GASAR JARUMTAKA 5 littafin Yaki by NAJIBIBULLAHI.txt

Author :  naji Category :  Romance

Chapter   2 / 2

3K to 5.5K   out of 5.5K words

samun nasarar wannan yaki.
Nan take suka fashe da kukan farin ciki a lokaci guda, suna masu kankame juna a jikinsu.
Hmmm! A hakika a wannan lokaci duk Wanda ya Kalli wadannan JARUMAN dole ne ya jin-jina masu Kuma ya tausaya masu, saboda ganin yanda kamanninsu ya sauya izuwa jini.
Gaba dayan jikinsu ya rine da jini tamkar an tsoma su a cikin KOGIN JINI.

Suna cikin wannan hali ne, suka ji Waziri Mikilas ya kwalla masu kira cikin tsananin farin ciki.
Waziri Mikilas ya taho ne tare da Dakaru na musamman wadanda zasu yiwa su Sarki Zurmatu rakiya izuwa cikin fadar.
Cikin matsanancin farin ciki SARKI ZURMATU, SADAUKI USAMA, BOKA RAKUL, SARKI FALWAN, SARKIN YAKI DURKUL suka rugo inda Waziri Mikilas yake tsaye.
Nan take Sarki Zurmatu ya bawa wani Sadauki Umarnin cewa yaje ya tattaro Dakaru dubu Dari domin suzo su kone duk gawarwakin mutane da aljanun da aka rasa a filin yakin.
Nan take wannan SADAUKIN ya ruga domin cika Umarni. Shi dai wannan Sadauki mataimakin Sarkin yaki DURKUL ne, Kuma sunansa MAHUSH ya kasance jarumi Mai tsananin karfin damtse na gaban kwatance, domin da kadan Sarkin yaki ya fishi Jarumtaka.
Bugu da Kari Kuma Yana da rikon gaskiya da Amana a dukkan harkokinsa, wannan yasa ya kasance Amintaccen Sarkin yaki DURKUL, ya zamana cewa duk Inda Sarkin yaki zashi to tare suke zuwa.

Lokacin da SADAUKI MAHUSH ya tafi debo wadannan Dakarun, sai su Sarki Zurmatu suka dunguma gaba dayansu izuwa gidan sarautar.
Suna tafiya ana buga masu Gangar cin nasarar yaki, gaba dayan jama'ar gari suka jejjeru sahu-sahu suna yiwa SARKI ZURMATU kirari da yabo da jin-jina saboda samun wannan gagarumar nasara da sukayi.
Nan fa aka cika birnin BALLUS da kade-kade da bushe-bushe bisa wannan nasarar yaki da sukayi.

Bayan SARKI ZURMATU sun iso fada, sai yace da jama'arsa," yaku jama'ar birnin BALLUS kuyi sani cewa a yau Muna cikin tsananin farin ciki, ba don komai ba sai domin samun nasarar wannan yaki da mukayi Wanda a zahirin gaskiya tuni mun saduda cewa rayuwarmu ta xo karshe, Amma Kuma sai gashi mun samu nasara.
Saboda haka inason kowannenku ya je gida ya huta gajiyar wannan yaki daga Nan zuwa gobe, kowa ya taru a kofar fada ta domin na sanar daku sirrin da ya sa muka samu nasarar wannan yaki, sannan Kuma har ila yau a goben zan tabbatar da Alkawarina akan SADAUKI USAMA.
Saboda haka kowa ya tafi gida na sallameku.
Nan take kowa ya watse ya kama gabansa, Sarki Zurmatu ya wuce Kai tsaye izuwa cikin turakarsa Yana zuwa ya wuce inda matarsa take wato sarauniya KALTISA.
Koda KALTISA ta hango mijinta tafe, sai ta rugo ta rungume shi cikin tsananin farin ciki.
Bayan wani lokaci sai ta dubi Sarki Zurmatu fuskarta cike da tsananin damuwa sannan ta ce, ya Kai mijina tayaya akayi kuka samu nasarar wannan yaki alhalin naji ance SARKI KALJUL ne tare da rundunarsa suka kawo mana harin bazato.
Cikin tsananin murmushi Sarki ya ce, yake matata kiyi sani cewa samun nasarar wannan yaki da mukayi na dauke da wannan babban Ala'mari, saboda haka ki kwantar da hankalinki idan naje nayi Wanka na kintsa, zan sanar Dake komai.

