Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

YA YANA Abin Alfaharina by sophieG

Author :  sophieG Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 36.4K words

tsaya ki saurareni dakyau idan da a can baya ina fada miki magana atakaice to yanzu
Zn miki bayani sbd kina bukatar sani Dan ke macece watarana kina gidan aurenki,

Lubna idan akace miki aure to magana ce da babu wasa acikin ta magana CE me girma kuma
aruyuwar duniya wuya ko dadi babu Wanda ze dauwama kamar yadda rayuwar mu bazata
dauwama a duniya ba,

Eh Allah ya hallatta saki amma koshi bayasonsa beside inason babanku sosae lokacin dough
yanada laifi babba ma dan bekamata yabarni da dawainiyar yayansaba Dan bayason haihuwa,
kuma tarbiyar yaya yakamata ace sunsameta ne daga gurin mahaifiyarsu,

Lubna kinsan duk abinda babanku yake yi ada dasa hannun mahaifyarsa?idan natafi nabarku Waze
kula min daku dukda lkcn ba ahaifekiba nasan abune me wahala idan narabuda babanku
subarminke sanin kanki ne banason hayaniya Allah ne kadai yakawoni gidannan, lubna inason
kusamu tarbiya mekyau idan nabarku wahala kawai zakuyi kiga yanzu da ace bananan ya auro
safara'u duk tarbiyr data doraku akai ita zakubi which bana tunani zaku samu tarbiya ta gari,



Yadda kikejin anacewa uwa uwace to haka ma uba ,iyaye dakika gani ba'acanza su duk yadda
sukakai ga lalacewa dole ne abasu girman su na iyaye Dan haka inaso ki kiyaye harshen ki akansa
kodan yadda kike ganin su Abdul sunayi kinji,(yanada kyau muringa nusar da yayan mu irin
wannan),



Bayan haka lubna akwai hakuri a rayuwar duniya bakitabajin Wanda yakeda hakuri ya wulakanta
ba Dan haka idan baki dashi tun yanzu kikoya ina fatan wannan rayuwar damuke ciki mu
gaggauta barinta Allah yatabbatar mana da alkhairi yakuma baki miji nagari,

Ameen ta amsa tana rufe fuskarta dadukan tafin hannayenta,

Murmushi kawai badee tayi tanajin son yayanta fiye datunanin me karatu,

Babuko sallama yafado dakin yana kiran sunan lubna fitowa tayi tana kokarin rufe zip din rigar ta,
Gani ta fada bayan tafito,yawwa sako hijab Dinki ga bako kinyi awaje sunansa Mubarak Dan
gidan wani abokin kasuwanci nane Dan naga kinfara kula maza yanuna kina son aurene dan haka
gara na aurar dake akan kizubarmin da mutunci,

To baba ni banfa cemaka inason aure ba,takarashe maganar tana turo baki,

Koma dai menene kije yana waje,fita yayi daga dakin,



Hmm wallahi se yatafi da kafafunsa haka kawai,




A tsaye ta same shi yajingina da motarsa taimasa sallama shiru be amsa ba,

Seji tai yace wooo wannan mezafin ce,dasauri takalleshi da alama besan maganar a fili yaiba,

Tab....wannan ko gaisawa bazata bari yayiba taga alamar riqaqqen Dan iska ne wato yama gano
me zafi ce hmm,



Ban baka damar yin magana ba inaso kasaurareni dakyau kaji,

Dafarko dai tundaga ganin ka danayi baka kwantamin ba in fact u'r not my type karkabari abata
ma lokaci idan aure kakeso kaje kanemi daidai kai, ina fatan zaka fadawa Wanda yaturo ka baka
dace dani ba? Nagode,

Baki asake yake kallonta harta bacema ganin sa,lallaima yarinyar nan dama haka take batada
mutunci to wallahi dole nasan yadda zanyi tazo hannuna nazata mesaukin kaice na wawusheta
nabar kasar gaba daya🤔,



Yaukam dukansu yaran suna gida Dan haka suka zauna palon mamansu sunata hira Sega majid
yashigo dukansu suka gaidashi be amsaba segun lubna ya tsaya beyi wata wataba ya kifa mata
mari afirgice ta miqe,



Ni zaki maida karamin mutun,naturo yaro gurinki ki walakanta shi dankina takama da rashin
mutunci?,

