GASAR JARUMTAKA Part 4 Complete By NAJIBIBULLAHI.txt

Author :  NAJIBIBULLAHI MUHAMMAD Category :  Romance

Chapter   2 / 2

3K to 4.5K   out of 4.5K words

wuya ya jefar da Gawarsa.

Nan fa jama'a suka Kara rudewa da shewa suna jin-jina ga DAKARUN SARKI, saboda ganin irin nasarar da suke samu a yau, domin har yanzu ko Daya ba'a kashe daga cikinsu ba.
Nan take aka Bada Umarnin cigaba da Gasa.
Batare da Bata lokaci ba Alkalan Gasar suka kira jarumin Gasa na uku, kawai sai akaga wani siririn mutum ya fito filin Gasar rike da wata siririyar takobi Mai kamar Sanda, a Saman kan mutumin babu gashi ko guda Daya, Kuma Yana da kwala-kwalan idanu masu kama da na mujiya.
Nan take mutumin ya fito daga cikin jaruman Gasar sannan ya nufi filin Gasar inda wannan badakaren yake.
Nan fa jama'ar filin Gasar suka cika da tsananin tausayin wannan mutumin domin sun San cewa tabbas hallaka zayyi, wasu ma har sun fara zubar da hawayen tausayi saboda tunanin irin mummunan Kisan gillar da za'ayi Masa.
A bangaren su Sarki Zurmatu kuwa dariya ce ta kwace masu a bisa ganin Wanda ya fito da niyyar tarbar wannan badakaren, domin sun San cewa wannan kawai ya gaji da rayuwarsa ne yake so hallakashi shiyasa ya shiga wannan Gasar.

Nan take alkalan Gasar suka buga Gangar cigaba da Gasa, ai kuwa ana bugawa sai wannan badakaren ya zare lafceciyar Addar sa sannan ya dako tsalle daga inda yake ya kaiwa wannan jarumin Gasar Sara a ka da nufin ya tsargeshi gida ba, abun da yaba kowa mamaki shi ne ganin yadda shi jarumin Gasar ko motsawa bayyiba ballanta ya kare Kansa, Nan fa mutane suka runtse idanuwansu saboda ganin yadda za'a raba wannan siririn mutumin biyu daga fara Gasa.
Ba zato ba tsammani Addar badakaren na Isa Kan siririn mutumin Nan, sai kawai akaji wata Kara Mai tsanani ta watsu a cikin birnin gaba Daya, Kuma Addar ta Kasa Koda kwarzanar Kan siririn mutumin.
Shi kuwa wannan badakaren ji yayi tamkar ya sari Dutse Mai tsananin tauri saboda tsabar karfin kan mutumin, ba zato ba tsammani Kuma sai akaga wannan hannun wannan badakaren ya bushe rakau tamkar an busar da danyen abu, a hankali gaba dayan sassan jikin badakaren ya cigaba da bushewa har sai da gaba dayan jikinsa ya bushe rakau, kawai sai akaga jikinsa ya fara tsattsagewa daga karshe ya tarwatse yayi bindiga sai ga sassana jikinsa yayi filla-filla a sama.

Cikin tsananin razana sauran Dakarun suka zare makaman su sannan sukayo caa akan wannan siririn mutumin da nufin su yagalgala shi, kawai sai akaga ya nuna su da dan yatsa, take wata iska Mai tsananin wari ta kanannade wadannan Dakarun suka Kam a wuri guda, ba zato Kuma sai akaga su ma jikinsu Yana bushewa kamar yadda na farko yayi, Nan da Nan su ma suka tarwatse sukayi filla-filla a sama tamkar an watsa Hoda a sama.

Cikin dimaucewa da razana SARKI ZURMATU ya Mike tsaye sannan ya dakawa Sauran Jaruman Gasar tsawa akan maza su kama Masa wannan mutumin..
Nan take gaba dayan Jaruman Gasar suka zare zabga-zabgan makaman su sannan suka rugo izuwa kan wannan siririn mutumin.

