Author : NAJIBIBULLAHI MUHAMMAD Category : Romance
da ya zagwanye a jikinmu, da haka da haka mu rube gaba Daya kafin cikar kwanaki talatin, Kuma irin mutuwar da mukayi irinta gaba dayan mutanen birnin Nan zasuyi har kowa ya mutu.
Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu Waziri Mikilas suka kamu da tsananin tsoro, saboda yanda rayuwarsu ta kasance a tsakanin tsaka-mai-wuya.
Cikin tsananin damuwa kamar yayi kuka, Waziri Mikilas yace ya Sarkin Duniya, na rokeka akan muyi duk irin abinda zamu iya don rayuwarmu, Kasarmu da mulkinmu.
Cikin tsananin damuwa Sarki Zurmatu ya dubi Boka RAKUL ya ce yanzu menene mafita akan wannan Ala'mari?
Boka RAKUL yayi shiru daga bisani ya dubi Sarki Zurmatu ya ce, mafita guda Daya ce kacal.
Shi ne dole ne mubi bayan wadannan Aljanun da suka sace Sadauki MARGIM kafin su samu nasarar kaiwa BOKA GARGUS shi har ya warkar dashi.
Sarki Zurmatu ya Kara duban Boka RAKUL cikin damuwa yace, tayaya kake ganin zamu iya cimmasu kafin su Isa birnin SIN alhalin ka fada mana cewa duk duniya babu Aljanun da suka Kai su tsananin karfin gudu?
Sannan Kuma tayaya zamu iya samun nasarar kwato jarumi margim har mu hallakashi daga hannunsu?
Koda Jin wannan tambaya sai Boka RAKUL ya ce" hakane kamar yadda na fada maku cewa Aljanun da Boka GARGUS ya Aiko sukayi wannan aikin sun kasance masu tsananin karfin gudu tamkar kibiya, to kayi sani cewa har ila yau akwai wasu ALJANU na musamman wadanda suka kasance manyan IFIRITAI masu tsananin gudu tamkar na tauraruwa Mai wutsiya.
Su dai wadannan Aljanu guda dubu ne, Kuma dukkansu sun kasance manya-manya kamar Tsauni.
A tarihin rayuwarsu ba a taba samun aljanin da ya rigasu zuwa wurin da suka dosa ba, domin sau dubu saba'in suna lashe GASAR TSEREN GUDU da ake shiryawa a duk karshen shekara cikin fadar babban Sarkin Aljanu.
Saboda tsananin karfin gudunsu a cikin kwana guda kacal suna iya yawace duniya Kaf!
Wato su je karshen bangwayen duniya na bangaren gabas, Kudu, yamma da Arewa.
Boka RAKUL ya ci gaba da cewa Ina Mai tabbatar maka da cewa, muddin muka bi bayansu tare da wadannan IFIRITAI to zamu iya cimmasu kafin su Isa birnin SIN da ragowar sa'a biyar.
Koda Jin wannan batu sai hankalin su Sarki ya fara kwanciya, sannan Waziri Mikilas ya dubi Boka RAKUL ya ce, to yanxu tayaya zamu iya samun nasara a kansu yayinda muka riski wadannan Aljanun?
Koda Jin wannan tambaya sai Boka RAKUL yayi shiru Yana tunani Mai zurfi, bayan tsawon lokaci Yana tunani daga can sai ya dago Kai ya Kalli Sarki Zurmatu da Waziri Mikilas sannan ya kyalkyale da dariya tamkar babu wata damuwa a ransa..
Bayan yayi Mai isarsa, ya dube su yace ku kwantar da hankalinku domin na gano mana babbar mafitar da zamu jefi tsuntsu biyu da Dutse Daya.
Sarki Zurmatu ya ce fahimtar damu mafitar domin muji.
Boka RAKUL yace mafitar ita ce, dole na Kasa Sarkin yakin ka ya tattaro mana gaba dayan JARUMAN GASAR JARUMTAKA su zo mu hadu mu hau Saman wadannan IFIRITAI domin muje dasu inda zamu yaki wadannan Aljanun.
Da zarar mun riskesu sai muyiwa sauran jaruman Gasar bayanin cewa duk Wanda ya samu nasarar Kwato jarumi Margim daga hannunsu to shi ne ya lashe wannan Gasa.
Kunga kenan burinmu zayyi saurin cika, domin nasan mawuyacin abu ne wani daga cikin jaruman Gasar ya tsira da rayuwarsa daga bala'in wadannan ALJANU.
