tana sa hannu tare da goge mata hawayen kana tace “ Mami kukan da kike yi ya nuna mun gaskiyar Kalaman jidder, Wasu irin ƙwallah ne suka biyo kuncinta kana tace “ Amma Yah Khalil shi Yaya na ne ko mami?....A'a shi ba yayan ki bane!

Muryar Ali ya katse wanda yayi Maganan kan sa tsaye . Duka saurin kallon sa suka yi , kamin ya cigaba da cewa “ Dukan mu ba familyn ki bane,maganan da jidderh ta faɗa duka gaskiya ne”.

“Haidar.....!

Wannan wacce irin magana ce so kuke ku kashe mun Ma'eesha? , Yarinya ce fa ƙarama? So kuke zuciyar ta ya buga

10 / 11