Nifa nagansa ne beminba shiyasa nafada mai gaskiya dankar na wahalar dashi,



Ni nace miki se Wanda kikeso zaki aura?Wanda nakeso naturo miki kuma dole kiyi yadda nakeso,
Wallahi ni banason sa nagwammace na mutu akan na auri wannan Dan iskan,



Chajan dake gefe ya zaro yahau dukanta, ko uwarki ba ta isa ina magana tana magana ba balle ke
kuma gidannan idan ana kaunar zaman lafiya dole ayi yadda nakeso,

Sunso su kyaleshi amma abdulrahim yaga hankalin baban baya jikinsa da haka dasauri ya kwaceta
yana boyeta bayansa dama yana cike da haushin baban,

Ya'isa haka baba tadaku sosae kalla har jini ya soma fita,inace kuma kasan yanayinda take ciki?
kuma ajirata takawo Wanda takeso bawai akakaba mata Dan iska ba,



Abdulrahim har dakai kakoyi rashin kunyar?inace kaima kasan halina Dan haka miqomin itanan,

Basuyi auneba suka soma jin ihun safara'u, labe take musu Dan taga yadda zasuyi,Ashe lubna
taganta kuma dama majid ya tabo abubuwan,



Dakyar da bala'i aka kwaci safara'u a jaka tabar part din badee sbd ta daku,majid kuwa kokarin
dukan lubna ya soma yi sedai abinda yagani ya matukar firgitashi duk yadda suke fada beyizaton
abin yakai hakaba,




Ka gani ko majid?yanzu a tsaye zamu kwana wallahi jiwa kanta ciwo zatayi abdulrahim kukama
min ita karta kashe kanta.




Anty Sophie ta gode😎
[7/23, 8:34 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)

By sophieG

A very heart touching story 2017




This page goes to u Jidda (dota) & umzeey Allah yanunamin aurenku in kwashi Shoki ameen❤.
To kardai kuyi min fada yadda kuka saba Dan nahade Ku a page daya😏.
Page 24




Wani kalar faduwa tayi da seda hankalinsu yatashi sun tsaya suna kallonta kowa yakasa isa inda
take, daganan kuma bata kara motsiba,



Ko mutuwa zakiyi sedai ki mutu akaiwa Mubarak gawarki aljanin jikin ki ma yaci ubansa,dakici
gaba da borin kiga inban saka muciya ko tabarya na bugeki ba bakar munafuka,

Fuuu yafita kamar ze tashi sama (kadai tafi zuwa gashin jikin enmatan baby😡),



Abdulrahim ya kwashe ta ya kaita dakin mamansu abduljabbar yai mata addua ajiyar zuciya
tasauke sekuma ta gyara kwanciyarta se bacci,

Zama sukayi adakin suna maida zancen,

Abdulrahim yace,mama waime baba yake nufi damu ne kusan shekara goma bamuda maraba da
babu a gidannan sedai idan yana Neman amfani damune musamman lubna,



Numfashi badee tasauke,Abdul nima bansaniba amma nasan duk kalar hakurin danake yakusa
kaini maqura,sundauki karan tsana sundorawa lubna karkaji mamakin safara'u ce tazugo shi in
kuma ba hakaba to yanada wata manufa,



Abduljabbar yace ,lallai kam dole dabiyu yabijiro da Wannan zancen haka kawai ya dauko mata
zancen aure ba batareda wata manufa ba,



Abdul'aziz yamiqe yana cewa karfa kuji mamakin saboda kudi ne zebada ita Dan babu abinda
baba yasawa gaba irin Neman kudi,

Abdulqadir yayi murmushi yace, idan dagaske auren yakeson yimata bayaso tazubarmai da
mutunci meyasa bazece ta kawo mijin dakanta ba?wallahi idan ya takurata bataso wannan
Mubarak din zamuyi wa duka seya fita hayyacinsa,



Bance kudaki Dan mutane ba amma dai kome zakuyi indai zakukarbowa kanwar Ku yancinta ne
kuyi amma karku illata yaran mutane,
Abdulrahim yatashi tsaye yana fadin Hajiya zamu fadawa kawai,

Yome hajiyar ta isa tayi banda tsufa daya tasomata ma,ga baba bayajin maganarta ko kadan, inji
aabduljabbar,



