Author : Maman Ussee Category : African Stories & Novels
batasan meyaje yiba bai jimaba sosai taga yadawo da Iedoji biyu a hannusa ya. bude set din baya daba kowa yasa su a ciki sa,ilin da yadawo yatada mota suka nufi hanyar gida,
Mummy suka tarar harta kammala komai na gyaran gida da Inda sukaci abinci sannu da aiki mommy yara ga kaya nasiyowa Rukayya da yadin uniform saiki bada dinki ayimata iri biyu iri. Nasu Sajeeda Dan gobe zata fara zuwa sauran kayan sa wane nixan fita sai nadawo aff ana manta kinsandai makarantar Boko suna jarabawa ne sai nadawo Hutu zan kaita zadai aci gaba da koya musu extra lesson kamin da dawo hutun Dan naga ba wani Hutu mai yawa bane murmushi tayi hadi da yimasa godiya da fatan alkhairi,
Rukayya kuma tana zaune ta kurawa TV Ido ko kyabtawa batayi mummy ta dafata tace muje kitayani gyaran daki sai mu Dora girkin rana Dan su sajeeda sai 4:pm zasu dawo ta fice yayinda Rukayya ta rufa mata. Baya tana nuna mata abubuwa da yakamata ta kula dasu wan nan kenan,
A cikin yan kwanaki n da tayi a gida. Bata fuskantar komai sai farin ciki ga soyayya da yan uwanta ke nuna mata suna debe mata kewa sosai sun shaku da sajeeda inka gansu gwanin sha,awa komai tare sukeyi Dan ko a Islamiya tare suke komai sajeeda itace take koya wa Rukayya wasu Abubuwan da bata gane ba cikin sa,a kuwa da am fada ta rike shikenan malamansu har mamakin irin Baiwar da Allah yayiwa Rukayya suke gashidai bawani dadewa tayi ba amma inka ganta saika rantse ta shekera a cikin islamiyar gida kuma ga lesson ana musu badama tana kawo wuta sosai Daddy yasan bayada haufin inya kaita skull za,a sakata aji daya da Sajeeda dayake ita jss 2 take, Tun tanajin kunyar saka wando da Riga harta saba Dan kuwa yanxu Rukayya ta goge dama can ita kai waye ne da ita batada matsala in basuda lesson itada Sajeeda suke taya mummy aikace aikacen gida dayake anyi Holiday.
Maman usseeπ Ina Alfahari da Ku my fans
π 'YAR BAIWAH π7β£
Maman Ussee
Haka Rayuwarsu taci gaba da kasancewa gwanin sha,awah har holiday ya kusa karewa yau ya kasance Sunday kowa da kowa na falon gidan anata firar duniya gwanin dadi fuskar kowa cike da annashuwa da anuri Abdallah ne yace Daddy gobe Holiday zai kare kuma kasan kamuna alkawarin zaka mana shopping yau ko Fadil ya amsa eah little bro Mummy tace harda ni kenan za'aje shopping din Daddy yace OK to Ku shirya sai muje tare kunji yes Daddy suka mike Dan shiryawa Rukayya an zama yan gida yanxu kowannen su yafito cikin shiri Rukayya da Sajeeda jalabiyace a jikinsu dark blue sukayi rolling abin yayi kyau fadil da Abdallah kuwa Riga da wandone suka sa mummy itama Doguwar rigace ta shadda taji kwado kai familyn fa sun birgeni haka suka fito suka shiga mota Mummy dasu Sajeeda a Baya fadil da Abdallah a gaba asu zarce ko inaba sai a Zabira shopping mall nan kowa yayi ta zabar abinda yakeso Rukayya dai kasa daukar komai tayi Dan ita kunya takeji Sajeeda CE kedaukar komai Biyu inta dauka saita daukar wa Ruky bayan sun karene sukaje wurin bill akayi bill Daddy yabiya suka sake fitowa kowa sai kallon su yake nusamman Ruky da Sajeeda kamar yan biyu ba karya Allah yayi Halitta Dan ko Sajeeda ba bayaba a fagen kyau, Daddy bai zarce dasu ko,ina ba sai Daddy's smart anan sukaje suka ci abinci suka zaga gari sosai kamin nan suka dawo gida.
