Author : NAJIBIBULLAHI MUHAMMAD Category : Romance
hallakashi a Kasa da dakika hamsin ba, Amma yau gashi su goma kuma sama da sa'a Daya da rabi Amma sun Kasa hallaka mutum Daya.
Nan take dukkansu ransu yayi mummunan 6aci, suka yo kukan kura gaba dayansu suka afka Masa da nufin su yagalgala shi, Kawai sai aka ga SADAUKI MARGIM ya daka wani wawan tsalle yana Mai daga takobinsa sama, cikin tsananin shammace da zafin nama sai kawai aka ya laftawa shugaban Dakarun Sara a wuya da nufin ya tsinke Masa Kai.
Amma bisa mamaki sai yaga ko Kwarzanewa bayyi ba, domin ji yayi tamkar ya sari Dutse.
Kafin yayi wani yunkuri tuni shugaban Dakarun yayi Masa wani wawan mangari a Fuska, saboda karfin dukan sai da SADAUKI MARGIM yayi tafiyar dakika Dari biyar a sama sannan ya fado Kasa a wani mummunan yanayi Mai kama da na Suma ko shurawa baya yi.
Koda ganin haka sai shugaban Dakarun ya kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya Mai nuna alamar nasara, kawai sai ya dubi Daya daga cikin yaransa yace yaje ya saro mashi Kan SADAUKI MARGIM.
Cikin tsananin zumudi wannan badakaren ya ruga da nufin cika Umarni, Yana zuwa kusa da Sadauki MARGIM sai ya daga falleliyar Addarsa da nufin fille Masa Kai.
Kwatsam ba zato ba tsammani, sai aka ga SADAUKI MARGIM ya yunkara cikin zafin nama sannan ya doke Kasa da hannayensa ya daga kafafunsa guda biyu ya bugi kirjin wannan badakaren, saboda karfin dukan sai da hakarkarinsa na hagu suka karye ji kake Kararas tamkar ana karya Kara.
Kawai sai aka ga SADAUKI MARGIM ya fizge takobin wannan badakaren sannan ya fille Masa Kai.
Nan fa filin Gasar ya rude da shewa da yiwa sadauki MARGIM jin-jina kasancewar yayi babbar bajintar da babu Wanda ya taba yin irinta.
Shi kuwa Sarki Zurmatu mamaki ne ya turnuke shi, saboda ganin yadda Sadauki MARGIM yake da tsananin Jarumtaka tamkar ba jinsin bil'adama ba.
Nan take hankalinsa ya dunguzuma domin Bai taba ganin sadauki Mai tsananin karfin damtse da zafin nama kamar sadauki MARGIM ba.
Nan take ya kudurce a ransa cewa lallai sai yayi zuzzurfan bincike akan Sadauki MARGIM domin sanin ko shi wanene.
Ala'marin SARKI FALWAN kuwa da Yarima FAZAMAL dukkansu fuskarsu babu annuri Kuma zuciyoyin su tafarfasa sukeyi saboda tunanin cewa kamar SADAUKI MARGIM na iya lashe wannan GASAR TA JARUMTAKA, saboda ganin irin tsananin sa'a da rabon da yake da ita.
Nan take suka kudurce a ransu cewa lallai kota wane Hali sai sunga bayan sadauki MARGIM, domin idan suka sake ya lashe wannan GASAR to shikenan duk burinsu ya rushe.
Ala'marin wadannan Dakarun Sarkin kuwa, cikin tsananin mamaki Basu San lokacin da suka tsaya cak, Sannan suka kurawa jarumi margim idanu ba.
Domin a tarihin rayuwarsu ba a taba samun wani mahaluki da ya taba yi masu irin wannan Barnar ba.
Nan take dukkansu guda Taran, suka takarkare suka kwarara wani uban ihu Mai cike da ban tsoro, Karar wannan ihu ta cika birnin gaba Daya.
Kawai Nan take suka rugo izuwa kan SADAUKI MARGIM.
Shima ya tare su rike da wannan Adda ta badakaren da ya kashe, suna haduwa sai ya dage iya karfinsa Yana saran Dakarun da wannan Addar, Amma abinda ya Kara bashi mamaki shi ne ko Kwarzanewa jikinsu baya yi.
Abinda Bai sani ba shi ne, wadannan Dakarun duk duniya babu wani makami da zai iya Huda jikinsu, duk makamin da kaga ya Huda jikinsu to na mamallakin makamin ne. Kuma Koda kayi Amfani da makamin Daya daga cikinsu domin yakarsu Nan ma bazayyi tasiri akansu ba, dole sai dai ka rinka kwace na kowannensu Sannan kana Amfani dashi wajen kashe Mai shi.
Koda ganin haka sai ganin haka sai ran sadauki MARGIM ya 6aci, kawai sai yayi jifa da wannan Addar, Nan take ya rinka tattara gaba dayan karfinsa wuri guda Yana sa gwiwar kafarsa Yana dukan hannuwansu da kafafunsu, Nan take Kasusuwan Dakarun suka rinka karyewa kamar ana sassabe a gona.