Aiko wallahi barmasa gidan zamuyi Dan baze kashemu daranmu ba, fadar abdulqadir,

Abdul'aziz yace wallahi kuwa dama bamuda wani amfani a gidannan sedai kawai yana amsa
sunan ubanmu ne,



Kuyi tunani dai dukanku bayara bane koba komai ubankune kuma shiyake cidamu,

Mama kidaina zancen abinci,muntaba ci mun koshi ne? Ana ganin mu anga yunwa kullum cikin
cin fara damai kekanki kina marmarin cinnama amma kinfi sati ko takardarsa baki ganiba, duk
abinda muke samu a sana'ar damuke tabawa aharkar makaranta yake karewa,inji abdulrahim
yadda yake maganar abin yakai shi maqura kenan,



Kusani dai duk lalacewar gidan uba gara ace kunadashi kuma inaso kudan masa uzuri dukda wasu
abubuwan dason ransa yake yi amma bayinkansa bane, kuma idan munbar gidan ina kukeso
mutafi?kunsandai banida inda zan kaiku ko?



Abdul'aziz yace mu babu ruwan mu dashi danki zamuyi danhaka mujira muga mezeyi ,in zancen
gidane ai akwai gidan Hajiya daki semun zaba danhaka ki kwantar da hankalinki,



Shiru kawai tamusu Dan taga alamar ba abinda yashafesu da mahaifin nasu,



Kukan lubna ne yasa duka suka maida hankalinsu gareta,

Yaya kubani ruwa don Allah karku dauko a cup nafison nacikin bucket Jinake kamar Na shekara
bansha ruwa ba,



Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yaukuma da shan ruwa abubuwan suka zo?



Abdulrahim yadebo ruwa a cup ya tofa adduo'i aciki yabata ko sauke hannun sa beyiba yaga ta
ajiye kofin yaleqa yaga bakomai aciki kallonta yai yaga ta lumshe idonta,
Dariya Abdul'aziz yai yace wannan mutanen na lubna inaga daga birnin sin suke kuma da alama
kasa suke zuwa wannan shan ruwa haka sekace garin kwaki😂

Dariya sukayi dukansu kafin suyiwa maman sallama suka nufi dakin su,



Washe gari koda suka tashi hannun lubna ya kumbura sosae da alama taji ciwo ne lkcn data fadi,
dakyar suka ga gari yayi haske danse kuka take,



Dole tace su Abdul sukaita gidan me gyara targade a duba hannun Dan babansu baya nan bazata
fita ba izinin sa ba,



Mama kikamamin nasa Riga,inji lubna,

Meye kuma sekin canja kaya kayanma na bacci?

Mama sababbi ne fa kuma kinga Wando ne banaso naje anajan hannun ina tsalle Allah tsaf zan
hankade zanennan, amma kinga inwando ne nayi wulli yadda raina yakeso,

Sosae badee tai dariya tace Allah ya shirye ki lubna
Ameen tace bayan sun gama saka rigar,



Da shigarsu zauren gidan taga wani hadadden saurayi da wata matashiyar mata agefe da
alamamatarsa ce Dan ga cikinan jikinta zekai wata biyar se matsar kwalla take tana kallon
kafarta data kumbura,se sannu matashin ke mata,



Lokacin da akazo Jan kafar ihu take tana lailayo ashar, shi kuma se sannu yake mata kiyi ahankali
karkiji wa baby ciwo,

Seda akazo daure kafar tayi shiru tana kallon mijin nata daya shagala wurin kallon cute face din
lubna,

Hawaye take ahankali ganin yadda wannan matar ke ihu kila da zafi sosae,

Me dorin yacewa su Abdul bisimillah,bayani sukai masa faduwa tayi kan hannun kafin safe
yakumbura yana mata zafi,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tafada lkcnda akafara Jan hannun, Dan matashin saurayinnan se
kallon yadda take damqe hannun nakusa da ita take tana kuka ahankali dukseyaji ta burgeshi,



Wani uban tsalle tayi lkcn da akasa abin daurewar ya tsuke sosae, dukansu seda sukayi
dariya,kekuma ki tsaya mana karki batamin aiki,

Bayan angama haryanzu mata damijinna zaune da alama wani Abu suke jira,

Tunda suka shigo talura yana kallonta har suka fice, jyuowa tai taga haryanzu ita yake kallo suna
hada ido se yasakar mata murmushi Dan kallon matar sa tayi se taga ta ware mata yatsunta guda
biyar ta motsa labbanta alamar Uwar ki?