Gab da magrib suka dawo zubewa sukayi a fallo kowa ya gaji Dan yau sunsha yawo sun more sosai gsky bayan su hutane Daddy yaja su Fadil da zuwa masallaci Mummy kuma ta wuce zuwa dakinta yayinda da umurci su Sajeeda dasuje su yi sallah suma kuma su shigar da kayan ciki haka suka kwashi kayan zuwa Inda yakamata su adanasu. Bayan sun idar da Sallar Isha suka fito bayan aka ci gaba da hira can Daddy Yakira sunan Rukayya, Rukayyatu ki shiryafa gobe zaki soma zuwa skull insha Allah saboda haka saiki shirya kinji murmushin jin dadi tayi yayinda da ta CE nagode Daddy Allah yakara girma bakomai ai kidage dai kinji ko to 'ya ' yan Daddy aje ayi bacci saboda a tashi da wuriko kunji yes Daddy af na manta Ga uniform din Ruky can a bed dina Sajeeda jeki kidauko mata gobe sai a shirya da wur wuri kinji tau Daddy bakida wata matsala Rukayya. Nariga nayiwa principal magana interview kawai za a maki su zasu baki komai da komai saboda haka kidage kawai inkiyi kokari za a sakaki class daya da 'yar uwarki Sajeeda tam ta amsa suka fice dakin su kowa yayi addu'a ya kwanta yayinda 'YAR BAIWAH take farin ciki sosai mafarkin ta yakusa yazama gaskiya.
Maman Ussee
π 'YAR BAIWAH π 8β£
Maman Ussee
Monday morning tun 6 suketa shirye shiryen zuwa skull Sajeeda CE ke nunawa Rukayya yanda zatasa kayan skull din ,kai gsky fa kinyi kyau tawan kinga yanda skull uniform din nan suka karbeki ta kashe mata idon daya Ruky ta kaimata duka ta goce suka fito falor sunata dariya yayinda su Fadil ma su. Shirya tsaf Daddy kawai suke jira bai wani jima ba ya fito sanye da kayan shi dagani shima aiki zaije daya aje yaran, ba bata lokaci Mummy tai musu addu' a suka fice dukkansu suna daga mata hannu,
Bayan sun shiga mota Daddy ya tuka zuwa skull din dake dai dai Bafarawa east, garin yacika sosai da mutane kasan cewar yau Monday masu zuwa skull na fita yayinda masu zuwa aiki ke kama ga bansu da zuwa aiki kai tsaye daddy cikin makarantar ya danna motarsa wato KEY SCIENCE ACADEMY, bawani bata lokaci Sajeeda dasu Fadil suka nufi assembly yayinda Daddy ya nufi principal office da Rukayya bayan yagabatar da ita a fadamai rules din makaranta ya amince kamin nan aka bashi takarda yasa hannu yayi godiya sosai ya wuce yayinda PC ta kira senior master domin a iyiwa Ruky inter view da Name dinta aka fara ta amsa Rukayyat Sa'eed bayan nan kuma sai aka cigaba da yimata sauran questions tana amsawa yanda yakamata, mintuna kalelan aka bata class yayinda aka kira, class master dinsu ya rubuta name dinta a Register kuma aka umurce shi daya kaita ya gaba tar da ita wa yan class as a new student kai tsaye , Jss 2 blocks ya nufa da Rukayya kamar dai yanda Daddy ya. Bukata cikin sa,a kuwa ajinsu Sajeeda ne bayan shigarsu, student suka mike tsaye,
Good morning sir, morning how r u today, we are All fine sir, OK sit down,
Anan yagabatarda ita yayi kiran register kuma ya umurci class rep data bata set shikenan yafita Dan yagama aikinsa,