Sama da Jarumai dubu Hamsin ne suka yanyameshi tamkar an ajiye kwayar gero a tsakiyar gidan tururuwa.
Nan fa wannan wannan siririn mutumin ya wanzu Yana ta dukan Jaruman Gasar da wannan siririyar takobi Mai kamar Sanda, duk Wanda ya doka da ita sai a ga ya bushe rakau daga bisani yayi bindiga, shi kuwa Koda wani daga cikin jarumin ya samu nasarar saransa da takobi sai yaji tamkar ya sari Dutse, kai ko naushinsa akayi sai suji tamkar suna naushin bishiya domin hannunsu ma har karewa yakeyi.

Nan fa hankalin mutane ya Dugunzuma ainun domin an rasa Wanda zai iya dakatar dashi, Kuma gashi sai Kara ragargazar Jaruman Gasar yake.
Kafin cikar rabin sa'a ya kashe sama da Jaruman Gasar dubu arba'in.

Koda ganin irin wannan mummunan kisan gillar da wannan siririn mutumin yake yiwa Jaruman Gasar sai ya kwarara wani uban ihu Mai tsananin razanarwa, Nan take ya bawa Sarkin yaki DURKUL Umarnin cewa Maza ya tattaro gaba dayan DAKARUN YAKINSA cikin gaggawa suzo a tari wannan makiyin.
Kafin cikar sa'a guda siririn mutumin Nan ya Karar da gaba dayan Jaruman Gasar, ya zamana cewa ya kashe dukkansu babu mutum Daya a tsaye face shi, Kuma har yanxu babu alamar gajiya a tare da shi.

Nan take ran SARKI ZURMATU ya Baci ainun, domin jikinsa gaba Daya karkarwa yakeyi saboda tsananin fushi, Bai San sa'adda ya zare lafceciyar takobinsa ba, sannan ya daka tsalle da nufin tunkarar wannan siririn mutumin.
Yana dirowa Kasa, sai ya falfala da gudu inda wannan siririn mutumin yake Yana zuwa suka kacame da sabon masifaffen yaki na gaban kwatance, Nan fa SARKI ZURMATU da SIRIRIN MUTUMIN Nan suka tashi hankalin kowa da ke wajen.
Domin a ranar kowa ya tabbatar da sadaukantakar SARKINSU ta yadda yake iya yaki da wannan siririn mutumin batare da ya iya lakutar Koda jikinsa ba.
Tsananin zafin naman Sarki Zurmatu yafi gaban kwatance domin duk irin Sara da dukan da wannan siririn mutumin yake kawo masa Bai taba samun nasarar Koda lakutar jikinsa ba.
Hasalima Sarki Zurmatu Yana yawan samun nasarar saransa da takobi, sai dai saran baya tasiri domin ji yake kamar Dutse yake Sara.
Ana cikin haka ne wannan siririn mutumin ya shammaci Sarki Zurmatu ya Doki kirjinsa da kafar hagu, saboda karfin dukan sai da Sarki yayi baya tamkar an janye shi da Kugiya sannan ya baje a Kasa, cikin tsananin zafin nama siririn mutumin ya dako tsalle sama da nufin ya fillewa SARKI ZURMATU Kai, ba zato ba tsammani sai aka SADAUKI USAMA tamkar an cilloshi ya Doki siririn mutumin iyakar karfinsa, saboda karfin dukan sai da siririn mutumin yayi tafiyar taku biyar sannan ya turje.
Tabbas kowa a filin hankalinsa yayi matukar mummunan tashi saboda ganin irin Jarumtakar wannan siririn mutumin, domin a tarihin Jarumtakar SARKI ZURMATU ba'a samun jarumin da iya fafatawa dashi na tsawon dakika hamsin ba batare da yayi nasara akanshi ba, Amma yau gashi wani hatsabibin Bil'adama yayi gagareshi har na tsawon sa'a guda.


SADAUKI USAMA ya rike hannun Sarki Zurmatu ya tashe shi tsaye sannan ya risina yace ya shugabana inaso ka bani akan wannan Matsafin mutumin domin na kawo karshensa.

