Author : Category : Romance
**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA HUDU 4 ♥️🥰
PART A ✍️✍️
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️🙋🥷
Whatsapp Num....08112778656
Lokacin da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya kutsa Kai izuwa birni na shida.
Da shigarsa sai ya tsinci Kansa a cikin wadansu irin mutane mabambanta wadanda gaba dayansu sun bambanta.
Su dai wadannan mutanen birnin adadinsu yakai dubu, Kuma kowa yarensa daban.
Ma'ana wannan bayajin yaren wancan, haka Kuma wannan baya jin yaren wancan.
Kuma asali kowa garinsa daban, wani hatsabibin Bokan Aljani ne ya rinka sato su Yana kawowa wannan birni yana ajiyewa don ya cika wani burinsa na sihiri..
Asalin wannan birni wadansu Kananan halittu ne masu matukar kankanta wadanda duk abinda suka kama sai sun cinye shi, hatta Dutse idan suka yanyameshi suna saranshi da mugayen hakoransu sai dai aga dutsen yana gutsirewa yana fashewa har su Karar da shi.
Haka Kuma idan bishiya suka samu suka tarar mawa sai sun cinyeta tass har jijiyoyin ta sannan suke Kara gaba.
Wannan yasa a iya rayuwar da sukayi cikin birnin suka Karar da gaba dayan bishiyoyi da Duwatsun birnin, ya zamana cewa babu komai a birnin face Fili fetal Wanda babu gine-gine ko wani abu a Kansa.
Amma Kuma daga 6angarorin wannan birni akwai wadannan bishiyoyin guda hudu a Raye wadannan halittun sun Kasa cinyesu, domin da zarar sunzo garesu da nufin tararwa bishiyar su cinyeta sai dai su rinka kamawa da wuta suna konewa kurmus.
Wannan yasa suka hakura da cinye bishiyoyin suka Cigiba da rayuwarsu a cikin birnin suna tunanin yanda zasu rinka samun abincin da zasu rinka ci suna rayuwa.
Dare daya suka ga wannan bakon Bokan Aljani yazo masu, da zuwansa sai ya rinka hura masu wata irin hodar sihiri Mai warin gaske, suka rinka kamawa da wuta suna konewa kurmus.
Kafin cikar sa'a biyu dukkansu sun gama cinyewa da wuta ya zamana cewa sai dai tokar su.
Koda ganin haka sai Bokan Aljanin ya kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya. Nan take yayi tsafi sai ga wata gagarumar iska ta bayyana, sannan ta rinka kwashe tokar wadannan halittun tana watsawa a sama har sai da birnin ya zama babu wani abun kazanta a cikinsa.
Sannan Bokan Aljanin ya cigaba da Gina gidajen sihiri a birnin har sai da ya Gina gidaje guda dubu, Kuma duk gida daya iyakar rayuwar mutum Daya ne saboda kankantar shi.
Daga tsakiyar wannan birni kuwa, sai Bokan Aljanin nan ya karkashin Kasar birnin, sannan ya Gina wani tafkeken gidan Kasa Mai matattakala guda dubu, sa'annan Kuma a karshen Kasar ya rinka Gina manyan dakuna har guda dubu.
Bayan kammala dakunan Kuma sai ya zubawa kowane daki zallan dodanni kala-kala har guda dubu.
Ma'ana dodannin daki na farko basa cin Naman mutane ko aljanu, su kawai amfaninsu yiwa duk halittar da aka jefo cikin wannan dakin azabobi guda dubu, sannan su jefata daki na biyu, haka Suma dodannin daki na biyu basa yiwa mutum komai sai dai su zukewa mutum jini, sannan suyi Masa sihiri Shima ya zama dodo Dan uwansu, bayan sun gama sai su jefa mutum izuwa daki na uku, da haka da haka dai har su kammala jefa mutum izuwa daki na cikon Dubu.