Koda Jin wannan tsantsar hikima da hangen nesa irin na Boka RAKUL sai dukkansu ukun suka bushe da mahaukaciyar dariya kamar bazasu dena ba, domin a zatonsu babu abinda zai hanasu samun nasara.
Nan take Sarki Zurmatu yayi gagarumin Shirin yaki sannan ya fito ya wuce fada Waziri Mikilas da Boka RAKUL na take masa baya.
Yana zama Kan KARAGARSA sai ya aika aka kira masa Sarkin yakinsa Mai suna DURKUL, wani gabjejen basamuden Kato ne Mai kirar manyan sadaukai majiya karfi.
Koda Sarkin yaki DURKUL yazo gaban Sarki sai ya risina ya kwashi gaisuwa.
Nan take Sarki Zurmatu ya fadawa Sarkin yaki duk irin abinda yake so akan Jaruman Gasa, cikin girmamawa Sarkin yaki yace angama ya shugabana Nan take Sarkin yaki yaje masaukin sauran jaruman Gasar sannan ya busa wani Kaho na musamman, Wanda da an busa shi to kowa daga cikin jaruman Gasar yasan cewa ana bukatar ganinsu cikin gaggawa.
Nan da Nan kowanne daga cikinsu yayi gagarumin Shirin yaki sannan suka fito filin Gasar suka tsaitsaya suna jiran Umarni.
Batare da Bata wani lokaci ba, Sarki Zurmatu yasa aka Tara gaba dayan mutanen birnin.
Dama tuni SARKI FALWAN da YARIMA FAZAMAL da sauran zakakuran dakarunsu sunzo fadar Sarki Zurmatu cikin gagarumar shigar yaki.
Bayan kowa ya halarci fadar, sai Sarki Zurmatu ya Mike ya fuskanci mutanen birnin gaba Daya sannan ya ce, " yaku jama'ar birnin BALLUS Mai albarka, kuyi sani cewa bayan fara Gasar Jarumtaka a yau din nan, wata Babbar matsala ta tunkaro mu, wadda indai bamuyi maganinta ba to tabbas sai kowa ya halakka a wannan birni..
A bisa wannan dalili ne muka shirya akan zuwa magance wannan matsalar, Sannan Kuma za'a cigaba da gudanar da Gasar Jarumtaka a can inda zamu tari abokan gaba, bayan mun gama da su sai mu dawo gida domin karasa Gasar da Kuma tabbatar da Alkawarinmu akan Wanda yayi nasara.
Don haka yanzu take zamu tattara namu'i namu domin muje mu tari makiya don jinkirin kadan na nufin hallakarmu gaba Daya.
Nan da Nan sai fadar ta kaure da hayaniya saboda Jin bayanin da Sarki yayi..
Nan da Nan kowa ya shiga cikin tsananin tashin hankali, domin wasu Nan take suka fara yin kuka.
Koda ganin yadda mutanen suka firgice suke ta kace nace, sai Sarki Zurmatu ya daka masu tsawa, Nan take kowa yayi tsit tamkar daukewar ruwan sama.
Kawai sai ya dube su a fusace ya ce bamu da isasshen lokacin batawa, kuyi hakuri kawai kuyi fatan Alheri, lallai mu ne da Nasara.
Don haka a yanxu zan bar Amanar Kasa ta a hannun Waziri Mikilas domin yaci gaba da tafiyar da al'amarin Mulki kamar yadda aka Saba kafin mu dawo.
Batare da wani Bata lokaci ba, Sarki Zurmatu da su Boka RAKUL da su Sarki FALWAN sukayi bankwana da sauran jama'a suka nufi babban filin Gasar Jarumtaka inda zasu hadu da Jaruman Gasa domin a dunguma a tafi.
Da zuwansu filin Gasar sai suka iske Jaruman Gasar a tsaitsaye kimanin su dubu Dari cikin mummunar shigar yaki.
Nan da Nan batare da Bata lokaci ba Boka RAKUL yayiwa Jaruman Gasar bayanin komai, sannan ya fiddo wani garin magani da cikin aljihunsa, sannan yayi tsafi garwashin wuta ya kama sannan ya barbada garin maganin a sama, kawai sai wani bakin Hayaki ya rinka tashi Yana taruwa a gefe guda, sai da hayakin ya shafe dakika Dari arba'in Yana tsiri a sararin samaniya sannan akaga ya rikide ya zama wasu manya-manyan halittu masu matukar girma har izuwa Kaso guda dubu, sannan kowannensu Yana da fuka-fukai guda Dari biyu da tamanin.
