Author : Indo Ce Category : African Stories & Novels
haɗu, karɓa yayi da sauri ya koma ya shigo da motar.
yana ajiyeta Kai tsaye ɗakinsa ya wuce sai da yasa mukulli ya kulleta gam sannan ya zame a gurin ya fashe da kuka me tsuma zuciya.
Allah me yadda yaso bashida wata damuwa a duniya wadda ta wuce ƴan uwansa mahaifinsu ɗaya amma sun maidashi kamar shaiɗan sun tsaneshi basa ƙaunar ganinsa kowannen su bashida burin da ya wuce ƙaga masa sharrin da ze jawo masa ƙuntata da ɓacin rai shi kuma tashi ƙaddarar kenan.
Ya daɗe yana kuka a gurin har ya gaji ya dena sai kansa da yake masa wani azababben ciwo, sai da aka kira sallar Magrib sannan ya tashi ya ɗauro Alwala.
Bayan ya idar da sallar ya ɗakko Alƙur'ani ya shiga karantawa cikin nutsuwa tareda fatan samun salama daga zafi da ƙunar da zuciyarsa takeyi.
Sai da yayi sallar isha'i a wajen sannan ya tashi yana ƙoƙarin kwantawa yaji murya Abansa yana kiran sunansa.
Da sauri ya tashi ya buɗe yana murna.
Hannu Aba yasa ya tallafo haɓarsa yana ƙare masa kallo cikin tausayawa yace, "Yaro!!! fuskarka tayi jajur shatin yatsune sosai akanta waye???"
Ƙasa yayi da lumsassun idanunsa hakan ya bawa hawayen da suka cicciko damar ɗigowa.
Aba yace, "mahaifiyarka ta kasa gaya min kaima haka??, Meyesa kuke son ɓoyemin abunda ya shafeni? ƴan uwanka ne ko??"
Faɗawa yayi jikinsa ya ƙanƙameshi sosai cikin harshen fulatanci yace, "Abana meyesa basa sona wane laifi na aikata musu da suka tsane ni? kenan kuskure ne kasancewata ƙaninsu??"
cikin sanyi Aba yaja hannunsa ya zaunar dashi sannan yace, "ba kuskure bane sune dai suke aikata kuskuren kayi haƙuri ka jure komai wata rana sai labari, ka gaya min waye ya taɓa ka yau?"
Girgiza kai yayi yace, "aa Abana dani dasu duk abu ɗaya ne suyi komai kawai lokacin su ne karkace musu komai, amma kasani akwai ranar da zata zo wadda ko yatsa ɗaya daga cikin su ya nuna min sai na karya yatsan"
Ya ƙarashe maganar cikin shashshekar kuka tareda tsananin ƙunar zuci.
Ummi da ta shigo yanzu ce ta daka masa tsawa da cewa, "kulll Jannah!!!!! karka bari naƙara jin makamancin irin wannan furucin daga bakinka, ko Jaafar shine autansu kuma kasani sama yake da kai ban yarda kayi rashin kunya wa yayyen ka ba koda da minti ɗaya suka girmeka, banaso"
Aba yace, "bazeyi ba ma dan ba halinsa bane amma ni zanyi ruwa da tsaki a ciki tinda ni na isa dasu"
da sauri tace, "banaso fa idan kayi musu faɗa duk akansa zasu juye raina ne ze ƙara ɓaci a banza"
Jinjina kai Aba yayi yace, "Yaro!! bana son ganin kana kuka kayi haƙuri ka dena ai na dawo"
Lafewa yayi a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya akai akai, Aba ya goge masa ƙwallar da tayi shaɓe shaɓe akan fuskarsa yana yi yana hura masa iskar bakinsa a hankali, hakan da yake masa kuwa ba ƙaramin daɗi yakeji ba ajiyar zuciya har har bibbiyu yake haɗawa kamar ƙaramin yaro.
sai da ya samu nutsuwa sosai har bacci yafara shirin ɗaukarsa sannan Aban yace, "tashi muje kaci abinci"
Ba tareda yayi magana ba ya tashi..
lokacin da suka fito Ummi ta gama shirya musu abincin dan haka suka zauna kawai,
Kamar kullum a baki Aba yake bashi yana ci kaɗan kaɗan yana yi yana shagwaɓa.
