Author : Ummu Affan Category : African Stories & Novels
yana da kyirki sosai dason mutane da girmama duk na gaba dashi,
Numfasawa Yusuf yayi lokacin da ya gama tuno abinda ya faru tashi yayi ya koma bedroom zcyrsa cike dajin d'acin abinda Hafeez kewa Inteesar d'insa,
Ita kuwa Inteesar da gudu ta sauka k'asa tana kuka sosai kai tsaye bedroom d'inta ta fad'a ta haye gado tana kuka sosai tana k'amk'ame jikinta ganin yadda duk ta 6aci da jar miya......
Plssss Share
Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
*IZGILI*
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
*Story and written by* .
*Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*
*Marubuciyar*
*UWANIN QAUYE*
*CIKIN WAYE?*
*NIDA YAYA LAMEER*
*KAINE SANADI*
*NAYI GUDUN GARA...*
*And now*
*IZGILI*
*DEDICATED TO*
*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL* .
*Ummu Inteesar*
*SPECIAL GIFT TO*
*Anty Hauwa*
*My fans ina godiya da jin dadi sbd yadda kuka amshi wnn littafin hannu bibbuyu kuma inajin dadin yadda kuke suburbudomin comment a cigaba da gashi ina yinku over*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Bismillahir rahmanir rahim
🅿️7️⃣-8️⃣
Saida tayi kukanta me isarta snn ta fad'a toilet,wanka tayi ta fito ta cenxa kaya snn ta fita gurin Baba Kulu me aikinsu,duk lokacin da zatayi aiki ta kan shiga kitchin domin ta temaka mata,tun Umma na hanata har ta gaji ta rabu da ita domin sam Inteesar yarinya ce meson aiki bata da kasala barta dai da rashin cin abinci,
Bayan ta gaisheta ta amsa ckn fara'a tace"Uwar dakina kin iso kenan,murmushi tayi tace"na iso Baaba yau me za'ayi a gidan,tace"to Hajiya dai batasanar minba daman kece me za6a murmushi tayi tace ina zuwa,
Sama ta hau bedroom d'in Yah Yusuf tashiga zaune yake yana aiki a Computer murmushi tayi ta k'arasa garesa tare da zaunawa gefensa,"yah Yusuf barka da aiki,a hnkl ya juye ya kalleta shima mrmsh ya sakar mata yace"barka dai Kyautar Allah,
Lokuta da dama sunan da yake kiranta dashi kenan shida Abba tace"yah Yusuf yau me kakeso kaci,lan gwa6ar da kai yayi yana kallonta da sauri tayi k'asa dakai domin batason yawan kallonsa sbd kwarjininsa yana cika mata ido yace"kome kikayi zanci Amanata,da sauri ta kallesa,lokacin da abin ya faru sam bata da wayau domin shekarunta hudu ne ba komai zata iya tunawa ba,tasan dai tabbas ita ba 'yar gidan bace domin tana hangen abun a kyaunyar kanta saidai bazata iya tuna komi ba byn wnn,
Cike da shagwa6ar da take masa tace"pls yah Yusuf yau ka fad'amin za6inka mu girka maka kullum za6ina kakeci,yace"yes sbd nasan duk wani abu da kikayi koda bancinsa to zan iya ci,gyad'a kai tayi shi kenan my Yayanah,ta fita yabi bayanta da kallo tare da jingina kansa jikin bed a fili ya furta Ina k'aunarki Inteesar Allah ya cikamin burina akanki,snn yaci gaba da aikinsa,
Tana fita Yah Hafeez na fitowa daga bedroom nasa,ai sauran kad'an ta kifa sbd furgici da tsoro,da sauri tayi niyyar kifawa a guje yace"munafukazo nan,hnkl a tashe taje ta duk'a gabansa tuni ta fara magiyar"don Allah Yah Hafeez kayi hkr wllh.....da sauri ya katseta cike da fusata"kinsan dai banason surutu ko?da sauri ta d'aga kai,Ckn tsawa yace"baki da baki ne,"kayi hkr,mtsuuuww yaja dogon tsaki"ki je ki had'amin coffee sauran kiyisa ba daidai ba,
Da sauri ta mik'e kitchin ta koma tasanarwa Baaba kulu abinda zasuyi snn ta had'a masa coffee kamar yadda tasan yanaso snn ta kai masa,tana nan tsugunne harya kul6a ta ga yawani ya mutsa fuska da cikinta ne taji ya bada tsuwwww cike da tsoro ta kallesa ganin baiyi mgn ba kuma bai k'ara kul6a ba aranta tace"shi kenan yau na mutu,