Fitarsa keda wuya Sajeeda ta doka uban tsalle ta rungume Rukayya tana murna sosai, Hi kinga Allah ya amshi addu,a na ko so yanxu muna class daya if u did not understand anything just ask me π murmushi kawai Ruky tayi hadi da samun set bayan nasu Sajeeda yayinda su Muhibba yan sit dinsu Sajeeda suke tambayar ta dama tasantane eah yar uwatace she's my sister daga nan kuma aka cigaba da gaggaisa irin na new students da old kundai ganeπ uncle me English ne ya shigo da yake ba musulmi bane ya gabatar da lesson dinsa ya kuma basu pappers dinsu na fist term bayan ya kare sai mai science yashigo shima yagabartar da nasa lesson din kamin nan aka buga aje break fast Sajeeda da Rukayya tare suka fito zuwa dinning area anan ne Sajeeda ta ringa nunawa Ruky abubuwa da dama wadanda bata saniba da kuma Inda ake komai da komai haka suka kasance har time dinda aka koma class ba laifi Rukayya ta dage sosai sai sun hada Kansu ita da yar uwarta ba abinda basayi tare har lokacin barin skull din yayi suka shiga skull bus Dan dama ita ke mayardasu gida saidai da safe Daddy ya kawosu su Fadil da Abdallah bangarensu daban kasancewar su a primary suke sunada masu bus din duk da skull din dayace amma kuma Nursery daban primary daban ss da jss ne kawai a hade Sajeeda da Ruky suka shiga tare aka yita sauke wadanda ke kusa yayi da aka zo unguwarsu suma suka sauka sunayiwa sauran yan mates dinsu bye bye sai mun hadu gobe inji su Hibba sajeeda ta amsa da to,
Bayan su shiga gida suka tar rar dasu Fadil da Abdallah har sun dawo kasancewar su 12:30 ake tayar dasu sukuma sai 1:30 suke tashi Daddy. Baidawoba haka suka cire uniform dinsu suka sake wanka kamin nan suka saka uniform dinsu na Islamiya da time yakusa yi.
A RABA FA?
Tun bayan tafiyat 'Yar Baiwah Baaba kullun cikin cewa take harda Dan zazzabin ta na kewar jikar tata kullun ta lisafe da ko kwana nawa yar baiwa tayi a birni kullun tunanin ta yanxu a wane hali jikarta take sai dai zuciyarta tana hayamata duk Inda yar baiwa take to addu,ar da take mata yana tare da ita da A kullun baaba sai taiwa Rukayya addu,a kuma batason taji lbrn komai indai ba firar mutuniyar ta bane hakan CE ta kasance ko a wuri mahaifinta sai dai yana da jarumta baya nunawa dankar ya karyawa baaba zuciya haka suka kasance gidan shuru shuru har na tsawon sati biyu tun basu saba ba har yazama jiki suka saba kowa yadan fara sakin jikinsa aka dawo yanda ake da saidai kuma in an tuna ayi kewa sabo kenan.
Maman usseeπ
π 'YAR BAIWAH π9β£
Maman Ussee
Ruky da Sajeeda zaune a dakinsu sunata fira sai dariya kakeji wow gsky nazata inaje skull din nan zan fuskanci Matsala, ashe ba haka nan bane, kai dadina dake tawajena tsoro gareki, ninasan ba abinda zai faru kawai dai kedince akwai tsoro. Kinga tashi kar muyi latti kinsan halin mutumin naki mai tajwid akwai disgi ni kuma na tsani mutun mai disgi hakafa ranar safa CE kawai bansaba ya hanani shiga ajin Ruky tace OK kinsan dai gobe akwai Hadda ko saboda haka yau. Ba, bacci Dan kar muje bamuyiba kinga gbe akwai skull cox Hutu yakare yanxu da dare zamu rika yin Hadda dinmu,
Bayan sun kammala ne suka fito sanye da uni din Islamiyarsu sama sama suka ci abinci Dan karsuyi latti ayi musu duka sauri sukeyi Rukayya rike da hannun Fadil yayin da Sajeeda take rike da hannun Abdallah Dan a kafa suke zuwa Islamiya tun bayan ranarda Daddy yakaisu,
Sunci sa,a suna shiga ana tare yan latti kai tsaye ajinsu suka nufa. Bayan sun aje su Abdallah a nasu ajin.
Ai kuwa basu tsiraba Dan koda suka je mai tajwid yariga yashiga hkr suka fara basa dakyar suka ci sa,a yabarsu suka shiga bayan shanyasun da yayi a waje haka yakaraci darasin sa yabar ajin.