Nan take Sarki Zurmatu yaje ya fesa Wanka sannan ya Saka kaya masu matukar kyau da tsada irin na manyan sarakunan duniya.
Sannan ya fito turakar sarauniya KALTISA inda ya isketa tuni ta gama jejjera Masa kayan abinci da Sha iri-iri akan wani Katon teburin Zinari.
Zaman Sarki Zurmatu keda wuya akan kujera, sai ya ji kamshin abinci kala-kala ya Doki hancinsa.
Nan take Sarki ya dubi sarauniya KALTISA ya ce, " yake matata ni da wa kike son mu cinye wannan abincin haka?
Kiyi sani cewa Koda mutum hamsin zasu taru bazasu iya cinye abincin da ke kan teburin Nan ba.
Cikin dariya sarauniya ta ce, saboda murnan dawowarka a raye ne, yasa ni da kaina nayi maka girki na musamman irin Wanda baka taba cin kamarsa ba.
Nan take Sarki Zurmatu ya sa matarsa KALTISA akan ta aika a kira GIMBIYA MARITA domin suyi tattaunawa ta musamman.
Nan take KALTISA ta kwalawa wata Jakadiyarta kira, nan da Nan Jakadiyar tazo ta durkusa a gabanta, KALTISA ta dubi Jakadiyar ta ce, je ki kira mana GIMBIYA yanxun Nan.
Cikin sauri Jakadiyar ta fice don cika Umarni.

Ba tare da Bata lokaci ba, Sarki Zurmatu ya hau abincin Nan da ci tamkar mayunwacin da yayi shekara guda Bai sa komai a bakinsa ba.
Lokacin da GIMBIYA MARITA ta shigo cikin turakar, sai ta rugo ta rungume Sarki cikin tsananin farin ciki.
Nan dai Sarki da iyalansa suka kasance cikin farin cikin kasance a wannan lokacin.
Bayan Sarki ya kammala cin abincinsa, sai ya dubi KALTISA da GIMBIYA MARITA a natse sannan ya ce to ku saurara da kyau domin na Baku labarin duk abinda ya faru a filin yaki da Kuma yadda akayi muka samu nasara.
Nan take Sarki Zurmatu ya kwashe gaba dayan labarin abinda ya faru ya bawa su GIMBIYA MARITA.
Cikin tsananin mamaki gaba dayansu suka kurawa SARKI ZURMATU idanu Kuma suka rasa ma abinda zasu ce.
SARKI ZURMATU yaci gaba da cewa, saboda haka a yanxu take nake so ku bayar da Gaskiya ga ubangijin musulunci saboda ta hakane zan iya jawo hankalin mutanen Birnina akan suyi Imani.
Batare da Bata wani lokaci ba, gaba dayansu suka amince.
Cikin tsananin farin ciki Sarki Zurmatu ya biya masu Kalmar Shahada suka maimaita.
Haka dai su Sarki Zurmatu suka kasance cikin aminci, Kuma suka kwashi lokaci Mai tsawo suna fira har dare ya raba sannan kowannensu yaje ya kwanta.

Kashe gari da sassafe bayan kowa ya kimtsa, sai gaba dayan mutanen birnin sukayi tururuwa a filin fadar Sarki Zurmatu.
Cikin kankanin lokaci fadar ta cika ta batse da jama'a, saboda nuna farin cikin su ga Sarkinsu da Kuma son Jin bayanin da Sarkinsu yake dauke da shi a garesu.

