Author : Ummu Affan Category : African Stories & Novels
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
IZGILI
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
Marubuciyar
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
NIDA YAYA LAMEER
KAINE SANADI
NAYI GUDUN GARA...
And now
IZGILI
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani ikon sake dawo muku da wani littafin nawa me taken IZGILI yadda na farasa lafiya Allah kabani ikon kammalawa lafiya.
Wannan littafin banyisa don wani ko wata ba k'irk'irarran lbr ne duk wanda yaji yazo daidai da rayuwarsa arashi ne,Wnn lbr mallakata ne banyarda a juyaminshi ta ko wacce sigaba ba tare da sanina ba,
Bazan ta6a mancewa da masoyana ba domin domin ku nake komai da fatan zaku biyoni cikin wannan sabon book nawa kuma ku kar6esa fiye da na baya.
Ina roko da addu'ar Allah ka yaye mana wnn cuta ta Corona virus a Nigeria gaba d'aya da duniya baki daya amin,
Kuna raina 'yan uwana abokan aiki na Arewa Writers gaisuwa da jinjina gareku ta ban girma,
Gaisuwa ta musamman ga Antynmu Anty Hauwa Maman Uswan k'aunarki a gareni ta dabance💖.
My qawassss Ummu Inteesar kema jinjina agareki💓
My qanwassss Autar arewa Doctor Maryamah Ibraheem jinjina kema agareki💘
Anty Laurat kema jinjina,Anty Zainab na miko gaisuwa,masu sunan 'yan gayu inji wata😜
Hafscal da Sa'amlad kums jinjina Zee 'yar Antynta ai yar mama kema jinjina,my bros Aliyu da Muhammad da wani Aliyu kuma ina d'aga muku hannu,
Wanda baiji sunansa ba amin afuwa❤️Allah ya qara had'a kanmu arewa writers🤝💘
Bismillahir rahmanir rahim
🅿️1️⃣-2️⃣
Haka kawai yau na tashi jikina banajin dadinsa,da k'yar natashi daga kwanciyar da nake,na juro dogayen k'afafuwana a k'asa na tallabe kumatuna wato nayi tagumi,duniyar tunani na fad'a akan abinda ke tsakanina da Yayah Hafeez,mutumin da duk duniya babu wacce ya tsana sama dani,kamar yadda nima araina kwatakwata bana k'aunarsa,dogon numfashi naja kafin na mik'e na fad'a toilet,
Wanka nayi,nafito na shafa lesion da powder kadan kasancewar ban ciki son inga na cika fuskata da kwalliya ba ko ja gira banayi barni da inshafa mai sai powder da ban le6e,yanxunma hakan nayi kafin na xura doguwar rigata,snn nayi sallah daman na d'aura alwala,
Zaune na iske Ummana tana kallon tashar Arewa24,a hankali na k'araso gurin da take na zauna tare da d'aura kaina bisa cinyarta,muryata cikin sanyi kamar yadda take ako da yaushe nace"Ummana sannu da hutawa,shafa kaina tayi cike da kulawa tace"yauwa kin tashi kenan na lek'a naga kinata barci,
Nace"aikuwa Umma kaina ne kemin ciwo amma nasha Panadol zuwa yanxu ya sauka,cikin alamun tausayawa Umma tace"Ayya Allah ya sawak'a,na amsa da amin,
Mik'ewa nayi na nufi kitchin,dubawa nayi anyi abinci 6ata rai nayi domin a rayuwata na tsani naci abinci,kuma idan banciba nasan Umma mgn xatamin kadan na zuba snn na nufi dinning table,a hankali nake tsakurar abincin kamar mecin magani,Umma wacce rabin hankalinta na kaina naji ta kira sunana"INTEESAR"da sauri na kalleta cike da marairaice murya nace"Am sorry Ummana,nan take saiga hawaye,kallona take takasa magana,daidai shugowar Yayana Yusuf,da sauri ya k'arasa gareni tare da rok'o hannuna yana tambayata lafiya,