Nan fa ihun Dakarun da karajinsu ya cika filin Gasar gaba Daya.
Domin cikin kankanin lokaci ya karya Kasusuwan Dakaru bakwai daga cikinsu, Kuma duk Wanda ya karya sai kwace Addarsa Sannan ya fille Masa Kai.
Koda Shugaban Dakarun yaga wannan mummunar barna da Sadauki MARGIM keyi masu, sai zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, kawai sai aka ga shugaban Dakarun yayi tsalle daga inda yake tsaye, sannan ya cafko wuyan Sadauki MARGIM da hannu Daya, Nan da Nan ya rinka fyada shi da Kasa da hannu Daya, cikin kankanin lokaci Sadauki MARGIM ya fita daga hayyacinshi saboda tsananin karfin kayen da shugaban Dakarun ke Yi masa ya wuce misali.
A cikin dakika sittin kacal sadauki MARGIM ya Suma, sannan shugaban Dakarun ya sake shi, shikuma ya sulale Kasa ko shurawa bayayi.
Cikin tsananin fusata shugaban Dakarun ya ya zaro wannan Adda tasa, sannan ya laftawa Sadauki MARGIM wani lafcecen Sara a baya Sannan ya Kara lafta mashi Sara a ciki, sannan ya daka wani wawan tsalle ya duro akan Kafafunsa Nan take duka kafafun suka karye.
Cikin tsananin Jin zafi da Zogi sadauki MARGIM ya takarkare ya kwarara wani uban ihu Mai razanarwa.
A dai-dai wannan lokaci ne shugaban Dakarun ya daga wannan lafceciyar Addar sama da nufin ya fille Masa Kai.
Kwatsam sai aka ga SADAUKI MARGIM ya hada hannuwansa guda biyu Sannan ya Doki cinyar shugaban Dakarun, take cinyarsa ta karye ba shiri ya durkushe Kasa tare da Sakin Addarsa, cikin zafin nama Sadauki MARGIM ya dauki takobin ya fillewa shugaban Dakarun Kai da ita.
Nan take sauran Dakarun da suka rage guda biyu suka rugo gare shi, kawai sai gani akayi SADAUKI MARGIM ya bugi Kasa da hannuwansa duka biyun ya tashi sama kamar tsuntsu, Yana zuwa wajen ragowar Dakarun sai Doki makoshinsu a lokaci guda, Nan take duk su biyun sukayi mutuwar tsaye, sannan addunansu suka subuce masu, cikin zafin nama ya Suri addunan sannan ya fille masu Kai suka zube a Kasa matattu.
Faruwar hakan keda sai aka aka ga Shima Sadauki MARGIM din ya sulale Kasa a sume saboda tsananin Gajiya, ga Kuma wadannan manyan-manyan raunikan da Shugaban Dakarun yayi mashi, suna ta malalar da jini tamkar idon teku, bugi da Kari ga Kafafunsa duk sun kumbura sakamakon karairayewar da yayi.
Nan take Sarki ya bayar da Umarnin ayi Maza a daukeshi domin a ceto rayuwarsa.
Sannan Sarki yayiwa jama'ar filin Gasar jawabi cewa lallai kowannensu ya kasance cikin shiri, domin a yanzu za'aje hutun cin abinci kafin da yamma a dawo aci gaba da gudanar da wannan Gasa.
Sannan idan an dawo za a canza sabon jarumin Gasa Wanda zai fafata kafin SADAUKI MARGIM ya dawo hayyacinsa.
Lallai wannan Gasa bazata Dakata ba, daga Nan har sai munga Wanda zai lashe Kambun GASAR JARUMTAKA.
Yayinda SARKI ZURMATU ya gama wannan jawabin Sai ya sallami kowa tare da shaidawa kowa lallai da yamma za'a ci gaba da gudanar da wannan Gasa.
Nan take kowa ya watse Yana fadin albarkacin bakinsa.
Sarki Zurmatu da sauran sarakuna suka tashi daga Kan kujerunsu sannan suka nufi ainihin Babbar fadar Sarki suna tafiya cikin kasaita da izzar Mulki.
Dakaru na take masu baya.
ME ZAI FARU IDAN YAMMA TAYI AKA DAWO FILIN GASAR JARUMTAKA?
SHIN JARUMI MARGIM ZAI FARFADO A CI GABA DA FAFATAWA DA SHI?
WANENE ZAI LASHE KAMBUN GASAR JARUMTAKA?
WANE IRIN BAKIN GUMURZU ZA'AYI DA YAMMA A FILIN GASAR JARUMTAKA?
WANE IRIN SHIRI SU SARKI FALWAN DA YARIMA FAZAMAL SUKE YI DOMIN GANIN SUN LASHE KAMBUN GASAR JARUMTAKA?
Domin Jin wadannan Amsoshi sai ku biyoni a cikin LITTAFIN GASAR JARUMTAKA na biyu Wanda ni Najibullah Muhammad na rubuta Kuma nake kawo maku shi✍️✍️✍️
Ina yiwa kowa fatan Alkhairi tare da cewa sai mun sake saduwa🤝♥️♥️