Bayan wannan bakon Bokan Aljanin ya kammala wannan aikin, sai ya rinka zuwa Kasa ya rinka mutane mabambanta masu yaruka daban-daban har sai da ya Ziyarci kasashe guda dubu, sannan ya dauko kabilu iri-iri guda dubu ya kawo wannan birni ya ajiye.
A halin yanzu wannan Bokan Aljanin na can gidansa na karkashin Kasa inda ya ajiye dodannin nan ya shiga halwar tsafinsa domin kammala aikinsa akan wadannan kabilun mutanen da ya tattara.
Lokacin da ALJANI RA'UFUL KALLUS ya shigo cikin wannan birni, sai ya cika da tsananin mamakin ganin mutane iri-iri musamman yanda yaga wasu farare, wasu bakake, wasu dogaye, wasu Kuma gajeru gasu Nan dai birjik iri-iri.
Yana cikin tafiya sai yaga wadannan mutanen sun rugo gareshi sun rikeshi sun daddaureshi a wani wuri Mai rumfa, sannan sun taru gaba dayansu suna koya Masa yarukansu.
Tun RA'UFUL KALLUS baya gane komai daga harsunansu har ya rinka fahimta, sai da yayi kwana arba'in a cikin wannan birni tare da wadannan kabilun mutanen.
A wannan lokacin ne ya kammala koyon gaba dayan harsunan mutanen guda dubu, har ya iya magana da kowannensu.
Inda ya fada masu dalilin zuwansa wannan birni sannan Kuma ya rokesu akan su kwanceshi, Nan take suka kwanceshi bisa yarjejeniyar lallai zai ceci rayuwarsu daga hannun wannan mugun Aljani, Kuma zai mayar dasu kasashensu cikin aminci.
Batare da dogon tunani ba, RA'UFUL KALLUS yayi masu alkawarin taimakonsu, tare da mayar dasu kasashensu dukkansu.
Nan take suka kwance igiyoyin da suka daureshi, sannana sukayi Masa kwatancen inda wadannan bishiyoyi suke.
Batare da Bata wani lokaci ba, RA'UFUL KALLUS ya zagaye kusurwowin birnin gaba daya tare da tsinko ganyayen bishiyoyin, sannan ya dawo ainihin tsakiyar birnin Nan.
Da zuwansa sai ya iske wannan wawakeken rami Mai matattakala Wanda Bokan Aljanin nan yayi.
Nan fa RA'UFUL KALLUS ya tsaya Yana mamakin yanda aka wawaken wannan wuri, da Kuma irin yanda aka tsara gini a karkashin Kasa haka.
Ba zato ba tsammani sai kawai RA'UFUL KALLUS yaji an bushe da wata mahaukaciyar dariya mara dadin ji, a cikin sautin dariyar yaji ana cewa...
Lale marhabun da Gwarzo Kuma jarumin Aljani wato RA'UFUL KALLUS Wanda ya gagari duk mutane da Aljanun duniya.
Kayi sani cewa irin burin da kake dashi, Nima shi ne nake dashi a cikin Raina.
Kuma nayi bincike na gano cewa Nan da wani lokaci zaka zo har wannan birni domin dibar Kasar birnin da kuma tattaro ganyayen bishiyoyin karshen birnin guda hudu.
To kayi sani cewa bincikena ya tabbatar min da cewa muddin nayi amfani da jininka na hadashi da jinin wadannan kabilun mutanen da na tattara, to a cikin dakika hamsin kacal burina zai cika.
Saboda haka Ina Yi maka bankwana da wannan kalami, saboda ka kawo kanka Tsibirin mutuwa inda ba a zuwa a fita, duk abinda ya shigo Nan ya shigo kenan har abada.
Kafin RA'UFUL KALLUS yace wani abu, tuni wannan Bokan Aljanin ya bayyana Tsulum a gabanshi, sannan ya runbabeshi sun bace.
Basu bayyana a ko'ina ba sai a cikin dakin dodanni na farko.
Bayyanarsu keda wuya sai bakon Bokan Aljanin ya bace bat Yana Mai cigaba da kyalkyala dariyar mugunta.
