Author : Category : Romance
ya taune shi ya hadiye.
Faruwar hakan keda wuya sai yaga girmansa ya koma kamar yadda yake da, Amma har yanzu a bangaren hannunsa na dama siffar dodanni gareshi.
Kafin yayi wani yunkuri sai yaga bangaren jikinsa na hagu ya rikide daga siffar Aljani izuwa siffar zannan Zakin.
Nan take ya wuce Kai tsaye cikin birnin, sai da ya yawace gaba dayan kusurwowin birnin ya cizgo ganyayen bishiyoyin nan sannan ya zo tsakiyar birnin ya debo Kasar birnin ya zuba a cikin battarsa sannan ya juya hanyar ficewa daga cikin birnin gaba Daya.
Sai da yayi tafiyar sa'a biyu Sannan ya iso birni na takwas.
Da shigarsa wannan birni sai yayi arba da wadansu irin jibga-jibgan TSUNTSAYE masu matukar girma da tsinin baki.
Saboda tsananin girmansu duk tsuntsu Daya na iya daukar rakuma goma da kafafunsa yayi tafiyar wuni guda batare da ya gaji ba.
Haka Kuma bakinsu yana da tsananin tsini tamkar mashi ne aka lika a jikin bakin.
Duk abinda suka soka da wannan bakin sai dai aga abun ya huje ya rarake tamkar ansa wuta an Kona abun.
Tsuntsayen na da manyan fuka-fukai guda biyu masu girman gaske, wadanda ko bishiya suka makawa wannan fuka-fukan sai dai aga bishiyar ta tuge saboda tsabar kwarin fuffuken.
Tsuntsayen dukkansu kama sukeyi da MIKIYA.
Koda RA'UFUL KALLUS ya shigo wannan birni sai ya cika da tsananin mamakin ganin yadda tsuntsayen Nan suka cika ko'ina a cikin birnin.
Kafin yayi wani yunkuri tuni wani NARKEKEN TSUNTSU daga cikinsu ya fyauceshi ya tashi dashi sama sai ga RA'UFUL KALLUS yana ta wutsil-wutsil da kafafu tamkar an rataye shi.
Yana cikin wutsil-wutsil din ne ya waigo kawai sai yaga gaba dayan tsuntsayen nan sun biyo bayansu cikin matsanancin gudu tamkar na tauraruwa Mai wutsiya...
MEZAI FARU A TSAKANIN ALJANI RA'UFUL KALLUS DA WADANNAN TSUNTSAYEN?
SHIN RA'UFUL KALLUS ZAI SAMU NASARAR TSALLAKE HADARIN WANNAN BIRNIN?
SHIN BURIN ALJANI RA'UFUL KALLUS ZAI CIKA AKAN ZAMA GAGARABADAU KUMA SADAUKIN SADAUKAI?
INA LABARIN YAKIN DA AKE TSAKANIN DODDANIN DA RA'UFUL KALLUS YA AJIYE A KOGONSA DA KUMA SAURAN SARAKUNAN DUNIYA A KOGON DURGAFUL KALLUS?
Don Jin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a littafin HATSABIBIN ALJANI na biyar 5.
Daga mai debe maku kewa wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️🙏🙏
Nake cewa ku huta lafiya ✍️♥️