Umma ce ta k'wala mata kira hakan yasa tayi saurin kallonsa harara ya zuba mata yace"kin zubamin banzayen idanunki bazakije ba ne?da sauri ta fita aranta tana mitar shidai ba'a iya masa da tashi tayi yace tayi laifi,
Bak'i ta gani Umma tayi,da sauri ta k'arasa tana gaishesu ko kallonta matar batayi ba sai wani cin magani take,jiki a sanyaye ta zauna,kusa da Umma,waya Umma ta d'aga ta kira Hafeez da Yusuf ba'a jima ba sai gasu,Hafeez ko kallon matar da yaranta biyu 'yan mata baiyi ba,shi kuwa Yusuf harda gaisheta yayi ta amsa a hankali tana harare harare,
Umma tayi gyaran murya tana kallon su Hafeez tace"kun ganeta kuwa?,kafin suyi mgn matar ta katseta da sauri "taya kuwa kuwa zasu ganeni tunda kin mallakemin d'an uwa kin kanainayeshi baya zuwa inda muke bare har yakai 'ya'yansa su sanni,
Numfashi Umma taja cike da takaici zatayi mgn saiga sllmr Abba yana ganin Yayarsa ya k'araso da sauri tare da zubewa gabanta"Anty Jummai kece yau a garin barka da zuwa,harara ta zuba masa tace"uhmm Musbahu kenan idunka kenan ko kunya bakaji ba,sai tasa kuka tanacewa"kai kenan kana gindin mace baka tunawa da 'yan uwa,mu kad'ai iyayenmu suka mutu suka bari dagani saikai amma ka mance dani naci kashinka hannuna ka tashi har kayi wnn arzikin amma ka mance dani,
Hankalinsa a matuk'ar tashe yace"kiyi hkr Anty Jummai wllh kina raina ko da yaushe,tace"taya zan zauna aranka bayan matar nan taka Hajara ta gama dakai ko yaranka wai basu sanni ba ina matsayin Uwarsu kuma kakarsu tunda ni na raineka da hannuna,hkr kawai yake bata,tace"to Malam dai Allah ya masa cikawa hakan yasa nazo nan kuma anan nakeso na zauna,da sauri yace"Allahu akbar Allah yaji k'ansa Malam mutumin k'yirki,
Babban bedroom aka bawa Anty Jummai kamar yadda Abba ke kiranta muma hk muke kiranta domin ko yaranta Maryam da Saima haka suke kiranta,Anty Jummai irin fitinannun matan nance sam bata da kyirki gasa ido,tunda tazo gidan tasaka Umma a gaba da jaraba gashi Abba najin tsoranta sosai saidai ya bawa Umma hkr,tanason Hafeez da Yusuf saidai sunfi shiri da Yusuf kasancewarsa me barkwanci wani lokacin ko masofa take idan ta gansa takan dena domin shid'in daya fadar mata wata mgnr sai hankalinta ya kwanta a rayuwar Yusuf ya maida komai ba komai ba,inda suke samun matsala da shi idan tanawa Inteesar wulak'anci domin duk a gidan ba wacce tafi tsana sama da ita tunda taji asalinta take wulak'antata,haka Saima bata da mutumci ko kad'an ga 'yan aiki amma saidai tasa Inteesar ta mata komi,Maryam kuwa suna mutumci sosai da Inteesar domin ko ashekaru zasuzo guda sai kuma halinsu ya zama iri daya,Anty Jummai da Hafeez basu shiri domin kai tsaye yake gaya mata balle idan yaga tana gayawa Umma mgn,Saima kuwa tunda taga Hafeez ta rud'e a duniya tace bata da mijin da takeso kamarsa,Saima shekarunta 23 ita kuwa Maryam tana da shekaru 15 sa'ar Inteesar ce don itama shekarunta kenan,
Su waye Hafeez da Yusuf?,