Cikin tsananin zafin nama dodannin nan sukayo caa akan RA'UFUL KALLUS suna suka daddaure shi.
Nan fa suka rinka gana Masa azabobi kala-kala har guda dari bakwai da saba'in.
A wannan lokacin gaba dayan siffar RA'UFUL KALLUS ta canza saboda tsabar azabar da ya Sha, domin dakyar yake iya daga hannunsa ma saboda tsabar galabaita.
Nan fa wadannan dodanni suka dauko wani irin murtukeken karfe Mai matukar tsini Kuma jajur a sama da nufin su tsire RA'UFUL KALLUS.
Koda RA'UFUL KALLUS yaga mutuwa muraran sai ya takarkare ya kwarara uban ihu, ba zato ba tsammani sai yaji sihirin tsafinsa ya dawo.
Nan take yayi Amfani da karfin sihirin tsafi ya tsittsinka Sarkar da dodannin suka daddaureshi.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wasu muggan makaman yaki na wuta sun bayyana a hannunsa, Nan fa ya hau dodannin nan da Sara da suka tamkar wutar da aka bulbulawa fetur.
Nan fa RA'UFUL KALLUS ya rinka gutsirewa dodannin nan Kai, jini ya rinka fantsama da Malala a cikin dakin tamkar ruwan teku ya balle.
Nan fa ihu da gurnanin dodannin nan ya yawaita a cikin wannan daki, kafin cikar dakika dari da arba'in RA'UFUL KALLUS ya kashe gaba dayan DODANNIN.
A wannan lokacin jinin dodannin ya kusa cika dakin gaba daya.
Saboda haka gaba dayan jikin RA'UFUL KALLUS a cikin jini yake, Koda jinin dodannin nan ya ratsa jikin RA'UFUL KALLUS sai gaba dayan raunikan da sukayi Masa suka cicciko Kuma fatarsa ta zama Mai tsananin tauri tamkar Dutse.
Nan fa ya rasa hanyar da zai wuce izuwa daki na gaba, kawai sai ya debo jinin wadannan dodannin yasha.
Faruwar hakan keda wuya sai kawai yaji anyi sama da shi, sannan an jefa shi izuwa daki na biyu.
Har a sannan akwai jinin wadannan dodannin a jikinsa sai diga yake, sa'annan Kuma yana rike da muggan makamansa.
Koda ganinsa izuwa wannan dakin, sai ya tsinci Kansa a tsakiyar wasu lafta-laftan dodannin da suka ninka na baya girma sai goma.
Kafin wani yace wani abu tuni dodo Daya daga cikinsu ya suri RA'UFUL KALLUS sannan ya shako shi da hannu guda, ya daga sama yana Lilo.
Faruwar hakan keda wuya sai wannan dodon ya wangame tafkeken bakinsa Mai dauke da wadansu zabtara-zabtaran hakora ya Kafa Masa a wuya da nufin zukewa RA'UFUL KALLUS ya jini.
Nan fa wannan dodo yaji fatar RA'UFUL KALLUS tauri tamkar Dutse ko kadan hakoransa bazasu iya hudata ba.
Domin har sai da hakoransa guda goma manya-manya suka kakkarye.
Ba shiri ya Sako RA'UFUL KALLUS ya fado, sannan suka rufar Masa da duka da mangari da nufin su kallashi.
Nan fa suka wanzu suna harba RA'UFUL KALLUS tamkar kwallo Yana gwaruwa da bangon dakin Yana faduwa.
Cikin kankanin lokaci RA'UFUL KALLUS yasha bakar wahala har jikinsa ya kukkumbura.
Ba shiri ya jawo makamansa sannan ya tunkari dodannin Yan karkashesu suna mutuwa tamkar ruwan sama.
Kafin cikar sa'a guda ya kashe dukkansu, sannan yasha jinin dodannin Kuma ya wuce izuwa daki na uku.
