Author : Category : Romance
Sarki ya Bada Umarni gaba Daya aka dunguma aka tafi tsakiyar birnin aka zuba wadannan ganyayen bishiyoyin Kuma suka yanka wadansu manyan dabbobi da nufin Kara Neman kusanci ga Abar bautarsu.
A Wannan lokacin Aljani RA'UFUL KALLUS Yana lura da duk Inda aka ajiye kowane ganye.
Saboda bayan sun gama bautarsu sun koma gida dare ya raba, sai Aljani RA'UFUL KALLUS ya sadado batare da kowa ya ganshi ba, ya rinka tafiya cikin Sanda don Kar aji motsinsa.
Haka ya rinka wuce wadannan halittun a tsaye tamkar gumaka Amma Basu iya ganinshi har yazo dai-dai inda aka ajiye wadannan ganyayen bishiyoyin, Nan take Yasa hannu ya diba Kuma ya debo Kasar birnin ya zuba su a cikin wata Katuwar battar fata wadda ya rataya.
Faruwar hakan keda wuya sai ya tunkari hanyar barin garin, Yana tafiya cikin sauri da Kuma gudu don Kar safiya tayi Masa.
Bai gushe ba Yana tafiya har tsawon sa'a biyar, a wannan lokacin ya kusa fita birnin gaba Daya, Amma Kuma hasken rana ya fara fitowa har halittun birnin sun fara gani Kuma sun fara cigaba da harkokinsu.
Koda suka hango ALJANI RA'UFUL KALLUS na Shirin guduwa sai sama da halittu dubu suka bishi da nufin su kamo shi.
Nan fa aka Kasa tsere, ya zamana cewa Aljani RA'UFUL KALLUS gudu yake iya karfinsa har tashi sama yake saboda karfin gudun, Amma da zarar ya waigo sai yayi arba da wadannan halittu dab da shi.
Nan fa hankalinsa ya dunguzuma ya Kara kaimin gudun, domin ya tabbatar da cewa indai ya sake ya Kara fadawa hannunsu to sai sun hallaka shi.
Haka dai akaci gaba da tsere har ya fara hango birni na biyu, Koda ganin haka sai dukkansu suka Kara kaimi.
Ya zamana cewa su halittun suna so su kama shi ne kafin ya shiga wannan birni na biyu, shi Kuma Aljani RA'UFUL KALLUS Yana so ya shiga wannan birnin kafin su cimmasa.
Haka wadannan halittun suka zage dantse wajen Kai Masa wafta da cizo da tunkuyi, shikuma Yana zillewa a haka har ya fada birni na biyu.
Da shigarsa cikin birnin, sai ya hango halittun sun tsaya cak sun dena binshi sun Kasa shiga birnin, sannan sai suka rinka zubar da hawayen bakin ciki bisa rashin nasarar kama shi.
Shikuwa Aljani RA'UFUL KALLUS sai yayi ta murnar kubuta daga hannun wadannan halittu, domin jikinsa gaba Daya wari yake sannan Kuma yayi tsami sosai saboda azabar da ya Sha, na yi Masa bulala Dari kullum har tsawon kwanaki goma Sha biyu.
Haka dai ALJANI RA'UFUL KALLUS yaci gaba da tafiya a cikin wannan birni batare da ya ga kowa ba.
Birni ne Katon gaske, Wanda akayi Masa manyan gine-gine da zallar danyar Azurfa, Kuma an kawata Katangar birnin da karfen yakutu Mai kyalkyali.
Sai da Aljani RA'UFUL KALLUS ya shafe sa'a biyar Yana yawo a cikin birnin Amma ko kaza Bai gani ba ballantana wasu halittu.
Amma duk Inda ya gifta sai dai yaga kayan alatu iri-iri, da kayan abinci da abin Sha.
Sannan Kuma gaba dayan birnin a haskake yake da matukar haske ta yadda ko allura ta fadi sai an ganta.
Hakika wannan birni ya cika Aljannar duniya, domin gaba Daya birnin an shafe kasansa da wasu duwatsu masu daraja da daukar idanu.