Alhj Musbahu Muhd ne mahaifinsu haifaffan garin Kaduna ne a unguwar shanu shida yayarsa Rabi'atu da ake kira Jummai iyayensu sun dad'e da rasuwa a hannun Yayarsa ya taso,domin tunda iyayensu suka rasu sai 'yan uwa duka suka juya musu baya sai wad'anda ba'a rasaba,haka suka taso rayuwarsu,Anty Jummai tayi sana'a iri da iri domin temakawa rayuwar k'aninta ita tasashi mkrnt amma ita bata zuwa lokacin da takai shekaru 18 Danginsu sukace aure zasu mata suka hadata da wani tshon mutumi ba kauye hk akayi auran bataso aka kaita cen k'auyen me suna Kujama,k'anin babansi yaci gaba da rik'e Musbahu amma sbd rashin abinci ya fille ba'a sake ganinsa ba yayi Kano acenne Allah ya had'ashi da wani ubangida ya mayar dashi mkrnt snn ya rik'esa tamkar d'ansa har ya kammala karatunsa kuma yasa shi a harkar kasuwancin sa,Alhj Hafizu mutum ne me kyirki da tausayin talakawa yana da arziki sosai ganin irin rik'on amanar da Musbahu yake dashi yasa ya aura masa 'yarsa wacce ita kad'ai ya mallaka wato Hajara,
Hajara yarinya ce ta gari tamkar mahaifinta saidai miskila ce mgn bata dameta ba,batason hayaniya amma tana da kyirki sosai ga hankali da natsuwa sunyi zaman so da kauna da Musbahu,
Wanda shima daga baya Allah ya azurtashi sosai yayi kud'i na kece raini,a yanxu hk har yafi uban gidan nasa kuma surikinsa arziki,
Shekarunsu tara da aure snn suka sami haihuwa,sosai sukayi farin ciki da samun yaransu 'yan biyu kyautar Allah,inda Hassan yaci sunan Surinkasa ubangidansa mahaifin matarsa wato HAFEEZ shi kuma Hussaini yaci sunan mahaifinsa wato YUSUF kuma ko wanne ba'a 6oye masa sunansaba........
Muje zuwa
Plsss Share
Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
IZGILI
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
*DEDICATED TO MY FANS*
*SPECIAL GIFT TO* .
*ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS*
*SPECIAL THANKS TO*
*NURADDEN SHU'AB LIight*
*HUSSAIN ABU SAMEER*
*NAZHIFI YAREEMAH*
*YUSUF NUHU*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Bismillahir rahmanir rahim
🅿️9️⃣-1️⃣0️⃣
Duka yaran sun taso cikin so da kyaunar iyayensu saidai abu guda tun suna yara sam basa ji tuwa,Hafeez zcy garesa abu kad'an zai rufe Yusuf da bugu wataran kuma su bigi juna,snn Tunda iyayen suka gane hk sai basa musu mgn a ganinsu ai yara ne nan gaba idan suka girma zasu bari,sun mance icce tun yana d'anye ake tankwarasa idan ya bushe kuwa saidai ya karye,
Haka suka taso wasu irin yara wanda a tarihi ba'a ta6a twins kalarsu ba,gashi dai sunyi kama komai nasu iri daya saidai rashin ji tuwarsu,Tun suna yara Umma ta nuna tafi son Babanta wato Hafeez wnn kuma babban kuskure da iyaye ke nunawa ko kafison wani kamata yayi kabarsa a ckn zcyrka amma k'arara Umma ta nuna tafi kaunar Hafeez akan Yusuf ganin hkn shima Abba ya nuna yafi kaunar Yusuf akan Hafeez tunda kowa ubansa ya dauka,hhhhhh kunji wani rikicin ckn gida sai kace wasu yara k'anana kuma har yaran suka girma akan hakan suke,
Sam Alhj Musbahu bai waiwayi gida ba kamar yadda itama Hjy Hajara wato Umma bata ta6a damuwa da sanin halin da dangin mijinta sukeba kuma bata ta6a tambayarsa suba,wata irin rayuwa kawai suke wanda basu damu da damuwar wani ba kansu kawai suka sani sai yaransu,tunda ga kansu kuma basu sake haihuwa ba har zuwa lokacin da suka sami INTEESAR,
Ita Anty Jummai ta bazama neman d'an uwanta tunda ta dawo gida sakamakon sakinta da mijinta yayi,wulak'anci dai iri iri tana shansa a gurin danginsu,har zuwa lokacin da wani attajiri ya sake auranta anan Kaduna babban malami ne,daman bata haihuba a cen kauyen,saida takusan shekaru sha biyar da aure snn ta haifi Saima saida kuma Saima ta shekara bakwai snn ta haifi Maryam,hk rayuwa taci gaba har xuwa lokacin da taga Alhj Musbahu a tv ana hira dashi tana ganinsa ta ganesa nan tayi ta kuka har saida Malam mijinta ya kaida garin Kano taga d'an uwanta sunyi murna sosai da zuwanta hk suka dunga zuminci har zuwa lokacin da Malam ya rasu ta dawo gidan sam Alhj Musbahu baiji mutuwarba kasancewar sun dad'e basu had'uba shi kuma sbd tafiye tafiyensa k'asashen k'etare wnn kenan,