Bayan shudewar rabin sa'a, sai aka hango SARKI ZURMATU, SADAUKI USAMA, BOKA RAKUL, SARKI FALWAN cikin shiga ta Alfarma sun tunkaro fadar cikin nishadi.
Nan take Dakaru suka Buda masu hanya, suka wuce Kai tsaye izuwa cikin fadar.
Da isar su Sarki Zurmatu ya wuce kan KARAGARSA ya zauna.
Sannan yayiwa su SADAUKI USAMA nu ni da su zauna a wasu kujeru a na Alfarma.
Bayan sun zazzauna kowa ta natsu, sai Sarki Zurmatu ya Mike tsaye sannan ya fuskancesu yayi masu gaisuwa da harsheMai dadi, suka Amsa Masa cikin biyayya.
Batare da Bata lokaci ba Sarki Zurmatu ya kwashe gaba dayan labarin duk abinda ya faru a filin yaki da Kuma yadda akayi suka karbi addinin musulunci daga hannun Sadauki Usama har suka samu nasarar wannan yaki, ya sanar da jama'arsa.

Koda yazo dai-dai Nan a jawabinsa sai gaba dayan mutanen wurin suka cika da tsananin mamaki, Kuma Nan take Mafi yawa daga cikin jama'ar garin sukaji cewa zuciyarsu ta fara natsuwa da wannan addini.
SARKI ZURMATU ya ci gaba da cewa, ya ku jama'ar birnin BALLUS kuyi sani Addinin musulunci shi ne, Addinin gaskiya Kuma Addinin tsira daga halaka.
Kuma tabbas mun gani da idanmu, Kuma ku ma dayawanku kunga irin karfin da Ubangijin musulunci yake da shi.
Kuyi sani cewa tuni mun Bada gaskiya ga ubangijin musulunci da ni da iyalina da Kuma su BOKA RAKUL, SARKI FALWAN, SARKIN YAKI DURKUL..
Saboda haka Ina son ku ma ku bayar da Gaskiya ga ubangijin musulunci domin tabbatar da rayuwarmu cikin aminci da kwanciyar hankali.

Nan take jama'ar wurin duk sukayi shiru aka rasa Wanda zai ce wani abu, daga can sai wani dattijo ya tako ya zo gaban Sarki ya tsaya.
Sannan ce ya shugabana tayaya zamu bar abinda muke Bauta mawa tun zamanin iyaye da kakanni, sannan mu rungumi wani bakon addini Wanda bamu San asalinshi ba?
Shin idan mun shiga wannan addini a Ina zamuga Ubangijin musulunci ballantana mu rinka Bauta Masa?
Sannan idan Muna cikin bukatar taimako tayaya zamuga Ubangijin musulunci har mu roke shi, ya temake mu?
Koda Sarki yaji wannan jawabi daga bakin wannan tsoho, sai yayi shiru daga bisani ya dago Kai ya ce bani da Amsar wannan tambayar taka Amma bari na kira SADAUKI USAMA ya bamu wannan Amsar tunda shi ya Dade a cikin wannan addini.

Nan take SADAUKI USAMA ya fuskanci mutanen birnin BALLUS ya ce, " ya ku jama'ar wannan birni kuyi sani cewa. Addinin musulunci shi ne Addinin gaskiya akan dukkan sauran addinai.
Kuma Ubangijin musulunci shi ne, Wanda halicci komai da kowa.
Shi ne Wanda ya halicci Sammai da kassai, sannan ya halicci mutane da da Aljanu da dabbobi da ruwa da iska, da bishiyoyi Kai da duk abinda kuke iya gani a duniya da ma Wanda Baku iya gani.
Kuma shi ne ubangijin da komai yake tafiya bisa ikonsa.
Haka Kuma duk abinda kuka gani a wannan duniyar Sammai da kassai mallakinsa ne, Kuma bayinsa ne.
Sannan Kuma Yana lura da duk halin da bayinsa suke ciki, Kuma Yana Amsa kiran duk Wanda ya nemi taimakonsa Nan take.
Haka Kuma Ubangijin musulunci ya kasance Mai kashewa da rayawa, Kuma Mai Azurta Wanda yaso ya talauta Wanda yaso, Kuma ya daukaka Wanda yaga dama sannan Kaskantar da Wanda ya Saba Masa.
Haka Kuma ya tanadi rahma da ni'ima da Jin dadi mara yankewa ga duk Wanda ya Bauta Masa yayi Masa biyayya, haka Kuma ya tanadi azaba Mai radadi ga mutane ko Aljanun da suka bijire Masa ta hanyar kin Bauta Masa shi kadai.

