Author : Binta Umar Abbale Category : African Stories & Novels
ne??? Muryarsa ta dawo da ita "Nasan zaku zauna lafiya da juna kan inje in auro muku wacce baku sani ba.""
Bakinta na rawa tace"Wace Azima wai."!? a sanyaye yace."Azima dai taki." Kirjinta ta nuna da hannunta sai wasu lafiyayyun hawaye suka shiga zubo mata. "Abunda zakayi min kenan.!!! Abunda zaka saka min dashi kenan.!! me nayi maka zakaci amanata."!! Sai ta dukufar da kai 'kasa tana wani irin kuka na tsantsar bakin ciki da nadamar wannan rayuwa data ke cikinta.
Shiru yayi yana kallonta shima a wannan ga'bar kuma jikinsa yayi sanyi yana ganin kamar be kyauta mata ba, wani gefan na zuciyarsa na fada masa "Ai ba harumun bane don ka auri kawarta kawai ka lallabata ka rareasheta komai zai zo da sauki
Rungumo ta yayi jikinsa saboda rashin kwarin jiki da fargaba yasa tayi likif a jikinsa ashe duk wannan abun da takeyi ba komai bane tashin hankali na gaba....Innalillihi wa'ina ilahi raji'un! Omar zai auri Azima amiyarta shin wannan wane irin cin amana ne me tayiwa omar zaiyi mata wannan yankan kaunar meyasa zata amincewa Azima ta haince ta ashe mijinta take so shiyasa mana sai yanzu ta soma gane irin alamomin da take nuna masa wanda da bata ganewa Azima taci amanarta Kuma har idan ya kafe sai ya auri Azima to kam sai dai ta hakura da zama dashi domin ba zata iya bude ido taga Azima a matsayin matar mijinta ba....Hawaye masu d'umi suka shiga zubo mata a kuncinta Azima!! Omar!! Azima!! Omar!!! ita kam sunyi mata abunda baxata ta'ba iya mantawa dashi ba har ta mutu...Wani mugun zazza'bi ne ya rufeta a take jikinta ya soma kyarma sosai jikinta yayi zafi...Duk sai ya rikice ya dinga lallabata " Idan bakya so na hakura aysha ni farin cikin ki kawai nake so da kwanciyar hankali ki fahimce ni matata ba don naci amanar ki ba yasa zan auri kawarki akwai dalilai masu karfi amma na hakura kawai saboda farin ciki ayshata."
Aysha sama-sama take jinsa saboda yanda kanta ke wani irin juyawa ta mike a guje ta nufi toilet ta dinga kwara amai Omar ya rikice! sosai ya talfeta a jikinta ta dinga kakari tana hawaye haka duk jikinsu ya baci ya hada ruwa mai zafi yayi mata wanka kallonsa kawai take tana kallon maciyin amana sam ta rasa karsashi da jarumar da zata hanashi ganin abun take kamar almara wai Mijinta da take bala'in so ta bashi duka yardar ta da amanarta shine zai tona mata asiri zai auri kawarta da wannan rayuwa gwara ta mutu ta huta.
Nad'ota yayi towel ya kwantar jikinsa sai kyarma yake yaje yayo nasa wanka ya fito gajeran wando kawai yasa yazo ya rungumeta a jikinsa sai kalamai yake mata na yaudara ta'ki tace masa komai sai faman lumshe ido take tana adduar Allah ya dauki ranta ta huta da ganin wannan bakin ciki.
[6/1, 9:13 AM] Bintu Novel: 68
Haka suka kwana cikin mawuyacin hali mussaman Aysha da zazzabi ya kusa kaita barzahu Omar duk ya firgice ya shafa mata ruwa cikin daran ya kai sau uku babu sauki gashi yayi yayi da ita tasha magani ta'ki kuka kawai takeyi.
Yana idar da sallah asubahi ya shigo gidan dakin nata dai ya koma tananan inda take a kudubdune tana makyarkyata ya zauna kusa da ita.