Share fisabilillah.
*INDO CE..*
[7/18, 9:03 AM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*
NA INDO CE..
Marubuciyar Sirrin Ƙeta A jini Ɗaya Tajmahaal paid book Ib ɗan wanka Rintsin So tareda Sihirin ƙauna da Dogon Yaro
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
Na kuɗi ne😂
300 kacal
FREE PAGE
*shafi na 3*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Sai da Aba ya tabbatar ya ƙoshi sannan shima ya ci, bayan sun kammala Aba yace, "Yaro ina fatan dai ba wani abun?"
Yace, "Abana bana rabo da ƙorafi wallahi fita nakesonyi kuma waccan farar yarinyar ta hanani "
Aba yace, "wa kenan ba dai Fauziya ba?"
Da sauri Ummi tace, "wace fa idan ba karkatacciyar kuka ba? tayi ma bacci ita idan zaka fita ka fita idan kuma bakai niya ba to, ko gurin wa ma zakaje a daren nan oho"
yayi ƴar dariya sannan yace, "Nan!! ina namiji idan ban fita ƙarfe taran dare ba waye ze fita?, Aba bar zancen kawai bazan fitan bane saboda nayi mata alƙawari kuma banason saɓawa"
Aba ya murmusa cike da farin ciki yace, "masha Allah ina matuƙar farin ciki da jin daɗin irin kulawa da ƙaunar da kake bawa ƙanwarka Harma da yayyen ka guda uku wanda sune suka kasance fansar sauran ƴan uwan naku a gurina, inada tabbacin ko bana raye zaka iya kulamin dasu indai da ranka da lafiyar ka, ina ƙara jaddada fatan alkairi na gareku baki ɗaya Allah ya yi muku jagora a duk lamuran ku"
Cikin jin daɗin addu'ar ya amsa da "amin Abana abun alfahari na, insha Allah bazaka mutu kabarni ba zamu rayu tare"
Aba yayi murmushin manyance ba tareda yayi magana ba .
cikin harshen buzanci Ummi tace, "Jannah! kaje ka kwanta dan Allah gobe litinin fa zaka tashi da wuri"
beyi musu ba ya tashi rungume Aba yayi yace, "Allah ya tasheka da rai da lafiya Abana"
Aba ya shafa kansa gami da cewa, "Amin Allah ya amsa tareda kai Yaron kirki"
Yana murmushi ya koma wajen Ummi itama rungumeta yayi yace, "Ummina karki manta kimin addu'a"
Tace, "Jan bazan manta ba"
Dariya yayi sannan ya nufi hanyar sashinsa yana tafe yana waiwayen su.
Ummi sai da ta tabbatar ya tafi sannan tabawa kukan da yake cinta damar fitowa.
Aba ya dawo kusa da ita ya zauna cikin tausayawa yace, "Aaminatu? meyesa zakiyi kuka? ni kuma yaya zanyi kenan idan ke da kika kasance ƙwarin guiwata kikayi kuka??"
Share hawayen ta shigayi tareda ƙoƙarin tsagaita kukan.
