Author : halima Abdullahi K Mashi Category : Romance
ya tattara komai ya barma Allah, da haka varci 6arawo yake ta fisgarsa sama-sama.
Canjin rayuwa
2⃣1⃣Cikin dare ne yaji shigowar nurses din, sunzo ne su sake duba ta, yayi musu sannunsu da aiki, suka amsa suka tambaye shi ko kwai wata matsala? Yace musu babu komai suka ce to. Suna fita ya shiga bandaki yayo alwala yazo ya soma yin sallah, yana fada ma Allah matsalolinsa. Washe gari misalin qarfe bakwai na safe yana zaune kan sallaya yana tilawar qur'ani, sai aka turo qofar tare da yin sallama, Mahmud ne dauke da flask din shayi a hannunsa. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jiki, Ismail yace, da sauqi, gata nan bata ma farka ba, tun jiya data farka suka yi mata allura, Mahmud yace, ta farka babu wata matsala ko? Ismail yace, babu matsala, don ta gane ni, tana ta kuma kiran daddyn ta da kuma khalil dinta. Ban san yaya zanyi mata ba. Da nace mata yaron yana raye. Kasan ni na tsani inyi qarya, amma hakanan na fada mata sbd kar ta qara tada hankalinta, Mahmud yace, to yaya za'ayi dama ka fada mata gsky? Gara dai in ta samu sauqi, sai a fada mata. Ismail yace, tunani na kenan. Sannan kuma likita ya tambaye ni wai anan za'ayi mata dori, ko kuma a gida,wai inyi shawara, shine nace bari dai kazo inji yadda za muyi. Mahmud yace gara dai ayi mata anan asibitin, kasan dalili? Ismail yace a'a, Mahmud yace, kasan masu kudinnan aje ayi mata na gida, Allah ya kyauta ba'a fata, a samu matsala suce an barta a gd babu kula. Ismail yace hakane, duk nayi wannan tunanin. Sannan ga matsalar gurin zama. Ina zan kaita in an dora ta? Ni mai daki daya a zaure, Mahmud yace, hakane koma dai yaya ne, mu roqi Allah yasa ayi a sa'a. Baki suka hada gurin cewa Ameen. Ismail ya kalli flask din yace, harda ruwan zafi kazo min? yace eh, inna ce tace in taho maka dashi, ynxun ma zanje in siyo maka bread, sbd lokacin dana fito duk masu shagunan basu fito ba. Ismail yace, ka bari sai kamar qarfe takwas, don ynxun zaiyi wuya ka same su.
[8/18, 12:01 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2⃣2⃣Mahmud yace, to shikenan dama kai nake tunani, qila ma jiya ba kaci komai ba. Ismail yace saida yaya Amina suka zo, sannan da suka zo da abinci nace nafi son, ruwan zafi, shine mijinta ya kawo min bayan sun koma. Mahmud zai sake magana kenan, sai yaga kamar mimi tana motsi. Da sauri yace Ismail kamar tana motsi. Cikin azama suka isa gaban gadon, Ismail yace mimi kin tashi? Ta lumshe idanunta, sannan ta sake budesu ta kallesu. Alamu sun nuna yau jikin da sauqi, Numfashinta ya daidaita. Hawaye suka soma zuba daga idanunta, Mahmud yace sannu ya jiki? Bata amsa ba, sai dai hawayen ne ka bin gefen kumatunta. Ismail ya dora hannunsa akan nata, cikin damuwa yace sannu kinji? Zaki sha ruwa? Taja wani numfashi, cikin muryar marasa lfy tace, ni daddy na zaka kai ni, ban son wannan asibitin. Mahmud ya daga ma Ismail kai alamun yace mata eh, zai kai ta, Ismail yace eh zan kai ki, amma sai kin samu sauqi, sbd kinsan ba za'a iya tafiya dake a haka ba ko? Ta lumshe ido, ina.. Ina hajiya ta? Da momy na? Yace duk zasu zo. Sunce inyi miki sannu. Tace malam kace suzo su tafi damu, ni da khalil, kirasu ynxun malam. Yace zan kira su, zaki sha ruwa? Ta sake juyar da kai, dai dai lokacin ne wayar Ismail ta soma ringing. Ya ciro ta daga aljihunsa, sannan ya kalli fuskar wayar, hajiya sauda ce, don haka sai ya fita waje, ya daga tare da sallama, suka gaisa. Tace masa, Ismail yaya mai jikin? Yace da sauqi, tace ta farka ne? Yace eh ta farka kuma Alhmdlh jikin da sauqi sosai. Tace to mungode ma Allah, kar ka manta ka turomin account number dinka. Yace insha Allahu. Tace nagode sosai.