Rarrashinta ya cigaba dayi kan ta tashi suje gurin Dr Rakiya tana jinsa tayi masa shiru ya gaji da magana ya mike ya fita palo ya jima a tsaye a palon yana tunanin mafita ya ciro wayarsa ya nemi numbar Dr Rakiya suka gaisa nan ya fada mata halin da ake ciki lokacin tana kan aiki ne tace idan babu damuwa ya kawo ayshan asibiti haka ya sake komawa dakin lokacin ta daddafa ta shiga toilet yana jin motsin ruwa yasan wanka take sai ya fita a gurguje ya shiga dakin safa suka gaisa yace."Maza ta shirya zasuje asibiti aysha babu lafiya.
Dakinsa ya shiga yayi wanka ya kimtsa jikinsa ya fito da key a hannunsa ya koma dakin aysha sai ya tarar da ita zaune kan dadduma ta idar sallah hannu a sama tana kuka da rokon Allah ya dauki ranta ta huta da wannan bakin ciki."
Ta matukar bashi tausayi ya karasa inda take zaune ganinsa bai sa ta daina adduar ba "Ya Allah ka dauki raina na huta Allah ka saka min idan an cuceni! Allah nayi nadamar wannan rayuwar da nake cikinta na amince musu sun cuceni Allah ka saka min abunda sukayi min."!!! Omar ya durkusa gabanta tare da yin kasa da hannunta yana kallonta idanunsa jawur yace." Aysha har ta kai ki daga hannu sama ki roki Allah ya kasheki idan kika mutu ni da Abdul fa! me yayi zafi wai ? nace dake na fasa auran azimi a zauna lafiya ni zan cigaba da zama dake da halayen ki aysha ki tashi muje asibiti a dubaki."
Ba tare da ta kalleshi ba ta mike daga gurin hijab din jikinta ta cire ta haye bed tana makyarkyata sanyi takeji sosai....Zuciyarsa sam babu dadi ya fita daga dakin duk ya rasa yanda zaiyi baya so ya fadawa nanne halin da ake ciki yasan zatayi mata fada a halin yanzu kuma baya bukatar abunda zai daga mata hankali saboda halin damuwar da take ciki ga cikinsa a jikinta.
Ya zauna a palo yana tunani Safarau ta fito a kimtse Yanda ta ganshi yayi zukud'um! sai ya bata tausayi tace"Yayana na shirya." Yace."Safa aysha bata da lafiya amma taki aminta da muje a dubata ya zanyi ne."!?
Tace."Allah sarki aunt gimbiya bari na shiga dubata." Sai ta nufi dakin ya bita da kallo duk ya wani burkice.
Koda Aysha taga safarau bata damuba safa ta zauna gefan ta A hankali tace"Aunt gimbiya ina kwana ashe bakiji dadi ba to Allah ya sawake."
murya na rawa tace"Lafiya Safarau Eh wallahi zazzabi ke damuna ameen nagode."
Tunda suke Aysha bata ta'ba yiwa safarau kyakykyawar magana irin ta yau ba.
Tace."Aunt ki daur ki tashi muje asibiti kinji Yayana ya shiga cikin damuwa da yawa gashi can a zaune palo."
Tace."Ba zan iya zuwa bane Safa kawai kice masa ya samo min magani." Safarau ta mike tana fad'in "Bari na sanar masa.'"
Yana zaune inda yake ta fito daga d'akin ta shaida masa abunda Ayshan tace'' Dole haka ya fita zuwa asibitin Dr Rakiyan domin ya kar'bo mata magani.
Safarau ta koma d'akin tace"Aunty bari in shirya miki break kafin ya kawo miki maganin Allah ya sawa'ke.
Aysha tace''Kar ki damu ikilima zata zo yanzu ki huta kawai." Safarau ta girgixa kanta "A'a aunty nice xanyi miki."
A sanyaye tace"Nagode." Safarau ta fita daga dakin Aysha ta shiga tunani ashe dama haka yarinyar take da mutunci a da ta tsaneta! to wai ma me tayi mata ta tsaneta wata zuciyar tace ta aurar miki mijinki ajiyar zuciya ta sauke tace idan hakane kuwa safarau ba ta cancanci in dora mata karan tsana ba in da akwai irin su Azima a gurin ma'kiya maciya amana sune ya kamata mutum ya gujesu hawaye ya fara kwaryanya a fuska.....Wai saboda shi din mugun mayaudari ne fad'i yake ta kwantar da hankalinta in dai aure ne ya fasa yi domin ta samu nutsuwa idan duk jikinta kunne ne baza ta ta'ba yarda da wannan maganar tasa ba tuntuni ta dawo daga rakiyarsa Auran Azima ba zata hanashi ba sai dai ita ta bar auransa har abadah tunda shi d'in butulu ne wanda ya fiye son kansa.