Cikin girmamawa wadannan gungun Aljanun sukayi gaisuwa a wajen Boka RAKUL, sannan suka Ce me kake da bukata ya Bokan duniya?
Nan take Boka RAKUL yace inaso ku dauke mu mu duka kubi bayan Aljanun da suka zo har fadar Sarki Zurmatu suka sace Sadauki MARGIM, lallai Ina so kuyi iyakar yinku domin mu riskesu kafin su Isa BIRNIN SIN.
Koda Jin wannan batu sai shugaban IFIRITAN ya bushe da dariya, sannan ya ce Ashe ma bukatar ku Mai sauki ce, na rantse da KARAGAR SARKIN ALJANUN DUNIYA zamu iya riskasu a cikin abinda Bai wuce sa'a bakwai ba.
Nan take suka kwashi gaba dayan Jaruman Gasar da su Sarki Zurmatu suka yi sama dasu a cikin tsananin gudun da yafi gaban kwatance.
Wannan shi ne abinda ya faru a birnin BALLUS bayan su Sarki Zurmatu sunyi gagarumar shigar yaki sannan sun tafi domin riskar abokan gaba.
******. ***** ***** *****
A yamma da Kasar birnin SIN Kuma akwai wata kyakkyawar Kasa ta musulmai Mai suna NURUL HAYAT, Ita dai wannan Kasa na karkashin mulkin wani Sarki Adali Mai rikon addini da son zaman lafiya ana kiransa da suna MUSBAHU.
SARKI MUSBAHU ya kasance tsoho dan shekaru casa'in da biyu, Amma Kuma har yanzu jikinsa Daram yake.
SARKI MUSBAHU ya kasance Yana da wani da guda Daya tal a duniya mai suna USAMA.
Usama shi kadai ne daa a wurin SARKI MUSBAHU Kuma ya kasance Gawurtaccen jarumi mai tsananin karfin damtse da Jarumtaka ta ban al'ajabi, domin shi kadai Yana iya yakar gari guda na Kafirai ya kashe na kashewa ya raunata na raunatawa, sannan kame matansu a matsayin bayi, ya kwashe dukiyarsu a matsayin ganima.
A halin yanxu shekarun YARIMA USAMA 35 a duniya, Kuma a Kalla ya yaki kasashe guda tamanin ya Kafa tutar musulunci.
Domin tun Yarima USAMA na Dan shekaru 15 a duniya yake fita Jihadi a duniya Kuma Yana samun nasara sosai akan Kafirai sbd kasancewarsa Jarumi na gaban kwatance.
Hakika wannan halayya ta Yarima USAMA ba karamin farantawa mahaifinsa Rai take ba, domin bincike ya tabbatar da cewa tun SARKI MUSBAHU na Dan shekaru Ashirin a duniya yake yaki da kasashen Kafirai da matsafa, Yana musuluntar dasu, domin izuwa yanxu ya yaki kasashe sama da guda Dari bakwai Kuma duk ya samu nasara akansu.
Tabbas SARKI MUSBAHU ya Sha gwagwarmaya da manyan Kafirai, Amma da karfin musulunci ba a taba kaishi Kasa a filin yaki ba.
Babban burin Sarki MUSBAHU shi ne ya zamana cewa musulunci ya mamaye ko'ina da Ina a fadin duniya, a dena Bautar gumaka da ALJANU da komai Wanda ba Allah ba, ta hakane sukaci gaba da yaki suna Kafa Kalmar musulunci har sai da suka ci gaba dayan kasashen dake nahiyar su da yaki.
To daman Yana daga cikin al'adar Kasar cewa duk Wanda zai hau KARAGAR MULKI ta Kasar, to dole ne ya shiga duniya domin JIHADI, Kuma bazai dawo ba har sai yayi nasarar musuluntar da kasashe a Kalla guda Dari biyar.
A bisa wannan dalili ne yasa YARIMA USAMA ya fara shirye-shiryen fita JIHADI, Kuma a halin yanxu saura uku ya fita.
Tun a wannan lokacin Banda farin ciki da murna babu abinda SARKI MUSBAHU da matarsa FADILA wato mahaifiyar USAMA sukeyi saboda ganin cewa dansu sauran kiris ya fita daukaka Kalmar Allah, domin sun San irin dimbin ladar da ke tattare da wannan JIHADI, Kai hatta sauran mutanen Kasar suna yin Taya YARIMA USAMA murna, sunaji a ransu cewa inama su ne zasu fita wannan JIHADIN.
Haka dai rayuwa taci gaba da gudana har kwana ukun suka shude, washe gari tunda sassafe jama'ar gari sun taru makil a fada domin yiwa Yarima bankwana bisa wannan fita da zayyi.