Janyota yayi zuwa jikinsa yayi mata masauki cikin sanyi yace, "Aamina kin jure kinyi haƙurin zama dani har lokacin nan, lokacin da mukejin ranar kukan mu ta wuce Allah ya azirta mu da ɗa kamar MUFTAHUL'''JANNAH amma ki zubda hawaye? meye ya ragewa rayuwar mu wanda ya wuce mu godewa Allah da ya bamu su? shine ya bamu kuma yasan halin da suke ciki kuma dukan mu muna gareshi ne duk abunda ya faru dani dake dashi dasu duka ma duk Allah yana sane kuma yasan me gaskiya yasan mara gaskiya koda ba a gidan duniya ba wata rana zakiga lokacin da Allah zeyi mana SAKAYYA (Littafin Gimbeeya) akan duk wanda ya zalumce mu, ƙwarara masa zuciya yakamata mu dinga yi ba mu raunana masa ita ba, dan Allah Aaminatu"
Shiru tayi tana sauraren sa har ya kammala sannan tace, "a koda yaushe idan da ɗan adam zeyi nazari? tabbas da ze gane lokacinsa kaɗan ne lokacin farin cikinsa ƙalilan ne, jiya ta wuce ɗazu ta wuce ko anjima bamu san ya zata kasance mana ba bare kuma gobe wannan sai Allah, kuma muna manta cewa mutuwa rigar kowa ce idan baka mutu ba to za'a mutuwar maka, za'a mutu a barka ko kuma ka mutu kabari bakasan halin da kabar baya ba, ina tunanin goben mu da ƴaƴan mu tabbas zuciyata tana gaya min akwai babban ƙalu bale da ɗanmu ze fuskanta a rayuwar sa ta gaba bayan na baya da ya fusjanta koma nace yake ka fuskanta kaga kuwa ni kuka ya kama idan kayi nazarin kalamai na zaka fahimci hakan"
Aba ya numfasa sannan yace, "wannan gaskiya ne Allah yasa mu dace ya iya mana akan duk abunda bazamu iya ba "
Jancy.
har ya gama ƙalular sa da tunane tunane ya kwanta bakinsa ɗauke da addu'o'i yana shirin bacci yayi awon gaba dashi yaji wayarsa tana ƙara , kamar baze ɗauka ba tsoro da shakka yasa shi ɗaukar dan dole cikin sanyi ya kara a kunne tareda yin sallama.
A ɗaya ɓangaren Fahad yace, "kai Dogo zo kaimin wankin ƙananun kaya dallah,
kamar zeyi kuka yace, "nafa kwanta har nafara bacci ka bari sai gobe"
Cikin isa da gadara yace, "yanze nake so kuma idan kanajin ka kai kace ba zakai ba"
share ƙwalla yayi gami da cewa, "ina zuwa amma kana ina?"
Yace, "kayan suna sashin Hajiya Murja kuma kazo sashin mu kayi wankin banaso kasa a injin wanki kuma"
"to" kawai yace sannan ya tashi ya nufi sashin Hajiya Murja yana tafiya yana sharar ƙwalla, raɓewa yayi ta hanyar da yasan bazeyi karo da Aba ko Ummi ba.
Sallama yayi a falon babu wanda ya amsa har sai da yayi sau uku sannan Fauzi tace, "gafara dallah kazo ka cikawa mutane kunne da sallama kamar wani maroƙi ubanme zakai anan??"
Ƙasa yayi da kai sannan yace, "Yaya Fahad ne yace inzo inyi masa wanki"
Tace, "sai dai kaje ɓangaren su dan bayanan bazaka shigo ba"
Hajiya Murja ta murmusa a ƙasaice tace, "barshi ya shigo Fauzi me ze iya ɗauka koma me ze iyayi?? zo ka wuce ka ɗauka sai ka shiga sashin nasu yana ciki"
Cikin sanyin jiki ya shiga yana tafiya a hankali cikin tsoron yayi takun da ba dai-dai ba ya faɗa ruwa.
Jaafar da yake zaune yana danne dannen waya ba tareda ya kalleshi ba yace, "kai maza ka kawo min 30k idan ka koma"
Cikin ƙarfin hali yace, "saboda me?? me zakai dasu??"
Yayi ƴar dariya sannan ya cigaba da danna waya.
har ze wuce ya dakatar dashi da cewa, "dakata!!"
Tsayawar yayi yana sauraron abunda ze ce, sai da ya gama danne dannen sannan yace, "shagali zanje nayi nida budurwa ta kai harma da abokaina bani 50k kawai ina jiranka gobe kafin ka tafi makaranta zan karɓa kuma idan ka bari tsohonka ya hana sai na saɓa maka kamanni"
da " to" kawai ya amsa dan baze iya yin jayayya dashi ba musamman anan da ya shigo tsakiyar su, wucewa yayi inda Fahad ya kwatanta masa ya ɗauki kayan sannan ya wuce sashin Hajiya Saratu.