Wayar ta dauka zuciyarta na turiri ta nemi numbar Azima bugu guda tayi aka dauka.
Hasina ce ta dauki wayar Aysha tace"Ina Azima ne."!? Hasina tace"Wai wacece ke ne kina wa mutane magana cikin isa da gadara ki fad'i ko menene domin dani da me wayar duk d'aya ne."
Cikin sanyin murya tace"Aysha ce baki da hurumi cikin maganar da zamuyi da ita don haka idan ta fito ki fada mata na kira." Sai ta kashe wayar tana jan tsaki.
Azima na fitowa daga toilet Hasina ta fad'a mata sai taja tsaki ta zauna kan stool tace"Kyale banza Aysha ce fa kawar nan tawa da nake baki labari ko uwarta zanyi mata oho ta kirani waya da sassafe.".
Hasina tace."No wander mana naji tana wata magana cikin isa! yo wa zatayi wa isa da gadara wai ita 'yar masu mulki mtsssw!
Azima tayi murmushi na takaici tace"Ki rabu da shegiya idan na shiga gidan duk wannan girman kan nata sai na sauke mata shi wallahi, da dai ina tausaya mata amma tun daga ranar da Omar ya fada min cewar ba zai taba daina sonta ba nake jin wani irin kishinta da tsanarta cikin raina shiyasa ai nake so tayi ta haihuwa duk ta tsufa komai abunsa ai dole yaga muninta." Sai suka fashe da dariya har da tafawa....Hasina tace"Ki kirata a waya kiji me zata ce miki." tace "Wallahi bazan kira ta in ta matsu ta sake kirana."
Aysha tayi ta tsammanin kiran Azima taji shiru jikinta yayi bala'in sanyi ashe al'amarin nan da gaske ne!? ashe Azima munafuka ce zata iya cin amanarta ashe dama da gaske ne wannan al'amari!!! innalili wa'ina ilahi raji'un! ta jima tana nanata wannan kalmar kafin Allah ya bata damar yunkurawa da kyar! ta dauki hijab dinta dake gefe ta zura ta mike a daddafe ta kama hanyar futa.
Suka ci karo da Ikilima ta shigo sama-sama ta amsa mata gaisuwarta tace"Muje sashen Nanne Ikilima ta bata hanya suka fara tafiya ganin tana tafiya tana jiri ne yasa ta roko hannun Ikilima suka fita daga sasheshn.
Nanne ita da jakadiya suna zaune suna hira Aysha ta shigo ganin yanayi da ta shigo a jigaje ya tashi hankalin Nanne take jikinta yayi sanyi ta mike tsaye aysha ta karasa da gudu ta rungumeta ta wani irin kuka na fitar hankali "Nanne gwara kawai na mutu na huta na gaji da wannan rayuwa da nakeyi babu dad'i Nanne wai me nayiwa mutane ne a wannan duniyar wayyo!! Allah na shiga ukuna na lalace."! Cikin gunjin kuka take wannan sambatun.
Nanne jikinta ya soma rawa ta kamata ta rike a jikinta suka nufi dakinta.
zaunar da ita tayi kan bed ta zauna kusa da ita tana rarrashinta itama tuni hawaye ya cika kwarmin idonta hakika yau 'yar tata ta bata tausayi matuka tace" Kiyi shiru ki nutsu ki fad'a min abunda ke faruwa shin Kulu ce tayi miki wani abu ko kuma waye wannan kukan da kikeyi yana d'aga min hankali."
"Nanne shine Shine!! wallahi ya cuceni na daina auransa har abadah na tsaneshi yaci amanata."!!! Nanne tace" Shine wa."! kina ta fad'in shine shine ? ki nutsu ki fada min abunda ya had'aku."
Tana fyatar hanci tace"Nanne Omar ya cuceni ya cuci rayuwata wai Aure zaiyi ya kuma rasa wacce zai aura sai aminyata da ta riga ta gama sanin sirrina ni me zanyi da shi Nanne wallahi tallahi sai ya sakeni."