Koda jama'ar birnin BALLUS sukaji irin jawabin da SADAUKI USAMA yayi game da Ubangijin musulunci sai gaba dayansu jikinsu yayi sanyi Kuma suka gamsu dari bisa Dari cewa lallai Ubangijin musulunci shi ne Mafi cancanta a Bauta Masa.

Nan take gaba dayansu suka ce tabbas mun amince Ubangijin musulunci shi ne abun Bauta da gaskiya, Kuma munyi Imani da shi.
Cikin tsananin farin ciki SADAUKI USAMA ya biya masu Kalmar Shahada suka maimaita a lokaci guda.
Wayyo musulunci dadi!♥️♥️🥰🥰
Inda ace mutum na wajen a lokacin da jama'ar wannan birni suka karbi addinin musulunci Kuma suke maimaita kalmar Shahada a lokaci guda, da sai ya ji kamar ya narke saboda tsananin dadi da farin ciki.

Ana cikin wannan hali ne, aka ga Shugaban likitocin Sarki Zurmatu ya rugo cikin fadar cikin tashin hankali.
Yana zuwa yayi gaisuwa ga sarki sannan ya ce, ya shugabana a gafarceni saboda mun Kasa ceto rayuwar YARIMA FAZAMAL yanzu haka ya mutu.
Nan take duk murnan da akeyi sai ta koma izuwa bakin ciki, saboda kowa yasan irin yadda SARKI FALWAN ke matukar kaunar dansa.
Nan take SARKI ZURMATU da sauran jama'ar wurin suka shiga rarrashin Sarki har suka shawo Kansa.
Batare da Bata lokaci ba aka shirya jana'izar YARIMA FAZAMAL za'a binneshi a birnin, Amma sai Sarki FALWAN yace Yana so a bari yaje da Yarima birninsa ya rufe shi a can, Kuma daga Nan zai musuluntar da jama'arsa Shima.
Nan take aka yiwa SARKI FALWAN shiri na musamman, SARKI ZURMATU ya bashi kyautar Dakaru masu yawa kyauta, da kyauta dukiya Mai yawa wadda za'a raya Al'umma Kuma a daukaka Kalmar Allah.
Nan dai sukayi bankwana suka rabu.
Bayan tafiyar Sarki FALWAN ne Sarki Zurmatu ya sanar da jama'arsa cewa insha Allah a Gobe za'a daura auren GIMBIYA MARITA da Kuma SADAUKI USAMA domin tabbatar da Alkawarin da Sarki yayi.
Nan da Nan aka shiga shirye-shiryen biki, aka gayyato mutane daga ko'ina domin halartar wannan gagarumin biki.

Washe gari aka daura auren GIMBIYA MARITA da SADAUKI USAMA aka Sha shagalin biki Mai yawa.
SARKI ZURMATU ya Baiwa SADAUKI USAMA kyautar wani katafaren gida Mai tsananin kyau da kawatuwa.
Batare da Bata lokaci ba Ango ya tare da Amaryarsa a sabon gidan da Sarki ya Basu, suka ci gaba da more Amarcinsu cikin Jin dadi da kwanciyar hankali.

Bayan kamar wata guda ne da bikin SADAUKI USAMA GIMBIYA MARITA ta samu ciki. Farin ciki a wurin SARKI ZURMATU da Sadauki Usama bazai misaltu ba.
Haka Kuma SADAUKI USAMA yasa aka Bude Masa wani Katon Fili a tsakiyar birnin inda yake Tara mutanen birnin Yana koya masu ibadoji na Addinin musulunci.

Cikin kankanin lokaci mutane suka kware a karatu da rubutu da Kuma sanin yadda za'a bautawa Allah yanda ya dace.
Haka dai akaci gaba da rayuwa cikin farin ciki har lokacin da GIMBIYA MARITA ta haifi da namiji Wanda ya kasance kyakkyawa na gaban kwatance.
Tun daga ranar da aka haifi wannan Yaro aka fara shagalin rada Masa suna, da sati ya zagayo aka Sanya Masa suna MAHARAJ.