Umma na kalla shima ita ya kalla,kamo hannuwa yayi mukazo gurinta muka zauna,yace"wai Umma me yafaru,tace"ka tambayeta mana,kallona yayi kobai fad'aba nasan kallon tambayane,turo baki tayi cike da shagwa6a cikin sanyina nace"Yaya Yusuf wai fa abinci ne...tunda tace haka ya gano inda matsalar take domin sanin kowa ne a gidan babu abinda Inteesar ta tsana sama da abinci,barta dai da kayan zaki danginsu chocolute,minti,sweet,dangin dai irinsu sai kuwa comefulas da su cerelac,to abinda fa takeci kenan a rayuwarta,
Murmushi yayi ya kalli Umma yace"don Allah Umma rabu da ita kinsan dai wnn halin nata kamar halittarta kenan,batace komaiba ta mayar da hankalinta ga kallo domin sam batason abinda zai 6atawa marainiyar Allah amma dole ne ta koya mata cin abinci tun farko Yayun nan nata ne suka 6atata,yanxun ma Yusuf aljihun wandonsa yasa hannu saiga tarin su sweet chocolate,ai nan take Inteesar ta saki fara'a tare da rungume Yayan nata tana masa godiya,
Girgiza kai kawai Umma tayi tana dubansu,daidai shugowar Yaya HAFEEZ,Ai tuni jikin Inteesar yayi sanyi mik'ewa tayi zatabar farlourn ya wani daka mata tsawa,a gigice ta juyo,tare da zubewa tana masa sannu da zuwa domin sam ta mance da gargad'insa akan idan yadawo saita duka har kasa ta masa sannu,
Harara a 6alla mata tare da d'aga mata hannu alamar ya isa,zata mik'e yasakar mata harara da sauri tadawo ta zauna,Tuni Yusuf ya 6ata ransa domin ya tsani abin nan da Yaya Hafeez kewa Inteesar,wnn wanne irin IZGILI ne abin yanaso yayi yawa,ita kanta Umma girgiza kai tayi tare da dubansa,
Tace"Hafeez andawo,"Eh Umma ya amsa mata kansa a k'asa,kowa yayi shuru,domin idan yana guri Inteesar natsuwa take domin sosai takejin tsoransa,Umma ita kuma bame hayaniya bace kusan daman Hafeez duk ita ya biyo,Yayin dashi kuma Yusuf me sanyin hali ne,
Kallon Inteesar Umma tayi tace"ki had'awa Yayanku abinci,da sauri ta mik'e domin daman ta gaji da dukuwar,kitchin ta wuce,shi kuma Hafeez mik'ewa yayi yace"Umma bari nashiga ciki na watsa ruwa,tace"ok ciki zata kawo maka abin cin,ya amsa da "eh yana haurawa sama cike da Izza da kasaita...。
Plss Share
My Fans ku dungamin share fah🙏🥰
Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
IZGILI
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
DEDICATED
HUSSAINI ATK gdyrka agareni me yawa ce saidai ince Allah ya biyaka ya kawo mata ta gari amin
Bismillahir rahmanir rahim
🅿️3️⃣-4️⃣
Yusuf yabisa da kallo,kafin ya kalli Umma yace"Umma wai ina Hafeez ya gado wnn halin nasa,hararar da ta zuba masa yasa shi k'asa da kai,kafin ya tashi jiki a sanyaye ya koma bedroom nasa daman daga Office yake saman bed ya fad'a ya tsunduma duniyar tunani,daga d'an uwansa har mahaifiyarsu yarasa me ya musu suke masa haka,
Mahaifiyarsu k'arara ta nuna tafi k'aunar Hafeez akansa hawaye yaji suna gangaro masa tabbas yana cikin damuwa Inteesar ce kawai ke tausarsa da dad'ad'an kalamanta shiyasa yake k'aunar yarinyar har cikin ransa,