Wannan kalmar ta batawa nanne rai tace"Ke shashasha bana son shirme da shashanci kada na kara jin kin ambaci kalmar saki duk abunda mijinki zaiyi miki."
Aysha ta mike tsaye kamar wata bugaggiya tace"Nanne Azima fa zai aura ki duba lamarin nan fa Nanne kin san yanda nake da Azima kawata ce da na amince mata ta san sirrina daga karshe ace kuma zata zama kishiyata wallahi nanne anci zarafina."
Nanne tayi shiru tana manakin al'amarin yaushe Omar zai kara aure basu da labari? Azima Azima anya kuwa Gaskiya idan hakane to wannan karon Omar yaso kansa da yawa duk matan duniya ya rasa wa zai aura sai Azima bayan yasan ita din kawar matarsa ce, aure babu wanda zai hanashi yayi to amma ai ana barin halas don kunya a wannan ga'bar duk abunda aysha zatayi to zatayi shine kan gaskiyarta don gaskiya ba akyauta mata ba mutukar Omar ya auri Azima baiyi aiki da hankali ba.
Kuka kawai take tana fad'in"Ni dai Nanne kuce masa ya sakeni don Allah ba zan cigaba da zama dashi a haka ba ni na amince yayi aure amma kada ya auri Azima idan yace tilas ita zai aura to ni kuma tilas ya sakeni."!
"Aysha zauna."! Nanne tad'i maganar tana kallonta....Kasan kafet ta zauna ta takur jikinta tana sauke ajiyar zuciya.
"Kwata-kwata bana so naji kina maganar saki aysha wai me yasa baki da hankali da hangen nesa ne? wannan kalmar da kike ta fad'i tana janyo miki fushin ubangiji sannan kuma mala'iku suna tsine miki, Don kyautawa kam ba a kyauta miki ba gaskiyar magana nima naji ciwon wannan abu hakika Omar ya shigo da son zuciya cikin lamarinsa kuma banta'ba tsammanin haka yake ba sai yau, aure bamu hanashi yayi ba amma wacce yake yunkurin auran itace bata dace da rayuwarsa ba, to idan ya kafe kai da fata yace dole sai ya aureta ni ko ke bamu isa mu hanashi ba tunda ba haramun ya aikata ba, ina so ki saurare ni da kyau aysha ki fahimci inda na dosa, Shi aure da mutuwa duk lokaci garesu idan ubamgiji ta kaddara Omar zai auri kawarki Azima to tuntuni dama a rubuce yake wannan kuke-kuken da kikeyi ba zai hanashi auransa ba ina so ki kwantar da hankalinki ki zubawa sarautar Allah ido komai kika ga ya faru to haka Allah yaso, wannan tashin hankalin duk bashi ne mafita ba a gurinki abunda ya kamata dake shine kiyi kokari kiga kin kara kama mijinki a hannunki ta inda ko ya auro ta ba zaki xama koma baya ba, na tabbatar rashin samu nutsuwa dake ne yake sa Omar hange-hangen mata ni shaida ce kan irin son da yake miki aysha da kina kula dashi yanda ya kamata to duk wannan al'amarin ba zai faru ba,Omar na sonki yana kaunarki shawarar da zan baki shine ki kwantar da hankalinki ki cigaba da addua zabin Allah ki daina yunkurin daukar mataki ko kuma ki dinga ambatar kalmar saki yin hakan da kikeyi shine shaid'an yake kara samun gurbin zama a jikinki yana sake dagula miki lamuranki Auran Omar da Azima idan da alkairi to Allah ya tabbatar mana dashi idan kuma babu alkairi Allah ya watsar dashi, wannan itace shawarar da zan baki a matsayina na mahaifiyarki."
Tana kuka tace"Nanne kina nufin yanzu na koma na zauna dashi alhalin yana cin amanata."!?
