Author : Maman Teddy Category : Romance
25.
Waro idanu waje Ma'eesha tayi tare da furta “ Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku wayyo Mami daddy.....Keeee!! Muryar Aliyu ya katseta cike da doka mata Wani irin gigitaccen Tsawa kana ya cigaba da cewa “ Wayyo Mami kike cewa? Yo sojan ne bakya so ko mene? . Cikin sauri ta katse shi tana gyaɗa kan ta sama Alamun eh ” kana tace “ Na tsani SOJA wallahi Uncle Haidar bana Son mace Soja, yanzu fa kaji Abinda Ya Khalil yace shima baya Son mace Soja. Ohhhh na fahimce ki”....ya furta yana kai hannun sa tare da sosa Gyefen saman cikakken gashin giran sa da Ya kusa haɗewa da Ɗan Uwan sa . Wato Saboda Khalil yace baya sha'awar mace Soja shine Kema bakya So kenan? . Hummm yanzu na fahimta , faɗa mun Son Khalil kike yi ne ko mene? Oya talk to me now . Faɗa mun yanzu!! Yayi maganan yana watsa mata Lulun idanun sa da suka saba rikitata , gashi a wannan lokacin magana yake kaman wanda zai kai mata hannu yasa duka”. Ma'eesha You keep silent? Hummm ya sauke yar taƙaitacciyar Numfashi kana ya cigaba da cewa “ Still you're a child , baki da hankali . To ki sani Bana ƙaunar wata alaƙa tsakanin ki da Khalil , ba Khalil kaɗai ba duka maza nake Miki magana babu alaƙa tsakanin ki da su . Sannan idan ma Soyayya kika fara to ki cire ma ranki do min kuwa karatu zaki yi na tsawon shekara 5 a SOJA kana ki zama cikakkiyar soja . Kin ga daga nan duk inda zani muna tare ....ya ƙare maganan yana kallon ta a kaikaice kana yace “ kar kiyi tunanin wani Abu na daban don na lura Ƙwaƙwalwar ki na juya Miki abun da ba dai dai ba .
Ni kawai kulawa dake nake yi , kuma Alƙawarin haka na Ɗauka , Sannan ina so ki Kaunaci soja a Zuciyar ki dama aikin duka , Saboda soja kaman ki zama , sannan kuma SOJA shine sanadin Rayuwar ki Ma'eesha , Don haka muna isa zan sa a fara baki atisayen motsa jiki . Daga nan kuyi na dambe .😱Uncle Dambe fa kace???? Ta katse shi tana waro idanun ta sai kuma hawaye shar-shar-shar . Wallahi Uncle Ni bana da ƙarfin dambe ban ma iyaba, sannan kuma wani irin Soja kake tunanin zan zama ? Wanne ciki ? Land Army kake nufi? . Yessss! Shi nake nufi . Ya furta a daƙile yana ƙara tattare giran sa . Land Army fa kace Uncle yau ya tabbata baka Sona, Sojojin da ake kaiwa daji a harbe kaman kiyashi kake so Nima na zama ɗaya daga cikin su .?
Wannan nayi niyyar ki zama , ko kina da Jah ko musu akai ne? . Daddy ma ai land Army yake mene kuma ya same shi , gashi har ya zama General a soja .
Kuka ta fashe dashi tana bubbuga ƙafarsa tare da cewa “ A'a wallahi Ni nurse nake so na zama , ba soja zan yi ba . Ai kaima Ba Land Army bane Sojan Airforce ne kai ni kuma nurse nake so na zama . A'a soyayya kika fara.............!
*Kuyi hakuri kwana biyu I'm busy shiyasa kuke ganin update din namu a haka 🙏🏻*
[1/13, 7:33 AM] +234 704 512 5150: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*
https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
Subscribe to my channel@maman teddy.
27.