Nan ma wasu nau'in dodannin ne suka azabtar dashi sau dubu sannan sukayi yunkuri kasheshi daga bisani ya yake su ya karkashe su, Kuma yasha jinin su.
Haka ya rinka yi har sai da ya tsallake dakuna dari Tara da casa'in da tara. Kuma a cikin kowane daki sai da ya hadu da dodanni na musamman Kuma sunyi Masa azaba Mai yawa har guda dubu daga bisani ne yake yakarsu sannan yasha jinin su ya wuce gaba.
Lokacin da RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa izuwa cikon daki na dubu, sai yaga gaba dayan siffarsa ta canza daga ainihin wadda ya sani.
Domin gani yayi rabin jikinsa daga hannun dama ta rikide izuwa siffar dodanni, sannan Kuma rabin jikinsa daga hannun Hagu Yana Nan a siffar aljaninsa.
Da shigowarsa wannan dakin na cikon Dubu, sai yayi arba da wasu gabza-gabzan dodannin da sukafi dukkan dodannin da ya wuto baya.
Sudai wadannan dodanni babu komai a hannunsu, duk lokacin da suka kama wata halitta sai suyi Amfani da karfin damtsen su, su rinka gutsire sassan jikinta suna ci a hankali-a hankali har ta kare.
Ba tare da Bata lokaci ba wadannan dodannin suka rirrike RA'UFUL KALLUS sannan Daya daga cikinsu ya bangaren hannunsa na dama ya Bude tafkeken bakinsa, sannan ya kaftara hakoransa a jikin RA'UFUL KALLUS.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan dodon ya kama da wuta ya kone kurmus.
Koda sauran dodannin suka ga haka, sai suka lura da kyau, cewa Ashe bangaren jikinsa na dama duk siffar dodanni gareshi.
Nan take suka juyo izuwa bangaren jikinsa na hagu, Nan ma wani daga cikin ya Bude lafcecen bakinsa ya lafta Masa cizo, sai gashi dodon nan ya cika bakinsa da Naman RA'UFUL KALLUS sannan cizgo wata lafceciyar tsokar nama daga jikinsa.
Nan take RA'UFUL KALLUS ya kwarara wani uban ihu har da kwallun wuya suka zuba Masa.
Bayan wannan dodon ya kammala cinye wannan tsokar Naman da ya cizgo ne, sai ya kauce wani dodon ma yazo ya Bude wangamemen bakinsa da nufin cika bakinsa da fatar RA'UFUL KALLUS, ba shiri RA'UFUL KALLUS ya fizgo wadannan makaman nasa da dayan hannun sannan ya fillewa wannan dodon Kai, Nan take RA'UFUL KALLUS ya takarkare wajen kisan dodannin nan Jini ya rinka malala da fantsama a sama.
Kafin a jima gaba dayan dakin ya cika makil da jinin dodannin nan.
A wannan lokacin ya kashe sama da dodanni dari biyar da hamsin.
Saboda tsabar yawan jinin dodannin da ya cika dakin ya zamana cewa shi kanshi RA'UFUL KALLUS jinin ya kusa shanye shi, dole sai da ya rinka iyo yana Kai hari da kisan dodannin.
Koda sauran dodannin suka ga haka, sai kawai suka rikide suka zama wani Katon dodo guda Daya.
A dai-dai wannan lokaci ne hannun RA'UFUL KALLUS yakai kan Kasar tsakiyar da aka daure a cikin wani Dan karamin kuttu.
Cikin zafin nama ya sure Kasar ya jefa a cikin battarsa, faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan jibgegen dodon ya dauko Aljani RA'UFUL KALLUS da hannu guda, Yana wutsil-wutsil da kafafu sannan ya wangame Katon bakinsa ya jefa shi ciki.
Nan take dodon ya rufe bakinsa, sannan ya hadiye RA'UFUL KALLUS.
Ba zato ba tsammani sai kawai akaga RA'UFUL KALLUS ya fado birni na bakwai.....
Mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na hudu part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰
Najibullah Muhammad legends ✍️♥️♥️
**HATSABIBIN ALJANI**
LITTAFI NA HUDU 4 ✅
PART B ✍️♥️
AUTHOR: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING: Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷
Whatsapp Num... 08112778656.
Lokacin da RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa a cikin birni na uku, sai yaga gaba dayan birnin zallan dabbobi ne.
Kuma dabbobin nau'i-nau'i ne gasu nan birjik babu kalar da babu.
Duk irin dabbar da mutum ya sani ko ya taba Jin labarin ta to akwai nau'inta a cikin wannan birni.
Saboda tsabar yawansu sun cika birnin gaba daya babu ta inda mutum zai bi ya wuce dole sai yabi ta cikinsu.
Su dai wadannan dabbobi gaba dayansu an rene su ne da Naman mutane da Aljanu saboda haka Basu da wani abincin da suke ci su rayu face Naman mutane da Aljanu.
Haka zalikha Kuma tsananin yawan dodannin yafi karfin a yake su, domin adadinsu ya haura milyan goma Kuma sun kasance jibga-jibga tamkar giwaye.
Bugu da Kari suna da tsananin gudu tamkar a Saman iska suke gudun.
Lokacin da RA'UFUL KALLUS ya tsinci Kansa a cikin wannan birni, sai yaga gaba dayan dabbobin nan sun rugu iyakar karfinsu da nufin yagalgala shi su cinye.
Cikin tsananin zafin nama ya hau Saman Gangar jikinsu ya rinka taka su Yana gudu iyakar karfinsa.
Nan fa wasu daga cikin dabbobin suka rinka tasowa sama suna kawo Maza bangaza da nufin kado shi daga Saman dabbobin da yake gudu, amma yana gocewa.
Wasu kuwa suka rinka amfani da jelarsu suna cilla Masa da nufin sargafo shi.
Cikin tsananin juriya da zafin nama RA'UFUL KALLUS yaci gaba gudu tare da tsalle-tsalle a Saman dabbobin nan tamkar Dan biri akan bishiyoyi.
Ana cikin hakane wata Mafi naci daga cikin 6aunaye ta daka tsalle sama ta cakawa RA'UFUL KALLUS kahonta guda a cinya, Nan take kahon ya Huda cinyar ya lume a jikinsa.
Nan fa jini ya rinka bulbula tamkar magudanar ruwa ta balle, ba shiri RA'UFUL KALLUS ya kurma wani wawan ihu.
Karfin ihun nasa ya cika birnin gaba Daya.
Nan take wannan 6aunar ta sargafo RA'UFUL KALLUS da kahonninta sannan ta mako Kasa a tsakiyar milyoyin dabbobin nan.
Fadowar sa keda wuya sai wata Katuwar giwa ta daga kafarta ta gaba ta take hakarkarinsa na dama inda siffar dodanni take.
Nan take kafar ta burma har sai da Kashin hakarkarinsa ya karye guda Daya.
Cikin tsananin radadin zafi da dimaucewa ya Kara kwarara uban ihu kawai sai ya langabe Kasa sumamme.
Ana cikin hakane wata Katuwar kura ta daka mugun tsalle ta duro ta cika bakinta da kafarsa da nufin cinyewa.
Nan fa sama da dabbobi dari uku da arba'in suka Afkawa RA'UFUL KALLUS da nufin kowa ta yagi rabonta.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai akaga Jikin RA'UFUL KALLUS ya rikide ya zama wani NARKEKEN DODO Mai tsananin girma da mummunar siffa.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan jibgegen dodon ya Bude tangama-tangaman hannuwansa masu kama da manyan Tsaunika, ya tattaro sama da dabbobi dubu uku a tafin hannunsa sai gashi yana mutsittsike su tamkar yadda ake mutsittsike danyen tuwo a hannu.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga wannan jibgegen dodon ya watsa gaba dayan dambun Naman dabbobin a cikin bakinsa ya taune, sannan ya kwarara wani uban ruri Mai tsananin razanarwa Wanda ya haddasa girgizar birnin gaba Daya, Nan take wasu daga cikin dabbobin suka rinka faduwa Kasa matattu saboda tsananin Karar rurin dodon.