Inteesar kuwa a d'arare ta shiga Parlournsa dinning ta nufa da sauri ta ajiye,zata juyo kenan taji tsawarsa,jiki na rawa ta juyo,harara ya zuba mata"ke wacce irin dak'ik'iyar yarinya 'yar k'auye ce,tuni hawaye suka tsinke mata da sauri ta tsugunna tana basa hkr,dinning ya zauna tare da bud'e abincin,cikin tsananin fusata yace"ubanwa zaici wnn abincin?tasowa yayi sai fau kakeji ya tsinka mata mari,tuni ta gigice tana basa hkr miyar abincin ya d'auko ya watsa mata tuni farar atamfar dake jikinta ta 6aci,runtse idanuwanta tayi k'amm tanajin wani tuk'ik'in bak'in ciki a zcyrta,
Yace''wawiya kawai karki mance a matsayin 'yar aikina kike me yasa kike 6atamin wllh idan kikaci gaba da bani haushi kinsan tsaf na koreki a gidan nan ba wani abu bane,a hnkl ta bud'e idanuwanta dasukayi ja tsabar bak'in ciki,tace"kayi hkr yaya Hafeez bazan sake ba,
Zaunawa yayi yana mayar da numfashi domin bai saba mgn me nisa hk ba sam bayasan surutu amma wnn 'yar k'auyen kullum cikin sashi mgn take,yace "ki kwashe abincinki ki barmin Parlour,da sauri ta mik'e tana tattara kayan ta fice,
Yusuf dake cikin bedroom fitowa yayi ya kalli Hafeez domin duk abinda ya faru yana jinsu kasancewar Parlournsu daya,yace"sam abinda kakewa Inteesar bai dacewa Hafeez me yasa kake mata hakan?yarinyar nan idan bakaji tausayinta ba baka zageta ba,
A fusace Hafeez ya mik'e yace"kaga Yusuf ban kasa da kaiba wai ina ruwanka da rayuwata ne?,Murmushin takaici Yusuf yayi yace"kadai bi duniya a sannu Hafeez ina tausaya maka wataran,
"Yusuf naga take takenka raini keso ya shiga tsakanunmu ko wai bani bane yayanka me yasa ka rainani ne,kallonsa Yusuf yayi na d'an sakonni kafin yace"uhmm sannu Yayana,
Umma ce ta shugo domin jin hayaniyar tasu tayi yawa,fuskarta a murtike ta kallesu tace"wai meke damunku ne?ku kullum kuna cikin rigima tunda nake ban ta6a ganin twins marasu had'in kai irinku ba,Kallon Hafeez tayi tace"Hassan kaine babba amma halinka saikai,kallon Hussain tayi wayo Yusuf tace "kai kuma baka basa girmansa shiyasa kullum kuke cikin rigima,Yusuf yace"Umma na basa girma fa kika ce bayan baifi sakonni ba a tsakaninmu kawai ni abinda ke damuna da Hafeez ji dakai IZGILI da rashin mutunci akanme zai dunga wulakanta Inteesar me tamasa,
Ai tuni Hafeez ya har zuk'a daman gashi da zcy gadan gadan yayo kan Yusuf,Umma ce ta rik'esa tace"Yusuf kashiga taitayinka banason rashin mutumci shin ina ruwanka da abinda yawa Inteesar na zaci shine ya kawota gidan?,Hafeez da Yusuf suka kalli juna donshi Yusuf yasan komai ko lokacin ai ba Hafeez bane ya kawota Yusuf ne amma ita Umma kullum cikin cewa Hafeez take,
Juyawa Hafeez yayi ya koma bedroom ransa a 6Ace,itama Umma kallon Yusuf tayi tace"babu ruwanka da duk abinda Hafeez zaiwa INTEESAR Yusuf ka kiyayeni a cikin gidan nan,bai ce mata komai ba har ta fita zaunawa yayi yayi tagumi lokacin da ya tuna ranar da suka sami INTEESAR Ranar da bazai ta6a mancewa da itaba a rayuwarsa,