*Don Allah kar ki karanta wannan labarin indai baki biya kuɗin sa ba . Ga masu buƙatar payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake.... Regular group₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
Jiki na Rawa Ma'eesha ta matsa ga Henry tana dai dai ta kafaɗanta da nashi , ba iya jikin ta ba harta Zuciyar ta rawa yake yana Kyarma tare da bugun uku uku ji take tamkar Zuciyar nata zata tarwatse ta watso waje . Cikin Sanyayyar Muryar ta yana rawa ta furta “ Wayyo Uncle ba zan iya ba ”. Wallahi tun yanzu na gaji gajiyar moto ta ishe Ni ban ci Abinci , kuma barci zanyiiiii.....keee rufe mun baki!! Yayi maganan yana ɗaga Muryar sa wanda sai da Sojojin wurin suka shiga taitayin su . Ji kake tsittt tamkar anyi Ruwa an ɗauke . Wani irin jan numfashi Ma'eesha ke yi tsoro duk ya gama rufe ta. Wannan yasata Fara ganin Jiri Jiri ......tamkar daga Sama take jin Muryar Uncle Haidar yana magana cikin sakewa tamkar bashi ne yanzu yake doka mata Tsawa ba . A'a mutumin kun iso . Yessss cononel da kan sa , Ina Ma'eesha take ne???. Jin baƙuwar murya wanda bata san shi ba kuma yana Tambayar ta yasa ta saurin juyowa tana cikin zazzaƙar Muryar ta ta furta “ Gani nan yallaɓai ta ƙare maganan cikin sanyi da neman agaji tamkar wacce ruwa ya kawo mata Wuya ”.
Saurin kallon ta Canonel Areef yayi yana Furta “ Ikon ALLAH Girma ba Wuya lallai jiya ba yau ba , give me warm hug...! Yayi maganan yana ware mata hannayen sa , wanda da Sauri Ma'eesha ta nufeshi tana rungume shi tare da lafewa bisa jikin sa , a Zuciyar ta tana faɗin Allah yasa ya ceceni daga Hannun Uncle , Da'alama ya Sanni tun ba yau ba , Gashi da ganin sa zaiyi Rahma kaman ba Soja ba . Maganar take a zuciya kamin taji Muryar Areef yana katse ta tare da Ɗagota daga jikin sa yana furta “ Ma'eesha kenan , ma'eeshan Uncle Aliyu, Yana ji dake sosai na sani, Don a da baya kina yarinya shi yake Miki komai , baya taɓa yarda ko sami namiji ya rungume ki kamar yanda nayi Miki harta Ni kuwa , wanka komai shi yake Miki sosai yasha wahala akan..... It's Okay please! Ya isa Areef , yanzu mu wuce dai daga ciki , sai kaji meke tafe Dani.
“ Aliyu ya furta yana katse shi tare da maganan yana kallon yanayin fuskar Ma'eesha wacce ta faɗa duniyar tunanin maganan Areef , Anya kuwa da gaskiya a maganar sa , Bai san yanda yake mun bane a yanzu , Da kuma ai abun da ya wuce ne🤗 ta furta a zuciyar tare da ɗaga kafaɗa alamun bai dame ta ba , Maganan ma bata yarda dashi ba . Da A yanzu nike shan wuyar kace i will definitely trust you for that , Amma kace wai shi yasha wuya akai na tabbas ƙaryata ka xanyi don Mami ke kulawa dani sai Ya Khalil . Duk mai Sona yaso ya Khalil shi ke kula dani yake So na sosai ...........“Ma'eesha!!! Muryar Areef ya katse Ta inda cikin sauri tace “ Na'am Canonel ”. No ki rani da Yayanki inda hali ɗauke Ni tamkar yanda kika Ɗauki Hausar i will be happy if you do that for me”. You are always welcome sir”. Ta furta cike da confidence ɗin nan nata . Shikam Ali caɓe baki yayi yana dalla mata harara a Zuciyar shi cewa yake “ See how she did like a brave girl , Amma Sam ba haka take ba, raguwa ce , Common running kasa ta yanzu zata fashe da kuka da yake hawayen basa mata wuyan zubowa ”. Common baby let go in ”. Muryar Areef ya katse su yana riƙo hannun Ma'eesha tare da fara barin wurin yana nufar Masaukin sa da su .