Canjin rayuwa
2⃣3⃣Bayan ya kashe wayar, zai juya kenan sai ya hango likitan ya nufo dakinsu don haka sai ya jira shi, likitan ya qaraso. Sun gaisa ta hanyar yin musabaha, sannan ya tambayi yadda ta kwana da jikin? Ismail yace jikin da sauqi yau, don ta daina wannan nishin. Likitan yayo ciki, Ismail ya biyo shi yana masa qorafin har ynxun bata ci wani abu ba. Daidai sunje kanta ne, likitan yake bashi amsa da cewa, kar ka damu da wannan, sbd ruwan da muka sa mata jiya da daddare yana dauke da sinadaran abinci, so, ko bata ci ba, ba zai zama matsala ba. Ynxun muje a debi jininka a gwada mu gani, in yayi sai muyi qoqarin saka mata a yau. In mun tabbatar da samun sauqin ta, sai mu saka ranar da za'a yi mata aiki, ina nufin dori. Ismail yace, na zaci yau za'ayi mata sbd kar qafar tayi tsami. Likitan yayi murmushi, kar ka damu zata samu sauqi, ba tare da wata matsala ba. Haka kuma babu abinda zai faru ko da takai sati daya ba'a dora ta ba. Ismail yace, shikenan Allah ya bata lfy. Ameen, inji likitan, tare da dafa kafadar Ismail ya jinjina. Sannan ya kalli mimi, sannu khadija. Ta dago, ta kalli likitan, ya kama hannunta mai lafiyar, inane yake yi miki ciwo ynxun? Tace duk jikina, amma qafafu na sunfi yimin ciwo da hannuna. Likitan yace, bayan nan fa? Ta soma kuka, nidai gidanmu nake son a kaini, can zanje gurin daddy na. Likitan yace, za'a kai ki da zaran kin samu sauqi, kinji ko? Tace ina khalil? Likitan yace, yana nan yana samun sauqi kinji? Cikin sigar lallashi yayi maganar. Kar ki damu kisha tea kinji ko? Tace ni banajin yunwa. Ina son in wanke baki na. Likitan yace, karki damu k8nji ko? Ya kalli Ismail, ka bini muje ko? Ismail ya dubi Mahmud, ina zuwa ynxun. Mahmud ya koma bakin daya gadon ya zauna tare da cewa to.
[8/18, 9:31 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2⃣4⃣Ismail yabi bayan likitan, suna fitowa, sai gasu yaya Amina, yace su shiga bari ya dawo Yanxun. Likita ne ya nuna masa har sashen masu dibar jinin, sannan ya kalleshi, in sun gama, ka sameni a office dina, kar ka damu ko kaga mutane ga shigo kawai, Ismail yace to nagode. Bayan an diba ne, sai suka ce ya tafi zasu kaima likitan sakamakon in sun fitar. Yace to, nan ya nufi office din likitan, kamar yadda likitan ya fada masa haka yayi, ya shiga duk da wadanda ya samu suna ganin likitan. Ya samu yana ganin wani a ciki, har zai fita, sai likitan yace, dan jira mu kadan, ynxun zan sallameshi, yana fita, ya nuna ma Ismail kujera, zauna nan. Ya dora hannuwansa saman babban teburin dake gabansa, sannan ya kalli Ismail wace, shawara kuka yanke? Game da daurin dorin matarka. Ko baku riga kun yanke shawara ba? Ismail yace mun yanke, kawai ayi mata anan. Likitan yace, shikenan za'a kawo maka takardar biyan kudi, sai kaje ka biya, sannan su baka takardar shedar biyan kudi, Ismail yace to, na gode. Likita yace, amma shi wanda ya mutu yaya suke da ita? Ismail yace, shi take so, likitan ya aje biron dake hannunsa, ya tattara hankalinsa a gurin Ismail, kamar yaya shi take so, gaka mijinta? Ismail saida ya danyi shiru, don ya tsani bada labarin, sannan yaba likitan labarin aurensu a taqaice. Likitan ya danyi jim, sannan yace, kayi haquri, ka kuma riqeta, wata rana zakaji dadin haqurinka. Ya miqe tare da cewa na gode likita, kar ka damu zan taimaka iyakar iyawa ta, inji likitan, Ismail ya sake cewa nagode, yace ba komai kaje, in sun kawo sakamakon kazo.