Haka sukai ta ciccira shi har 12:00am sannan suka barshi ya koma sashin su lokacin bacci ya gama cin galabarsa.
Washegari da ƙyar ya tashi saboda bacci me nauyin da ya danneshi, sai da yayi addu'a sannan ya tashi ya nufi ɗakin wanka shower ya sakarwa kansa ruwan yafara dukansa yana ratsa shi a sannu a sannu ajiyar zuciya ya sauke gami da lumshe ido sannan ya shiga shafa sumar kansa ya a yamutsa ta, tunanin mafarkin da yayi a daren ne yake ta yimasa yawo aka ya rasa ina abun ya dosa ko kuma yake son zuwa amma yasan mafarkin ba shawai ɗin mafarki bane me hujja ne, ya rasa meyesa baya taɓayin mafarki me daɗi sai dai mummunan mafarki kullum, yana ganin abubuwa da yawa wanda ya kasa fahimta kuma baya son sanarwa wani irin munanan mafarkan dan yana matuƙar gujewa damuwar su.
ya daɗe yana tunane tunane kafin yayi wankan ya fito ya kintsa, lokacin da ya fito tini Natiee ta gama shiri dan kuwa tana tsoron barazanarsa idan ya rigata shiryawa ƙarshe ma baze bari tayi shiri me kyau ba.
Sai da ya tanadi kuɗin da ze bawa Jaafar sannan ya samu ƙwarin guiwar fita a wajen motarsa ya tarar da Jaafar ɗin yana jiran fitowarsa kuɗin kawai ya bashi ya shige mota dan bayason hayaniya bare tashin hankali duk abunda ze zamo matsala ba ƙaunarsa yake ba.
Zaune take a gaban madubi tana ƙarewa kanta kallo fara ce sol kyakkyawa sahun farko ƴar duma duma hannu tasa ta kwashe gashinta da ya bazu har kan fuskarta tayi baya dashi ta cigaba da kallon fuskart, Masha Allah, tana da ƴan saffa saffan idanu ba manya ba ba ƙanana ba farare sol sai ƙwayar idon da tayi sirki da brown color sai dogon hancinta irin wanda ake kira hanci har baka ɗan bakinta ɗan madai-dai-ci.
Cikin shauni tayi ƴar kwalliya mara yawa daga kwalli sai manbaki sai hoda.
Zahra ce ta shigo tana kiranta, ta amsa sannan ta cigaba da cewa, "na rasa ma da yaya zanje makaranta yau Zahra bani shawara mana"
Zahra tace, "kai Queen gaskiya Allah ya fiddake dai kawai, amma wannan kwalliyar duk akan wanda ko kallonki ma ba lallai yayi ba bare ya gani, Shawarar da zan baki kawai ki dena kwalliyar ma"
tace, "wallahi bazan dena ba son gaskiya nakewa Jan dan haka zan juri ko me zeyi min na rashin mutunci wata rana sai labari idan na mutu sai dai ace ai da Zuhra ta So Jancy sosai, to irin wannan tarihin nakeson kafawa a rayuwata"
Zahra tace, "banajin wata rana ma Jan ze kalle ki a matsayin mace, kinfiye zaƙewa da yawa ki tsaya iya matsayin ki tinda ya riga ya nuna miki iyakar ki"
Tace, "dena wannan maganar Zahra, banida iya tsakanina da Jancy babu wani layi da ze shata wanda ze shiga tsakani na dashi sonshi ba? to Yanzu na fara"
Zahra tace, "to naji amma ya zakiyi da masoyiyar sa da ya mutu akanta"
Zuhra tace, "Zeety!!!!!!............"
*INDO CE..*
[7/18, 9:03 AM] Indo ce: *🌴🌴🌴DOGON YARO🌴🌴🌴*
*(Jancy)*
NA INDO CE..
Marubuciyar Sirrin Ƙeta A jini Ɗaya Tajmahaal paid book Ib ɗan wanka Rintsin So tareda Sihirin ƙauna da Dogon Yaro
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
Na kuɗi ne😂
300 kacal
FREE PAGE
*shafi na 4*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana