HATSABIBIN ALJANI Part 2 Littafin Yaki .txt

Author :  Category :  Romance

Chapter   2 / 2

3K to 3.4K   out of 3.4K words

Gangar jikinsu tana yin gaba tamkar macijiyar da ke yin Loma guda da kwayar gero.
Sai ta tarwatsa mutum Dari biyar sannan take dakatawa.

Ana haduwa a tsakanin rundunar mutane da DODANNIN aka kacame da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da tashin hankali na gaban kwatance.
Nan fa wasu daga cikin dodannin nan suka rinka Amfani da wani Katon Sangwami suna fyade mutane duk da dawakansu suna sulalewa Kasa matattu, su kuwa suna tattarasu su zuke masu jini sannan su watsa kwarangwal din gangar jikinsu a cikin Baki.
Kafin cikar dakika hamsin jikin dodannin yayi bulbul ya zama jajur saboda tsabar zukar bil'adama da suke yi.

A duk dodo daya Yana iya zuke jinin bil'adama dubu sannan ya watsa kwarangwal din gangar jikinsu a cikin Baki ya taune.
A bisa wannan dalili ne zafin namansu ya yawaita, suka rinka kashe mutanen tamkar GOBARA DAGA KOGI.
Kuma Koda Dakarun mutanen sunyi nasarar datse ma wani dodon hannu ko Kai ko Kafa, Kai ko ma wane sashe ne.
To zarar digon jinin dodon ya taba Kasa, sai aga sama da dodanni hamsin sun tashi irinshi sak.
A bisa wannan dalili ne yasa a cikin dakika Dari bakwai da hamsin, sai da yawan dodannin ya ninku sau goma yazamana cewa yanxu yawansu yakai kimanin Milyan dari da tamanin.

Faruwar hakan keda wuya sai akaga gaba dayan wadannan dodannin sun rikide sun zama wani NARKEKEN DODO Wanda tsayinsa yafi karfin kogon gaba Daya, dole sai dai ya durkusa kamar yadda gwaggwan biri ke yi.

Kafin wani daga cikinsu yayi wani yunkuri tuni wannan jibgegen dodon ya Mike lafcecen hannunsa ya cafko gaba dayan ragowar Dakarun rundunar mutanen Nan duk da dawakansu wadanda adadinsu yakai Milyan bakwai da dubu dari biyar.
Faruwar hakan keda wuya sai akaga ya wangame kanfacecen bakinsa ya watsa dukkanninsu cikin bakinsa ya taune...


SU WAYE ZASU SAMU NASARA A WANNAN YAKI TSAKANIN DODANNI DA KUMA RUNDUNAR MUTANE DA ALJANU?

INA LABARIN ALJANI RA'UFUL KALLUS?

WANE IRIN KALUBALE ZAI FUSKANTA A SHIGARSA BIRNI NA HUDU?

SHIN BUKATARSA ZATA BIYA KUWA,?

SHIN DAGASKE ZAI SAMU NASARAR ZAMA GAGARABADAU KUMA SADAUKIN DA BABU KAMARSA A FADIN DUNIYA?

Domin Jin amsoshin wadannan tambayoyi sai mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na uku.
Na ku har kullum a Koda yaushe wato NAJIBULLAH MUHAMMAD ke cewa ku huta lafiya, sai mun hadu a na uku in-sha Allah✍️✍️🙏🙏🙏

2 / 2