Abinda ya tayarwa ALJANI RA'UFUL KALLUS hankali shi ne, tunda ya shigo wannan birni Bai ga Kasa ba balle ya diba, Nan fa rinka yawo cikin birnin Yana Neman inda Kasar tsakiyar birnin take Amma Bai gani ba, a haka yaci gaba da yawo har yazo kusa da wani Katon Tsauni Mai tsananin girma a tsakiyar garin Wanda ya cika hanyar babu ta inda za a bi a wuce.
Nan take ya yanke shawarar bin kowace kusurwa ta garin domin neman wadannan ganyayyakin alla-bashi daga baya sai yaci gaba da Neman Kasar birnin.
Nan take ALJANI RA'UFUL KALLUS yayi Amfani da wannan shawarar, ya rinka bin kowace kusurwa Yana tsinko ganyayen bishiyoyin Nan, har sai da ya zagaye birnin Kuma ya samu nasarar samo duka ganyayyakin sannan ya dawo cikin tsakiyar birnin Yana ta dubawa har yazo wurin da aka killace Kasar wurin batare da an shafeta ba.
Cikin tsananin farin ciki Aljani RA'UFUL KALLUS ya Debo Kasar sannan ya zuba ta a cikin battarsa.
Faruwar hakan keda wuya sai ya falfala da matsanancin gudu ya tunkari hanyar barin garin.
Sai da Aljani RA'UFUL KALLUS yayi gudun sa'a goma batare da Jin motsin komai a bayansa ba.
Ba zato ba tsammani sai kawai ALJANI RA'UFUL KALLUS yaji an dauko shi sama da 'yan yatsu biyu Sannan anyi sama dashi an dawo dashi ainihin inda ya fara gudun an ajiye shi.
Koda ya daga Kansa sama sai ya hango wani shirgegen mutum, Wanda girmansa ya wuce misali.
Ashe daman wannan Katon tsaunin da Aljani RA'UFUL KALLUS ya gani a tsakiyar birnin, ba Tsauni bane wannan shirgegen mutumen ne..
Nan fa wannan shirgegen mutumen ya sunkuyo da Kansa Kasa, ta yadda Aljani RA'UFUL KALLUS zai iya ganin fuskar mutumen.
Koda suka hada idanu sai Aljani RA'UFUL KALLUS ya kamu da tsananin razana, saboda tsananin munin fuskar mutumen.
Shidai Wannan shirgegen mutumen tsawonsa zira'i dubu biyu ne, sannan fadinsa zira'i dubu ne.
Yana da kahonni guda biyu a tsakiyar Kansa, Kuma tsawonsa ya kere gaba dayan gidajen birnin.
Idan ya Mika hannunsa guda daga inda yake zai iya kaiwa can Karshen birnin, duk da cewa sai anyi kusan tafiyar wata guda ana gudu kafin a fita birnin.
Shirgegen mutumen ya takarkare ya kwarara wata mahaukaciyar dariya wadda ta rinka haifar da wata irin mummunar Kara tamkar ana ruwan kwarankwatsa, har wani irin farin Hayaki ne ya rinka fita daga bakinsa, Koda wannan Karar da wannan hayakin suka Doki Aljani RA'UFUL KALLUS sai ya fadi Kasa sumamme...
ME ZAI FARU TSAKANIN ALJANI RA'UFUL KALLUS DA WANNAN SHIRGEGEN MUTUMEN?
SHIN ALJANI RA'UFUL KALLUS ZAI SAMU NASARAR ZIYARTAR DUKA BIRANEN GUDA DUBU DOMIN CIKAR BURINSA?
WANE IRIN YAKI ZA'AYI A TSAKANIN DODDANIN DA ALJANI RA'UFUL KALLUS YA KAWO A MATSAYIN MASU GADIN KOGONSA DA KUMA SAURAN BOKAYE DA SARAKUNAN DUNIYA?
SU WAYE ZASU SAMU NASARA A WANNAN YAKI?
SHIN BURIN ALJANI RA'UFUL KALLUS NA CIKA?
Domin Amsar wadannan tambayoyin sai mu hadu a HATSABIBIN ALJANI na biyu don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️♥️🥰🥰