Mutanen birnin BALLUS suka wanzu cikin tsananin farin ciki da kwanciyar hankali. Tattalin arzikin kasarsu ya habbaka ainun, ya zamana cewa 'yan kasuwa da fatake da duk wani Mai arziki sun naje kolinsu a birnin ya zamana cewa a kowane lokaci hidimar Kasuwanci a ke.
A sakamakon hakane yasa Addinin musulunci ya Kara fantsama a ko'ina cikin duniya saboda kasancewar bakin fatake da ke zuwa fatauci birnin, Kuma dayawansu suna karbar Addinin musulunci suna zuwa can kasashensu suna yada Addinin.

Bayan kamar shekaru uku da faruwar wannan Ala'mari, sai wani babban bala'i ya rinka faruwa a birnin.
A Arewa da birnin BALLUS akwai wani surkukin daji Mai duhuwa Wanda hatta mafarauta basa iya shigarsa saboda duhuwarsa.
To a cikin wannan Dajin akwai wadansu jibga-jibgan ZAKUNA masu tsananin girma da karfi Kuma adadinsu yakai guda dubu.

A kullum da dare wadannan ZAKUNAN suna shigowa cikin birnin BALLUS suyiwa mutane mummunar barna, Kuma su kashe mutane sama da guda dubu, sannan da zarar anzo yakarsu sai su zama haske su bace.
Haka suka rinkayi har tsawon wata guda, a cikin wannan lokacin sunyiwa mutane mummunar barna.

Nan da nan domin ya gano daga inda ZAKUNAN ne ke zuwa suna masu barna Amma ya Kasa.
Nan fa hankalin Sarki ya dunguzuma ainun ya rasa abinda ke Masa dadi a duniya.
Koda SADAUKI USAMA yaga halin da Sarki Zurmatu yake ciki, sai ya ce ka kwantar da hankalinka ya Kai Sarkin sarakuna, kayi sani cewa babu abinda yafi karfin Allah.
Don haka ka Dogara gareshi Kuma ka kwantar da hankalinka domin Allah Yana tare damu.
Yanzu ka bani daga Nan zuwa gobe zanyi Istihara domin na roki Ubangijina ya sanar Dani duk abinda ke faruwa.
Nan dai sadauki Usama yayita rarrashin Sarki Zurmatu har ya shawo Kansa, sannan sukayi bankwana suka rabu.
Da dare yayi Usama yayi Istihara sannan ya kwanta, cikin iKon Allah, sai Allah ya bayyana Masa duk abinda ke faruwa akan lamarin wadannan bakin zakuna masu Yi masu barna.
Washe gari tunda sassafe SADAUKI USAMA yaxo ga sarki yayi gaisuwa Sannan ya sanar dashi abinda Allah ya gwada Masa kamar haka...

Yakai wannan Sarki kayi sani cewa, wadannan ZAKUNAN sun kasance sihirtattu ne, Kuma suna daga cikin jinsin ALJANU marasa Imani wadanda adadinsu yakai dubu.
Sannan Kuma babban Dan SARKI KALJUL ne ya turo su, domin su zo su hallakamu gaba dayanmu saboda ya dauki fansar ran Mahaifinsa da jama'arsa.
Yanxu haka wadannan ZAKUNAN suna can Dajin wannan birnin Dake arewacin garin.

Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu yayi Umarni da ayi Shirin yaki domin aje a Karar da wadannan zakuna masu cutar da su.
Nan take SARKI ZURMATU SADAUKI USAMA da sauran JARUMAN birnin sukayi Shirin yaki suka tunkari wannan daji....

A dai-dai wannan lokaci ne littafi na biyar ya kare🥱🥱🥱Kuma alkalami na ya kafe saboda rubutun da yasha✍️✍️

ME ZAI FARU IDAN SU SARKI ZURMATU SUKA ISA DAJIN DA ZAKUNAN SUKE?

SU WA ZASU SAMU NASARA A YAKIN DA ZA'AYI?

WANE MATAKI ZA'A DAUKA TSAKANIN BABBAN DAN SARKI KALJUL DA SU SARKI ZURMATU?

mu hadu a GASAR JARUMTAKA na shida don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰

2 / 2