"Humm! Aysha kenan! nanne ta fada tana murmushin karfin hali tace"Omar Namiji ne wanda yake da iko da komai yana ji da kansa kuma yana kan lokacin sa bazaki hanashi abunda yake so ba kina maganar cin amana aysha ina mazan da suke siyar da kayan d'akin matayen su suje suyi aure wannan ba akanki aka fara ba wai mijinki yaga kawarki ya aura ba'a fara kanki ba kuma baxa a kare kanki ba, ni dai ina kara tunasar dake cewa kuskuren duk daga gurinki ne a yanzu ma kina da damar da zaki gyara kuskuranki tunda kina da sauran lokaci ki kame mijinki ki zauna dashi lafiya rashin kunya da rashin kirki duk babu inda zasu kaiki Kuma wallahi tallahi duk sanda na sake jin kin sake furta kalmar saki a bakinki sai ranki ya 'baci ki kiyaye kije kiyi aiki da shawarar dana baki."
Aysha ta dinga wani irin kuka wai shin yaya zatayi ne? rana zafi inuwa 'kuna!!! Nanne kam duk da tana tausaya mata hakan bai hanata yi mata fad'a da tayi maza ta gyara kuskuranta tun kafin lokaci ya kure mata.
Jakadiya ce ta le'ko ta sanar musu da zuwan Omar d'in.
Nanne tace"Jakadiya tace ya shigo kawai...Jikinsa duk babu kwari ya shiga sai yaji yana jin kunyar hada ido da Nanne ita kuma dake macace mai saukin kai sam bata nuna masa komai ba suka gaisa a mutumce,
Yace."Ashe nan tazo batajin dadi ne naje kar'bo mata magani sai na duba naga bata sashen.
Nanne tace"Aifa ga alama nan na gani nan ta shigo tana kuka kana tana sanar min da abunda yake da akwai."
Sai ya sunkuyar da kansa cikin jin kunya da nauyi yace."Nanne magana ta kare insha Allahu na fasa auran ni dai kawai bukatata ta kwantar da hankalinta."
Nanne tace"Haba waye ya isa ya hana abunda Allah ya halasta Omar kaje kayi auranka munayi maka fatan alkairi da samun zuria me albarka."
"Wallahi Nanne na hakura da auran nan Mutukar aysha zata samu nutsuwar da nake bukata to zan iya hakura da komai."
Nanne tayi murmushi kana tace"Omar kenan to mu dai ba za mu daina yi muku addua ba kuma shi aure zuwa yake ko kana so ka baka so idan Allah ya nufa to sai anyi kai dai kawai ka kyautata adalci."
tana gama maganarta ta mike ta futa daga d'akin.
Ya kalli gefan da take zaune tana kukan bakin ciki.
Cikin tattausan harshe yace."Yanzu Aysha meye amfanin zuwanki sashen nan cikin wannan hali me yasa bakya boye sirrinki tun a can fa nace miki na janye maganar aure me yasa zaki zo ki fadawa Nanne abunda ke faruwa kina so ki sanya ta dinga ganin 'bakina ko? na zauna nayi nazari da tunani nagane cewar yin hakan ba adalci bane duk da ba haramun na aikata ba amma saboda farin cikin ki na janye maganar auren ina so ki samu nutsuwa ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya."
Ko kallonsa batayi ba yace."Kiyi hakuri ki tashi muje kina sha maganinki. komai ya wuce insha Allah."
Wani kallo ta watsa masa tace"Kamar yanda Nanne ta fada maka cewa mu bamu isa mu hanaka kayi auranka ba don bamu san abunda Allah ya lullu'be ba saboda haka kaje ka auri Azima amma ka sani daga ranar da aka daura maka aure da ita to ni kuma zaka bani takardata don Wallahi ba zan zauna da kai ba."
Yace."Wato baki yarda da maganar dana fada miki ba ko aysha."!?
Tsaki taja ta dauke kanta sai ya ciro wayarshi ya fara laluban numbar Azima bugu daya tayi ta dauka sai ya bude hands free cikin wata kwarkwasa take masa magana yace."Ina lafiya ya mutan gida.'' ta sake makale murya da fad'in"Duk sunanan lafiya suna jiran ranar zuwanka. Yace."Azima wannan alakar dake tsakanina dake ina tunanin daga yau ta warware kiyi hakuri kawai." sai ta fashe da kuka tana fadin"Shikken mutuwa zanyi dama d'azu haka na yini da zazzabi kuma nasan ciwon sonka ne don girman Allah kar kayi min haka." Kashe wayar yayi ya aje sai ta sake kira Aysha ta d'auka "Wallahi ina sonka zan