Tafiya suke cikin mota su biyu tun lokacin basu jituwa da Hafeez su tagwaye ne amma sam halinsu ya banbanta hakan yasa tun suna yara basa ji tuwa,Yusuf ke jan motar makaranta zasu shi kuwa Hafeez yana zaune kujerar me zaman banza ransa a murtuk'e koda cen bashi da fara'a abinda yafi 6ata masa rai mota guda da suke hawa da Yusuf akan me Abbansu bazai sayawa kowa motarsa ba wai sai mota guda zasu dunga hawa idan zasu skul,
Sauran kad'an su bige wata mata wacce hannunta rik'e da wata kyakkyawar yarinya tazo zata tsallaka,nan fa YUSUF yaja burki ya fita da sauri yana bata hkr dukda itace ta shigar musu hanya,cikin 6acin rai HAFEEZ ya fito yace"kaga malam kabani key na wuce tunda neman suna zaka tsaya,taya mata tazo ta shigar mana hanya snn zaka tsaya kana wani bata hkr,bai kulasa ba yace"baiwar Allah fatan bakiji ciwo ba tace"a'a yaro na gode sosai da kulawa Allah ya maka albarka ya haskaka rayuwarka ya rabaka da sharrin mak'iya,cike da jin dadi ya amsa da amin,
HAFEEZ fitowa yayi yazo gurin ckn masifa yace"bani key na wuce ku.....jin abinda matar kecewa yasashi yin shuru,hannun YUSUF ta kama ta had'a da na yarinyar dake hannunta tace"yaro daga ganinka nasan kafito daga gida na gari ga wnn yarinyar wllh rayuwar na cikin wani k'aton hatsari ka temaka ka tausayawa rayuwarta katemaketa ni kaina aiki akasani akanta ance idan banyi ba za'a kasheni ni kuma wllh bazan iya cutar da INTEESAR ba,
Kallon yarinyar yayi wacce itama shi take kallo,kafin ya kalli HAFEEZ da sauri HAFEEZ yace"ina ruwana amma shawarar da zan baka karka amshi yarinyar nan don banyarda da matar nan ba,
Juyowar da zasuyi tuni suka nemi mata suka rasa,hankalin YUSUF ya tashi ya fara nemanta amma sama ko k'asa babu mata babu me kama da ita,tsaki HAFEEZ yaja ya koma mota yana wani cika da batsewa dole Yusuf ya komo mota,Hafeez yace"wllh karka shugo mana da wnn aljanar yarinyar domin ni bazan shiga mota daya da itaba,tuni Inteesar ta k'amk'ame Yusuf don ba karin tsoro Hafeex ya bata ba,
Gardama suka dungayi HAFEEZ yace wllh bazata shigaba,YUSUF yana da hkr da sanyin hali hakan yasa yabasa key,shi kuma ya hau motar haya zuwa office d'in Abbansu,
Bayan ya gama masa bayani,Abban ya d'aga waya ya kira Hafeez yace yazo yanason ganinsa,bayan yazo Abba tace ya fad'a masa yadda suka sami yarinyar nan,kamar yadda Yusuf ya masa bayani shima haka numfashi yaja yace"tabbas ya zama wajibi mu temakawa yarinyar nan,da sauri Hafeez yace"haba Abba ni wllh ban yarda da matar nan ba,Yace"to idan bamu temaka mata ba ya zamuyi da ita kenan tunda matar ta gudu,Hafeez yace akaita police kawai ayi cigiyarta,Yusuf yace"bazai yuwuba domin matar nan ta sanar mana rayuwar yarinyar nan yake nema don haka ni taba amanarta kuma in Allah yayarda zan rik'e mata amanarta,
Abba yace"nayarda da maganarka Yusuf kuma hakan za'ayi,sosai Hafeez yaji haushi domin daman duk abinda Yusuf yace shi Abban keyi kamar duk abinda Hafeez yace shi Ummansu keyi,
Abba yace"saidai idan munje gida mu sanarwa Ummanku HAFEEZ ne aka bawa amanar yarinyar,daga Hafeez har Yusuf da sauri suka kalli Abba tare da had'a bakinsu wajen tambayar"me yasa Abba?.......