Mamaki ne ya kama ma'eesha ganin yanayin tsaruwar Musamman falon Canonel Areef tamkar ba'a wurin training ɗin sojojin yake ba . Ɗaga kan ta tayi sama tana kallon Hoton Areef cikin kakin soja inda yayi ƙyau Ainun, kana ta kalli Aliyu da suke zaune suna ɗan taɓa hiran su . Wow Uncle Areef you look so Gentle man , Kuma kana da kyau kaman ya Khalil 😄 . Murmushi Areef yayi kana yace “ Ko Ma'eesha yanzu a ina kike da karatu ?”. Yanzu ina M.S.U international school , I'm SS 1 student . Wow that's very good. Yayi ƙyau, me kike sha'awar zama a matsayin ki na mace nan gaba?. Yayi maganan yana kallon ta kana ya ɗan gyara zaman sa yana cewa “ No need nayi Miki wannan tambayar ba yanzu ba tukuna atleast sai kun kai SS2 kana hankali ya ɗan fara shiga ko?” . Shiru tayi masa tana ƙasa da idanun ta tare da wasa da dogayen yatsunta . A'a SOJA zata zama! Muryar Aliyu ya katse su .
Soja? Areef ya furta yana kallon Haidar kamin ya kalli Ma'eesha yana furta “ Amma tsarinta bai kama dana macen SOJA ba . Just forget about that topic , Wani Soja barta tayi karatu har ta kammala secondary You will understand what I'm trying to say now”. Amma Sam bata yi kalan soja ba . Kalli yarinya the most cutest girl kace Wani SOJA ? Ko da yake ban sani ba ko itace ke da Wannan Ra'ayin ?.
“Ɗan kallon Areef Ali yayi kana ya kalli ɓangaren da Ma'eesha take , Yana mai cizar laɓɓansa na ƙasa tare da Ɗan taunawa kana yace “ No nike da Wannan Ra'ayin , Sannan abin da nake so dole tabi layin nan , Saboda Hatta numfashin ta nawa ne. 🤔kame baki Ma'eesha tayi a Zuciyar ta tana cewa “ Me yake nufi? Ai Allah ne mai yi ma mutum numfashi ba wani Ɗan Adam ba ”. “Alright it's okay . Yanzu ina so ka fahimci Ma'eesha ba zata iya soja ba . Heeeeee!!! Keep standing don't move anywhere! Muryar Areef ya katse ta , yana sauya mata lokaci guda ya koma sojan da ya amsa sunan shi na soja , fuskar sa ya murtiƙe . Kusan mintina biyu tana ƙame kana taji ya furta “ Fara gudu ki dingi zagaye falon nan ina kallon time ɗin da zaki ɗauka har ki gaji, Oya start it now! . Da gudu Ma'eesha ta fara zagaye falon inda kaiwa da dawowa biyu tayi ta zube a ƙasa tana fara kuka tare da cewa “ Wayyo Uncles ba zan iya ba ,kuyi mun rai 😭”.
Kallon ma'eesha duka suka yi , kana Ali ya kalli Abokin nasa yana mai sauraren Abun da zaice .
Ka gani she can't be a soja at all , just ka barta a hanyar ta na ƴa mace , ka duba ko gudun minti ɗaya bata iya yi, Wannan zata fi dacewa da....... Enough 🙌🏻 , ya isa haka da ALLAH. Aliyu ya katse shi cike da ɓacin rai kana ya kalli inda Ma'eesha take Yana furta mu wuce masauki na . Yana furta zancen tare da miƙewa yana barin Falon . Kallon Areef Ma'eesha tayi kana tace “ Gaskiya kai me SO nane, thanks to meet you Uncle, ka bani Numbern ka don kana faɗa masa gaskiya ....Ga Wayata! Murmushi Areef yayi kana ya Girgiza kai yana furta faɗa mun number naki i will call later ”. Saurin Amsan wayar tayi tana loda masa nombobin tare da Ficewa da Sauri bayan ta basa Wayan tana bin bayan Haidar ”.