Basu suka tashi ba sai misalin 6:pm aka tayar dasu kowace daliba ta kama hanyar zuwa gidansu, Ruky da Sajeeda tare da yan kannesu suma suna dai daga cikin masu zuwa gida kasancewar magrib ta kusa da isarsu gida kowane ya nufi dakinsa Dan bayarda farali suna idar da Sallah falo suka xo , a nan suka tararda mummy itama ta fito yaran Daddy sannuku har kunyi sallar ne eah OK to Allah ya karba ya bada lada suka amsa a tare ameen mummy, yadai Ruky hope ba matsala a skull ko karki damu da sannu zaki sabane fatana kawai Allah yataimaka yabada sa,a kuma a dage kunji eah suka sake amsawa, haka sukata fira jefi jefi kiran sallar Isha ne ya tayardasu bayan sun kammalane suka fito domin cin abincin dare,
Anan suka tarar da Daddynsu Dan rabon da suganshi tun safe daya ajesu a skull gaida shi suka fara kamin nan kowa ya zauna a set dinsa mummy tayi serve din kowa akaci akasha aka koshi sai kowaya kama gabansa yayinda Ruky da sajeeda suka fara tilawar Haddan su dakuma assignment dinsu bayan su kammala sukayi addu,a suka kwana sai. bacci.
Kashe gari haka ta kasance tun wuri suka kimtsa suka fito inka gansu kanar wasu twins gwanin sha,awa yau ma Daddy ne yakaisu skull daga nan ya wuce GT Bank da acan yake aiki bayan an kare Assembly kai tsaye kowace daliba ajinsu ta nufa Dan daukar darasi Sajeeda da Ruky a tare suke tafiya har class dinsu kowace ta zauna a set din ta kamin class master yaxo yakira register daga nan kuma
Malami mai lesson ya shigo ya fara gabatar musu da lesson.
Maman Usseeπ
Naga sakonku nagode sosai da kulawa nasoyana Allah yabar zumunci.
π YA RBiAWAH π 1β£0β£
Maman Ussee
Time din break yayi Sajeeda da Ruky suka fito waje class sunayin break yayinda sauran student ke lamarin gabansa, Ruky nikuwa Sajeeda kinsan abinda yake bani mamaki a,a saikin fada wan nan malamin nan na daxu mai disga mutane din nan kinga yanda yabar ummy nata zuba surutu ya kyaleta amma na tabbatar da wani member din class ne daya sha zagi yau kuma na ga sai wani shige mata yake kodan yaga tafi kowa girmane a class din, hey are u jealous π Ruky takai mata duka wane irin jealous kuma ni ina ruwana dashi kawai dai naga hakan baidaceba ne shiyasa na gaya miki OK to kawo takalminki na ajiye miki kije ki gaya musu ustaziya Rukayyatu 'YAR baiwa π dalla Banason rainin hankali daga kawai na fada miki Abu shikenan sai ki wani canja min magana πππ dariya sajeeda tayi hardasu kyalkyatawa kamar zata fado kasa aiko Ruky ta ji haushi ta kwashi kayanta fuu ta fice daga wurin hava ke kuwa sorry mana tsayani muje tare INA ko saurarenta bataiba ta fice class abinta sai daga baya ta saiko suka shirya kamin adawo break.