Anty Jummai ce ke cika da batsewa cikin parlour kallon Alhj Musbahu tayi tace"wai hk rayuwa take yanxu don Allah Musbahu hk zaka zuba idanuwa kana kallon yara sun isa aure ka zuba musu ido to wllh bazai yuwuba idan da aure sukayi yanxu ya isa suna da yara biyu ko uku,
Umma shuru tayi ta kasa mgn sbd ita mgn ba damunta tayi ba sam batason fitina a rayuwarta yaranta kuma bazata musu dole ba lokacin da suka shirya aure sai suyi,
Abba yace"Anty dukansu ba wanda yace yanason aure su ai ba yara bane idan sunason aure ai zasuyi mgn,rik'e baki tayi kafin ta tafa hannu tana salati tace"yo tunda ka zuba musu ido taya zasuce sunason aure wad'an nan zaratan maza a gida,Mgnrta ta fara isar Hafeez yace"wai Anty Jummai ina ruwanki da rayuwarmu ne ko kuwa sa'ido,tace"Musbahu kanajin abinda Hafeezu ke cemin ko?yanxu sbd tsabar rashin kunya ya kalli idanuwa na yacemin hk,to wllh ko suyi aure ko kuma ni na za6a musu mata da kaina,
Kan ubancen Hafeez ya fad'a a zcyrsa aransa yace kamarmu za'ace za'a za6awa mata,Yusuf kuwa murmushi yayi sarkin barkwanci yace"haba dai Anty Jummai sha kuriminki ki ba mu shekaru a qalla biyar zamu kawo miki mata ko da yake bro na yana da wacce yakeso ni kuwa tawa bata isa aure ba,harara Hafeez ya zuba masa da yatuno Yusuf yasan budurwarsa domin tun suna skul suke tare da BAHEERAH yarinyar da yakeso tamkar ransa suna zuba soyayya sosai duk da wani lokacin ita ke haukanta duk tare suka kammala karatu domin shi mutum ne meson mace me ilmi wacce tayi zurfi a karatu kuma me shekaru kusan nasa don beson yarinta Baheerah a qalla shekarunta 29 domin shakara uku rak ya bata a duniya tana matuqar son suyi aure amma shine keja mata aji har yanxu,
Anty Jummai tace"da kyau akan yayi daidai kai Hafeez ka shirya sanar da budurwarka za'a turo kai kuma Yusuf kashirya da SAIMA za'ayi,ai gaba d'ayansu suka kalli juna,
INTEESAR taji wani irin yarrr gabanta ya buga da qarfi zuciyarta ta mata zafi ta rasa dalili,Yusuf kuwa cewa yayi "haba Anty Jummai kikasan ko da wanda takeso,Saima kuwa wani dadi taji aranta domin burinta daman cikinsu ta auri daya tunda duk kamarsu guda ce wllh tanason YUSUF musammanma shi da yayi k'irki,tace"haba Yaya Yusuf ai kai d'an uwa nane taya zan k'ika,gaba daya akasaka dry idan ka cire mutum biyu Yusuf da Inteesar sai kuwa Hafeez dukda shima ya d'an murmusa don arayuwarsa yanason mace wayayyiya shi kuwa Yusuf a gurinsa ai Saima rashin kunya tayi,Inteesar kuwa k'asa tai dakai hawaye na jirara batasan dalili ba,
Abba yace"gsky naji dadi da abin yazo ckn sauqi haka Allah ya qara zuminci,Umma tace"nima abin ya mini dadi na kusan zama suruka,sukasaka dry,Anty Jummai tace"da baku kun zuba musu ido ba ku son 'ya'ya,
Inteesar a hnkl ta tashi ta nufi bedroom d'inta wanda yanxu ita da Maryam suke kwana,kan bed ta fad'a tana kuka qasa-qasa,Yusuf yana ganin ta tashi ya mik'e zaibi bynta Anty Jummai tace"sai ina?ko don kaga 'yar gwaltaka ta tashi zaka bita?ransa a jagule yace"ina zuwa,
Bedroom d'in yashiga ganin yadda take shashsheqar kuka ya qarasa da sauri tare da d'agota,tana ganin shine ta rungumeshi tare da sakin kuka murya ckn sanyi yace"Inteesar me yasaki kuka?,rasa me zata ce masa tayi tace"uhmm uhmm uhmm nima ban saniba hk kawai naji ina kuka,yace"dole da dalili me yasaku kuka Inteenah?a hankali ta d'ago kai daga qirjinsa karaf suka hada ido ckn raunin murya tace"............