Zaro ido tai sosae sekuma tayi saurin dauke idonta tacigaba da tafiya da sauri sauri Dan su Abdul
sunyi gaba.




Anty Sophie na fatan yauba korafin yayi kadan? 🤗
[7/28, 3:03 PM] Babee Feeya: [7/26, 12:40 PM] Safiyyah galadanchi❤: Y'AY'ANA (abin alfahari
na)

By sophieG

A very heart touching story 2017

Wannan shafin nakine yar uwa rabin jiki billy galadanchi❤

Page 25



Daganan gidan Hajiya suka wuce dama Abdul'aziz ne kawai se abdulrahim suka kaita suna zuwa
suka samu hajiyar azaune tsakar gida ita kadai da kofin koko agabanta da sauri lubna ta karasa
gaban hajiyar tana murmushi,



Hajiya barka da hutawa,barka dai kanwar maza yakuke ya mamanku?

Lpy lau suka amsa,
Kokon dake gaban ta lubna tadan kurba tace haji wai anya ba kwakwa a kokon nan jinake ina
wani lulawa,

Dariya sukayi dukansu Hajiya tace kikarasa shanyewa naga alamar ko karyawa bakiyiba,
Wlhy kuwa Hajiya kamar kinsani,

Meyasameki a hannu?
Jiya na fadi Ashe naji ciwo seyau dasafe natashi hannun yakumbura shine aka gyara,

Nan abdulrahim ya zazzage mata abin da yafaru,

Tabdijam...idan aure yakeson yimata aiseyace ta fito damiji, towaima yaushe yasan Ku yayansa ne
dahar zenuna isa akanku?

Kunga Ku tashi Ku tafi zuwa sabogoginku kubarmin ita nan nayi wanka naje gidan kobayanan zan
jira shi Nagano take takensa iskanci ne danhaka wallahi dole na dauki mataki danyaga nazuba
masa ido ne shiyasa iskancinsa ke ta'azzara harni zekawowa batun banza,

Shiru sukayi suna saurarenta dasuka masifarta bamekarewa bace suka barmata gidan,



Wanka kawai tayi komai bata shafa ba tasaka kayanta suka nufi gdan majid,

Suna tafiya kafin su samu adaidaita tana faman mita,

Yaushe zanyadda atura yarinya gdn mijin da bataso, daya aka kare ma da auren soyayyar balle
Wanda babu ko digonso acikinsa,ga yaron fandararre wallahi dasake,



Har suka samu adaidaitan suka isa gdn surutu take har tsoro tabawa lubna ,wannan mita har ina er
tsohuwa?

Batakobi takan lubnar ba ta shiga gidan dakin safara'u tafara zuwa taringa buga kofa amma bata
bude ba dole tahakura tayi bangaren badee,



A kwance suka sameta Palo tayi shiru tana tunanin abin duniya,

Gaisawa sukayi da Hajiya ta kawomata Dan waken datayi yau dashi suka karya kuma dashi zasuyi
abincin rana,



Kai amma er nan kin kyauta dama inajin yunwa da babu komai acikina tunjiya se ruwan kunu,



Allah sarki Hajiya yakika zauna da yunwa kunu aiba ya rike ciki?,
Badi babu komai gidan se farar shinkafa komai babu, er wannan yarinyar dake gurina
shekaranjiya uwarta tazo ta dauke ta wai aure zasu mata banida Dan aika ga su Abdul ma
sunkwana biyu basujemin ba,



Zaro ido badee tayi tace, Hajiya zama ke kadai a gida babu dadi ko zaki tafi da lubna ne?,

Bazan je da iyaba kema ai kina bukatarta sedai inkosu Abdul dayansu ze koma can,amma lubna
kam kodan Wannan munafukar matar ta majid bazan daga da itaba Dan nasan koba komai tana
tare miki wani abin,



Hakane kuma bari abdulrahim yazo muji seya fadi Wanda zekoma candin Allah yakauda bacin
rana kar wani Abu yataso bakowa kusa,

Uhm,ke dalilin zuwana gidannan abdulrahim yacemin wai aure majid zewa lubna kuma batason
mijin?