Plsss Share
Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
IZGILI
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
♦️♦️♦️♦️♦️♦️
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
Dedicated to
_Hussain Atk_
Special gift to
_Anty Hauwa mmn Uswan_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Bismillahir rahmanir rahim
🅿️5️⃣-6️⃣
Abba yaja numfashi yace"sbd idan mukace Hafeez ne aka bawa yarinyar zata fi d'aukarta da muhimmanci kuma ta amince ta rik'eta nasan kunsan komai ai,dukansu sukan jugum shi kuwa Hafeez aransa yanajin wani tuk'uk'in bak'in ciki,bayan bayason ya musa mgnr Abbansu da yace'a'a,
Shima Yusuf shuru yayi tabbas mgnr Abban gsky ce shi kuma daman mai sanyin hali ne yace"hakan yayi Abba,Hafeez mik'ewa yayi,"Ina zaka cewar Abba,yace"zan koma mkrnt ne,Abba yace"mu fara zuwa gida tukun,
Abba ya shiga motarsa su kuma suma suka shiga tasu,INTEESAR na jikin Yusuf duk ta kanannad'eshi tunda Hafeez ya mata tsawar nan taji duk duniya bata da abin tsoro kamarsa,bayan sun isa Yusuf bisa kafad'arsa ya d'aura Inteesar yayin da Hafeez yaza wani dogon tsaki yayi gaba,Abba dake bayansa ya girgiza kai tunda yake bai ta6a ganin 'yan biyu marasu had'in kaiba irinsu kuma yasan duk matsalar da gurin Hafeez shine babba amma sam bashi da mutumci sai d'aga kai da IZGILInci yarasa me yasa hakan ke shiga tsakaninsu addu'arsa kullum Allah ya daidaita tsakaninsu amin,
A parlour suka iske Umma kusa da ita Hafeez ya zauna zata masa mgn kenan saiga su Yusuf sun shugo,cike da mamaki ta kallesu bakinta na rawa tace"Yusuf me zan gani haka wnn yarinyar waye?ta fad'a tana nuna Inteesar wacce ta sake k'amk'ame Yusuf,zaiyi mgn Abbansu ya rigashi yace"kwantar da hankalinki yarinya ce Allah ya bamu kyautar Allah,nan ya bata labarin komai,cike da tausayin yarinyar taje ta amsheta tana shafa kanta tace"Allah sarki kyakkyawar yarinya wad'an nan anyi muggan mutane yarinya kisha kuriminki zan rik'eki tamkar mahaifiyarki,Yusuf yaji sanyi aransa,
Haka rayuwar INTEESAR ta fara a gidan cikin so da kauna kai bazaka kalleta kace ba 'yar gidan bace komai takeso ana mata ba kamar Yusuf komai nata shine,saidai wani abu guda tunda aka kawo Inteesar gidan aka bata abinci tak'ici akayi akayi da ita tak'i bata da abinci sai kayan k'wad'ayi kayan zaqi sune abincinta tun Umma na matsawa har ta rabu da ita ganin yadda yayun nata suka d'aure mata gindin saya mata musamman ma Yusuf wani lokacin kuma Hafeez idan 'yan mutuncin nakai har takai ta kawo kwalayen su sweet minti choculate haka Yusuf ke saya mata,
Haka rayuwarta taci gaba a gidan har zuwa lokacin da akasata mkrnt kammala karatun su Yusuf da fara aikinsu,Hafeez Lecturers ne dake koyarwa a jami'ar jahar Kaduna wato Kaduna State University,shi kuma Yusuf Injiniya ne yana aiki a companyn Abbansu sosai suke samun ci gaba,
Hafeez da Yusuf kamanninsu guda ne domin wani lokacinma idan ba farin sani kamusu ba bazaka ganesu ba,kyawawan samari masu jini ajika matasan samari yanxu suna da shekaru 32 a duniya,dogaye nesu fatarsu wankan tarwad'a ce su ba farare bane snn baza'a kirasu bak'ak'e ba duk inda kyau yake sun kai,ta inda zaka ganesu shine shi Hafeez sam bashi da fara'a ko kad'an snn fuskarsa ko da yaushe a d'aure take snn yad'anfi Yusuf tsayi kadan,shi kuma Yusuf mutum ne mai sakin fuska da fara'a kowa nasa ne