Sai da Yarima ya shafe sama da sa'a Daya da rabi Yana yin bankwana da mahaifiyarsa sannan ya samu ta sallameshi dakyar sbd tsananin sabo da shakuwa Dake tsakanin da da uwa.
Batare da Bata wani lokaci ba, Yarima ya fito fada sukayi sallama da Mahaifinsa sannan suka yi sallama da sauran jama'ar gari, ya kama dokinsa dauke da jikkar guzurinsa da battar ruwansha ya hau ya tunkarin hanyar barin garin.
Koda fitowarsa wajen birnin sai ya tunkari hanyar BIRNIN SIN Kai tsaye.....
Wannan shi ne abinda ya faru a birnin NURUL HAYAT bayan YARIMA USAMA ya fito duniya yada kalmar Allah.
***** **** **** ****
Ala'amarin wadannan gungun Aljanun na BOKA GARGUS kuwa, lokacin da suka sato Sadauki MARGIM sai suka kasance suna tsala matsanancin gudu a sararin samaniya, suka rinka gifta gajimare tamkar kibiyar da aka harba ta..
Sai da suka shafe sama da sa'a shida suna tsala gudu batare da wata matsala ba..
Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka hango wani bakin Hayaki ya turnuke a gabansu, Kuma ya cika hanyar daga sama har Kasa.
Saboda tsananin yawan hayakin har tokarewa yake da sararin samaniya, Nan take wannan bakin Hayakin ya rikide ya zama wadannan gungun IFIRITAN masu dauke da su Sarki Zurmatu da sauran jaruman Gasa.
Koda ganin haka sai gaba dayan Aljanun suka ja birki sannan suka sauko Kasa bisa turba, sai Suma su Sarki Zurmatu suka sauko daf da su.
Kawai sai Boka RAKUL ya dubi wadannan Aljanun ya tuntsire da mahaukaciyar dariya wadda Amsa kuwwarta ta cika Dajin gaba daya, bayan yayi Mai isarsa sai ya dube su yace, " ya ku wadannan ALJANU tabbas Kun tafka babban kuskure da har kuke mafarkin rushe mana burinmu ta hanyar sato Sadauki MARGIM domin kaiwa SHUGABAN KU BOKA GARGUS.
To kuyi sani cewa a yau zamu dandana maku azabar da tunda akayi duniya ba'a taba yiwa wani ba, domin babu dayanku da zayyi Rai.
Koda Jin wannan batu daga bakin Boka RAKUL, sai wadannan Aljanun suka kyalkyale da dariya tamkar ana ruwan aradu, daga bisani sai shugaban bakaken aljanun ya nuna rundunarsu Boka RAKUL yace, yanzu ku a tunaninku iya ku kadai zaku iya kashe mu sannan ku kwace jarumi margim daga hannunmu?
To kuyi sani cewa mun rantse da shugabanmu Koda yawanku ya ninka haka sau Dari ba zaku iya hanamu aiwatar da wannan aikin ba, don haka Muna masu shawartarku da ku kauce daga Kan hanyarmu domin mu cika aikin Dake gabanmu, idan ba haka ba Kuma dayanku bazai tsira daga kaifin takobinmu ba..
Koda Jin haka sai ran Boka RAKUL da na Sarki Zurmatu ya 6aci har ma zuciyarsu ta kama tafarfasa kamar zata kone, Nan take yace wa wadannan JARUMAN GASAR guda dubu Dari Maza ku afka masu Muga iyakar jarumtakarsu.
Koda Jin wannan batu sai gaba dayan Jaruman Gasar Nan suka zare makaman su sannan suka ruga izuwa kan wadannan Bakaken Aljanun, Suma sai suka rugo garesu duk da cewa yawan Aljanun Bai wuce dubu tamanin ba..
Wohoho! Inda ace mutum na Nan lokacin da rundunoni biyu zasu hadu, da sai yayi tunani kamar tsakanin mutanen duniya da aljanun duniya ne za'a kafsa yaki saboda tsananin yawansu.
Karar sawayen Jaruman Gasar da na Aljanun ya haddasa girgizar Kasa Mai tsanani, kururuwar mazaje ya haifar da dodewar dodon kunnuwan mutane Nan take wasu suka rinka kurumcewa.
Yayinda wadannan rundunoni biyu suka hadu, Kaico! Bala'i ba'a sa masa Rana, Kuma tabbas idan kwana ya kare to dole ne sai anje, haka Kuma idan Kaji ance ga ki gudu, to sa gudu ne Bai zo ba..