Muze zuwa
Plsss Share
Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
IZGILI
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
Dedicated to
_Hussain Atk_
Special gift to
_Anty Hauwa Maman Uswan_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Bismillahir rahmanir rahim
🅿️1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣
Tace"Yaya Yusuf haka nan naji banji dadi ba da akace an baka auran Anty Saima don Allah Yayanah kada ka aureta,
Zaiyi mgn saijin tafin hannun Anty Jummai sukayi tana tafa hannu tare da sallallami tana zuwa ta shaqo wuyan Inteesar ta matse qara tasaki tare da rik'e hannun Anty Jummai dake wuyanta tana kuka,
Yusuf yace"Anty Jummai meye hk kasheta zakiyi ko me?tace"ai gara na kasheta ko arage mugun iri wllh wnn yrnyr fitinace yarinya qarama sai shegen iyayi da feleqe iye kada ya amince da auran Saima to sannu Hajara da kika kawo Yusuf duniya,
Yusuf yace"plss Anty ki sakar mata wuya,da qar ta saketa tana bambamin masifa,jikin Yusuf ta fada tana kuka sosai tana murza wuyanta hura mata wuyan yake yana cewa kiyi hkr INTEESAR,tace"nidai don Allah karka aureta bakaji yadda zcyta kemin ba Yaya Yusuf kai wani jigone na cikin rayuwata inajin hakan a tattare da mu,share mata hawaye ya fara shikansa ji yake kamar ya sakar mata kukan yace"ki dena kuka Inteesar pls ki share hawayenki,tace"to zaka fasa,gyada mata kai kawai yayi alamar eh domin ya kasa mgn tunani ne fal ransa da tambayoyi saidai baida amsoshin,shin itama Inteesar tanajinsa kamar yadda yake jinta kenan?gashi har batason yayi aure?amma kuma taya zai gasgata mgnr nan tabbas qila itama tana qaunarsa kamar yadda yake qaunarta idan kuwa haka ne da yafi kowa sa'a a duniya,
Lumshe ido yayi kad'an kana ya bud'e yace"kina sona Inteesar?kallonsa tayi da sauri shi d'inma da sauri ya gara kalamansa domin baiyi zaton a waje yayi mgnr ba,
Yace"don Allah ki cire komai aranki banaso nayi jayayya da Anty Jummai sarai kema dai kinsan halinta kuma sai abinda tace"Abba yakeyi,kwantar da kanta tayi bisa kafad'arsa tace"wllh Anty Saima bata da kyirki ne kuma....rufe mata baki yayi yace"karki ce komi nidai nasan ba abinda ta isa tamin,
Sosai a zcyrta taji haushin Yaya Yusuf aranta tace"kodai shima yana sonta ne?to amma fa ko mgn taga basu cikayi ba,tashi yayi ya fita zcyrsa cike da rud'u shidai bason Saima yake ba kuma bayajin zaiwa iyayensa gaddama snn ko ba komai ai shima yana buqatar auran snn yasan Inteesar bata isa aure ba ko yace yana sonta yanxu ba aura masa ita za'ayi ba hkn yasa zaibar komai aransa har zuwa lokacin da zata isa auran snn ya sanar da ita yana sonta (uhmmm Yusuf a bari ya huce dai akace shi ke kawo rabon wani),
.............................................
An aika gidansu Baheerah an nemi auranta kuma sun basu sosai masoyan ke cikin farin ciki,yauma har office d'insa dake ckn universityn ta je kasancewarsa na babban malami,daman kuwa mafi akasari ita ke zuwa gurinsa zance kafin yaje gidansu sau daya tazo gurinsa fiye da goma,kamar ko da yaushe 'yan mata ne ke ta shawagi ta wajen wundow dinsa domin ko zai taya hk mata ke mugun sonsa dason kawo masa hari saidai ba fuska domin akwai riqe gida gashi ba fara'a ga kuma shegen kwarjinin da yasa 'yan mata ke shakkarsa,
K'wankwasawa tayi yace"yes,cikin takunta na kasaita ta shugo,sai yanxu na k'are mata kallo eh baza' kirata mummuna ba amma ba wata kyakkyawa cen bace zamu iya kiranta da hasken fatarta ne ya temaketa domin da baka ce za'aga muni,siririya ce sosai bata da kiba kuma babu wani diri ajikinta hk take sungul kamar kyendir hhhhhh sanye take ckn wani material da yasha wulaqantaccen dinki doguwar rigace amma ta kamata sosai ita kuma babu wani abun nunawa a jikinta domin ko k'irjinta babu wasu manyan nonowa qananu ne ko mayafi bata saba