[1/17, 5:06 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*
https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
Subscribe to my channel@maman teddy.
28.
*Don Allah kar ki karanta wannan labarin indai baki biya kuɗin sa ba . Ga masu buƙatar payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake.... Regular group₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
________________________
Mami~.
Saukowa Mami take yi gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta , Haka zalika bata ko kallon gaban ta , a haka ta sauko daga stairs ɗin nan . Su duka maida hankali suka yi ixuwa gare ta . Janar Khalil da Kuma Jidder . Cikin Sauri Khalil ya miƙe daga tsaye yana kallon Mami kana bakin sa ta furta “ Mami lafiya kuwa? Meke faruwa ne?” . Kallon shi Mami tayi wacce take isowa inda suke. Kamin ta juya tana kallon direction ɗin da Daddy yake shima ita yake kallo tare da jiran jin Menene ke faruwa don babu makawa yasan da Aƙwai Abun dake faruwa a halin yanzu ” .
“Janar....! Janar Wai yanzu Hajiya Alawiyya ke faɗa mun anga Hajara kuma tana Raye!
Saurin miƙewa General Saleh Yelwa yayi yana kallon Mami kamin cikin Sauri yace “ Me kike ce ? Hajara fa kike magana an ganta ? Wacce ta bar gida Na Tsawon sheƙaru sha shida(16) . Ƙwarai Janar yanzu Alawiyya ke sanar dani, Wai yanzu haka tana Gidan Mahaifinmu Bara na tafi yanzu ”. Tayi maganan tana gyara zaman Keys ɗin hannun ta tare da juyawa tana nufar ƙofa . Cike da Rashin Sanin Wacece Hajara ? Jidder ta furta “ Mami zan biyo ki , Sannan kin manta baki ɗauki mayafi ba”.
Hummm Jidder idan zaki biyo Ni bismillah amma mayafi bana takan shi a yanzu . Mami ta furta tana mai saurin ficewa daga Falon .
Da Sauri jidder ta bi bayan ta , don itama a yau tana son sanin Wacece Hajara , duk da Tasan Ƙanwar Mami ce , Amma bata san menene yabar da ita gida ba , kuma sannan a yanzu a wani hali take ? Tabbas zata so ganin ta Wannan yasata bin bayan Mami cikin Sauri , Don sau da yawa kafiyar Aliyu da gayunsa ana cewa “ Babu inda yabar ƙanwar Mami wato Hajara , sai dai ita kuma rashin son jama'a musamman talakawa , sam bata son raɓuwa da ƙaasƙantattu , a cewan ahalin Wai ita wayayyace Shiyasa . Bayan Mami jidder tabi inda ita take Driving, Mami ba ɓangaren Hannun dama gaba Ɗaya hankalin ta baya jikin ta duk ta ƙosa ta gan ta gata ga Hajara , damuwarta na tsawon shekaru ”.
Early in the morning
7:00am......
Gudu take yi kaman tare da jijjiga jikinta tana kaiwa da komowa takaici duk ya ishe ta ga zufa dake tsatstsafo mata . Ƙwallah na bin kuncinta . Tun da nake ban taɓa ganin mugu irin Uncle Aliyu ba . Ta furta tana kallon can inda yake daga nesa yana kallon yanda take running exercise ɗin, shikam Hannun sa Ɗauke da Wani mug na coffee yana kaiwa bakin sa a hankali ƙwance ”.
Go! go...!!!
Ta tsinkayi Muryar sa daga can yana mata magana ganin ta tsaya , tana hutawa .
Da Sauri Ma'eesha ta ɗaga ƙafafunta tana cigaba da gudun tare da kukan zuci dana zahiri .