Eh haka yazo jiya yana fada Dan ma yaturo yaron nibansan me lubnar tace mai ba shine yaje
yahado majid din yazo nan yaimata duka ciwon ta yamutsafa shine kikaga taji ciwo a hannun,



To ana auren dole ne kuma idan aure zemata seya bata damar kawo mijin datake so,
Inji Hajiya,



Hmmm,yaushe zeyi haka tunda zugoshi akayi saboda ba akaunar ganin farin cikin mu,



Kardai kicemin safara'u ce ta zugoshi?,

Itace fa hajiya kuma wallahi nasan dabiyu yayi haka baze rasa wata manufa akan wannan ba tunda
baban yaronma abokin kasuwancin sa ne,



Aiko yadebo ruwan bala'i Dan wallahi bazata sabuba baridai yadawo yau inanan
inajiransa,mukayi rashin mutuncima ba gaira ba dalili balle antabo mu?(yau antuna da baya kenan
hajiya),



Bayan azahar safara'u tatafi part din bade tana zuwa ta tabe baki,
Tsohuwa sarkin jaraba anzo?toyau dai koda mekikazo keda munafukar matar danki dabatada
maraba da sharar gidannan awurinsa inada yadda zanyi daku domin Dan naki atafin hannuna yake,



Badee dai shiru tayi Dan ita batason tashin hankali sedai tasani Hajiya ba kyaleta zatayi
ba,tunkafin tagama tunanin tajiyo muryar hajiyar,



Yo safara'u akwai munafukin dayakaiki keda uwarki?anyi muku inuwa amma kuna saka Wanda
yakaiku inuwa rana?karki manta taimakonki nayifa keda uwarki Dan nazata son Allah da annabi
kike wa majid Ashe ba haka bane Dan abin hannunsa ne ya tsokale muku ido,

Tawani gefen bana ganin laifinku sbd shine yabaku dama babu abinda yasawa gaba seneman kudi
shiyasa kuka samu damar rufe masa ido yana tunanin kune masoyansa kukasa ya guji uwar data
kawo shi duniya,yabar mace guda daya dadaukar dawainiyar yayansa harsu biyar,

Idan kin lura mumunkama Allah shiyasa muka zamemiki kadangaren bakin tulu,danke kina er
bakin ciki zakije ki zugoshi ya aurar da yarsa gawani can Dan iska wato haka kikeso kiga rayuwar
bayin Allah cikin mugun yanayi bakisan shi Allah ba azzalumin sarki bane danhaka munanan
dubunki zata cika,

Kuma wallahi yau koda bala'i da masifa da rashin mutunci babu Wanda ya isa ya aurar da lubna
ga wanda bataso kuma inanan inajiran shi majid din dakike ta kamar ke kike juyashi,
Shegiya mekar kama dabakar zuciya,



Duk abinda zakice kice danki dai a hannuna yake kuma yau zakiga yadda miji ke tsallake umurnin
uwarsa yabi na matar sa,

Majid yadawo jinhayaniya bangaren badee yasa shi tafiya can yana fadin
Allah yasa ba enmatan baby aka taba ba,(kuji Dan iska),



Aiko safara'u tana hango babbar rigarsa na cika da isaka ta daka tsalle tafadi kasa,

Wayyo Allah wayyo nikaina namutu na lalace Na shiga uku na,

A gigice ya isa yamiqar da ita yana tambayar menene,

Wai Hajiya ce tazo shine nazo ingaisheta sukafara zagina itada badee'a wai nafita karna shafa
musu tsiya kuma dannace lubna tazo ta tayani fito dakayan wanki shine sukemin gorin haihuwa
wama yasani koni ke zubar da cikin danake samu lubna bazatajeba karna koyamata bin bokaye da
malaman tsibbu Dana saba bi Nida uw...
Ransa yakai kololuwar baci yasan uwarsa bazata dakuba danhaka yaikan badee dake tsaye cike da
tsoro tana firfito da ido dama irin haka take gudu shiyasa duk yadda safara'u keson suyi fada bata
biye mata saboda duk laifin duniyarnan hukuncinsa duka ne ita da yayanta duk basu wuce hakan
ba,

Marin daya gaura matane yasata dawowa daga tunanin datake atake kanta dake ciwo yasara mata
dafe kan tayi tana zama ahankali take kuka,

Hajiya takoma gabansa takwada mai mari har yadaga hannunsa sekuma ya sauke hannun,

Wannan abin safara'u taso yakasance tasan daya daki uwarsa lallai daga uwar har badee'a da
yayanta barin gidan zasuyi sekuma Allah yadauki mataki akan majid da kansa batareda tasha
wahalar kawar dashiba,



Ashe kai karamin Dan iska ne tunda bazaka iya rama marin da uwarka tamakaba?,

Duk ba wannan yakawo ni ba inaso kasani wannan auren dazakiyiwa lubna babu shi banason
nasakejin batun yatashi,

Kasan halina sarai Abdulmajid idan tayi nasarar rufemaka ido har kake tsallake bin umurnin
uwarka tayi nasarar sawa ka mance da matar ka baiwar Allah uwar yayanka to nasan batayi
nasarar kawar ma da memories dinka na daba wallahi tallahi kaji na rantse zandawo Hajiya Rabin
daka sani ada kuma ba karamar barna zamu aikata ba kaji na fada maka kuma mu zuba ni dakai
shege ka fasa,



Sosae maganganunta suka shigeshi har yadanyi sanyi yana hada ido da safara'u ya birkice,



Yarinya y'atace kuma na bada ita Dan haka koduk duniyarnan zata taru akaina babu Wanda ya is a
yasa na chanja maganata danhaka nanda sati daya za ayi komai agama kuma wani acikinku yayi
trying something stupid kuga yadda zan tada hankalin kowa agidannan,

Fuuu kamar zetashi sama yafita,

Lubna ta sulale akasa tana kuka sosae harda sheshsheka,
Badee ma haka ta kalli Hajiya,



Yaushe zamuji dadin rayuwarmu ?Hajiya zuciyata nauyi take min abubuwa dayawa marasa dadi
take dauke dasu,kikalli yarana koda sundauko jin dadi nawuni daya dole se an wargaza musu shi
bansan me safara'u take nufi damuba,
Sosae Hajiya take tausayinsu,seda ta lallashe su sukayi shiru tace zata tafi se dayadaga cikin
yaran yazo,kuma duk abinda yataso su aika mata Dan daga yau bazata kuma yin shiru ba dan
tagano badee kamar doluwa ce komai akemata bakin nan gum kamar ruwa yaci shirwa,



Seda ta sakata a adaidaita kafin tajuya gida tana tunanin yadda za asaka wa rayuwar erta kunci tun
tana yarinya.



(Ashe akwai Dan karamin yaki a gdn majid).




Don Allah fans kuyi hakuri dajina shiru kwana biyunnan banji dadi bane shiyasa nagode❤,



Bansan me mutane sukeso su saniba amma dayawa suke tambaya na wai billy galadanchi yayata
ce wasu har private suke bina,to ga amsarku nan,

Anty Bilkisu yayata ce the same father the same mother ita nake bi☺
[7/28, 1:48 PM] Safiyyah galadanchi❤: Y'AY'ANA (abin alfahari na)

By sophieG

A very heart touching story 2017.




Taskar billy galadanchi
Miemiebee novels
Ummeeja'afar novel group
Zauren biebie isa
Billyn Abdul novels
Zarah bukar novels
Shukra novels
Ayusher fans club
Feedo novels,Wannan shafin nakune ina godiya sosae da kwarin gwiwar dakuke bani inajin dadi
sosae Allah yabiyaku❤ameen.



Page 26
[7/29, 1:13 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG

A very heart touching story 2017.




Taskar billy galadanchi
Miemiebee novels
Ummeeja'afar novels
Zauren biebie isa
Billyn Abdul novels
Zarah bukar novels
Shukra novels
Ayusha fans club, nagode sosae da kwarin gwiwar dakuke bani Allah biyaku da mafificin alkhairi
ameen.



Page 26




Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba domin majid ya haukace hagaga shirin biki yake
dukda ba ayi komaiba yace Daura aure kawai za'ayi,



Sosae suka shiga firgici bakamar lubna Dan dayazo baban yatursasata dole tafita a motarsa ta
same shi,



Sauke glass yayi ganin ta tsaya tana kumbura Fuska,

Madam shigo mana kika tsaya awaje,
Shiru ko motsi batayi ba yaita magana

7 / 13