Canjin rayuwa
2⃣5⃣Lokacin daya dawo, ya samu mimi tana ta kuka, yaya Amina tana ta bata haquri, ya isa gurinsu, yaje cikin damuwa, daidai kunnenta ya rusuna yana cewa, yi haquri mimi, ki fadamin me kk so? Tace ni gurin daddy zanje, ka bani wayata in kira daddy na.Yasa dan yatsansa yana share mata Hawaye, wayarki ta 6ace a gurin da kukayi hadari, amma ki bari zan siya miki wata. In kinji sauqi, zan kaiki gurin daddyn ki. Sabon kuka ta saka, tana fizge-fizge, ya miqe ya koma kusa da Mahmud yace, nifa gsky zan kira mata shi suyi magana, Mahmud yace ka kira shi kawai don kada ta zarge ka. A handsfree ya saka wayarsa, sannan ya kira layin daddyn nata, tayi ta katsewa ba'a daga ba. Ya sake kira, gab da zata katse aka daga, tare da cewa hello! Ta gane muryar daddy, don haka cikin kuka tace, daddy kazo ka tafi dani. Zan mutu anan. Daddyn cikin zafin rai, a fusace yace kar ki sake kiran layina. Ni ba mahaifinki bane, baki daga cikin 'ya'ya na, da farko nayi niyyar in huce sbd kinyi min biyayya a karo na biyu, kinbi wanda na baki, ashe ke kina kan bakanki, to inaso ki sani, ko mahaifiyarki na samu labarin inda kk, sai na kada ta ta barmin gidana, bare wata nafisa da kk kira tazo, kisa a ranki bakida kowa sai wannan mijin naki. In kinga dama ki zauna. In kuma sake tafiyar za kiyi, duk ba damuwa ta bace. Nidai gargadina kar ki sake kirana, ko ke ko mijinki! Yakai qarshen zancen tare da kashe wayar sa. Ihu mimi ta saka, tare da fizge ruwan da aka sa mata a hannunta mai lafiyar. saboda tsananin kukan da takeyi, ya hana Ismail lallashinta, don bai san ta ina zai fara ba. Tayi kuka har muryarta ta dushe, babban takaicin ta, ba zata iya tashi ba, don da tuni ta fita titi, mota ta taka ta ta huta.
[8/18, 10:13 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 2⃣6⃣ Ganin abin bana qarewa bane, yasa Ismail kiran likitan. Yayi fada sosai, ganin halin da mimin ke ciki, yace bai dace mara lfy irin haka a sata cikin damuwa ba. Ya kalleta, khadija kiyi haquri dadyn ki zai huce insha Allahu, kinji ko? Tace ya daina so na, tunda ya iya hadani aure da talaka, nasan ya daina so na, kuma da gske yake yi, abinda yz fadamin, ya cire ni daga cikin 'ya'yan sa. Likita ka taimake ni, kayi min allurar guba in mutu, likita yaja kujera ya zauna, bai kamata ki nemi mutuwa ba bayan Allah ya raya ki, kun yi mugun hadari fa, da Allah ya ga dama, sai ya dauki ranki a lokacin. Ki natsu koda daddyn ki ya qi ki, ba ga mijinki ba? Tace bana sonshi! Malami ne fa? Ismail ya lumshe ido cikin takaici, kar ki damu, ki bari ki qara samun sauqi, muga yadda za'ayi, kinji? Ta dago ido ta dubeshi, zaka barni mu tafi tare da khalil? Ynxun bani da kowa sai shi, yace zaku tafi, da qyar suka lallashe ta tayi shiru
Kwadayi madudin wahala na'im da mom Nafisa bakuga komaibama ai
Canjin rayuwa
2⃣7⃣Ismail yace, ga ruwan da ta cire nan a maida mata. Likitan yace, babu damuwa, tunda ta dawo hayyacinta, zata iya cin komai ba sai an maida ba. Sannan jininka za'a iya ba kowa, don haka za'a zo a diba ynxu. Ismail yace, zanje can ne? A'a ba sai kaje can ba, inji likitan. Anan ma za'a zo a diba. Da qyar Mahmud ya matsa ma Ismael yasha ruwan tea. Shi kansa duk ya rame sbd tashin hankali. Tara da kusan rabi, Sai ga wata nurse ta shigo da wasu mata guda biyu, lokacin yaya Amina tana cewa bari ta tafi, shi kuma Ismail yana cewa Mahmud, ya kamata kaima ka tafi. Shi kuma yana cewa, bari dai in an dibi jininka din sai na wuce. Sallamar wasu matan ne, yasa su yin shiru daga zancen da suke yi don jin ko su waye. Dai dai lokacin mimi ta dangana daga kukan da takeyi har ma ta yanke hukuncin yadda zatayi. Nata ganin, abin da zai fissheta, in sun samu sauqi ita da khalil, zata bishi gidansut tunda shi hajiyarsa tana sonsu tare, sai ta zauna a gidansu, in ya kammala karatu sai ayi musu aure, Amma ta daukar ma kanta alqawarin yadda daddy yace ya barta, ita ma har abada ba zata sake nemansu ba. Dama hajiya bata sonta, shikenan zata yi Rayuwar ta da khalil, ta amince bata da kowa sai shi din. Sallamar matan ne ta katse mata tunani. Ta daga ido ta kalle su. Ko cikin mata dubu ba zata kasa sheda fuskar mahaifiyar khalil ba. Ba wai don kamar da sukayi dashi ba, domin tun kafin suje gidansu a kwanan baya ita da khalil din, ta mallaki hotunan mahaifiyar tasa masu dinbin yawan gske a wayar ta wadanda khalil din ke turo mata. A ranta tace shikenan ma tazo tafiya damu. Nasan khalil ya riga ya fada mata komai. Sai taji wani farin ciki ya darsu acikin zuciyar ta.
[8/19, 11:13 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 2⃣8⃣Kukan da mahaifiyar khalil din ta fashe dashi ne ya katse tunaninta, tare da tattaro dukkan hankalinta zuwa gurin ta. Ji tayi tana fadin. Alahu Akhbar! Yarinyar nan babu rabon kuyi aure da khalil, ajalinsa ya jawo miki wahala. Ni dama nayi tunanin wannan zazzafar s soyayyar da khalil ya kamu da ita, da qyar in zai rayu, yaron nan bai ta6a min sata ba tunda ya taso, sai dalilin wannan soyayya. In da mahaifinsa ya bada hadin kai, kila da ynxun khalil yana raye. Allah ya baki lfy. Mimi ta zaro idanu tana kallonsu. Qwaqwalwarta ta kasa saita zantukansu. Wai suna nufin khalil ya mutu ne? Ismail kuwa ya rikice, yana ta yi wa nurse din alama da yatsansa a baki wai suyi shiru, amma sam basu lura ba. Saima fadi da nurse din take yi, wai iyayen wanda ya mutu dinne suka zo daukar gawarsa, shine suka ce a rakosu su duba ta. Daya matar kuwa wadda suka zo tare, fadi takeyi, kiyi haquri aunty Amina, Addu'a kawai zaki yi masa, kinyi dauriya a gida, baki masa kuka ba, sai anan? Cikin kuka mai tsanani mahaifiyar take cewa, ban gaskata mutuwarsa ba saida nazo naga gawar khalil. Ihun da mimi keyi ne ya katse mahaifiyar khalil. Wani yunquri da mimin tayi shine ya saka su nufar gadonta. Sai dai Ismail ya rigasu isa. Duk da haka kafin yakai ta riga ta kai qasa a sume. Ya dauke ta yana fadin, inata alamta muku cewa kuyi shiru. Sbd batasan komai game da mutuwarsa ba, amma sam baku kula ba, gashi kunsa itama za'a rasa ta. Ya dora ta akan gadon yana cewa, ku taimaka ku kiramin likita! Mahaifiyar khalil fadi take, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Ai ban san bata sani ba, nurse kuwa tuni tayi qasa da gudu don kiran likita.
Canjin rayuwa
2⃣9⃣Qarfe sha daya da mintina momy Nafisa ta shiga gidan 'yarta Na'ima. Aljannar duniya. Ha ta furta lokacin data iso cikin falon farko, Ta kalli 'yar tata, wadda tazo ta bude mata qofa. Na'ima kina cikin irin wannan gdn kk daga hankalinki? Na'ima ta turo baki, momy ni wannan gdn yayi mintg girma, abin haushi kuma ni hadai ke yini a cikin sa. Momy tace, a'a ina masu aikin da akace an kawo miki? Tace, suna gefensu. To ai su ba abokan hirana bane momy. Suje su raina ni? Momy tace, ba nufi na kenan ba, ba wai kuyi hira ba, ina nufin a qalla kina jin motsin wasu a cikin gdn. Na'ima ta turo baki, to momy shifa bashi da lokaci na. Momy tace, matsalarki dai mijinki ko? Na'ima tace eh. Momy nafisa tace, kije kice masa inason ganinsa, ko har ya fita? Na'ima tace, yananan banji fitar sa ba. Ta miqe ta nufi sama cikin zumudi. Tana bude qofar ta jiyo shi yana waya, yana zaune a kujerar computer. Daidai abinda kunnenta ya jiyo yana cewa, "tsaya mana kiji Jennifer. Kar kisa ma kanki damuwa, na fada miki ba wadda nakeso din na aura ba, ko da ita dince ma kinsan cewa ke ta musamman ce, kina tsammanin rayuwa ta zata tafi sak ne in babu ke? Cikin turanci yake magana. Yayi jim, alamun yana sauraron abinda take fada. Sannan yayi 'yar dariya, tare da cewa, na san dai zaki iya bada sheda ta kan fadar gsky komai dacinta. Ya sake yin jim, sannan yace, to zan tabbatar miki da cewa kinfi wadda aka kawomin a matsayin mata. Zan tabbatar miki yadda ke da kanki zaki gamsu da batun, ya sake saurawa. Sannan yace, fadamin me zan miki ki yarda tunda naga kina tantama, kamar kin manta ni waye. Dariya taji ya saki, tare da fadin, ai wannan mai sauqi ne, in dai kwana da nine, ina me yi miki albishir cewa, ni da ke yau a gida na zamu kwana. In nayi miki haka, zaki gamsu cewa ni dake mutu-ka-raba?
[8/19, 5:55 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3⃣0⃣Maganar ta maqale, bai qarasa ba, sakamakon jin muryar Na'ima da yayi cikin kuka tana cewa, dama mata kk nema? Ya saki murmushi, sannan ya maida wayarsa kunnensa. Baby zan kira ki zuwa Anjima. Ya kashe wayarsa, sannan ya juyo da kujerarsa gaba daya, don irin mai jujjuyawarnan ce, cikin fara'a yace, baki sani ba dama? Ta tsaya tana Numfashi, tare da mamaki, gami da zaro idanu. Yayi murmushi mai sauti, kina nufin dama bakuyi bincike ba? Ya girgiza kai ayya. Ni qasurgumin manemin mata ne. Sannan ina shan wiwi da giya kadan, akwai wata matsala ne? Ta rasa me zata ce, sai kuka. Cikin kuka take cewa, ba zan iya zama dakai ba. Mutumin da baya iya 6oye laifinsa. Yace, oho, dama kinzo kin la6e min ne? Kada ki zauna dani din mana, dama ni na kawoki? Ko na riqe ki ne? To kazo momy na tana jiran ka a falo, ya ta6e baki, wacece kuma momy? Tace, don wulaqanci, mahaifiyata dince baka sani ba? Ya kalli danqareren agogon bangon falon, me kuma tazo yi da wannan safiyar? Ya kalli computer dake gabansa. Ta jirani, aiki nakeyi, in zata iya, in kuma ba tada lokaci, taje ta dawo