Sannu sannu.bata hana zuwa sai dai a Dade ba,a kai ba yau su Ruky zasu zana end of second term examination, a cikin skull kuwa bawanda baisan Sajeeda Abubakar &Rukayya Sa,eed ba komai nasu atare sukeyi duk Inda kagansu tarene ba abinda yake rabasu ko a gida ma hakan ne gasu da ilmi uwa uba kyau gasudai ba wani girmane dasu ba Dan daka gansu zaka yarinta karara a tare dasu sai dai sunada ladabi ga girmama na gaba dasu a class inkaji suna surutu to lallai Abu mai mahimmanci suke tattaunawa. Baruwansu da wasu frnds sudai barsu da karatu Dan kullun abinda Daddynsu yake jaddada musu kenan kosunyi fada to yanxun nan zakaga sun shirya al,amarinsu yana mutukar.birge jama,a ko unguwarsu bamai cewa sun tsokaneshi Dan su karatun ne kawai yasha musu kai alhmdllh cikin sa,a suka fara Rubuta exams dinsu har suka karashe akayi holiday,
Murna gurin Rukayya ba,a magana Dan dama ta matsu ayi Hutu Dan taje Raba dama Daddy yace da anyi Hutu zasuje tare suyi one week sai sudawo sabida islamiyarsu dayake sunyi nisa sosai, bayan sun dawo gida da kwana biyar suka daga sai Raba gabaki dayansu harsu Fadil da Abdallah ai kuwa kuxo kuga murna wurin Baaba kamarme taga yan jikokinta musamman ma Yar baiwa taga yanda tayi Haske ta goge hardasu kiba gwanin sha,awa kai lale marhabin da yan sokoto cewar Malan sa,idu nan nan kawai yake da 'ya'yan nasa yanajin wani farin ciki a ransa yarsa CE ta dawo haka tubarkallah masha Allah, bayan an nutsa kowa yaci ya koshi aka fara sabuwar fira yayinda suka gode sosai da namijin kokarin da Daddy yayi musu godiya suka ka rayi da fatan alkhairi, satinsu daya a Raba suka juyo yar baiwa kawai suka bari koshima badan sunsoba saidan rokon da Baaba tayine shi,isa suka barota ta kara sati sai Daddy yazo ya dauketa sukoma, bayan kwana biyu Baaba na zaune itada Rukayya suna tadi take tambayarta bawata matsala daiko eah bakomai lfy lau wllhi bakiga yanda ake bani kulawa ba sosai da sosai to madalla ai hakan akeso Allah dai yasaka musu da alkhairi Rukayya ta amsa da ameen amin shiyasa nake sonki Baabata dankin iya addu,a π dariya Baaba tayi tace ja,ira har yanxu dai sakarcin naki nanan Ruky tace to in ban maki ba wanikeda shi Wanda yafiki ai kekadaice dagake. Bakari π tabdi wai yar baiwah yaushene kika iya surutu haka lallai zaman birni ya saka ki iya magana π³ai baaba Dan baki zauna da Sajeeda bane haka take kamar parrot indai surutune uhum menene fara kuma me Ruky zatayi in banda dariya aikuwa Baaba takaimata duka ta goce tsaya kiji parrot akecewa inaga sai naje sake skull dinmu kin kara wayewa ja,ira kekam dai Allah ya shiryeki ta CE ameen tana murmushi.
Maman Usseeπ
πYAR BAIWAH π1β£1β£
Maman Usseeπ
Satin Rukayya biyu daddy yazo yadauketa suka koma sokoto cike da kewar iyayenta musamman ma Baaba dasuka shaku sosai,
Haka Rayuwa taci gaba da kasancewa yau farin ciki gobe akasin haka dama ita rayuwa haka ta gada , amma a wurin Rukayya abin ba,a cewa komai Dan kullun cikin farin ciki take yayinda duk tayi sallah saita Roki Allah yasa kama daddy da aljannah hakama mummy dakuma iyayenta. Haka suka karaci holiday dinsu har ya kare duk Wanda yasan Rukayya ada idan yaganta a yanxu bazai ganetaba inhar ba farin sani yayi mata ba Hutu kwanciyar hankali haiba kwarjini duk sun baibayeta batada wala matsala a skull ma hakan ne Dan so dayawa tasha samun kyaututuka da dama awajen malamai kai harma da students akan baiwar da Allah yayi mata ilmi. Ba,a magana Dan ko quiz za,ayi to Ruky da sajeeda na ciki haka ma divert ko inter schools compotions za,ayi to dolene asaka yar baiwa ga tada da speach mai dadinji dakuma saurare takowane fanni gata ilmin addini Dan kuwa saura kadan ta Haddace alkur,ani mai girma, Sajeeda namatukar son Rukayya kamar yan uwanta na jini haka take jin ta kamar uwa daya uba daya suke ba,abinda Rukayya zata CE tanaso Sajeeda. Batace tana sonsa ba koda kuwa. Baimata ba a duniya inhar kanason kaga. Baccin ran Sajeeda toka taba Yar baiwa haka ma ko a wurin Rukayya batason ko kadan taga yar