Nan da Nan Aljanun Nan sukayiwa Jaruman Gasar Nan rubdugu da nufin su yagalgala su, sai dai kaga Aljani ya kawowa mutum caka da tsinin bakinsa, da zarar ya goce to duk abinda ya samu take yake kamawa da wuta ya kone kurmus Koda kuwa Dutse ne.
Nan da Nan farmakin da aljanun suke kawowa Jaruman Gasar ya haddasa kamawar wuta a cikin Dajin gaba Daya, Amma har kawowa i'yanzu ko jarumin Gasa Daya Basu kashe ba.
Domin Jaruman Gasar suna kaucewa duk harin da aljanun ke kawo masu.
Sai da aka shafe dakika biyu cur ana fafatawa Amma ba Wanda ya samu nasarar komai, tabbas wadanda Jaruman Gasar sun kasance sadaukai na gaske, domin duk Wanda yaga irin harin da aljanun ke kawo masu Kuma suna kaucewa harin to dole ne ya ya jin-jina masu.
Koda cikar biyu da rabi, sai shugaban bakaken aljanun yace kowa ya Dakata, Nan take kowa ya cak kawai sai ya dubi Jaruman Gasar yace " tabbas Kun tafka babban kuskure da har kuka yarda kuka sallama rayuwarku domin yakarmu, don haka idan Kun yi a wannan farmakin na farko bari Muga yadda zakuyi da na biyu..
Gama fadin hakan keda wuya sai aka ga shugaban bakaken aljanun Nan ya wangame bakinsa Yana Mai kyalkyala wata irin dariya ta musamman Mai hade da wata irin iska Mai matukar karfin tsiya..
Nan take sauran Aljanun suka rinka zama iska suka shigewa ta cikin bakinshi, yayinda iskar ta rinka surar Jaruman Gasar tana makasu a jikin bishiya, Nan da Nan iskar Nan ta galabaitar da sama da Jaruman Gasa dubu arba'in, a wannan lokacin tuni gaba dayan Aljanun sun gama shiga cikin jikinsa.
Kawai sai ya tsuke bakinsa sannan ya takarkare ya kwarara wani uban ihu Mai tsananin Karar da har sai da bishiyoyi suka rinka karyewa suna faduwa Kasa, ruwan korama ya rinka fantsama, dabbobin daji suka rinka fadawa ramuwa suna mutuwa saboda tsananin razana, Kai hatta tawagar su Sarki Zurmatu sai da rabinsu suka rinka faduwa Kasa sumammu saboda tsananin razana, shi kanshi Sarki Zurmatu inba don Boka RAKUL ya tsafance inda suke ba, da tuni sun kurumce sbd tsananin Karar wannan aljanin..
Ba zato ba tsammani sai akaga wannan Aljanun sun rikide sun zama wani NARKEKEN ALJANI guda Daya Mai matukar girma da tsawo, saboda girmansa kamar kansa zai rinka tabo giza-gizai..
Nan da Nan wannan aljanin yayo Kan Jaruman Gasar ya rinka tamola dasu tamkar Yaro ya samu kwallo, Nan da nan ya rinka halba su sama suna shawagi tamkar karmami, kafin cikar dakika Dari da hamsin ya kashe sama da Jaruman Gasa guda dubu goma.
Yayinda wannan jibgegen aljanin ya zage dantse wajen kashe jaruman Gasar, kawai sai yaji wani abu Mai tsananin gudu ya doke bayanshi, saboda tsananin dukan sai da yayi tafiyar taku goma sannan ya tsaya da kyar, Nan da Nan sai ya waigo don ganin Wanda yayi Masa wannan aika-aikar...
WANENE YA DOKI BASAMUDEN ALJANIN NAN HAR YA KUSA FADUWA?
WANE BANGARE ZAI SAMU NASARA A TSAKANIN SU SARKI ZURMATU DA KUMA ALJANUN BOKA GARGUS?
SHIN A WANE MATSAYI RAYUWAR JARUMI MARGIM TA KE, ZAI RAYU KO KUWA HALLAKA ZAYYI?
YA BATUN CIGABAN GASAR JARUMTAKA A BIRNIN BALLUS?
WANENE ZAI ZAMA ZAKARA A CIKIN JARUMAN GASAR?
Mu hadu a GASAR JARUMTAKA littafi na 3 don Jin cigaban wannan Kasaitaccen littafi Wanda ni Najibullah Muhammad nake kawo maku shi✅✅✍️🙏🙏🙏