SARKI ZURMATU ya ce je ka na baka wannan damar, sannan ka sani cewa muddin ka samu nasara akan wannan siririn mutumin to Kai ne Wanda ya lashe KAMBUN GASAR JARUMTAKA, Kuma a take zan tabbatar da Alkawarina a gareka.
Nan take SADAUKI USAMA ya falfala da gudu ya tunkari wannan siririn mutumin suka kacame da sabon masifaffen yaki mai tsananin tashin hankali...

Ala'marin Boka RAKUL kuwa, hankalinsa ne yayi mummunan tashi a bisa ganin irin 6arnar da wannan siririn mutumin yayi musu.
Kuma yayi iyakar bakin kokarinsa don gano ko wanene wannan siririn mutumin Amma Abu yaci tura, domin yayi Amfani da dukkan sihirin tsafinsa donyi bincike a madubin tsafinsa Amma daga karshe sai ya ga madubin tsafin yayi bindiga ya tarwatse..
Sannan Kuma yayi iyakar kokarinsa don ganin ya shiga halwar tsafinsa Amma Abu ya gagara, domin da ya matsa da bincike ma sai yaji gaba dayan jikin ya dume da mugun zafi tamkar an tsoma cikin RIJYAR WUTA GABA DUBU, ba shiri ya hakura ya zauna cikin zullumi da tsananin razana.

Bayan SADAUKI USAMA ya tari wannan siririn mutumin sai suka kacame da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro...
Wohoho! Idan SADAUKANTAKA ta hadu da JARUMTAKA dole ne yaki ya zamo TURMUTSUSUN BALA'I.
Nan fa suka wanzu suna kaiwa junansu Sara da suka cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance tamkar walkiya, duk lokacin da Takubbansu suka hadu sai aga tartsatsin wuta ya tashi yayi sama tamkar Batoyi Yana feshin wuta..
Yayinda bala'i yakai bala'i sai aka ga wannan siririn mutumin ya kumbura ya zama wani Katon mutum cikin zafin nama ya harba SADAUKI USAMA Nan take SADAUKI USAMA yayi sama sannan ya fado Tim! A matukar galaibace har idanunsa na gani dishi-dishi saboda tsananin wahala.

Ba zato ba tsammani sai aka ga wannan mutumin ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya Mai kama da kukan beraye, sannan ya rike ya zama wasu gungun bakaken aljanu wadanda adadinsu yakai Milyan biyu, kowannensu rike da muggan makamai.
Sannan sai ga wani Gabjejen basamuden Katon Aljani ya fito gaba Sannan ya ce" SUNANA SARKI KALJUL Mai Mulkin BIRNI GIRWAL na jinsin bakaken aljanun Duniya.

Bincike ya tabbatar min da cewa babu wani Sarki Mai karfin mulkin ka a duniyar bil'adama kamar ka, sannan kafi kowane Sarki Jarumtaka a cikin jinsin bil'adama.
Ni Kuma Ina kishin naga Sarkin da ya hada duk irin siffofin da nake da su, wato Karfin Mulki da Jarumtaka.
A bisa wannan nake yaki da duk Wanda naga Yana Neman kwatanta irin IZZAR MULKIN da nakeyi.
A halin yanzu na kashe sarakuna DUBU HAMSIN DA BAKWAI masu irin wannan halayyar.
Don haka Kai ne na cikon Dubu hamsin da takwas, don haka babu wani bala'i da zai Hana ni ganin bayanka da ni da jama'ata.
Kuma tabbas sai mun shafe komai na wannan birnin ya zama tarihi...
Ana cikin hakane Sarkin yaki DURKUL ya tattaro duk Dakarun yaki guda Milyan ARBA'IN suka shigo cikin filin Gasar..

Nan take Sarki Zurmatu ya bayar da Umarnin a Afkawa wadannan shedanun Aljanun...


SU WA ZASU SAMU NASARA A CIKIN WANNAN YAKIN?

WANENEN ZAI LASHE KAMBUN GASAR JARUMTAKA?

DA GASKE BIRNIN BALLUS ZAI ZAMA BIRNIN MUSULUNCI?

WANENE ZAI MALLAKI GIMBIYA MARITA?

sai mu hadu a GASAR JARUMTAKA na biyar don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️✍️

2 / 2