Sai da dodon nan ya shafe dakika dari da arba'in yana ruri sannan ya tsuke bakinsa.
Nan fa dodon nan ya dage iyakar karfinsa yana talitse dabbobin da kafafunsa, a duk lokacin da ya daga kafarsa guda Yana iya talitse dabbobi dubu.
Cikin abinda bai wuce sa'a guda ba RA'UFUL KALLUS ya kashe da dabbobi Milyan Daya da dubu dari biyu.
Ashe duk wannan Gumurzu da akeyi, akwai kimanin dabbobin ZAKUNA guda dubu Dari bakwai a can gefe guda sun tsaitsaya suna ta kallon yadda ake ta bakin GUMURZU.
Koda wannan dodon ya gama kashe gaba dayan dabbobin Dake gabansa,
Sai ya tunkari wannan rundunar zakunan take.
Koda isowarsa sai ya daga kafarsa guda da nufin talitse su, cikin tsananin zafin nama sama da zakuna dubu Dari suka cunkushe wuri guda sukayi wani ruri.
Koda kafar dodon ta dira akansu sai ta haifar da wata Kara wadda ta cika birnin gaba Daya.
Shi kuwa dodon sai yaji tamkar ya taka kafarsa akan karfe ne saboda tsananin taurin zakunan.
Faruwar hakan keda wuya sai ya janye kafarsa, Nan take wadannan ZAKUNAN sukayi wani gurnani Mai matukar razanarwa.
Faruwar hakan keda wuya sai aka ga gaba dayansu sun rikide sun zama wani JIBGEGEN ZAKI guda daya, wannan girmansa ya ninka na giwaye Arba'in.
Nan fa aka kacame da azababben yaki mai tsanani a tsakanin dodon nan da Kuma Zakin, ya zamana cewa suna bugun juna hannu da kafa.
A duk lokacin da dodon nan ya naushi Zaki sau Daya, sai da aga ya fadi Kasa sannan ya sake tashi cikin tsananin zafin nama yaci gaba da GUMURZU.
Shi kuwa Zakin idan ya naushi dodon sai yaga dodon ya shanye dukan sannan ya mayar da martani.
Nan Zakin ya fusata ainun ya rinka makalkale dodon Yana yakushinsa da manyan farata masu matukar girma da kaifi tamkar takubba aka lillika a jikin kafafun.
Kuma ya hada cizo da yakushi.
A duk lokacin da Zakin ya soka faratansa akan fatar dodon nan, sai yaji fatar tauri sosai tamkar karfe da karfe ne suka hadu har wani tartsatsin wuta ne ke tashi.
Amma saboda tsabar nacin Kai harin wannan Zakin har ya fara samun nasarar fara huda fatar dodon nan.
Kafin cikar dakika hamsin Zakin Nan ya samu nasarar yiwa dodon nan raunika arba'in a sassan jikinsa.
Koda ganin wannan Ala'mari sai ran dodon ya Baci, cikin tsananin Kunan rai, sai akaga wannan jibgegen dodon ya takarkare iyakar karfinsa ya matse wannan Zakin da dukkan hannayensa.
Nan fa Zakin Nan ya rinka wani irin ruri da gurnani saboda tsabar zafi da radadin da yake ji.
Koda dodon nan ya Kara matse shi sai ya fara kakkarya Kasusuwan jikin Zakin.
Nan fa dodon nan ya rinka Amfani da dukkan karfinsa yana gutsittsira sassan jikin Zakin Nan tamkar yadda ake gutsittsira Albasa akan fai-fai.
Kafin a jima yayi filla-filla da sassan jikin Zakin, sannan ya wangame tafkeken bakinsa ya juye shi a ciki, Nan take