Fiye da minti talatin tana a haka , kana ta fara ganin Jiri Jiri na ɗibarta .
Cak taja ta tsaya tana ganin hazo² 🫨 tana ganin duniyar na juya mata zuwa gida da yawa . Cike da ɗaga murya babu wasa ya furta “ Tsayuwar mene kike yi anan , Ma'eesha na iso inda kike ranki zai ɓaci , zan zane ki anan Wurin , a haka ne zaki je training ɗin Sojan? What kind of nonsense exercise is that? . Zaki Cigaba ko kuwa sai na ƙariko nan??? Ya ƙare maganan cike da Tsawa da Ɗaga murya mai tare da amsa kuwa na cikakken Gwarzon namiji”. Maimakon ya ga tayi wannan kiɗimewar da ta saba yi a duk sa'ilin da taji Muryar sa ko faɗan sa amma a yanzu sai gani yayi tayi baya luuuuuuuuui tana zubewa a ƙasa sharaffff”. Hasbunallahu wani'imal wakeel Innalillahi wa'inna.....ƙasa ƙare magana yayi da Gudun sa a matuƙar kiɗime ya nufo inda take yana ɗagota cak tamkar bai ɗauki mutum ba , kaman ƴar tsana ya ɗaga....yana mai barin wurin tare da nufar moton sa yana bude gidan baya yana shimfiɗa ta , don ya lura Ko numfashi bata fitarwa ,ƙwance take tayi sharɓan wannan yasa hankali a tashi ya fice daga Barikin Sojojin yana nufar Wata asibiti na kuɗi (private hospital) dake kusa dasu .
A harabar asibitin tun daga saman Upstairs ɗin Wannan katafaren Asibitin Nurses da gudu suka fara saukowa zuwa Farfajiyar ajiye moto inda suka hango Aliyu Haidar fuskar sa a kiɗeme, haka gumi ke zubo masa . Idanun sa sun kaɗa sunyi jah . Ɗagota yayi tamkar ƴar tsana yana saɓa ta tare da wani irin manna ta da ƙirjin sa . Su kam Nurses hango kalon handon jikin sa na soja ne yasa su gudu irin haka , don sun san halin sojoji da bakar zuciya . Ƙarikowa garesa suka yi suna kai hannu tare da Kokarin Amsar Ma'eesha tare da cewa “ Yallaɓai kawota mu bata taimakon gaggawa”. Hummmmmm wata irin numfashi ya sauke tare da Ajiyar zuciya mai nauyi, fuskar sa ta sauya , a hankali cike da sarewa da karaya ya furta “ Rayuwata ce! 💔, ku yi mata kallo tun daga nan , idan zaku iya tada mun Ma'eesha na tsaya , idan ba zaku iya ba , na yi gaba na nemi asibitin da suka amsa sunan su ....idan kuma kuka ce zaku iya ,amma kuka ɓata mun lokaci abubuwa suka wuce sai daga baya kuka gaxa... wallahi tallahi na rantse da ALLAH Ma'eesha ta mutu a asibitin nan ko wani Abu ya ƙara samun ta kowa na Asibitin nan babu mai fita da rai .😲buɗe baki Nurse Zulfa'u tayi kana ta kalli nurse narret tana cewa “ Sister ma'amshe ta.....Saurin katse ta Nurse narret tayi tana kai Hannun ta tare da Amsan Ma'eesha daga hannun Aliyu kana tace “ Cool your mind Sir , everything will be okay ” .kamin ta jira jin mene Haidar zai furta da Sauri ta nufi Emargency da Ma'eesha .
Yallaɓai taho ga wuri ka zauna kamin mu fito .
Muryar nurse Zulfa'u ya katse Ali wanda yake kaiwa da kawowa , Goshin sa har wata jijiya ya fito masa na tsananin tashin hankali . Kallon banza ya watsa mata yana cigaba da kaiwa da komowa hankalin sa sam baya jikin sa